HAUSA NOVELWANI LABARI

WANI LABARI

Murmushi tayi hade da cewa “zaka iya
tunawa da KADANGARAN da abokinka yai
kokarin kashewa yau tsawon shekara 14 kenan
da faruwar hakan.
Cikin yanayin rudani mai tattare da mamaki
nace “wannan kadangaran shine ya addabi
rayuwata na tsawon wadannan shekarun daki
ambata.
Hakane yasa bana bukatar jin labarin daya
shafi kadan-gare balle ganinshi ido da ido.
Al’amarin ya samo asaline tun ina dan
kimanin shekara 8 lokacin muna zuwa
makarantar primary.
=> 13
Cikin yanayin rudani mai tattare da mamaki
nace “wannan kadangaran shine ya addabi
rayuwata na tsawon wadannan shekarun daki
ambata.
Hakane yasa bana bukatar jin labarin daya
shafi kadan-gare balle ganinshi ido da ido.
Al’amarin ya samo asaline tun ina dan
kimanin shekara 8 lokacin muna zuwa
makarantar primary.
Aduk lokacin damu halarci makaranta bani da
wani sukunin daya wuce maida hankalin rike
koda abu biyune daga cikin abunda
malamanmu su koyar damu domin hakane
yake bani kwarin guiwar samun kyaututtuka
daga mahaifina hade da mahaifiyata.
Saboda ako wace ranar dana halarci school
mahaifiyatace take fara tambayata abun da’a
koyar damu idan mahaifina ya dawo shima sai
ya dora da nashi tambayoyin.
Mahaifina hade da mahaifiyata suna matukar
alfahari dani ganin yadda nake kokarin zuwa
makaranta.
Sai dai kuma a zaman takewar rayuwa dolene
kaci karo da mutane biyu na banza dana kirki.
Abokan banzane suyi sular canza halayyata
izuwa halayyar da suke ciki.
Tun Ina dari-dari dasu har na kaiga sakin
jikina a cikinsu.
Da zaran mun halarci school bama daukar
awa daya ba tare damun arce bayan gari
yawon banza ba.
Tafiya mukeyi ba yar karamaba dan zuwa
kwarin daya daga cikin abokanmu domin shan
kayan itatuwa.
Kafin mahaifina ya ankara tuni wannan yawon
banzan yayi karfi a zuciyata ta yadda sai
ankai ruwa rana kafin a dakatar dani.
Tabbas ni nasan da cewa mahaifina yana
matukar sona amma duk da hakan bai hanashi
yimin shegen duka ba domin bansan adadin
dukan da nasha a dalilin yawace yawacen
banzana ba.
Sai dai kuma akwai wata dabi’ar da nake
tattare da ita wadda hakan yasa nake yawan
samun matsala da abokan nawa.
Wannan dabi’ar tawa ta samo asaline tun
wata ranar Monday kafin halayyata ta samu
nakasu ta hanyar yawace yawacen banza.
Musalin karfe 8 na safiyar Monday na fito
daga gida a gaggauce ko karyawa ban samu
damaryi ba domin gudun kar a dakeni a
makaranta saboda nima kaina nasan a
wannan ranar na makkara.
Har nayi nisa sai kular abincin da nake rike
da ita hannunta ya fita nan take taliyar dake
ciki tayi watsa-watsa.
Tabbas abun mamaki ya bani sakamakon
ganin yadda kadangaru su tasa abincinnan
daci.
Ban bar wajan ba har saida su cinye abincin
tas.
Duk da cewa ayunwace nake haka na nufi
makaranta ba tare da bayyana wata damuwa
ba domin a cikin littattafaina akwai wata naira
hamsin din dana dade da ajewa.
Haka nayi hakuri har a tashemu break sannan
na samu abun da zanci.
Tun daga wannan ranar na kuduri niyar cigaba
da tallafama kadangaru.
Ako wace rana bana taba rasa yan kudaden
kashewa daga abbana ko mahaifiyata wani
lokacin kuna yayata zainab nake tunkara da
bukatar ta bani kudin da zan dan kashe.
Ta wadannan hanyoyin nake samun yan
kudaden da nake sayan taliya domin ciyar da
kadangaru.
Tafiyayya nakeyi zuwa wani kango domin
kaiwa kadangaru abinci badan komai ba sai
dan kar al’umma su samin ido.
Saboda abun yana matukar burgeni a yayin
da naga sun dukufa cin taliyar.
Gaba daya sai wannan al’amarin ya zamemin
kamar wani bangare na rayuwata wanda idan
ban aikatashi ba to ba yadda za’ai naji dadi.
Haka naita gudanar da wannan aikin ba tare
da kowa ya sani ba domin a wannan lokacin
bani da wasu abokai na musamman.
A yayin da halayyata ta samu canjine ta
hanyar samun abokan banza sai wannan
dabi’ar tawa ta fito fili.
Amma ba kowane ya sani ba domin iya
abokainane kadai susan da wannan dabi’ar
tawa.
Koda nakai kimanin 10 years sai na aje
lokacin da zan rika kai masu wannan abuncin
wato taliya kenan.
Musalin karfe 7:30 na safiyar nake zuwa dakin
abokina ANAS domin dafa taliyar da zankai
masu.
Musalin karfe 2 na rana kuma bayan an idar
da sallar Azahar kudi nake cirewa daga
aljihun domin siyan taliyar da zan kai masu.
Da zaran naga yamma tana neman yi haka
zan sake siyan wata taliya na aje masu idan
magariba ta tunkaro sai naje na kai masu.
Abun ba kadan yake bani dariya ba ganin
yadda kadangarunnan suyi kiba kuma ni ba
ma’abocin cin kadangare ba balle na rika
yankawa inaci.
Duk yawon da zanyi da abokaina bana taba
yin sake wajan kai madu abinci akan lokaci.
Idan har nasan zanyi tafiyar da zata haifar da
rashin kai masu abinci akan lokaci to ba
makawa sai naje garesu domin basu hakuri.
Da zaran sunji sallamata sai su rugo zuwa
gareni.
Abun da nake ce masu idan zanyi tafiya shine
“kuyi hakuri domin yau zanyi wata yar tafiyane
kuma ina tunanin hakan zai iya haifar da
rashin kawo maku abinci da wuri.
Haka zasuyita gyada kai hade da buda baki
ba tare da nasan abun da suke fada ba.
Idan kuma a samu akasi wani uzirin ya hanani
kai masu abincin akan lokaci haka zan basu
hakuri hade da sanar dasu dalilin faruwar
hakan.
Ganin yadda wannan al’amarin ya game
jikinane yasa abokaina suke nuna bacin ransu
wanda a karshe suyi yunkurin kashe
kadangarun gaba daya ta hanyar sa masu
guba a taliya.
Amma Allah bai basu ikon cin taliyar ba.
A majalissa da muke zama akasin daya
haifarmin da tsanar kadangare ya samo asali.
Muna cikin zamanmu NUHU ya kira mai
gyada.
A gabanmu ya siyi ta 20 naira ya murjeta a
gaban idonmu da kudurin cinyeta shi kadai.
Ganin hakane yasa na nace akan sai naci
gyadar.
Cikin yanayin wasa muyita kokawa har mu
kaiga fita daga majalissar tamu ta hanyar yin
tafiya mai dan nisa.
Ba yadda ya iya haka ya bukaci na bude
hannuna domin ya samman gyadar.
Wajan zuba min gyadarne a samu akasi wasu
su zuba kasa.
Sai kuwa wani kadangare ya rugo a guje ya
dauki daya daga cikin gyadar data zuba a
kasan.
Nan take naga ran NUHU yai matukar baci
wanda hakan yasa yayi ko karin kashe
wannan kadan garan.
Haka yabi kadangaran a guje domin ganin
bayanshi sai Allah ya taimaka kadangaran ya
afka wani rami to ashe kadangaran baisha ba
domin ramin ba wani mai nisa bane.
A gaban idona nuhu ya zura hannu ya kamo
kadangaran.
Ganin yadda yake neman ganin bayanshi ne
yasa nayi kokarin dakatar dashi amma hakan
bai yuwu ba domin bugashi yai da kasa.
Tabbas ba kadan nayi mamakin ganin yadda
kadangaran ya kunbura ba.
Haka naja abokina mu tafi tun a hanya ya
sanar dani shifa kanshi ciwo yakemai wanda
hakan yasa yayi gaggawar tun karar gida.
Ko cikakken 30 minutes da rabuwarmu ba
aiba sai batun rasuwarshi ya karade gari.
Ba kuma kowane yasan abun daya faru kafin
rasuwar shi ba sai ni da abun ya faru a gaban
idona.
Bayan kwana ukku da rasuwar nuhu wato
abokina kenan sai babban kalubale ya fara
bibiyata.
Cikin dare muslin karfe 2 naji matsin abu a
kirjina wanda ban gane ko menene ba.
Tsoran da najine yasa na kwalla kara ban
kuma san lokacin dana fado daga kan gado
ba.
Cikin yanayin furgici na haska tocila.
Ganin kadan garan da NUHU yayi kokarin
kashewa a dakinane yasa nayi matukar
tsorata.
Wanda hakan yasa nayi kaura daga dakina
zuwa dakin anti zainab.
Da shigata saina tasheta daga bacci hade da
cewa anti wallahi tsoro nakeji.
Haka ta tilastamin akan saina sanar da ita
tsoran da nakeji amma naki domin nasan
muddun nayi gaggawar sanar da ahalina
wannan batun to ba makawa sai an samu
wanda zaiyi kokarin hallaka wannan
kadangaran.
Kuma na tabbata hakan zai iya haifar da sular
hallaka rayuwar wasu daga cikin ahalina hade
dani kaina.
Kuma ni faruwar hakane banaso.
Ganin yadda naki sanar da itane yasa ta
kyaleni mu kwanta tare a gado daya.
Ban saniba ashe akwai sauran rikici a gaba.
=> 14
Ba karamin tashin hankali na shigaba a dalilin
kasancewar wannan kadangaren a tattare
dani.
Bani da wata sakewa domin aduk inda zan
tsunci kaina dolene shima wannan kadadaren
ya kasance a wajan.
Idan ina cikin abokaina ko wasu mutanan da
ban baya kusanto inda nake saiya koma can
gefe.
Wallahi har fargabar zama ni kadai nake
domin har hawa jikina yakeyi.
Aduk lokacin da naji yahau jikina ba karamin
zabura nake a guje ba.
Domin har faduwa nashayi wajan gudu wanda
hakan yake sawa naji ciwuka a hannayena
hade da kafafuwana.
Bana taba yadda na kwana ni kadai domin a
dakin anti zainab nake kwana.
Bacin ran kwanan da nakeyi tare da itane
yasa tayimin mugun duka alhalin kuma ba
laifina bane domin duk laifin wannan ad-
dababben kadangaren ne.
Duk dukan da anti zainab zatamin baya taba
damuna domin ko zubar da hawaye banayi ni
dai kawai na gwammaci ta ganamin duk wata
azabar da taga dama maimakon na kwana
tare da wannan kadangaran a dakina.
Koda ta gaji da ganina a dakinta sai ta
gargadeni dana daina kokuma ta sanar da
abbanmu.
Tun daga wannan ranar saina koma kwana a
dakin abokina ANAS.
Tsawon sati daya na dauka ina kwana a dakin
anas sai mahaifina ya gane cewar bana
kwana a gida.
Duk da irin fadan da abbana yakemin baisa
na daina kwana a dakin anas ba.
Ganin hakane yasa abbana yamin dukan da
bantaba tunanin fuskantar irinshi a fadin
duniyar nan ba.
Gudun karna sake fuskantar irin wannan
dukanne yasa na bukaci abokina ANAS daya
rika zuwa dakina muna kwana tare amma yaki
domin shima cewa yayi abbanshi bazai taba
lamuntar haka ba.
Haka dai wannan kadangaran ya hanani
sakewa.
Hmm!! Lokaci daya kadangaran ya bijiromin
da wani sabon iskanci.
Dazaran na sayi wani abun da niyarci sai
kadangaran ya rugo a guje zuwa gareni tsoran
da nake tattare dashine yake sawa na saki
abun ya fadi kasa nan take kadangaran zai
hau abun daci.
Musalin karfe 3 na rana na tunkari gida da
kudurin cin abinci.
Da shigata dakina sai kuwa nayi ido biyu da
wannan kadangaran a saman marfin abincin
da’a ajemin.
Hakika nima nayi matukar mamakin ganin
yadda kadangare ya addabi rayuwata.
Kuma gashi idan na nemi takurama
rayuwarshi to ba makawa sai na rasa
rayuwata kamar yadda abokina NUHU ya rasa
tashi rayuwar.
Ganin hakane yasa na durkusa har kasa ina
zubar da hawaye domin neman sulhu a
tsakanina da wannan kadangaran.
Cikin yanayin kuka nace “haba bawan Allah
meyasa kake neman takurama rayuwata ta
hanyar bibiyata, alhalin ban aikata laifin komai
a garekaba?
Abokinanefa ya nemi kasheka ganin hakane
yasa na nemi ceton rayuwarka.
Kuma ai ka dauki fansar abun daya aikatama
meye zaisa kaci gaba da bina.
Dan Allah idan har bazaka daina binaba to
kadaina hawa jikina kuma ka daina kokarin
tunkarar inda abincina yake.
Kuma nayima alkawarin duk abun da zanci
zan rabashi biyu daya naka daya nawa.
Haka tunanin wannan kadangaran ya addabi
zuciyata lokaci daya duk nabi na rame ganin
hakane yasa iyayena suyi yunkurin tilastamin
ta hanyar sanar dasu lalurar da take damuna.
Ganin yadda naki yimasu cikakken bayanine
yasa su dangantani da asibiti domin duba
lafiyata.
Abunda likitan daya duba lafiyata ya sanar da
iyayena shine “ba wani abune yake damun
danku ba illah yawaitama zuciyarshi tunani.
Dan haka rage tunanin dake zuciyarshine
kadai zai kawo mai sassauci.
Anti zainabce ta tilastamin har saida nayi
mata cikakken bayanin abun da yake
damuna.
Haka aita nemamin magani domin rabani da
wannan kadangaran amma hakan yaci tura.
Haka wannan kadangaran yaci gaba da
bibiyata na tsawon shekara 14 amma da
taimakon Allah a dalilin maganin da iyayena
su dukufa nemamin sai Allah yasa wannan
kadangaran ya rage bibiyata.
Yana zuwa garenine lokaci-lokaci kuma idan
ya tashi zuwa gareni tofa a duk inda nake
Kwatsam zan ganshi amma baya hawa jikina.
Yau kimanin shekara biyu kenan rabona da
sake ganin wannan kadangaran.
Matsowa kusa dani Aisha tayi fuskarta cike da
murmushi.
Budar bakinta sai tace “bani ya kamata kaba
wannan labarin ba domin nice wannan
kadangaran kuma nice sular afkawarka a cikin
duk wani rudanin daka tsunci kanka a ciki.
Zumbur na mike tsaye a yayin da naji fitar
wannan furucin daga bakin Aisha.
=>15
Tsoran da Aisha ta gani a tattare danine yasa
tayi gaggawar rike hannuna.
Fuskarta ba alamar wasa tace ko kadan ban
nemi shiga rayuwarka domin na cutar dakaiba.
Bukatar rayuwata da taka su zama dayane
yasa nayita bibiyarka.
Ganin yadda ka tausayamin a yayin da
abokinka yai yunkurin cutar danine yasa
ruhina ya aminta da kai wanda hakan yasa
naita bibiyarka a suffar kadangare alhalin
kuma ni aljanace.
A duk lokacin daka kwanta bacci kai kadai ni
kuma sai nazo na kwanta a saman kirjinka
domin ba karamin dadi nakeji ba a yayin da
sautin bugun zuciyarka yake ratsa kunnuwana.
Kwatsam sai naga take-taken soyayya tana
neman shiga tsakaninka da UMMY kafin ka
gane cewar ita kanwarka ta jinice.
Gudun karka takurama kanka wajan bibiyar
ummey da sunan soyayyane yasa nayi kokarin
dakatar dakai ta hanyar yima hannunka mai
sanda ba tare dana fito fili nayima cikakken
bayanin cewar ummey kanwarka ta jini bace.
Bayanin da nayima a lokacin dana kiraka a
wayane ya tunzuraka wanda hakan yasa
kayima ummey bayanin abun dana sanar da
kai na cewar ba aure a tsakaninka da ummey
soyayyar da take zukatankuce tasa baku dauki
maganar tawa da mahimmanci ba.
Mahaifiyarka itace wadda ta fara gane alakar
da take tsakaninka da ummey.
Bukatar ganin farin cikin mahaifiyarkane yasa
ka shirya tafiyar da zaka dauki dogon lokaci
kafin ka dawo ga ahalinka badan komaiba sai
dan ka rusa son da ummey takema a
zuciyarta.
A hanyarka ta dawowa ga ahalinkane nayi
amfani da wannan damar domin kusanta kaina
dakai wanda hakan yasa ka bani masauki a
gidanku.
Tabbas banyima bayanin komai dangane da
rayuwata ba mahaifiyarkace kadai taji
labarina.
Amma ita a tunaninta kaima kana wajan
alokacin da nake bata labarin wanda har
hakan yasa ka daukarmin alkawarin
kasancewa dani na tsawon har abada
sakamakon tausayamin din da kayi batasan
cewar duk shirina bane domin ba kai din
bane.
Batun mutuwatama ba gaskiya bane domin
kai kadaine kaga haka saboda shima duk a
mafarki na nunama faruwar hakan.
Dan haka zan nisanta dakai na tsawon har a
bada bazan sake bibiyarka ba domin na
fahimci akwai tsoro a tattare da kai.
Sai dai kuma akwai sauran kalu bale a
gabanka domin tun daga lokacin daka dawo
gida iyayenka hade da kanwarka ummey ba
wanda yaji furucin komai daga bakinka.
Nan take naji kaina ya daure na kalleta a
sufane nace Aisha ban fahimci abunda kike
nufi ba.
Cikin yanayin tausayawa tace “Dan Allah kayi
hakuri nasan nayi matukar rikitar da kai.
Ba kuma komaine yasa na aikata hakanba sai
dan bukatar mallakarka a matsayin abokin
rayuwata.
Ganin inna aikata hakan banyima adalci bane
yasa na yanke shawarar fadama gaskiya.
Durkusawa tayi har kasa sannan ta dago kai
ta kalleni tace “kayafemin akan karyar da
nayima akan cewar UMMEY kanwarkace
domin ba wata dangantaka a tsakaninka da ita
wadda zata hana ka aureta domin gaba daya
abun daya faru a wannan al’amarin duk
shirinane domin har kawo yanzu ummey
batayi aure ba.
Na aikata hakane domin na maye gurbinta.
Tabbas ummey tana matsanancin sonka
domin bata da wani muhimmin tunanin daya
wuce naka.
Na bude baki zanyi magana bat ta bace.
Ko cikakken munti daya da bacewarta ba ai
ba sai naji karar bude kofa ummey na gani
hannunta rike da abinci a plate.
Da zuwanta sai ta aje abincin a gabana
sannan ta zauna a kusa Dani.
Yanayin kallon da naga tamin ne yasani
murmushi! budar bakina sai nace “ummey
meye alakata dake.
Zumbur ta mike tsaye cikin yanayin farin ciki
ta fara kiran mahaifiyata “umma! umma!. Kizo
yayi magana.
Cikin kan kanin lokaci saiga mahaifiyata ta
shigo hade da anti zainab yayata kenan.
Cikin yanayin mamaki nace “umma wai me
yake faruwane??
Cikin yanayin alhini zainab ta rungumeni tana
jukan farin ciki.
Bayanin da ummey tayiminne ya tabbatarmin
da cewa maganar aljana Aisha gaskiyace
domin ummey cewa tayi tun daga lokacin
dana dawo gida bana iya furta kalmar komai.
Shiru nayi na dan wani lokaci sannan na
jinjina kai hade da cewa ashe dai Aisha da
gaske take.
Budar bakin zainab sai tace “wacece kuma
Aisha?
Fuskata cike da mamaki nace “kina nufin
bakisan Aishar data zauna a gidannan ba
kenan wadda na dawo tare da ita.
Girgiza kai naga mahaifiyata tayi hade da
cewa tabbas ba wata mace mai suna Aishar
data zauna a gidannan koda kuwa na kwana
dayane amma tabbas bakai ka dawo da
kanka ba domin wata baiwar Allah ce ta kawo
mana kai sakamakon ID CARD din data gani a
tattare da kai kuma sunanta ya banbanta da
wanda ka fada a yanzu domin cewa tayi
hafsat shine sunanta kuma ko kwana batayi
ba ta koma.
Kaina a daure nace to amma umma meye
alakata da ummey?
Cikin yanayin mamaki ummey tace “kardai
kace har ka manta da soyayyar da take
tsakanina da kai?
Girgiza kai nayi hade da cewa a’a ban
mantaba amma akwai sarkakiyar dana tsunci
kaina a cikinta.
Banyi kasa a guiwa ba har saida nayi masu
cikakken bayanin abun daya hadani da Aisha
wanda hakan yai matukar kidimasu domin
basu da masaniyar komai dangane da
bayanin da suji daga bakina.
Bayan na gane cewar akwai aure a tsakanina
da ummey sai na nuna kaguwata akan ayi
hanzarin daura aurena da ita domin gudun kar
wata matsalar ta sake biyo baya.
Wani kallo naga anti zainab tamin hade da
cewa “kai kaji yaro da rashin kunya ai komai
gaggawarka dolene kajira sai nayi aure
sannan ayi naku bikin.
Cikin yanayin dariya ummey taja hannuna
muyi waje.
Da fitowarmu sai na kalli ummey nace “wai
dama har kawo yanzu ummey batayi sure ba.
Murmushi naga ummey tayi hade da cewa
kaga ya kamata ka mance da duk wata
bakuwar rayuwar da kayi a baya saboda
wannan itace asalin rayuwarka domin ba wani
auran da anti zainab tayi.
Ummey tayi matukar sabawa dani domin ko
kadan batason na nisanta da ita.
Makarantace da kuma bacci suke rabamu da
zaran an tasosu daga school ba inda take fara
yada zango sai a gidanmu ba kuma zata fito
ba sai tare dani duk da cewa tsakanin
gidanmu da nasu ba wata tazara bace mai
nisa haka zan rakata har cikin gidan nasu.
Bayan anyi aurena da ummey sai zuciyata ta
kasa samun natsuwa sakamakon yawaita
tunanin Aishan da nakeyi saboda har kullun
bana cire tsammanin bazata dawo gareni ba
wanda hakan yasa na kasa gane shin sonta
nake ko kuma tsoranta nakeji.
Alhamdulillah.
Anan zan dakata da wannan labarin sai kuma
mun sake haduwa a wani sabon labarin da
zan kawo maku nan bada jimawa ba.
Farin cikinku shine farincikina addu’arku itace
garkuwa a gareni.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button