HAUSA NOVELWANI LABARI

WANI LABARI

 

=> 6
Haka na kwana cikin rudani hade da
matsanancin tunani washe gari da sassafe
saiga ummey ta shigo kamar yadda ta saba
kanta tsaye ta shigo dakina a kwance nake
amma idona biyu duk da cewar babu wani
annuri a tattare dani haka na dan saki fuskata
cikin yanayin sakin fuska nace “ummey kardai
kice kinzo tashina baccine? Murmushi naga
tayi sannan tace “amma ya ai kasan abun
daya kawoni? Budar bakina sai nace ” ai
saboda zukatanmu sun riga da sun zama
dayane shine dalilin da yasa na fahimci haka.
Sai tace “kaga malan tashi kazo muje kayi
breakfast domin akwai inda nakeson ka
rakani. Bayadda na iya haka na fita ba’a son
rainaba domin ko kadan banason na batawa
mahaifiyata ranta gudun kar ummey ta fahimci
na fara ja da baya da itane yasa na fito.
Bayan nayi brush haka na zauna a falo ina cin
abinci ga kuma ummey ta zauna kusa dani
tanamin irin kallon da masoya sukewa junansu
mai kawar da kunci da bacin rai bayan na
kammala saina fita tare da ita domin rakata
inda take son zuwa bayan na dawo gida sai
na fahimci ran mahaifiyata yayi matukar baci
gaba daya saina rasa hanyar da zanbi
danganin na ciwa mahaifiyata burinta ba
tareda ummey ta fahimci komai ba duk da
cewar nasan hakan ba abune mai yuwuwaba
amma ko kadan zuciyata bata daina nazarin
neman mafita ba. rana daya nayi duk wani
shirina na tafiya garin jigawa amma sai dai
kuma ina duba yiwuwar tafiyar da zanyi zata
dauki dogon lokaci domin bana tunanin cewar
zan dawo har sai lokacin da ummey tayi aure.
Koda na sanar da iyayena batun tafiyata da
kudurin bazan wuce sati daya ba. Sai suyimin
fatan alkairi hade da sa albarka a gareni.
Ummey har zubar da hawaye tayi a dalilin
wannan tafiyar tawa inaji ina gani haka nayi
bankwana da abar kaunata wadda ko tuntube
batason taga nayi a yayin da muke tafiya tare
da juna. Tafiya nake amma ina tunanin irin
soyayyar da mukewa junanmu hade da
tunanin halin da ummey zata tsunci kanta a
yayin da taji shiru ban dawoba. Duk da irin
wannan tunanin da zuciyata take ciki bai
hanani tafiyaba badan komaiba sai dan
cikawa mahaifiya burinta saboda kokadan
banason mahaifiyata ta shiga damuwa a
dalilina amma sai dai kuma a zuciyata ba
jahar jigawa nake da kudurin zuwaba domin
kuwa jahar kebbi ce a zuciyata. Musalin karfe
1 na dare na sauka a kebbi state. Da saukata
nayi calling din abokina faruq wanda na hadu
dashi a social network wato facebook kenan
cikin kankanin lokaci faruq yazo gareni cikin
girmamawa ya saukeni a gidansu a wannan
ranar ne na sanar da faruq duk abun daya
faru dani hade da makasudin barowata gida.
Daga karshe kuma sai nace “faruq bana
muradin komawa gida har sai lokacin da
ummey tai aure shiru naga yayi na dan wani
lokaci zuwacan ya kalleni cikin tausayawa
yace ” tabbas kayi matukar burgeni tunda har
ka zabi farantawa mahaifiyarka fiye da son
zuciyarka dan haka zakaci gaba da zama dani
har zuwa lokacin da wannan burin naka zai
cika. Duk da cewar na nisanta da ummey
amma hakan baisa mun fasa yin waya da
junaba domin kullunne sai ummey tayi calling
dina hade da aikomin da sakon text message.
Nanfa na rasa hanyar da zanbi dan ganin
hakan ta daina faruwa kwanana biyar da zuwa
kebbi sai wata mota (kano line) tai accident/
hadari a yayin da take gaf da fita daga cikin
garin kebbi zuwa jahar kano abun takaici duk
jama’ar ciki basu rayu ba domin kuwa
konewa tai gaba daya babu wanda zaka iya
shaida fuskarshi. Sai nayi amfani da wannan
damar dan ganin na batar da rayuwata a idon
ummey ta wani bangaran kuma ina tunanin
irin hawayan da iyayena zasu zubar a yayin
da sakon mutuwata ya isa kunnansu amma
naji hausawa suna cewar da ruwan ciki akanja
na rijiya, domin kuwa sai an fuskanci wani
bacin ran sannan ake samun wani farin cikin.
Bayan mun shira komai ni da abokina faruq
saina damka wayata a hannunshi a gaban
idona ya damka wayar a hannun daya daga
cikin jami’an yan sandan dake wannan wajan
hade da cewa “yallabai ina tunanin wannan
wayar daya daga cikin mutanan da wannan
hadarin ya auku dasune. Ta wannan wayarne
sakon barina duniya ya isa kunnuwan iyayena
saboda wannan ita kadaice hanyar da zatasa
ummey ta auri wani ba tare data fahimci
komai ba.
=> 7
Duk da cewar abokina faruq yasan da cewar
ina raye kuma tare muyi wannan shirin. Hakan
bai hanashi zuwa sadakar ukkuna jahar kano
ba. A ranar daya dawo jahar kebbine ya
sanar dani maganar data kidimani. Zama yai a
kusa dani ya kalleni yace “abokina abunda
mu aikata sam bai dace ba domin saura kiris
na bayyana gaskiyar abun daya faru. Amanar
da take tsakanina da kaice tasa na kasa
aikata hakan bayadda na iya haka na baro
jahar kano hankalina a tashe sakamakon
mawuyacin halin dana tsunci ummey a ciki.
Hawaye nagani a idonshi a yayin daya dago
kanshi ya kalleni. Budar bakinshi sai yace ”
tabbas ummey tana matsanancin sonka
saboda tun daga lokacin da sakon mutuwarka
ya isa kunnanta ta yanke jiki ta fadi sai da ta
dauki dogon lokaci kafin ta farfado daga
dogon suman da tayi kuma ba’anan al’amarin
ya tsaya ba domin har yanzu bata iya furta
kalmar komai haka take zaune ba umm ba a’a
dan haka shawarar da zan baka a matayina
na abokinka itace “kawai ka komaga ummey
domin hakanne zai kawo sassauci ga
rayuwarta. Cikin yanayin damuwa na kalli
faruq nace ” tabbas nasan ko kadan ban
kyautaba amma inason kasan da cewar babu
yadda za’ai naso ganin bacin ran mahaifiyata
kuma a dalilina duk da cewar taki sanar dani
dalilinta na rabani da ummey hakan bazai
taba sawa na kasa cika mata burin taba kuma
inason kasan da cewar duk inda tsanani yake
to ka tabbata sassauci yana nan zuwa dan
haka ummey zata samu sauki domin Allah
maji rokon bayinsane kimanin shekarata daya
da wata takwas a jahar kebbi tare da abokina
faruq ba tare da ahalina sunsan da cewar ina
raye ba amma saidai har kawo wannan
lokacin ummey batayi aure ba domin bata
kula kowa kwatsam wata rana abokina faruq
yazomin da wani sabon labari wanda yai
matukar sani farinciki. A yayin dana sake
turashi jahar kano domin ya jiyomin ko kuma
ince ya ganomin abun da yake faruwa a
tattare da ahalina da kuma abar kaunata wato
ummey sai yazomin da labarin ansama
ummey rana tare da yayata zainab wanda
za’ayi bikin nasu 04/07/2017 tabbas ba kadan
naji dadin wannan albishirin ba. sai dai kuma
na tabbata ummey zatayi auranne ba’a son
ranta ba jahar kebbi sai da ta kasance tamkar
mahaifata domin babu abundana rasa a
tattare da abokina faruq hakane yasa faruq
yai matukar damuwa a yayin da nake shirin
komawa gida sati biyu da bikin anti zainab
hade da ummey na nufi jahar kano saidai
kuma na tabbata saisun shiga rudani a yayin
da suyi ido biyu dani kuma dolene su nemi jin
yadda ai har hakan ta faru dani tun a mota
nake nazarin hanyar da zanbi amma ina gaba
daya sai kaina ya kulle.
=> 8
harna shiga cikin garin kano zuciyata bata
daina sake-saken amsar da zanba iyayena ba
musamman idan su nemi sanin yadda ai haka
ta faru dani tare mu sauka mota da wata
baiwar Allah harna juya zan tafi. Sai naji tace
“dan Allah malan dan tsaya mana. Koda ta
karaso gareni sai tace “dan Allah malan ni
bakuwace a wannan garin kuma gashi dare
yayi shine nakeson ka taimakamin da aron
wayarka domin na kira wadda nazo wajan
nata saboda wayar tawa tun a mota cajinta ya
kare. Cikin yanayin tausayawa na miki mata
wayar. Haka taita trying din numbar amma
bata samu shigaba ganin hakane yasa duk
tabi ta kidime. Wani kallon maraici naga
taimin sannan ta miko min wayar. Cikin
yanayin sakin fuska nace ” hakika na fahimci
damuwar da kike tattare da ita amma idan
bazaki damuba mezai hana na kaiki gidanmu
ki kwana kinga idan gari ya waye saiki kirata.
Cikin sanyin murya tace “to shikenan nagode.
Tun kafin mu karasa gidan sai na nemi sanin
sunanta hade da garin data fito. Cewa tai
sunanta AISHA kuma ita yar asalin jahar
tarabace. Batun dalilin zuwanta jahar kano
kuma labarine mai matukar tsayi hade da ban
tausayi amma a halin yanzu ba abunda nake
bukata face abincin da zan ba cikina saboda
ina matukar jin yunwa dan haka idan Allah
yasa mun wayi gari lafiya to zan baka labarina
gaba daya domin bazan ragema ko daya ba.
Sai nai murmushi sannan muci gaba da tafiya.
Gaba daya harna manta da kalubalan dake
gabana na tunanin yadda iyayena zasuyi
mamakin ganina a raye. Na tura kofa kenan
saina tuna jinai kirjina yai wata irin bugawa
amma ko kadan ban bari aisha ta fahimci
komai a tattare dani ba da shigarmu koda
mahaifiyata tai ido biyu dani a yayin da nai
sallama sai ji nai ta zafga salati sannan ta
mike a tsorace. Cikin yanayin rudani tace ”
waye wannan Allah yasa dai ba mafarki
nakeyi ba. Saboda jin dadin ganin mahaifiyata
da nai a wannan lokacin nan take naji hawaye
ya zubomin. Budar bakina sai nace “umma
tabbas dankine ya dawo gareki domin ba
mutuwa nai ba kamar yadda kuke tunani. bani
da wani burin daya wuce na faranta miki rai
hakane dalilin da yasa nabar gida domin cika
miki burin ki. Cikin yanayin mamaki tace
“wane irin burine kakeson cikamin wanda har
zaisa kabar gida kasan irin kunar da muji a
yayin damu samu labarin cewar kabar duniya?
Haka muita zubar da hawayanmu akanka
bamu saniba ashe ba sonmu kakeyiba kawai
zubar hawayanmu kake son gani. Nan take na
durkusa har kasa inamai kukan bakinciki haka
na dago kaina na kalli mahaifiyata nace ” dan
Allah umma ki yafemin nasan na aikata
kuskure kawai na aikata hakanne domin cika
miki burinki ta buda baki zatai magana sai
nace “a’a umma nasan maganar da zakimin
bazata wuce neman sanin burin da nakeson
cika miki ba saboda nasan kin manta da
alfarmar daki nema a gareni ta batun rabuwa
da ummey wadda nake matukar sonta a
zuciyata to amma sai dai son da nake miki ya
zarce nata. Koda mahaifiyata taji wannan
batun nan take ta rike baki cikin yanayin kuka
tace ” tabbas na cuceka kuma bana tunanin
Allah zai yafemin a kan wannan abun daya
faru. Nan take na mike tsaye nace “haba
umma kefa mahaifiyatace wadda take da ikon
sani duk wani abun da taga dama muddun
bai sabawa addinin musulunci ba. Kuma ina
da tabbacin surrin da kike boyemin bai
sabawa addinin musulunci ba dan haka umma
zanso ki manta da wannan al’amarin, tunda
Allah yasa ummey tayi aure bani da wani farin
cikin daya wuce haka. Sai mahaifiyata ta
shafa kaina tace ” Allah yaima albarka. Koda
na kalli aisha sai nace “au dan Allah aisha kiyi
hakuri alhinin da muke cikine yasa na shafa’a
dake. Murmushi naga tayi sannan tace “kar
kaji komai domin nima nayi matukar tausaya
muku. Bayan an bata dakin da zata kwanta
sai na dauki abinci na kai mata har dakin da
kaina bayan na fito sai nace ” umma wai ina
abba ya shigane naga tun da nazo ban ganshi
ba sai tace “aikon abbanka yana jahar katsina
yau kwananshi biyu a can amma gobe nakesa
ran dawowarshi haka na zauna kusa da
ummata ina cin abinci sai tace ” yaune zan
bayyanama sirrin dana dade ina boyewa a
zuciyata badan komai ba sai dan ina da
yakinin bazaka sanarma kowa ba saboda na
yadda da kai kuma bani da kowa yanzu a
gabana wanda ya wuce kai tunda yayarka
zainab ta riga da tayi aure. Haka na gyara
zama dan jin sirrin da mahaifiyata ta dade
tana boyewa a zuciyarta. Ma haifiyata tace
“sanin kankane mahaifin ummey abokin
mahaifin kane ita kuma mahaifiyarta
kawatace. Hakane yasa mu kasance tamkar
yan uwan juna sai dai kuma tun daga lokacin
da Allah yasa suyi aure har kawo yanzu basu
taba hai huwa ba. Cikin yanayin mamaki nace
” to amma umma ita kuma ummey fa? Sai
tace “ummey yarsuce amma ba wadda su
haifa da cikinsu ba. Kwatsam wata rana sai
Allah yaba mahaifiyar ummey ciki a dai-dai
lokacin da nima nake dauke da juna biyu
tsakar dare musalin karfe 2 lokacin kowa yai
bacci sai haihuwa tazomin haihuwata kenan
sai abokin mahaifinka yazo mana da batun
hajiya ameena ta haihu amma dan baizo da
raiba ganin damuwar da suke cikine na rashin
samun haihuwa yasa mu dauki daya daga
cikin yayan damu haifa mu sadauka musu
domin yaya biyu na haifa a wannan lokacin ko
cikakken wata daya da faruwar hakan ba aiba
sai Allah ya dauke ran hafsat. Cikin yanayin
mamaki nace ” umma kina nufin yaya biyu ki
haifa a wannan lokacin kuma hafsat itace
abokiyar haihuwar ummey sai ta jinjina kai
tace kwarai kuwa. Sannan tace “wannan shine
dalilin da yasa na shiga tsakaninka da ummey
domin ita kanwarkace ta jini kuma tabbas kayi
matukar dubara gami da hangen nesa da har
ka nisancemu na tsawon shekara biyu da
wasu watanni dan haka zan kasance mai yima
addu’ar samun nasarar duniya da lahira. A
wannan ranar haka na kwana cikin farin ciki
hade da kwanciyar hankali bayan gari ya
waye sai nai alwallah na nufi masallaci tabbas
al’amarin yai matukar dauremin kai ganin
yadda al’umma suke darewa ayayin da suyi
ido biyu dani tsamo-tsamo a masallaci ganin
hakane yasa na tuna da batun mutuwata. Nan
take na mike tsaya nace “ko kadan banzo
masallacinnan domin na tsoratar daku ba
amma nasan dolene ku shiga rudani
sakamakon ganina da kuyi a raye. Tabbas
hadarin motane ya auku damu a yayin da
nake kan hanyata ta dawowa gida kano daga
jahar kebbi Allah cikin ikonsa motar tanayin
karo sai kofar da nake bangaranta ta bude
can na fada cikin wasu ita tuwa wanda hakan
yai sanadin buguwar kaina tun kafin mutane
su karaso garemu tuni nayi nisa haka naita
tafiya ciki daji banma san inda nake dosa ba
domin tuni hankalina ya gushe ban da wayata
ai amfani wajan sanar da iyayena abun daya
faru damu domin a wurin dana fado na barta
haka na kwashe tsawon shekara biyu ba’a
hayyacina ba. A yayin da hankalina ya dawo
gareni ba abun dana fara tunawa dashi face
iyayena. Wannan shine abun daya faru dani
dan haka kar kuji tsorona domin nima dan
adam ne tankarku. Haka su jajantamin cikin
yanayin tausayawa. Bayan na koma gida nine
har wajan karfe 9 banga fitowar aisha ba
hakane yasa na shiga dakin domin dubawa
ganin halin da aisha take cikine yai matukar
kidimani wanda hakan yasa kafafuwana su
kasa daukata in takaice muku dai bansan
lokacin dana zauna kasa ba ina mai zafga
salati domin ban samu aisha a raye ba.
=> 9
Hakika a lokacin da nayi ido biyu da gawar
aisha ba kadan na shiga rudaniba. Koda
jami’an tsaro su gane cewar bamu da hannu
wajan mutuwar aisha sai su sallamemu ba
tare da an wahalar damu ba. sakamakon
rashin sanin iyayanta da kuma dangintane
yasa ayi jana’idarta a gidanmu dawowarmu
daga makabarta kenan sai nai kacibus da
ummey a kofar gidanmu. Duk da cewar
ummey tayi aure haka ta tunkaroni fuskarta
cike da mamaki da zuwanta ta rike hannuna
sannan ta fashe da kuka tace “yayana wallahi
ji nake kamar mafarki nakeyi. Dan Allah
dagaske kai dinne kuma taya ai har hakan ta
faru? Cikin yanayin tausayawa nace “ummey
zan sanar dake komai domin bazan taba
barinki a cikin rudani ba amma ki tabbata zaki
daukarmin alkawarin bazaki taba nunawa
kowa kinsan wannan sirrin ba domin ko
iyayankima bana bukatar susan kinji wannan
sirrin balle wasu daban. amatsayinta na
kanwata ta jini haka nasa hannuna na share
hawayan dake fuskarta sannan nace ” amma
wannan sirrin bazai yuwu na sanar dake a
yanzuba saboda gudun sa’idon al’umma, dan
haka ki bari sai Allah ya kaimu zuwa gobe.
Cikin yanayin mamaki ummey ta dago kanta
ta kalleni. Tace “wane sa’ido kuma kake gudu
karfa ka manta ni takace har abada. Budar
bakina sai nace “ummey koda ace bakiyi
aureba to babu yadda za’ai ki taba
kasancewa matata. Nan take naga wani sabon
hawaye ya faso daga idanun ummey cikin
yanayin kuka tace ” idan auran da nayine
zaisa kayi tunanin kin kasancewata a matsayin
mallakinka to kasa a ranka wannan auran
nawa tamkar na yanke igiyarshine. Sannan ta
juya ta tafi tana kuka duk al’ummar dake
wannan wurin gaba daya sai idonsu yayo
kanmu. haka na shiga gida cikin ta’ajibi.
Kwatsam cikin dare musalin 10:30pm na dare
ina kwance a dakina lokacin bamu kaiga rufe
gidaba sai jinai an tasheni daga bacci juyowar
da zanyi sai nayi ido biyu da ummey zaune a
kusa dani nabuda baki zanyi magana sai naga
ta mikomin wata farar takadda koda naga
takaddar saki daya dauke da sunan ummey.
Cikin yanayin takaici hade da nuna bacin rai
nai mata wani kallo nace haba ummey taya ai
haka tafaru? Budar bakinta sai tace “akanka
ba abunda bazan iya aikatawaba, tace “kawai
durkusawa nayi har kasa idanuwana suna
zubar da hawaye na rike kafarshi nace ” dan
Allah dan Annabi idan yanayiwa iyayanshi
kuma yana kaunar zaman lafiya to ya
gaggauta bani takaddar saki. Budar bakinshi
sai yace “amma ummey wane laifi namiki da
har kike neman takaddar saki daga gareni?
Sai nace “baka aikatamin laifin komaiba
amma zanso kasan da cewar tunda wanda
nake kauna ya dawo to bazan taba samun
kwanciyar hankaliba muddun bai zama
mallakina ba dan haka ina mai rokonka daka
bani takaddar da zata zamto shaidar rabuwata
da kai saboda hakan shine zaifi kasancewa
zaman lafiya a tattare da kai. Sai yayi
murmushi sannan yace “tun daga lokacin
daya samu labarin dawowarka yaji a jikinshi
hakan zata iya faruwa dan haka shi maison
zaman lafiyane kuma maison ganin farin ciki a
tattare dani. Wannanne dalilin dayasa ya
rubuta takaddar saki a gareni. Bayan ta gama
yimin wannan jawabin, raina a bace nace
“amma ummey kin aikata kuskure. Domin ke
kanwatace ta jini wadda mahaifiyata ta
haifeku a matsayin yan biyu da cikinta. nan
take na fara bata labarin duk yadda ai hakan
ta faru tun daga lokacin da mahaifiyata ta
haifesu har zuwa lokacin danabar gida domin
cikawa mahaifiyata burinta. Amma duk da
hakan baisa ummey tayi na’am da
bayaninaba. Nan take ta mike tsaye tace
“karka fake da wannan hanyar dan guduna
saboda idan har ka gujeni a wannan lokacin to
zuciyata bazata taba yafemaba sannan tayi
waje tana kuka ganin hakane yasa nabi
bayanta domin gudun kar iyayanta susan abun
daya faru fitowata kenan daga daki sai nayi
arba da AISHA zaune a falo cikin yanayin
furgici nace “aisha!!!!!! Wanda hakan yasa
ummey ta juyo fuskarta da sauri sannan taja
burki ta tsaya. A tsorace na karasa kusa da
aisha! cikin yanayin rudani nace “aisha a iya
sanina da kuma tunanin mutuwa ba karya
bace amma hakan yana neman jefa zuciyata a
rudani. Murmushi naga tayi! Sannan tace
“waya fadama cewar na mutu? Alhalin kai ka
rakani har tashar motoci nahau mota zuwa
jahar jigawa. Sai nayi shiru na dan wani
lokaci sannan na dago kai na kalleta nace
“tabbas naga haka amma a mafarki. murmushi
naga tayi sannan ta jinjina kai ta kalleni tace
“ba mafarki kaiba domin azahiri hakan ya
faru.
=> 10
Fitowar mahaifiyata daga daki kenan. Cikin
yanayin firgici nace “umma kinga aisha wai ba
mutuwa tai ba. Cikin yanayin mamaki
mahaifiyata ta kalleni tace “to kai a ina
kasamu labarin ta mutu? ina kai ka rakata har
tashar mota domin ta hau mota zuwa jigawa.
Nan take na kalli ummey nace “ummey anya
acikin hankalina nake kuwa? Tabbas idan har
maganar da aisha tayi gaskiyace to babu
shakka kwakwalwata ta samu tabuwa. Budar
bakin ummey sai tace “ita kuma wannan
aishar wacece kuma meye alakarka da ita?
Nan take na shiga bata labari. nace “motace
ta hadani da ita tun daga jahar kebbi bamu
mu sauka motaba sai musalin12 na dare
hakane yasa ta nemi taimakon aron wayata
domin takira wadda tazo wajan nata amma
sai wayar taki shiga koda naga tayi matukar
shiga cikin damuwa saina nemi tabini zuwa
gidanmu idan Allah yasa gari ya waye sai taji
dadin kiran nata. Haka mu jero tare zuwa gida
tun a hanya na nemi sanin sunanta hade da
jin dalilin zuwanta jaharmu ta kano. Cewa tai
aisha ne sunanta batun dalilin zuwanta kano
kuma labarine mai tsayi hade da ban tausayi
dan haka nayi hakuri zuwa safiya sabida tana
matukar jin yunwa hade da bacci. Da isarmu
gida cikin yanayin farin ciki nagaisa da
mahaifiyata sannan na kaiwa aisha abinci
domin nasan tana matukar bukatarshi a
wannan lokacin. kwatsam musalun karfe 8 na
safe ina shiga dakin da’aba aisha a matsayin
masauki sai nai arba da gawarta ga kuma
abincin dana kawo mata koci bataiba hakane
yasa jami’an yansanda su gudanar da bincike
akaina hade da iyayena mahaifiyatace ta
matso kusa dani sannan ta dafa kafadata tace
” to indai hakane babu shakka akwai matsala
a tattare da kai domin duk wannan batun da
kayi ba wanda ya faru kawai ni dai abun dana
sani shine kazo da aisha gidannan washe gari
da safe kuma ka rakata ta hau mota zuwa
jahar jigawa. Budar bakina sai nace “to amma
umma meya makasudin dawowarta gidannan?
Sai ummata tace ” ai dama ta sanar dakai
cewar kwana daya zatayi sannan ta dawo
gareka saboda ka daukar mata alkawarin zaka
aureta sakamakon tausaya mata din da kayi a
dalilin jin labarin data baka haka na samu
waje na zauna jikina a sanyaye haka na kalli
aisha da ummey hade da mahaifiyata sannan
nace “tabbas ina cikin rudani domin bansan
wani labarin da aisha ta bani ba har da zaisa
na dauki alkawarin aure a tsakanina da ita
sannan na kara da cewa dan Allah ku taimaka
ku fitar dani daga wannan matsanancin
rudanin. sai aisha tace ” ikon Allah! Yanzu
kana nufin harka manta da duk labarin dana
baka? Cikin yanayin kidimewa nace “aisha
nifa bansan wani labarin daki baniba. Sannan
na kalli mahaifiyata nace “umma kenan batun
da kimin na batun ummey kanwatace ta jini
shima baki da masaniya akanshi kenan sai tai
shiru na dan wanilokaci sannan ta dago kanta
ta kalleni fuskarta cike da mamaki.
=> 11
Sai tayi shiru na dan wani lokaci sannan ta
dago kai ta kalleni fuskarta cike da mamaki
tace “tabbas ni banyi wannan maganar da
kaiba.
Amma a ina kasamu wannan labarin?
Koda naji wannan batun daga bakin
mahaifiyata nan take naji kaina yayi wata irin
bugawa sakamakon ganin yadda nake neman
komawa zararre alhalin kuma ni nasan a
hayyacina nake.
Jin hakane yasa ummey tayi tunanin so nake
na juya mata baya ta hanyar kame-kamen
hanyoyin da zasu kawo rabuwata da ita
wanda hakan yasa tayi waje tana kuka.
Jim kadan da fitar ummey sai Allah yai
dawowar mahaifina daga tafiyar da yayi.
Kamar dai yadda mahaifiyata tayi mamakin
sake ganina a raye haka shima wannan
mamakin hade da rudani ya bayyana a
fuskarshi.
Rudanin da nake cikine ya hanani bayyana
farin cikin sake haduwa da abbana, domin ba
abun daya fara fitowa bakina illah neman
sanin alakar dake tsakanina da ummey.
Budar bakina sai nace “abba wace alakace a
tsakanina da ummey?
Mahaifiyata naga ya kalla sannan ya kalleni
hade da cewa “wace ummey?
Matsawa nayi kusa dashi nace “abba a halin
yanzu ina cikin rudanin da bawanda zai iya
cireni a kaf fadin duniyarnan bayan kai da
kuma mahaifiyata.
Dan haka yanayin kallan da naga kayiwa
mahaifiyata ya tabbatarmin da cewar akwai
wani abun da kuke boyemin.
Nan take na durkusa har kasa ina mai zubar
da hawaye nace “umma sanin kankine ni mai
son ganin farin ciki a tattare dakune.
Wanda hakan yasa nabar gida na tsawon
shekara biyu da wasu watanni badan komaiba
sai dan ganin na cika umarnin daki bani ba
tare da nayi kuskure ba.
Ji nayi abbana yace “bakai kankaba nima
kaina a cikin rudani nake domin gaba daya
ban fashimci inda wannan maganar taka ta
dosa ba.
Na buda baki zanyi magana sai mahaifiyata ta
dakatar dani ta hanyar cewa “a’a nice wadda
zanyimai bayanin komai dangane da wannan
al’amarin.
Dakin mahaifina mu shiga gani ga mahaifiyata
hade da abbana.
Mahaifiyata ta kalli abbana tace “soyayyace ta
shiga tsakanin wannan yaron da ummey.
Gudun kar soyayyar tasu tayi nisane yasa na
bukaci ya janye kanshi daga batun kula
ummey da sunan soyayya, amma banason
hakan yai sular daina shigowarta gidan nan
domin ganin yadda take gudanar da
al’amuranta a gidannan ba kadan nakejin dadi
ba.
Ganin yadda na nemi shiga tsakaninsune yasa
ya bukaci na sanar dashi dalilin da zaisa na
rabasu.
Alkawarin dana dauka akan cewar ba wanda
zaiji wannan surrin ne yasa naki sanar dashi
batun komai.
Bukatar cika umarnin dana bashine yasa ya
kirkiri tafiyar da zai dauki dogon lokaci ba tare
daya sake waiwayar inda muke ba, wanda a
karshe sakon mutuwarshi ya iso garemu
alhalin kuma ba mutuwa yai ba ya aikata
hakane duk dan ya cire son da ummey
takemai a zuciyarta.
Bai kuma tashi dawowa ba har sai da ummey
tayi aure.
Koda mahaifina yaji wannan bayanin sai naga
ya jinjina kai hade da cewa tabbas wannan
al’amarine mai rikitarwa.
Kuma wannan hanyar dakabi dan ganin ka
cika mana burinmu itace tafi dacewa dan
haka ba wani abun da zamuce a gare face
fatan alkairi.
Sannan kuma inamai baka hakurin rashin
sanin wannan surrin da yake zukatanmu
domin alkawari mu dauka akan cewar bazamu
sanar da kowa ba.
Cikin hanzari mahaifiyata tace “to ai ya riga
yasan komai kuma babban abun daya
dauremin kai shine yadda ai har yasan da
cewa ummey kanwarshice ta jini.
Zumbur na mike tsaye fuskata cike da mamaki
nace “umma ashe dai gaskiyane ummey
kanwatace ta jini kenan?
Nan take ta jinjina kai hade da cewa “kwarai
kuwa ummey kanwarkace ta jini domin ba
yadda za’ai aure ya shiga tsakaninka da ita.
Sannan ta kara da cewa to amma taya ai har
kasan da cewa ummey kanwarkace alhalin ba
wanda yama bayani a cikinmu.
Cikin yanayin mamaki nace “umma kefa ki
fadamin komai jiya lokacin ina cin abinci a
kusa dake.
Domin abun da ki sanar dani shine “ummey
yarkice wadda ki haifeta tare da hafsat a
matsayin yan biyu.
Ganin yadda abokin mahaifina hade da
matarshi su shiga damuwa a dalilin rasuwar
yar dasu haifane yasa ku mallaka UMMEY a
garesu badan kimaiba sai dan duba da
yadda su dauki dogon lokaci ba tare dasun
samu haihuwaba.
Ba’a dauki wasu dogwayen kwanaki ba sai
Allah ya dauke ran hafsat yar uwar ummey
kenan.
Jinjina kai naga mahaifiyata tayi hade da
cewa “tabbas akwai matsala a tattare da kai
domin ko kadan banyima bayanin komai a
tattare da wannan surrin ba.
=> 12
Duk da cewa wannan al’amarine ba dan
karami ba, haka nayi kokarin mantawa da
wannan batun.
Bayan gari ya waye nayi wanka fitowata daga
gida kenan da kudurin yawatawa cikin gari.
Sai Aisha ta biyo bayana.
Koda na hada ido da ita sai tace “ya kuma
zaka tafi ka barni alhalin kuma kayimin
alkawarin bazaka taba nisanta kanka dani ba.
Wani kallo nayi mata hade da cewa nifa
bansan komai dangane da rayuwarki ba, balle
ki kawo batun daukar alkawari a tsakanina
dake.
Nan take naga fuskarta ta canza ta hanyar
bayyana bacin rai.
Har ta juya da kudirin komawa sai na dakatar
da ita ta hanyar cewa “da zaki taimaka ki
bani cikakken labarinki zata iya yiwuwa hakan
ya taimaka wajan rage rudanin da nake ciki.
Hawaye nagani a fuskarta a yayin data juyo
zuwa gareni.
Murmushi nayi hade da cewa haba Aisha
meye kuma na zubar da hawaye akan wannan
kankanuwar maganar.
Budar bakinta sai tace “hakika banyima
halacci ba amma kayi hakuri domin bani da
wata hanyar data dace nabi wadda ta wuce
wannan hanyar.
Cikin yanayin bacin rai nace “Aisha a halin
yanzu bana bukatar sakejin duk wata maganar
da zatayi sular sake afkani a cikin rudani.
Dan haka duk wata maganar da zata fito
bakinki zanso kiyita wara-wara yadda zan
fashimci inda maganar ta dosa.
Hannuna ta rike zuwa wani kebabben wajan
dake kusa damu da’a ware domin bukatar duk
wani mai son hutawa.
Koda mu zauna gani ga ita sai tace “tabbas
nice sular haifar da duk wani rudanin daka
tsunci kanka a ciki.
Kuma ba komaine ya haifar da hakan ba illah
kaunarka din da take zuciyata.
Azahirin gaskiya inasonka kamar yadda na aje
kaunarka a zuciyata.
Amma dan Allah zanso kafin na sanar dakai
koni wacece kasanar dani, shin kaima kanajin
sona a zuciyarka koda kankanine?
Kallanta nayi hade da cewa “ai shi so a zuci
yake samun masauki, kuma zanso ki gane
wani abu dangane da batun SO.
Duk girman abu hade da kasaitarsa ko
kyawunsa ba yadda za’ai ya samu masauki a
sansanin zuciyar koma waye muddun zuciyar
batayi na’am dashi ba.
Wani abun mamaki kuma sai kiga dan abu
kankani ya haifar da soyayya ga zuciyar wasu.
Tabbas kina da kyawun daya zarce na ummey
domin ke kyakkyawace amma hakan bazai
taba sawa na daukeki a matsayin wadda tafi
ummey ba.
Koda naga ta dan bata rai sai nace “haba
Aisha hakan bawai yana nufin cewar bana
sonki bane domin tun tuni zuciyata ta alkinta
sonki a cikinta.
Kuma hakan ya samo asaline sakamakon
tausayawar da tagani a tattare dake a yayin
da idanuwana suga zubar hawayen idanunki.
Gyara zama tayi sannan ta kalleni tace “dan
Allah kar kaji tsorona domin ba yadda za’ai na
cutar da rayuwarka.
Kallanta nayi hade da cewa “ki fadi duk abun
dake ranki kanki tsaye.
Ban tashi auneba sai jin saukar mari nayi a
fuskata.
Juyo fuskar da zanyi sai nayi ido biyu da
ummey tsaye a gabana.
Cikin yanayin fusata ummey tace “kai
azzalimine macuci wanda baisan darajar
kansaba.
Hakika wannan da kake tare da ita tafini
kyawun fuska.
Dan haka bazanga laifinka ba dan kayi watsi
dani ta hanyar maye gurbin soyayyata data
wannan.
Amma ka tabbatar da cewar ba yadda za’ai
na bari ka kulla wata alakar data shafi
soyayya da wata har sai ka kwashe gubar
soyayyar daka shayar dani wadda ta daskare
a zuciyata.
Sannan zaka samu damar kula wata ya mace.
Domin ko iyayena banajin cewar zasu iya
dakatar dani akan abun da zan iya aikatama
saboda gubar daka shayar dani ta dode duk
wasu hanyoyin dasu dace shawara mai
amfani ta isa kunnena.
Jin hakane yasa ran aisha yai matukar baci.
Cikin yanayin bayyana bacin rai aisha tace
“haba ummey wannan ai halayyace irin ta
marasa hankali da tunani ya za’ai da ganinmu
zaune zaki daga hannu ki mareshi.
Bansan lokacin dana dakama aisha tsawaba
hade da cewa karki sake danganta ummey a
sahun marasa hankali domin bazan taba jurar
ganin bacin rantaba.
Tsawar dana daka matane yasa ranta yai
matukar baci.
Nan take naji kaina yana sarawa kamar wanda
yai karo da bango.
Cikin kankanin lokaci naji duk ilahirin jikina ya
dauki zafi.
Ganin hakane yasa nayi gaggawar shiga gida.
Da shigata falo sai kuwa na yanke jiki na fadi.
Saida na dauki tsawon lokaci kafin mahaifiyata
ta ankara dani.
A yayin da mahaifiyata tayi ido biyu dani sai
ta rugo zuwa gareni.
Koda taga alamun suma nayi sai tayi
gaggawar dakko ruwa a fridge ta yayyafamin
har ta fara kuka a yayin da taga naki
motsawa.
Mikewar da zatayi sai taji nayi tari hade da
jan wani dogon numfashi.
Cikin gaggawa a garzaya dani zuwa asibiti.
Tsawon kwana biyu na dauka kwance a gadon
asibiti kafin na iya gane wadan da ke kusa
dani.
Da mahaifiyata na fara hada ido sai kuma
abokina ANAS zaune a kusa dani.
A yayin dana hada ido da ummey sai naji
kirjina yai wata irin bugawa.
Saboda nasan dolene a samu matsala, domin
ko kadan banason ganin ummey a cikin
damuwa ko bacin rai.
Sai dai kuma bani da masaniyar dalilin
faruwar wannan rashin lafiyar tawa.
Na dauka ummey zata nisanta dani amma sai
al’amarin ya sake rikicewa haka sona yaci
gaba da sake sabon toho a zuciyar ummey.
Wanda hakan yasa ummey ta turje akan batun
ba wanda zata zauna dashi a matsayin miji
idan bani ba.
Tun daga lokacin da’a dawo dani daga asibiti
ummey bata da wata sakewar data wuce ta
ganta a tare dani.
Ganin hakane yasa nace da ita “ummey
yaushe zaki koma gidan mijinki?
Budar bakinta sai tace “amma me yasa ka
zabi kamin wannan tambayar sabanin wadda
nayi tunanin fitowarta daga bakinka? domin
ba abun da nakeson ji daga bakinka face
batun aurena dakai.
Fuskata ba alamar wasa nace “amsar
tambayar dana miki nakesonji.
Cikin yanayin damuwa tace “Ba rana balle
wata.
Jinjina kai nayi hade da cewa to bari kiji
tarayyata da ke bazata taba yiwuwa ba balle
ayi batun aure.
Dan haka shawarar da nakeson na baki a
matsayina na dan uwanki itace “ki koma ga
mijinki domin wannan ita kadaice hanyar da
zata bulle dake.
Cikin yanayin alhini tace “meyasa kake son
dangantani da batun ni yar uwarkace
amatsayin hanyar da zata haifar da rabuwa a
tsakaninmu.
Haka ta kalleni tana kuka tace “me yasa zaka
juyamin baya a lokacin da sonka ya makantar
dani ta hanyar daina ganin duk wata hanyar
da zata kawo batun rabuwata da kai?
Ganin halin da ummey take cikine yasa na
yanke shawarar sanar da ita gaskiyar abun da
iyayenmu suke boye mana.
Budar bakina sai nace “ummey sanin kankine
tun kafin ki kamu da sona narigaki kamuwa da
hakikanin kaunarki.
Tabbas kafin zuwan wannan lokacin ba kadan
nakejin shaukin sonki ba amma a halin yanzi
idan akwai abun da zai iya kasancewa
danasani ga rayuwata to bazai taba wuce
faruwar soyayya a tsakanina dake ba.
Kallanta nayi nace “ummey kefa kanwatace ta
jini wadda mahaifiyata ta haifeku a matsayin
yan biyu abokiyar haihuwarki itace “hafsat
wadda allah yaima rasuwa.
Tun da nake a rayuwata ban taba tunanin
durkusawa a gaban wata ya mace da sunan
rokon wata alfarma a tattare da itaba. Amma
sai gashi nine na durkusa har kasa a gaban
kanwata domin rokonta.
Koda na durkusa a gaban ummey sai nace
“dan Allah ummey ki taimaka ki rufa mana
asiri ta hanyar janye batun soyayyar dake
tsakanina dake ki kuma yi kokarin rike wannan
surrin a iya zuciyarki ta hanyar kin sanar da
kowa wannan surrin.
Kuma zanso kikasance mai kokarin samawa
zuciyarki hakurin zama da wadanda suke rike
dake a matsayin yarsu ta hanyar cigaba da
daukarsu a matsayin iyayenki wadanda su
durkusa su haifeki.
A karshe kuma ina mai rokonki daki koma ga
ainashin mijinki domin ba aure a tsakanina
dake.
Nan take naga fuskarta ta canza sannan ta
share hawayen dake fuskarta ta fita daga
dakina.
Ban saniba ashe kanta tsaye wajan
mahaifiyarmu ta nufa.
Koda ta samu mahaifiyar tamu sai tace
“umma me yasa ke da abba ku zabi kuyi
watsi da kyautar da Allah ya baku ta hanyar
damkata ga wasu.
Umma bansan irin azaftar dake din da nayi
alokacin da ina cikinki ba wanda har hakan
zaisa kiyi sadaka dani ga wadanda ko
dangantakar jini bamu hada dasu ba.
Gashi a dalilin faruwar hakan zuciyata tana
neman cutuwa.
Abu na farko nayi rashin ingantacciyar
tarbiyyar data dace na samu daga gareku.
Abu na biyu a dalilin rashin sanin wannan
sirrin daku dade kuna boyewa har zuciyata ta
kamu da son kasancewa da yayana wanda
nake jini daya dashi a matsayin matarshi.
Nan take ummey ta durkusa har kasa cikin
yanayin kuka tace “dan Allah umma ku
taimaka ku dawo dani gida.
Ina zaune a dakina cikin yanayin damuwa sai
naji karar bude kofa.
Dago kan da zanyi sai nayi ido biyu da
AISHA.
Budar bakin Aisha sai tace “yanzu kana
tunanin abun daka aikata kayi dai-dai kenan?
Dago kan da zanyi sai nace “waike wacece?
Kuma meye alakata dake da har kike yima
rayuwata shish-shigi akan abun da bai shafeki
ba?

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button