__ abun yana matukar bani mamaki hade da bani dariya musamman idan naji al’umma suna kuranta soyayya. Abun har kunya yake bani musamman idan naga wani ya shiga bacinrai akan soyayya. Ban sani ba ashe nima soyayya ba mantawa tai da shafinaba sai dai kuma soyayyar data tashi budo shafina saita budomin bakin shafi wanda bansan ta ina zan fara sarrafa linzamin soyayyar ba. Lokaci daya khadeeja ta shiga zuciyata ko kuma ince muku ummey domin dashi a saba kiranta. Duk da cewar unguwarmu daya kuma layinmu daya da ummey bamu cika yima juna magana ba domin ni ko kadan banason raini ya shiga hanyata sai bayan ummey ta dan tasa nima shekaruna sunja. Sai na fahimci ummey ba yarinyace mai raini ba kawai tsantsar alkunyace a tattare da ita. Hakika ummey tana da fasalinta na kyau dolene nasata a jerin masu kyan diri bawai dan zuciyata tana bukatar kasancewa a tare da itaba na tabbata duk wanda yai ido biyu da ummey dolene ya yaba surarta. Ummey bata da wata abokiyar yawo wadda ta wuce anti zainab yayata kenan wannan al’amarin yana matukar burgeni ganin yadda zainab ta dauki ummey tamkar kawarta. Ummey takan shiga gidanmu tayi duk abunda taga dama kamar yadda antita zainab take gudanar da harkokinta a gidanmu. Tabbas zuciyata tayi matukar kamuwa da son kasancewa a tare da ummey a matsayin wadda zata kasance uwar yayana. Amma sai dai nakasa samun hanyar da zata kasance mafi sauki wajan cimma burina na samun tabbataccen wajan zama a zuciyar ummey. Tabbas ni kaina nasan ummey tafi karfin ajina ganin hakane yasa na nemi tausar zuciyata ta hanyar mantawa da ita amma ina hakan bazai taba yuwuwaba domin ako wace rana nakanyi ido biyu da ummey fiye da sau talatin kai banmasan iyakaba kuma duk sanda zanganta sai shaukin sonta ya sake sabon toho a zuciyata. Gaisuwace kawai take hadani da ita idan ba wannan ba bazan iya cewa ga wata maganar data taba hadani da ummey ba tabbas zuciyata tana matukar girmama ummey fiye da anti zainab amma saidai zuciyar tawa bata da ikon fito da wannan girmamawar a fili ta yadda ummey zata fuskanta a wannan lokacinne na fahimci girman soyayya. A yayin danabi duk wata hanyar data dace wajan mallakar numbar ummey saina sayi sabon layin MTN ako wace rana nakan tura mata da sakonnin jan hankali kamar sau ukku domin cimma burina sai da na dauki kimanin sati ukku ina aika mata da sakonni iri-iri amma ban taba ganin replay dinta ba furucin da taimin a karshe ba kadan yasani kukan zuci ba. Da sassafe na dakko layin dana saba aika mata da wannan sakonni da kudurin aika mata da sakon barka da safiya koda na dora layin sainai arba da sakonta cikin yanayin shauki na bude sakon abunda tace shine “dan Allah dan Annabi idan kana ganin girman iyayenka kayi hakuri ka daina aikomin da wadannan sakonnin. Nan take naji duk ilahirin jikina ya mutu kamar wanda aima dukan kawo wuka. Duk da haka ban hakuraba. A wannan lokacin karamar wayace dani kirar nokia E72 duk da cewar ba wani dadin hawa social network zanji da ita ba haka na bude sabon account a shafin facebook da boyayyan suna nayi amfani kafin kowa ya sanni dashi a yanzu wato Young Uzee ummey itace farkon wadda na farayin adding kaina tsaye nashiga bangaran search dayake bansan cikakken sunan da take amfani dashiba sai nayi amfani da numbar wayarta wato waddana saba aika mata da sako a baya kenan saboda ina kyautata zaton dashi ta bude account din koda na rubuta numbar nan take nayi ido biyu da account dinta cikin gaggawa na aika mata da frnd rqst saida a dauki tsawon kwana takwas sannan na samu karbuwa a matsayin frnd dinta duk da hakan dai ban tsiraba domin bansan adadin maganar da nai mata ba amma shiru babu replay har raina ya fara kuna saina tuna ummeyfa kyakkyawace dolene al’umma suyi mata katutu/yawa ta hanyar aika mata da sakonni iri-iri wanda hakan zaisa taki tsayawa dan karanta sakon kowa daya bayan daya. Ganin hakane yasa na aika mata da sakon da zai jawo hankalinta zuwa gareni. Abun da nace shine {“haba malan sam wannan ba halin mutun nagari bane kaji tsoran Allah ka rufe wannan account din. yanzu a matsayinka na musulmi meye amfanin bude account da sunan mace hade dasa hotan wadda bakasan ko waceceba kaji tsoran Allah ka daina amma kayi hakuri idan na batama rai”} bayan 7 minutes da aika mata da wannan sakon. Sai replay dinta ya shigo wayata abun da tace shine {“subhanallah dan Allah karkayi tunanin wannan account din na wanine to bana kowa bane face nawa kuma ni macece kuma hotan daka gani a profile dina bana kowa bane face nawa”} sai nayi mata replay nace {“dan Allah ummey kiyi hakuri wallahi nasan wannan account din nakine banawani namiji ba kawai na rasa yadda zanyine domin naga kin kulani a matsayina na frnd dinki a kalla nayi miki magana tafi ashirin ba tare da nayi kacibus da replay dinkiba hakane yasa nayi miki wannan maganar sai gashi kuma nayi sa’a kin kulani dan haka wallahi ko yanzu kiyi blocking dina bazan wani damu ba tunda har nayi nasarar magana da kyakkyawar mace kamarki”} hakika na dauka zata fadamin wata mummunar magana sannan tayi blocking din. Amma sai naga sabanin haka. Murmushi tayi tace {“humm”} ba tare da furta wata kalmaba. Sai nace {“to amma ummey ko zan iya sanin abunda yasaki murmushi haka cikin kankanin lokaci mai makon ki nuna bacin ranki akan abun da nai miki?”} Sai tace {“kawai salankane ya burgemi.} Wannanne yasa najawo hankalin ummey zuwa gareni. Yanayin yadda nake chating da itane yasa ta kagu taji muryata numbarta ta turomin tace dan Allah na kirata ko kuma nayimata plashing domin ta kirani anannefa na fashinci wannan hanyar bazata taba bullewa dani ba domin muddun nayi kuskuran kiran ummey a waya to babu makawa saita ganeni ni kuma hakane banaso domin kuwa so nake sai munyi matukar shakuwa da juna sannan zan bijiro mata da ainashin kudurina a kanta. Hakane yasa gaba daya nayi forget din facebook dina domin canza wata sabuwar hanyar wadda kuma nake kyautata zaton zata bulle dani. Kwatsam wata ranar asabar musalin 5:00pm nayi wankana kamar yadda na saba zan fita kenan sai nayi kacibus da abbana ayayin da yashigo gida wani kallo naga yaimin hade da cewar kasan yaune za’a fara aikin gyaran gidannan amma saboda tsabar wulakanci tun dazu nake nemanka ban samu ganinkaba gudun karna batawa masu aikin lokacine yasa na daga aikin zuwa gobe saboda key din dakin da’a aje simintin yana wajanka dan haka maza kaje ka dakko key din ka fito da gaba daya simintin dake dakin ba yadda na iya duk da wankan da nayi haka na bude dakin na fara fito da simintin dake dakin tabbas buhun siminti ba karamin nauyine dashi ba a yayin dana dakko na farko dakyar na iya fitowa dashi waje koda ummey tazo wucewa ta kusa dani tare da anti zainab sai Allah ya jarabceni ta hanyar taka wani dutse bansan lokacin da wannan simintin yaje kasba koda kurar wannan simintin ya dan budesu cikin yanayin wasa ummey tace “kash dadina da yaran zamani sun fiye gaggawa kasan karfinka baikai ba taya zaka dauki wannan simintin gashi har kana neman batamu da kura. Koda na dago kai na kalleta sai nayi dariya hade da cewar zan ramane yarinya tun daga wannan lokacin sai wasa ya fara shiga tsakanina da ummey. => 2 haka naita nazarin hanyar da zata haifar da wasa a tsakanina da ummey amma kwata- kwata na rasa. Kwatsam wata rana ina zaune a falon gidanmu ranar banje ko inaba haka na tasa set light da kallo. Karar bude kofa naji dubawar da zanyi sai kuwa nayi ido biyu da ummey bayan tayi sallama na amsa mata kanta tsaye ta wuce dakin anti zainab ko cikakken 3 minutes da shigarta ba aiba sai gata ta fito da zuwanta gareni kamar zata zauna a kusa dani sai tace “kaga dan komacan inason nai kallone. Kallonta nayi tun daga sama har kasa sannan nace ” ummey idan har na tashi rama wulakancin da kikemin to babu makawa sai kin koka dani. Murmushi naga tayi sannan tace “au da yayar taka kake sa’insa to dan Allah karka janye wannan kudurin naka mu fara daga yau. Saina jinjina kai sannan na tashi na bata wuri. A kalla an daki kimanin 1 week da faruwar haka kwatsam da musalin karfe 8 na dare nazo wucewa a kan hanyata ta komawa gida dayake layin mu daya da ummey a yayin da nazo dai-dai kofar gidan su ummey sai kuwa muyi ido biyu da juna a yayin da take tsaye da wasu samari biyu a matsayinta na wadda nake so kokuma ince wadda nake kauna ko kadan ban waji ji haushin kasancewarta a tare da wadannan mutanan ba domin duk mai kaunar abunda nake kauna shima masoyinane amma sai nayi amfani da wannan damar dan rama abunda tayimin da isata gida ba inda naci burki sai a dakina wasu tsofaffin magungunan da wani doctor ya taba rubutamin na dakko kati biyu wadan da nima kaina na manta adadin dadewarsu a wajena cikin yanayin kwarin guiwa na fito daga gida da zuwana inda suke nai sallama kamar yadda addinin musulunci ya tanadar mana cikin yanayin sakin fuska na mika musu hannu mu gaisa. Haka nasa hannuna a aljihu na dakko wannan maganin koda na kalli ummey sai nace “ummey dama dazune anti zainab ta aikoni wajanki domin na karbar mata sakon data baki, sai kuma ayi rashin sa’a a wannan lokacin bakyajin dadi sakamakon gudawar da take damunki hakane yasa ban samu damar ganinki ba sakamakon a wannan lokacin kina toilet saboda gudawar ta matsa miki shine abbanki ko kuma ince abbanmu ya aikeni domin na siyo miki wannan maganin saboda yasan bakya shiri da allura. Nanfa ummey tamin wani kallo cikin yanayin bacin rai tace ” kaga karka sake yimin irin wannan. In banda tsabar wulakanci yaushene na kamu da wata rashin lafiya balle ayi batun gudawa ina gudawarne zan dauki tsawon wannan lokacin a waje. Koda naga alamun bazata karbi maganin ba kaina tsaye nashiga gidansu. Saidai kuma na dauki tsawan lokaci rabona da shiga gidan da shigata sai kuwa nayi kacibis da mahaifinta a harabar gidan bayan mun gaisa cikin yanayin sakin fuska yace “yau kuma kaine a gidan ai na dauka ka manta damune sai nayi dariya nace ” abba ai ba yadda za’ai na manta daku nima kaina nasan ban kyautaba yanzu nazo wucewa saina hadu da ummey anan kofar gida shine take cewa ai bani da mutunci kullun zataje gidanmu ammani banason zuwa gidansu hakane yasa na shigo domin na wanke wannan laifin a idonta sai yai dariya hade da cewar aikon ta kyauta. Haka na karasa ciki na gaisa da mahaifiyarta sannan na fito koda na dawo gareta sai nace “ummey abba yace kije yanason ganinki ba yadda ta iya haka tayi bankwana dasu ranta a bace. Bayan sun tafi sai nace ” ummey ai bai kamata ki nuna bacin ranki akan wannan kankanin wulakancin ba domin tun farko ke kice muzuba mugani. Sai ta jinjina kai hade da cewa “hakika kayimin wulakancin da yai matukar konamin rai amma kasani muddun ina raye babu abunda zai hanani rama wannan cin mutuncin da kaimin a wannan lokacin saida mu dauki kimanin wata daya ba tare da mun sake yima juna maganaba kwatsam wata rana zamu garin kaduna daurin auran wani kanin mahaifiyata mutuncin da yake tsakanin gidanmu danasu ummey ne yasa ummey ta bimu wannan bikin ashe raban za’a samu dai-daito tsakanina da ummey ne muna cikin tafiya sai nace ” anti karfa ki manta da kudin da kice zaki cikamin domin siyan wayar da nake bukata budar bakinta sai tace “kaga karfa ka takuramin tunda nace zan baka kawai ka zuba ido mana da isarmu kuwa haka na sake tambayarta batun kudin domin na kagu naga iPhone 6 ta shiga hannuna nan take ta hauni da masifa hade da cewar na bari saimun koma gida ganin hakane yasa ummey ta nuna tausayawarta a gareni koda ta kalleni sai tace “nawane cikon kudin da zata baka cikin yanayin bacin rai nace 8 thousands ne sai ummey tayi dariya sannan tace “indai dan 8 thousands ne to karka damu ni zan cikama da yake akwai wani shagon saida wayoyin dana sani a kasuwar bacci dake kaduna haka mutafi tare da isarmu bayan anyi cinikin waya iPhone 6 akan kudi naira dubu 67 sai kuwa ummey ta karbi kudin dake hannuna ta cika naira 8,000 sannan ta mikawa mai waya nannefa na gane cewar ashe ummey gadar zare ta shiryamin domin daukar fansar wulakancin da nai mata a baya domin kuwa sunanta naji tace asa a resit din haka na zuba ido a kammala komai a gaban idona sannan ta kalleni tace ” nagode yayana kasiyamin waya. Cikin yanayin nadama nace dan Allah ummey kiyi hakuri nasan nayi kuskure amma daga yau babu yadda za’ai na sake aikatamiki abunda zai haifar da bacin rai a tattare dake murmushi naga tayi sannan tace da zakayi hakuri ka cire wannan wayar daga zuciyarka zaifiyema komai dadi domin wahalar da kanka kawai kakeyi koda taga alamun zan takura mata nan take ta damka wayar a hannun wannan mutumin tace “malan ka’ajemin wayarnan na tsawon wata biyu sannan ta damkamai 2 thousands a matsayin kudin ajiyarshi inaji ina gani haka nayi bankwana da kudina ba tare da cikon burina ba. Bama wannanne yafi damuna ba illa rashin sanin hanyar da zan bullo mata dan ganin sakon zuciyata ya isa gareta abunda nake nufi shine nasamu soyayyarta. Amma duk da haka ban ja da baya ba haka muci gaba da yima junanmu wulakanci mai kama da rashin mutunci. => 3 Haka ummey taita min dariya domin tasan dolene raina ya baci ganin yadda mu koma gida ba tare da ummey ta karbi wayar bane yasa na tabbatar da cewar eh lallai babu yadda za’ai ta bani wannan wayar balle ayi batun dawowar kudina. Duk da irin wannan ta addancin da ummey taimin baisa taja da baya wurin ci gaba da yimin abunda taga dama ba bazan taba mantawa da wata ranar monday/ litinin ba ranar mahaifiyata da abbana basanan sunyi wata tafiya garin bauchi haka na dawo gida a yunwace koda na duba inda asaba ajemin abinci banga komaiba face emptying plate haka na shiga dakin anti zainab cikin yanayin damuwa nace “wai anti baki girka mana komai bane? Budar bakinta sai tace ni baiwarkace da zan zauna naima girki. Cikin yanayin sakin fuska nace ” ammafa zainab baki da mutunci. Wani kallon hadarin kaji taimin hade da cewar a ina kuma ka manta antin da zaka kira sunana kaitsaye ba girmamawa? Budar bakina sai nace “ai idan har kiga yara suna kiran yayarsu da anti to ki tabbata tana kyautata musune ammake ko kadan wannan sunan bai kamaceki ba domin bana samun wannan kyautatawar daga gareki. Koda naga alamun ranta ya baci sai nace ” haba antita dawasafa nake miki domin nasan bazaki rasa yan kudin da zaki baniba domin naje na samu dan abunda zanci. Dakyar na shawo kanta ta dauki two hundred #200 ta bani domin naje naci abinci ba yadda na iya haka na karbi wannan kudin majalissarmu na nufa domin nasan acan bazan rasa abunda zan siya ba da isata ko zama banyi ba nace da maryam mai shin kafa ta kawomin ta dari hade da coke mai sanyi da kawowarta ko faraci banyi ba saiga musta bangis abokina kenan yazo gareni a gaggauce wayar dake hannunshi naga ya mikomin hade da cewar wata yarinyace mai suna aisha takeson magana dakai haka na tashi na koma lungu domin jin ko wacece ban saniba ashe tun daga nesa ummey taga lokacin da’a kawomin wannan abincin da zuwanta ta dauki wannan abincin hade da coke din ta damkawa almajirai tace “ku karbi sadaka. Tabbas bayanin da naji daga bakin aisha wadda nai waya da ita kenan ba kadan ya jefani a rudani ba. Haka na dawo wurin abincina kaina a daure. Koda na duba naga ba abinci kuma ba coke sai na kalli bangi hade da sauran abokaina nace ” ina kuma abincin nawa? Budar bakin bangis sai yace “gashican a hannun almajirai cikin yanayin fusata na daka musu tsawa! Cikin yanayin dariya nuhu ya dafa kafadata yace ” kaga abokina karkaga laifinsu domin ummey ce ta dauka da hannunta ta basu. Saina jinjina kai nace “ammafa wannan yarinyar tafini wulakanci. Haka bangis ya karbarmin wani abincin daga wajan maryam. Inacin abincin ina tunanin maganar da aisha ta fadamin bayan naba bangis wayar sannan nace ” dan Allah ya tabbata yayi saving din numbar domin ina bukatar sake magana da ita bayan kwana ukku da faruwar haka musalin karfe 5:00pm ina zaune a kofar gida saiga ummey tazo gareni kaida ganin fuskarta kasan akwai damuwa a tattare da ita kusa dani ta zauna koda naga idanuwanta duk sun canza daga yadda na saba ganinsu sai nace “amma ummey ban taba ganinki a cikin irin wannan yanayin ba ko zaki iya sanar dani abunda yake faruwa? sai tace “tabbas na aikatama laifi mafi muni domin abbana ya fasa wannan wayar daka siya a garin kaduna. Kuma wallahi ban hanaka wayar domin ta zama mallakinaba kawai na hanakane domin na gane shin soyayyar da kakemin gaskiyace ko kuma wasa kakeyi domin tun daga lokacin daka fara aikomin da wadannan sakonnin na gane cewar ba kowa bane yake aikomina da wannan sakon illah kai cikin yanayin mamaki nace amma ummey taya ai har kisan da cewar nine nake aikomiki da wadannan sakonnin? => 4 Ummey tace wata ranar juma’a lokacin ina zaune tare da zainab a falon gidanku koda zainab taji karar horn din motar abbanku cikin yanayin tsoro naga ta afka dakinka da sauri ganin hakane yasa nabi bayanta dan jin abunda yake faruwa cikin yanayin mamaki nace amma zainab lafiya kuwa naga kin shigo nan a tsorace? Budar bakinta sai tace “wallahi tun dazu abba ya kirani a waya yace na dakkomai wasu takaddu a durowarshi kuma shaf na manta nasan idan yai ido biyu dani sai nasha fada da shigowar abbanku bayan yai sallama sai ya fara kiran zainab amma zainab sai tai shiru ba tare data amsaba Allah cikin ikonsa sai kira ya shigo wayarta cikin yanayin furgici ta jefar da wayar haka wayar tai watsa-watsa ba tare da sanin wa yake kiranta ba ashe tuni karar wayar ta isa kunnan abbanku a wannan ranar ba kadan zainab tasha fada ba bayan abbanku ko kuma ince abbanmu ya dauki abunda zai dauka ya fita sai zainab tace naje na dakko mata wayarta a tsakar dakinka naga wayar batirin hade da marfin kuma a karkashin gadonka na dakkosu amma Allah baisa naga naga layin ba wani littafin geography na gani a kasa koda na dagashi sai naga layin MTN ya fado kasa kasancewar bansan layin da take amfani dashi bane yasa na dorashi a wayar tata da yake wayar irin karamar nokiyar nance ina kunnata ta kawo bayan na damka wayar a hannunta sai tayi kokarin duba wannan numbar da’a kirata kafin ta jefar da wayar kenan amma bataga numbar kowaba face numbata koda ta shiga bangaran message sai taga sakonnin da ba ita ta turasuba sai ta kalleni tace “ummey wannan ai ba layina bane kuma ni ai airtel nake amfani dashi ba mtn ba duk yadda ai wannan layin brother dinane domin na tabbata wadannan sakonnin babu wanda zai turasu face shi. dariya naga tayi a yayin data kalleni sannan tace ummey yashe ku fara soyayya cikin yanayin mamaki na karbi wayar na duba hakane ya tabbatarmin da cewar kaine kake aikomin da wadannan sakonnin a wannan ranarne na roki zainab akan karta nuna wata alamar da zatasa kagane mun duba wannan layin naka. Sannan na bukaceta data kauda kanta akan duk kan wani abunda zai faru a tsakanina da kai. Haka naita yima abubuwan da zasusa ranka ya baci amma domin auna mizanin soyayyar da kakeyimin a zuciyarka wanda hakan ta tabbatarmin da cewar lallai kana matukar sona a karshe saina yanke shawarar komawa kaduna domin karboma wayarka haka na tafi ba tare da kowa ya saniba domin ko mahaifiyatama bata sani ba balle abbana sai a samu akasi a yayin dana isa garin kaduna ba inda na tsaya sai a shagon damu sayi wayar akasin da’a samu shine ban samu shagon a bude ba domin a rufe na sameshi da yake ya rubuta numbar wayarshi a gaban shagon sai nayi kokarin kiranshi koda ya daga bayan mun gaisa hade da sanar dashi dalilin kiranshi a wannan lokacin sai yace to gaskiya yanzu haka yana zaria daurin auran wani abokinshi haka na zauna zaman jiranshi har ya dawo ba kuma shi ya dawo ba sai musalin karfe 5 ban saniba ashe abbana ranshi yayi matukar baci sakamon rashin ganina in takaicema dai bani na dawo gidaba sai musalin karfe 8 na dare da shigata falo sai nai kacibus da abbana cikin yanayin damuwa hade da bacin rai yace “ummey daga ina kike? Sai nai shiru ba tare dana bashi amsaba domin na tabbata idan na sanar dashi inda naje raina ba karamin baci zaiyi ba gudun kar raina ya bacine yasa naimai karyar zainab na raka zaria. Jinai ya daukeni da mari hade da cewa munafukar banza kawai ni zaki rainama hankali a kalla na kira wayarki yafi a kirga amma sam bata shiga. Muryata tana rawa/ bari. Nace “abba babu cajine. Jinai ya dakamin tsawa hade da cewa ina wayar take? Cikin rawar jiki nasa hannuna a aljihu domin dakko wayar sai a samu akasi na dakko wannan iPhone din koda abbana yaga iPhone a tattare dani sai yace ” ummey a ina kuma ki samo wannan wayar? Cikin yanayin kidimewa nace “au! Abba ba ita bace wannan. Wani kalar kallo naga abbana yamin hade da cewar ummey a sanina wannan wayar mai matukar tsadace kamar yadda nasan bana baki kudin da zasu sa har ki sayi wannan wayar haka na tabbata bazaki samu kudin wannan wayar daga wajan mahaifiyar kiba dan haka ki gaggauta sanar dani yadda ai ki samu kudin da kisayi wannan wayar. Cikin yanayin kuka nace ” wallahi abba ajiyarta abani. Ban tashi auneba sai jinai ya bugata da kasa sannan ya nunani da yatsansa yace ko wayar uban waye ya sake ganinta a tattare dani to babu makawa sai ya fasata kuma yaci mutuncina. Bayan ta gama bani wannan labarin sannan ta kalleni hade da cewa bansan wane irin hakuri zan bakaba a dalilin faruwar wannan al’amarin. Sai nayi murmushi nace “haba kefa tamkar kanwata na daukeki dan haka zan iya sadaukar miki da koma menene. Sai dai kuma ummey akwai wani bakon al’amari wanda ya jefa zuciyata a rudani ko kuma ince sarkakiya wanda nake ganin muddun hakan ya kasance gaskiya to zuciyata zata iya cutuwa. Cikin gaggawa ummey tace ” yayana dan Allah kayi gaggawar sanar dani wannan sarkakiyar. Sai nace “ummey akwai wata yarinya kokuma ince budurwa mai suna aisha wadda ta kira wayar abokina bangis da bukatar magana dani bayan bangis ya kawomin wayar maganar da naji daga bakinta ba kadan ta girgizani ba. Bayan mun gaisa sai tace ” kai dan uwanane dan haka bazan taba bari ka cutar da zuciyarka wajan fadawa soyayya da wadda aure bazai taba kasantuwa a tsakaninka da ita ba dan haka ina mai tabbatarma da cewar har abada babu aure a tsakaninka da wadda kake shirin fadawa soyayya da ita wato ummey domin addinin musulunci yayi hani da hakan na bude baki zanyi magana kenan sai ta yanke wayar. Saina kalli ummey nace “babban abunda yake dauremin kai shine taya ai tasan akwai soyayyarki a cikin zuciyata kafin na bayyanata a gareki kuma ta wace hanya ta samu numbar abokina bangis sarkakiyar da nake ciki itace shin dagaskene babu aure a tsakanina dake? Sai ummey ta girgiza kai hade da cewa meyasa kake kokarin haifarma zuciyarka da damuwa kafi kowa sanin cewar babu wata dangantakar da zatakawo batun hana aure a tsakanina da kai dan haka kamar yadda na dauki wannan maganar a matsayin shirme zanso kaima kayi kokarin daukarta a matsayin hakan. =>5 Tun daga wannan ranar komai ya sauya a tsakanina da ummey lokaci daya ta janye kanta dangane da batun yawo tare da anti zainab sai ya zamto ba kowane abokin rakiyartaba face ni tun ina dan nuna jin kunyar jerawa tare da ummey a matsayina na bakon soyayya rannan kuwa sai ummey ta kalleni tayi murmushi hade da cewa na fahimci kana matukar jin kunyar jerawa tare dani musamman a yayin dana bukaci rakiyarka a gareni to amma ni a ganina hakan ba wani abun kunya bane a matsayinmu na masoyan juna kuma ta wani bangaran ni tamkar kanwarka nake domin gidanmu da naku ya zama tamkar daya duba da yadda iyayanmu suke mutunta junansu wanda hakan yasa nake aikata duk wani abunda naga dama a gidanku ba tare da ahalinka sun nuna wata damuwa ba abun yana matukar bani haushi ganin yadda kai baka damu da zuwa gidanmu ba kamar yadda na maida gidanku tamkar gidanmu zanso kaima kayi kokarin daukar gidanmu tamkar gidanku kamar yadda nakeson ka cire duk wata kunyar da take tsakanina da kai haka dai soyayyarmu taita bayyanuwa a idon kowa ko wace safiya mukan turawa junanmu da sakon barka da safiya ta waya idan dare yayi bama taba yin bacci ba tare da munyi waya da juna ba. Kwatsam wata rana muna cikin fira nida ummey da musalin karfe 8:30pm sai calling.. Ya shigo wayata. koda naga bakuwar numbace ban wani bata lokaciba cikin gaggawa na daga kiran muryar mace naji ayayin da tai sallama a gareni. hakane yasa na gane ko wacece domin ba wata bace illa aisha. budar bakinta sai tace wato har yanzu kananan akan bakanka kenan to bari kaji wallahi wahalar da kanka kawai kakeyi domin ummey bazata taba zama matarkaba. Cikin yanayin bacin rai nace kinga wallahi muddun nayi ido biyu dake wallahi ina mai tabbatar miki da cewar sai kinyi matukar raina kanki. Dariya naji tayi sannan tace “ai bansan zaka iya aikata hakanba domin yanzu na wuce ta kusa daku nan take na sauke wayar daga kunnena na fara waige-waige domin tabbatar da maganarta koda ummey taga ina waige- waige sai tace ” yayana lafiya kuwa, me kuma ya faru? cikin yanayin mamaki nace ummey kinga wata ta wuce tanan yanzu sai ta danyi shiru na dan wani lokaci sannan tace kwarai kuwa akwai wadda ta wuce ta nan kusan tsayinmu daya da ita tana sanye da wasu kaya ruwan madara sanye da wani farin gyale. Sannan ta kalleni tace “wai me yake faruwa? Bayan na sanar da ita duk abunda ta fadamin driya naga ummey tayi sannan tace ” ko wacece wannan to babu abunda zata karu dashi face bakin ciki hade da takaici. Haka mu dauki wannan maganar a matsayin shirme. amma duk da hakan zuciyata bata gaza wurin afkawa cikin katafaran rudanin yadda ai har wannan addababbiyar yarinyar ta samu numbata ba. maimakon mutsaya muyi dogon bincike a kanmu kawai sai muci gaba da soyayyarmu ashe maganar aisha tana kama da gaskiya koda a tsakanin iyayan ummey da iyayena mahaifiyatace ta fara gane cewar akwai soyayya a tsakanina da ummey. Cikin dare musalin karfe 11:00pm mahaifiyata ta shigo dakina. koda ta tasheni daga bacci cikin yanayin mamaki nace “umma lafiya kuwa? Sai ta jinjina kai tace ” lafiya kalau nazo garekane da wata bukata a matsayina na mahaifiyarka. Cikin gaggawa nace “umma ki fadi duk wata bukatarki nayi miki alkawarin zan biya miki ita domin nasan bazaki taba tunkarata da bukatar da zatafi karfina ba. Budar bakin mahaifiyata sai tace ” meye alakarka da ummey? Nan take na sumkuyar da kaina kas, na dauka wannan ita kadaice bukatarta a gareni. cikin kwarin guiwa nace “umma ba wani abu bane a tsakanina da ummey illa soyayya. Sai tace ” to indai har kanajin maganata a matsayina na mahaifiyarka zanso daga yau ka dakatar da wannan soyayyar taku kuma karka bari ta fahimci cewar nice makasudin faruwar hakan balle wasu daban kai ko yayarka zainab banason tasan da wannan maganar domin banason hakan yai sular daina shigowar ummey gidannan. Cikin yanayin rudani nace “to amma umma ni a sanina mafi yawanci iyaye sukan hana yayansu auran wadda sukesone saboda wasu dalilai ko wani dalili. Amma sai gashi ke da kanki kin nemi na guji ummey ba tare da kin sanar dani dalilin hakanba kuma ta wani bangaran sai naga kamar ummey bata aikata wani laifin da zaisa ki nemi rabani da itaba saboda naga alamun kina matukar kaunarta wanda hakan yasa bakyason wani dalilin da zaisa ta daina shigowa gidannan. Sai na kalleta nace ” dan Allah umma ki sanar dani abun daya faru? Sai ta girgiza kai hade da cewar na riga na daukar wa mahaifinka da iyayan ummey alkawarin bazan taba sanarma kowa wannan sirrin ba dan haka kawai kayi hakuri ka biyamin wannan bukatar tawa ba tare da kaji komai ba. Nan take hawaye ya kwaranyo daga idanuna. Cikin yanayin kuka nace “umma karkisa zuciyata ta fara zarginki da aikata ba daidai ba. Nan take tasa hannunta ta share hawayen dake fuskata. Hade da cewa ko kusa karka taba barin zuciyarka ta zargeni da sabama ubangijinsa domin ban taba aikata fasikanci ba kamar yadda kake tunani. Sanannan ta tashi tayi waje ta barni cikin rudani. => 6 Haka na kwana cikin rudani hade da matsanancin tunani washe gari da sassafe saiga ummey ta shigo kamar yadda ta saba kanta tsaye ta shigo dakina a kwance nake amma idona biyu duk da cewar babu wani annuri a tattare dani haka na dan saki fuskata cikin yanayin sakin fuska nace “ummey kardai kice kinzo tashina baccine? Murmushi naga tayi sannan tace “amma ya ai kasan abun daya kawoni? Budar bakina sai nace ” ai saboda zukatanmu sun riga da sun zama dayane shine dalilin da yasa na fahimci haka. Sai tace “kaga malan tashi kazo muje kayi breakfast domin akwai inda nakeson ka rakani. Bayadda na iya haka na fita ba’a son rainaba domin ko kadan banason na batawa mahaifiyata ranta gudun kar ummey ta fahimci na fara ja da baya da itane yasa na fito. Bayan nayi brush haka na zauna a falo ina cin abinci ga kuma ummey ta zauna kusa dani tanamin irin kallon da masoya sukewa junansu mai kawar da kunci da bacin rai bayan na kammala saina fita tare da ita domin rakata inda take son zuwa bayan na dawo gida sai na fahimci ran mahaifiyata yayi matukar baci gaba daya saina rasa hanyar da zanbi danganin na ciwa mahaifiyata burinta ba tareda ummey ta fahimci komai ba duk da cewar nasan hakan ba abune mai yuwuwaba amma ko kadan zuciyata bata daina nazarin neman mafita ba. rana daya nayi duk wani shirina na tafiya garin jigawa amma sai dai kuma ina duba yiwuwar tafiyar da zanyi zata dauki dogon lokaci domin bana tunanin cewar zan dawo har sai lokacin da ummey tayi aure. Koda na sanar da iyayena batun tafiyata da kudurin bazan wuce sati daya ba. Sai suyimin fatan alkairi hade da sa albarka a gareni. Ummey har zubar da hawaye tayi a dalilin wannan tafiyar tawa inaji ina gani haka nayi bankwana da abar kaunata wadda ko tuntube batason taga nayi a yayin da muke tafiya tare da juna. Tafiya nake amma ina tunanin irin soyayyar da mukewa junanmu hade da tunanin halin da ummey zata tsunci kanta a yayin da taji shiru ban dawoba. Duk da irin wannan tunanin da zuciyata take ciki bai hanani tafiyaba badan komaiba sai dan cikawa mahaifiya burinta saboda kokadan banason mahaifiyata ta shiga damuwa a dalilina amma sai dai kuma a zuciyata ba jahar jigawa nake da kudurin zuwaba domin kuwa jahar kebbi ce a zuciyata. Musalin karfe 1 na dare na sauka a kebbi state. Da saukata nayi calling din abokina faruq wanda na hadu dashi a social network wato facebook kenan cikin kankanin lokaci faruq yazo gareni cikin girmamawa ya saukeni a gidansu a wannan ranar ne na sanar da faruq duk abun daya faru dani hade da makasudin barowata gida. Daga karshe kuma sai nace “faruq bana muradin komawa gida har sai lokacin da ummey tai aure shiru naga yayi na dan wani lokaci zuwacan ya kalleni cikin tausayawa yace ” tabbas kayi matukar burgeni tunda har ka zabi farantawa mahaifiyarka fiye da son zuciyarka dan haka zakaci gaba da zama dani har zuwa lokacin da wannan burin naka zai cika. Duk da cewar na nisanta da ummey amma hakan baisa mun fasa yin waya da junaba domin kullunne sai ummey tayi calling dina hade da aikomin da sakon text message. Nanfa na rasa hanyar da zanbi dan ganin hakan ta daina faruwa kwanana biyar da zuwa kebbi sai wata mota (kano line) tai accident/ hadari a yayin da take gaf da fita daga cikin garin kebbi zuwa jahar kano abun takaici duk jama’ar ciki basu rayu ba domin kuwa konewa tai gaba daya babu wanda zaka iya shaida fuskarshi. Sai nayi amfani da wannan damar dan ganin na batar da rayuwata a idon ummey ta wani bangaran kuma ina tunanin irin hawayan da iyayena zasu zubar a yayin da sakon mutuwata ya isa kunnansu amma naji hausawa suna cewar da ruwan ciki akanja na rijiya, domin kuwa sai an fuskanci wani bacin ran sannan ake samun wani farin cikin. Bayan mun shira komai ni da abokina faruq saina damka wayata a hannunshi a gaban idona ya damka wayar a hannun daya daga cikin jami’an yan sandan dake wannan wajan hade da cewa “yallabai ina tunanin wannan wayar daya daga cikin mutanan da wannan hadarin ya auku dasune. Ta wannan wayarne sakon barina duniya ya isa kunnuwan iyayena saboda wannan ita kadaice hanyar da zatasa ummey ta auri wani ba tare data fahimci komai ba. => 7 Duk da cewar abokina faruq yasan da cewar ina raye kuma tare muyi wannan shirin. Hakan bai hanashi zuwa sadakar ukkuna jahar kano ba. A ranar daya dawo jahar kebbine ya sanar dani maganar data kidimani. Zama yai a kusa dani ya kalleni yace “abokina abunda mu aikata sam bai dace ba domin saura kiris na bayyana gaskiyar abun daya faru. Amanar da take tsakanina da kaice tasa na kasa aikata hakan bayadda na iya haka na baro jahar kano hankalina a tashe sakamakon mawuyacin halin dana tsunci ummey a ciki. Hawaye nagani a idonshi a yayin daya dago kanshi ya kalleni. Budar bakinshi sai yace ” tabbas ummey tana matsanancin sonka saboda tun daga lokacin da sakon mutuwarka ya isa kunnanta ta yanke jiki ta fadi sai da ta dauki dogon lokaci kafin ta farfado daga dogon suman da tayi kuma ba’anan al’amarin ya tsaya ba domin har yanzu bata iya furta kalmar komai haka take zaune ba umm ba a’a dan haka shawarar da zan baka a matayina na abokinka itace “kawai ka komaga ummey domin hakanne zai kawo sassauci ga rayuwarta. Cikin yanayin damuwa na kalli faruq nace ” tabbas nasan ko kadan ban kyautaba amma inason kasan da cewar babu yadda za’ai naso ganin bacin ran mahaifiyata kuma a dalilina duk da cewar taki sanar dani dalilinta na rabani da ummey hakan bazai taba sawa na kasa cika mata burin taba kuma inason kasan da cewar duk inda tsanani yake to ka tabbata sassauci yana nan zuwa dan haka ummey zata samu sauki domin Allah maji rokon bayinsane kimanin shekarata daya da wata takwas a jahar kebbi tare da abokina faruq ba tare da ahalina sunsan da cewar ina raye ba amma saidai har kawo wannan lokacin ummey batayi aure ba domin bata kula kowa kwatsam wata rana abokina faruq yazomin da wani sabon labari wanda yai matukar sani farinciki. A yayin dana sake turashi jahar kano domin ya jiyomin ko kuma ince ya ganomin abun da yake faruwa a tattare da ahalina da kuma abar kaunata wato ummey sai yazomin da labarin ansama ummey rana tare da yayata zainab wanda za’ayi bikin nasu 04/07/2017 tabbas ba kadan naji dadin wannan albishirin ba. sai dai kuma na tabbata ummey zatayi auranne ba’a son ranta ba jahar kebbi sai da ta kasance tamkar mahaifata domin babu abundana rasa a tattare da abokina faruq hakane yasa faruq yai matukar damuwa a yayin da nake shirin komawa gida sati biyu da bikin anti zainab hade da ummey na nufi jahar kano saidai kuma na tabbata saisun shiga rudani a yayin da suyi ido biyu dani kuma dolene su nemi jin yadda ai har hakan ta faru dani tun a mota nake nazarin hanyar da zanbi amma ina gaba daya sai kaina ya kulle. => 8 harna shiga cikin garin kano zuciyata bata daina sake-saken amsar da zanba iyayena ba musamman idan su nemi sanin yadda ai haka ta faru dani tare mu sauka mota da wata baiwar Allah harna juya zan tafi. Sai naji tace “dan Allah malan dan tsaya mana. Koda ta karaso gareni sai tace “dan Allah malan ni bakuwace a wannan garin kuma gashi dare yayi shine nakeson ka taimakamin da aron wayarka domin na kira wadda nazo wajan nata saboda wayar tawa tun a mota cajinta ya kare. Cikin yanayin tausayawa na miki mata wayar. Haka taita trying din numbar amma bata samu shigaba ganin hakane yasa duk tabi ta kidime. Wani kallon maraici naga taimin sannan ta miko min wayar. Cikin yanayin sakin fuska nace ” hakika na fahimci damuwar da kike tattare da ita amma idan bazaki damuba mezai hana na kaiki gidanmu ki kwana kinga idan gari ya waye saiki kirata. Cikin sanyin murya tace “to shikenan nagode. Tun kafin mu karasa gidan sai na nemi sanin sunanta hade da garin data fito. Cewa tai sunanta AISHA kuma ita yar asalin jahar tarabace. Batun dalilin zuwanta jahar kano kuma labarine mai matukar tsayi hade da ban tausayi amma a halin yanzu ba abunda nake bukata face abincin da zan ba cikina saboda ina matukar jin yunwa dan haka idan Allah yasa mun wayi gari lafiya to zan baka labarina gaba daya domin bazan ragema ko daya ba. Sai nai murmushi sannan muci gaba da tafiya. Gaba daya harna manta da kalubalan dake gabana na tunanin yadda iyayena zasuyi mamakin ganina a raye. Na tura kofa kenan saina tuna jinai kirjina yai wata irin bugawa amma ko kadan ban bari aisha ta fahimci komai a tattare dani ba da shigarmu koda mahaifiyata tai ido biyu dani a yayin da nai sallama sai ji nai ta zafga salati sannan ta mike a tsorace. Cikin yanayin rudani tace ” waye wannan Allah yasa dai ba mafarki nakeyi ba. Saboda jin dadin ganin mahaifiyata da nai a wannan lokacin nan take naji hawaye ya zubomin. Budar bakina sai nace “umma tabbas dankine ya dawo gareki domin ba mutuwa nai ba kamar yadda kuke tunani. bani da wani burin daya wuce na faranta miki rai hakane dalilin da yasa nabar gida domin cika miki burin ki. Cikin yanayin mamaki tace “wane irin burine kakeson cikamin wanda har zaisa kabar gida kasan irin kunar da muji a yayin damu samu labarin cewar kabar duniya? Haka muita zubar da hawayanmu akanka bamu saniba ashe ba sonmu kakeyiba kawai zubar hawayanmu kake son gani. Nan take na durkusa har kasa inamai kukan bakinciki haka na dago kaina na kalli mahaifiyata nace ” dan Allah umma ki yafemin nasan na aikata kuskure kawai na aikata hakanne domin cika miki burinki ta buda baki zatai magana sai nace “a’a umma nasan maganar da zakimin bazata wuce neman sanin burin da nakeson cika miki ba saboda nasan kin manta da alfarmar daki nema a gareni ta batun rabuwa da ummey wadda nake matukar sonta a zuciyata to amma sai dai son da nake miki ya zarce nata. Koda mahaifiyata taji wannan batun nan take ta rike baki cikin yanayin kuka tace ” tabbas na cuceka kuma bana tunanin Allah zai yafemin a kan wannan abun daya faru. Nan take na mike tsaye nace “haba umma kefa mahaifiyatace wadda take da ikon sani duk wani abun da taga dama muddun bai sabawa addinin musulunci ba. Kuma ina da tabbacin surrin da kike boyemin bai sabawa addinin musulunci ba dan haka umma zanso ki manta da wannan al’amarin, tunda Allah yasa ummey tayi aure bani da wani farin cikin daya wuce haka. Sai mahaifiyata ta shafa kaina tace ” Allah yaima albarka. Koda na kalli aisha sai nace “au dan Allah aisha kiyi hakuri alhinin da muke cikine yasa na shafa’a dake. Murmushi naga tayi sannan tace “kar kaji komai domin nima nayi matukar tausaya muku. Bayan an bata dakin da zata kwanta sai na dauki abinci na kai mata har dakin da kaina bayan na fito sai nace ” umma wai ina abba ya shigane naga tun da nazo ban ganshi ba sai tace “aikon abbanka yana jahar katsina yau kwananshi biyu a can amma gobe nakesa ran dawowarshi haka na zauna kusa da ummata ina cin abinci sai tace ” yaune zan bayyanama sirrin dana dade ina boyewa a zuciyata badan komai ba sai dan ina da yakinin bazaka sanarma kowa ba saboda na yadda da kai kuma bani da kowa yanzu a gabana wanda ya wuce kai tunda yayarka zainab ta riga da tayi aure. Haka na gyara zama dan jin sirrin da mahaifiyata ta dade tana boyewa a zuciyarta. Ma haifiyata tace “sanin kankane mahaifin ummey abokin mahaifin kane ita kuma mahaifiyarta kawatace. Hakane yasa mu kasance tamkar yan uwan juna sai dai kuma tun daga lokacin da Allah yasa suyi aure har kawo yanzu basu taba hai huwa ba. Cikin yanayin mamaki nace ” to amma umma ita kuma ummey fa? Sai tace “ummey yarsuce amma ba wadda su haifa da cikinsu ba. Kwatsam wata rana sai Allah yaba mahaifiyar ummey ciki a dai-dai lokacin da nima nake dauke da juna biyu tsakar dare musalin karfe 2 lokacin kowa yai bacci sai haihuwa tazomin haihuwata kenan sai abokin mahaifinka yazo mana da batun hajiya ameena ta haihu amma dan baizo da raiba ganin damuwar da suke cikine na rashin samun haihuwa yasa mu dauki daya daga cikin yayan damu haifa mu sadauka musu domin yaya biyu na haifa a wannan lokacin ko cikakken wata daya da faruwar hakan ba aiba sai Allah ya dauke ran hafsat. Cikin yanayin mamaki nace ” umma kina nufin yaya biyu ki haifa a wannan lokacin kuma hafsat itace abokiyar haihuwar ummey sai ta jinjina kai tace kwarai kuwa. Sannan tace “wannan shine dalilin da yasa na shiga tsakaninka da ummey domin ita kanwarkace ta jini kuma tabbas kayi matukar dubara gami da hangen nesa da har ka nisancemu na tsawon shekara biyu da wasu watanni dan haka zan kasance mai yima addu’ar samun nasarar duniya da lahira. A wannan ranar haka na kwana cikin farin ciki hade da kwanciyar hankali bayan gari ya waye sai nai alwallah na nufi masallaci tabbas al’amarin yai matukar dauremin kai ganin yadda al’umma suke darewa ayayin da suyi ido biyu dani tsamo-tsamo a masallaci ganin hakane yasa na tuna da batun mutuwata. Nan take na mike tsaya nace “ko kadan banzo masallacinnan domin na tsoratar daku ba amma nasan dolene ku shiga rudani sakamakon ganina da kuyi a raye. Tabbas hadarin motane ya auku damu a yayin da nake kan hanyata ta dawowa gida kano daga jahar kebbi Allah cikin ikonsa motar tanayin karo sai kofar da nake bangaranta ta bude can na fada cikin wasu ita tuwa wanda hakan yai sanadin buguwar kaina tun kafin mutane su karaso garemu tuni nayi nisa haka naita tafiya ciki daji banma san inda nake dosa ba domin tuni hankalina ya gushe ban da wayata ai amfani wajan sanar da iyayena abun daya faru damu domin a wurin dana fado na barta haka na kwashe tsawon shekara biyu ba’a hayyacina ba. A yayin da hankalina ya dawo gareni ba abun dana fara tunawa dashi face iyayena. Wannan shine abun daya faru dani dan haka kar kuji tsorona domin nima dan adam ne tankarku. Haka su jajantamin cikin yanayin tausayawa. Bayan na koma gida nine har wajan karfe 9 banga fitowar aisha ba hakane yasa na shiga dakin domin dubawa ganin halin da aisha take cikine yai matukar kidimani wanda hakan yasa kafafuwana su kasa daukata in takaice muku dai bansan lokacin dana zauna kasa ba ina mai zafga salati domin ban samu aisha a raye ba. => 9 Hakika a lokacin da nayi ido biyu da gawar aisha ba kadan na shiga rudaniba. Koda jami’an tsaro su gane cewar bamu da hannu wajan mutuwar aisha sai su sallamemu ba tare da an wahalar damu ba. sakamakon rashin sanin iyayanta da kuma dangintane yasa ayi jana’idarta a gidanmu dawowarmu daga makabarta kenan sai nai kacibus da ummey a kofar gidanmu. Duk da cewar ummey tayi aure haka ta tunkaroni fuskarta cike da mamaki da zuwanta ta rike hannuna sannan ta fashe da kuka tace “yayana wallahi ji nake kamar mafarki nakeyi. Dan Allah dagaske kai dinne kuma taya ai har hakan ta faru? Cikin yanayin tausayawa nace “ummey zan sanar dake komai domin bazan taba barinki a cikin rudani ba amma ki tabbata zaki daukarmin alkawarin bazaki taba nunawa kowa kinsan wannan sirrin ba domin ko iyayankima bana bukatar susan kinji wannan sirrin balle wasu daban. amatsayinta na kanwata ta jini haka nasa hannuna na share hawayan dake fuskarta sannan nace ” amma wannan sirrin bazai yuwu na sanar dake a yanzuba saboda gudun sa’idon al’umma, dan haka ki bari sai Allah ya kaimu zuwa gobe. Cikin yanayin mamaki ummey ta dago kanta ta kalleni. Tace “wane sa’ido kuma kake gudu karfa ka manta ni takace har abada. Budar bakina sai nace “ummey koda ace bakiyi aureba to babu yadda za’ai ki taba kasancewa matata. Nan take naga wani sabon hawaye ya faso daga idanun ummey cikin yanayin kuka tace ” idan auran da nayine zaisa kayi tunanin kin kasancewata a matsayin mallakinka to kasa a ranka wannan auran nawa tamkar na yanke igiyarshine. Sannan ta juya ta tafi tana kuka duk al’ummar dake wannan wurin gaba daya sai idonsu yayo kanmu. haka na shiga gida cikin ta’ajibi. Kwatsam cikin dare musalin 10:30pm na dare ina kwance a dakina lokacin bamu kaiga rufe gidaba sai jinai an tasheni daga bacci juyowar da zanyi sai nayi ido biyu da ummey zaune a kusa dani nabuda baki zanyi magana sai naga ta mikomin wata farar takadda koda naga takaddar saki daya dauke da sunan ummey. Cikin yanayin takaici hade da nuna bacin rai nai mata wani kallo nace haba ummey taya ai haka tafaru? Budar bakinta sai tace “akanka ba abunda bazan iya aikatawaba, tace “kawai durkusawa nayi har kasa idanuwana suna zubar da hawaye na rike kafarshi nace ” dan Allah dan Annabi idan yanayiwa iyayanshi kuma yana kaunar zaman lafiya to ya gaggauta bani takaddar saki. Budar bakinshi sai yace “amma ummey wane laifi namiki da har kike neman takaddar saki daga gareni? Sai nace “baka aikatamin laifin komaiba amma zanso kasan da cewar tunda wanda nake kauna ya dawo to bazan taba samun kwanciyar hankaliba muddun bai zama mallakina ba dan haka ina mai rokonka daka bani takaddar da zata zamto shaidar rabuwata da kai saboda hakan shine zaifi kasancewa zaman lafiya a tattare da kai. Sai yayi murmushi sannan yace “tun daga lokacin daya samu labarin dawowarka yaji a jikinshi hakan zata iya faruwa dan haka shi maison zaman lafiyane kuma maison ganin farin ciki a tattare dani. Wannanne dalilin dayasa ya rubuta takaddar saki a gareni. Bayan ta gama yimin wannan jawabin, raina a bace nace “amma ummey kin aikata kuskure. Domin ke kanwatace ta jini wadda mahaifiyata ta haifeku a matsayin yan biyu da cikinta. nan take na fara bata labarin duk yadda ai hakan ta faru tun daga lokacin da mahaifiyata ta haifesu har zuwa lokacin danabar gida domin cikawa mahaifiyata burinta. Amma duk da hakan baisa ummey tayi na’am da bayaninaba. Nan take ta mike tsaye tace “karka fake da wannan hanyar dan guduna saboda idan har ka gujeni a wannan lokacin to zuciyata bazata taba yafemaba sannan tayi waje tana kuka ganin hakane yasa nabi bayanta domin gudun kar iyayanta susan abun daya faru fitowata kenan daga daki sai nayi arba da AISHA zaune a falo cikin yanayin furgici nace “aisha!!!!!! Wanda hakan yasa ummey ta juyo fuskarta da sauri sannan taja burki ta tsaya. A tsorace na karasa kusa da aisha! cikin yanayin rudani nace “aisha a iya sanina da kuma tunanin mutuwa ba karya bace amma hakan yana neman jefa zuciyata a rudani. Murmushi naga tayi! Sannan tace “waya fadama cewar na mutu? Alhalin kai ka rakani har tashar motoci nahau mota zuwa jahar jigawa. Sai nayi shiru na dan wani lokaci sannan na dago kai na kalleta nace “tabbas naga haka amma a mafarki. murmushi naga tayi sannan ta jinjina kai ta kalleni tace “ba mafarki kaiba domin azahiri hakan ya faru. => 10 Fitowar mahaifiyata daga daki kenan. Cikin yanayin firgici nace “umma kinga aisha wai ba mutuwa tai ba. Cikin yanayin mamaki mahaifiyata ta kalleni tace “to kai a ina kasamu labarin ta mutu? ina kai ka rakata har tashar mota domin ta hau mota zuwa jigawa. Nan take na kalli ummey nace “ummey anya acikin hankalina nake kuwa? Tabbas idan har maganar da aisha tayi gaskiyace to babu shakka kwakwalwata ta samu tabuwa. Budar bakin ummey sai tace “ita kuma wannan aishar wacece kuma meye alakarka da ita? Nan take na shiga bata labari. nace “motace ta hadani da ita tun daga jahar kebbi bamu mu sauka motaba sai musalin12 na dare hakane yasa ta nemi taimakon aron wayata domin takira wadda tazo wajan nata amma sai wayar taki shiga koda naga tayi matukar shiga cikin damuwa saina nemi tabini zuwa gidanmu idan Allah yasa gari ya waye sai taji dadin kiran nata. Haka mu jero tare zuwa gida tun a hanya na nemi sanin sunanta hade da jin dalilin zuwanta jaharmu ta kano. Cewa tai aisha ne sunanta batun dalilin zuwanta kano kuma labarine mai tsayi hade da ban tausayi dan haka nayi hakuri zuwa safiya sabida tana matukar jin yunwa hade da bacci. Da isarmu gida cikin yanayin farin ciki nagaisa da mahaifiyata sannan na kaiwa aisha abinci domin nasan tana matukar bukatarshi a wannan lokacin. kwatsam musalun karfe 8 na safe ina shiga dakin da’aba aisha a matsayin masauki sai nai arba da gawarta ga kuma abincin dana kawo mata koci bataiba hakane yasa jami’an yansanda su gudanar da bincike akaina hade da iyayena mahaifiyatace ta matso kusa dani sannan ta dafa kafadata tace ” to indai hakane babu shakka akwai matsala a tattare da kai domin duk wannan batun da kayi ba wanda ya faru kawai ni dai abun dana sani shine kazo da aisha gidannan washe gari da safe kuma ka rakata ta hau mota zuwa jahar jigawa. Budar bakina sai nace “to amma umma meya makasudin dawowarta gidannan? Sai ummata tace ” ai dama ta sanar dakai cewar kwana daya zatayi sannan ta dawo gareka saboda ka daukar mata alkawarin zaka aureta sakamakon tausaya mata din da kayi a dalilin jin labarin data baka haka na samu waje na zauna jikina a sanyaye haka na kalli aisha da ummey hade da mahaifiyata sannan nace “tabbas ina cikin rudani domin bansan wani labarin da aisha ta bani ba har da zaisa na dauki alkawarin aure a tsakanina da ita sannan na kara da cewa dan Allah ku taimaka ku fitar dani daga wannan matsanancin rudanin. sai aisha tace ” ikon Allah! Yanzu kana nufin harka manta da duk labarin dana baka? Cikin yanayin kidimewa nace “aisha nifa bansan wani labarin daki baniba. Sannan na kalli mahaifiyata nace “umma kenan batun da kimin na batun ummey kanwatace ta jini shima baki da masaniya akanshi kenan sai tai shiru na dan wanilokaci sannan ta dago kanta ta kalleni fuskarta cike da mamaki. => 11 Sai tayi shiru na dan wani lokaci sannan ta dago kai ta kalleni fuskarta cike da mamaki tace “tabbas ni banyi wannan maganar da kaiba. Amma a ina kasamu wannan labarin? Koda naji wannan batun daga bakin mahaifiyata nan take naji kaina yayi wata irin bugawa sakamakon ganin yadda nake neman komawa zararre alhalin kuma ni nasan a hayyacina nake. Jin hakane yasa ummey tayi tunanin so nake na juya mata baya ta hanyar kame-kamen hanyoyin da zasu kawo rabuwata da ita wanda hakan yasa tayi waje tana kuka. Jim kadan da fitar ummey sai Allah yai dawowar mahaifina daga tafiyar da yayi. Kamar dai yadda mahaifiyata tayi mamakin sake ganina a raye haka shima wannan mamakin hade da rudani ya bayyana a fuskarshi. Rudanin da nake cikine ya hanani bayyana farin cikin sake haduwa da abbana, domin ba abun daya fara fitowa bakina illah neman sanin alakar dake tsakanina da ummey. Budar bakina sai nace “abba wace alakace a tsakanina da ummey? Mahaifiyata naga ya kalla sannan ya kalleni hade da cewa “wace ummey? Matsawa nayi kusa dashi nace “abba a halin yanzu ina cikin rudanin da bawanda zai iya cireni a kaf fadin duniyarnan bayan kai da kuma mahaifiyata. Dan haka yanayin kallan da naga kayiwa mahaifiyata ya tabbatarmin da cewar akwai wani abun da kuke boyemin. Nan take na durkusa har kasa ina mai zubar da hawaye nace “umma sanin kankine ni mai son ganin farin ciki a tattare dakune. Wanda hakan yasa nabar gida na tsawon shekara biyu da wasu watanni badan komaiba sai dan ganin na cika umarnin daki bani ba tare da nayi kuskure ba. Ji nayi abbana yace “bakai kankaba nima kaina a cikin rudani nake domin gaba daya ban fashimci inda wannan maganar taka ta dosa ba. Na buda baki zanyi magana sai mahaifiyata ta dakatar dani ta hanyar cewa “a’a nice wadda zanyimai bayanin komai dangane da wannan al’amarin. Dakin mahaifina mu shiga gani ga mahaifiyata hade da abbana. Mahaifiyata ta kalli abbana tace “soyayyace ta shiga tsakanin wannan yaron da ummey. Gudun kar soyayyar tasu tayi nisane yasa na bukaci ya janye kanshi daga batun kula ummey da sunan soyayya, amma banason hakan yai sular daina shigowarta gidan nan domin ganin yadda take gudanar da al’amuranta a gidannan ba kadan nakejin dadi ba. Ganin yadda na nemi shiga tsakaninsune yasa ya bukaci na sanar dashi dalilin da zaisa na rabasu. Alkawarin dana dauka akan cewar ba wanda zaiji wannan surrin ne yasa naki sanar dashi batun komai. Bukatar cika umarnin dana bashine yasa ya kirkiri tafiyar da zai dauki dogon lokaci ba tare daya sake waiwayar inda muke ba, wanda a karshe sakon mutuwarshi ya iso garemu alhalin kuma ba mutuwa yai ba ya aikata hakane duk dan ya cire son da ummey takemai a zuciyarta. Bai kuma tashi dawowa ba har sai da ummey tayi aure. Koda mahaifina yaji wannan bayanin sai naga ya jinjina kai hade da cewa tabbas wannan al’amarine mai rikitarwa. Kuma wannan hanyar dakabi dan ganin ka cika mana burinmu itace tafi dacewa dan haka ba wani abun da zamuce a gare face fatan alkairi. Sannan kuma inamai baka hakurin rashin sanin wannan surrin da yake zukatanmu domin alkawari mu dauka akan cewar bazamu sanar da kowa ba. Cikin hanzari mahaifiyata tace “to ai ya riga yasan komai kuma babban abun daya dauremin kai shine yadda ai har yasan da cewa ummey kanwarshice ta jini. Zumbur na mike tsaye fuskata cike da mamaki nace “umma ashe dai gaskiyane ummey kanwatace ta jini kenan? Nan take ta jinjina kai hade da cewa “kwarai kuwa ummey kanwarkace ta jini domin ba yadda za’ai aure ya shiga tsakaninka da ita. Sannan ta kara da cewa to amma taya ai har kasan da cewa ummey kanwarkace alhalin ba wanda yama bayani a cikinmu. Cikin yanayin mamaki nace “umma kefa ki fadamin komai jiya lokacin ina cin abinci a kusa dake. Domin abun da ki sanar dani shine “ummey yarkice wadda ki haifeta tare da hafsat a matsayin yan biyu. Ganin yadda abokin mahaifina hade da matarshi su shiga damuwa a dalilin rasuwar yar dasu haifane yasa ku mallaka UMMEY a garesu badan kimaiba sai dan duba da yadda su dauki dogon lokaci ba tare dasun samu haihuwaba. Ba’a dauki wasu dogwayen kwanaki ba sai Allah ya dauke ran hafsat yar uwar ummey kenan. Jinjina kai naga mahaifiyata tayi hade da cewa “tabbas akwai matsala a tattare da kai domin ko kadan banyima bayanin komai a tattare da wannan surrin ba. => 12 Duk da cewa wannan al’amarine ba dan karami ba, haka nayi kokarin mantawa da wannan batun. Bayan gari ya waye nayi wanka fitowata daga gida kenan da kudurin yawatawa cikin gari. Sai Aisha ta biyo bayana. Koda na hada ido da ita sai tace “ya kuma zaka tafi ka barni alhalin kuma kayimin alkawarin bazaka taba nisanta kanka dani ba. Wani kallo nayi mata hade da cewa nifa bansan komai dangane da rayuwarki ba, balle ki kawo batun daukar alkawari a tsakanina dake. Nan take naga fuskarta ta canza ta hanyar bayyana bacin rai. Har ta juya da kudirin komawa sai na dakatar da ita ta hanyar cewa “da zaki taimaka ki bani cikakken labarinki zata iya yiwuwa hakan ya taimaka wajan rage rudanin da nake ciki. Hawaye nagani a fuskarta a yayin data juyo zuwa gareni. Murmushi nayi hade da cewa haba Aisha meye kuma na zubar da hawaye akan wannan kankanuwar maganar. Budar bakinta sai tace “hakika banyima halacci ba amma kayi hakuri domin bani da wata hanyar data dace nabi wadda ta wuce wannan hanyar. Cikin yanayin bacin rai nace “Aisha a halin yanzu bana bukatar sakejin duk wata maganar da zatayi sular sake afkani a cikin rudani. Dan haka duk wata maganar da zata fito bakinki zanso kiyita wara-wara yadda zan fashimci inda maganar ta dosa. Hannuna ta rike zuwa wani kebabben wajan dake kusa damu da’a ware domin bukatar duk wani mai son hutawa. Koda mu zauna gani ga ita sai tace “tabbas nice sular haifar da duk wani rudanin daka tsunci kanka a ciki. Kuma ba komaine ya haifar da hakan ba illah kaunarka din da take zuciyata. Azahirin gaskiya inasonka kamar yadda na aje kaunarka a zuciyata. Amma dan Allah zanso kafin na sanar dakai koni wacece kasanar dani, shin kaima kanajin sona a zuciyarka koda kankanine? Kallanta nayi hade da cewa “ai shi so a zuci yake samun masauki, kuma zanso ki gane wani abu dangane da batun SO. Duk girman abu hade da kasaitarsa ko kyawunsa ba yadda za’ai ya samu masauki a sansanin zuciyar koma waye muddun zuciyar batayi na’am dashi ba. Wani abun mamaki kuma sai kiga dan abu kankani ya haifar da soyayya ga zuciyar wasu. Tabbas kina da kyawun daya zarce na ummey domin ke kyakkyawace amma hakan bazai taba sawa na daukeki a matsayin wadda tafi ummey ba. Koda naga ta dan bata rai sai nace “haba Aisha hakan bawai yana nufin cewar bana sonki bane domin tun tuni zuciyata ta alkinta sonki a cikinta. Kuma hakan ya samo asaline sakamakon tausayawar da tagani a tattare dake a yayin da idanuwana suga zubar hawayen idanunki. Gyara zama tayi sannan ta kalleni tace “dan Allah kar kaji tsorona domin ba yadda za’ai na cutar da rayuwarka. Kallanta nayi hade da cewa “ki fadi duk abun dake ranki kanki tsaye. Ban tashi auneba sai jin saukar mari nayi a fuskata. Juyo fuskar da zanyi sai nayi ido biyu da ummey tsaye a gabana. Cikin yanayin fusata ummey tace “kai azzalimine macuci wanda baisan darajar kansaba. Hakika wannan da kake tare da ita tafini kyawun fuska. Dan haka bazanga laifinka ba dan kayi watsi dani ta hanyar maye gurbin soyayyata data wannan. Amma ka tabbatar da cewar ba yadda za’ai na bari ka kulla wata alakar data shafi soyayya da wata har sai ka kwashe gubar soyayyar daka shayar dani wadda ta daskare a zuciyata. Sannan zaka samu damar kula wata ya mace. Domin ko iyayena banajin cewar zasu iya dakatar dani akan abun da zan iya aikatama saboda gubar daka shayar dani ta dode duk wasu hanyoyin dasu dace shawara mai amfani ta isa kunnena. Jin hakane yasa ran aisha yai matukar baci. Cikin yanayin bayyana bacin rai aisha tace “haba ummey wannan ai halayyace irin ta marasa hankali da tunani ya za’ai da ganinmu zaune zaki daga hannu ki mareshi. Bansan lokacin dana dakama aisha tsawaba hade da cewa karki sake danganta ummey a sahun marasa hankali domin bazan taba jurar ganin bacin rantaba. Tsawar dana daka matane yasa ranta yai matukar baci. Nan take naji kaina yana sarawa kamar wanda yai karo da bango. Cikin kankanin lokaci naji duk ilahirin jikina ya dauki zafi. Ganin hakane yasa nayi gaggawar shiga gida. Da shigata falo sai kuwa na yanke jiki na fadi. Saida na dauki tsawon lokaci kafin mahaifiyata ta ankara dani. A yayin da mahaifiyata tayi ido biyu dani sai ta rugo zuwa gareni. Koda taga alamun suma nayi sai tayi gaggawar dakko ruwa a fridge ta yayyafamin har ta fara kuka a yayin da taga naki motsawa. Mikewar da zatayi sai taji nayi tari hade da jan wani dogon numfashi. Cikin gaggawa a garzaya dani zuwa asibiti. Tsawon kwana biyu na dauka kwance a gadon asibiti kafin na iya gane wadan da ke kusa dani. Da mahaifiyata na fara hada ido sai kuma abokina ANAS zaune a kusa dani. A yayin dana hada ido da ummey sai naji kirjina yai wata irin bugawa. Saboda nasan dolene a samu matsala, domin ko kadan banason ganin ummey a cikin damuwa ko bacin rai. Sai dai kuma bani da masaniyar dalilin faruwar wannan rashin lafiyar tawa. Na dauka ummey zata nisanta dani amma sai al’amarin ya sake rikicewa haka sona yaci gaba da sake sabon toho a zuciyar ummey. Wanda hakan yasa ummey ta turje akan batun ba wanda zata zauna dashi a matsayin miji idan bani ba. Tun daga lokacin da’a dawo dani daga asibiti ummey bata da wata sakewar data wuce ta ganta a tare dani. Ganin hakane yasa nace da ita “ummey yaushe zaki koma gidan mijinki? Budar bakinta sai tace “amma me yasa ka zabi kamin wannan tambayar sabanin wadda nayi tunanin fitowarta daga bakinka? domin ba abun da nakeson ji daga bakinka face batun aurena dakai. Fuskata ba alamar wasa nace “amsar tambayar dana miki nakesonji. Cikin yanayin damuwa tace “Ba rana balle wata. Jinjina kai nayi hade da cewa to bari kiji tarayyata da ke bazata taba yiwuwa ba balle ayi batun aure. Dan haka shawarar da nakeson na baki a matsayina na dan uwanki itace “ki koma ga mijinki domin wannan ita kadaice hanyar da zata bulle dake. Cikin yanayin alhini tace “meyasa kake son dangantani da batun ni yar uwarkace amatsayin hanyar da zata haifar da rabuwa a tsakaninmu. Haka ta kalleni tana kuka tace “me yasa zaka juyamin baya a lokacin da sonka ya makantar dani ta hanyar daina ganin duk wata hanyar da zata kawo batun rabuwata da kai? Ganin halin da ummey take cikine yasa na yanke shawarar sanar da ita gaskiyar abun da iyayenmu suke boye mana. Budar bakina sai nace “ummey sanin kankine tun kafin ki kamu da sona narigaki kamuwa da hakikanin kaunarki. Tabbas kafin zuwan wannan lokacin ba kadan nakejin shaukin sonki ba amma a halin yanzi idan akwai abun da zai iya kasancewa danasani ga rayuwata to bazai taba wuce faruwar soyayya a tsakanina dake ba. Kallanta nayi nace “ummey kefa kanwatace ta jini wadda mahaifiyata ta haifeku a matsayin yan biyu abokiyar haihuwarki itace “hafsat wadda allah yaima rasuwa. Tun da nake a rayuwata ban taba tunanin durkusawa a gaban wata ya mace da sunan rokon wata alfarma a tattare da itaba. Amma sai gashi nine na durkusa har kasa a gaban kanwata domin rokonta. Koda na durkusa a gaban ummey sai nace “dan Allah ummey ki taimaka ki rufa mana asiri ta hanyar janye batun soyayyar dake tsakanina dake ki kuma yi kokarin rike wannan surrin a iya zuciyarki ta hanyar kin sanar da kowa wannan surrin. Kuma zanso kikasance mai kokarin samawa zuciyarki hakurin zama da wadanda suke rike dake a matsayin yarsu ta hanyar cigaba da daukarsu a matsayin iyayenki wadanda su durkusa su haifeki. A karshe kuma ina mai rokonki daki koma ga ainashin mijinki domin ba aure a tsakanina dake. Nan take naga fuskarta ta canza sannan ta share hawayen dake fuskarta ta fita daga dakina. Ban saniba ashe kanta tsaye wajan mahaifiyarmu ta nufa. Koda ta samu mahaifiyar tamu sai tace “umma me yasa ke da abba ku zabi kuyi watsi da kyautar da Allah ya baku ta hanyar damkata ga wasu. Umma bansan irin azaftar dake din da nayi alokacin da ina cikinki ba wanda har hakan zaisa kiyi sadaka dani ga wadanda ko dangantakar jini bamu hada dasu ba. Gashi a dalilin faruwar hakan zuciyata tana neman cutuwa. Abu na farko nayi rashin ingantacciyar tarbiyyar data dace na samu daga gareku. Abu na biyu a dalilin rashin sanin wannan sirrin daku dade kuna boyewa har zuciyata ta kamu da son kasancewa da yayana wanda nake jini daya dashi a matsayin matarshi. Nan take ummey ta durkusa har kasa cikin yanayin kuka tace “dan Allah umma ku taimaka ku dawo dani gida. Ina zaune a dakina cikin yanayin damuwa sai naji karar bude kofa. Dago kan da zanyi sai nayi ido biyu da AISHA. Budar bakin Aisha sai tace “yanzu kana tunanin abun daka aikata kayi dai-dai kenan? Dago kan da zanyi sai nace “waike wacece? Kuma meye alakata dake da har kike yima rayuwata shish-shigi akan abun da bai shafeki ba? Murmushi tayi hade da cewa “zaka iya tunawa da KADANGARAN da abokinka yai kokarin kashewa yau tsawon shekara 14 kenan da faruwar hakan. Cikin yanayin rudani mai tattare da mamaki nace “wannan kadangaran shine ya addabi rayuwata na tsawon wadannan shekarun daki ambata. Hakane yasa bana bukatar jin labarin daya shafi kadan-gare balle ganinshi ido da ido. Al’amarin ya samo asaline tun ina dan kimanin shekara 8 lokacin muna zuwa makarantar primary. => 13 Cikin yanayin rudani mai tattare da mamaki nace “wannan kadangaran shine ya addabi rayuwata na tsawon wadannan shekarun daki ambata. Hakane yasa bana bukatar jin labarin daya shafi kadan-gare balle ganinshi ido da ido. Al’amarin ya samo asaline tun ina dan kimanin shekara 8 lokacin muna zuwa makarantar primary. Aduk lokacin damu halarci makaranta bani da wani sukunin daya wuce maida hankalin rike koda abu biyune daga cikin abunda malamanmu su koyar damu domin hakane yake bani kwarin guiwar samun kyaututtuka daga mahaifina hade da mahaifiyata. Saboda ako wace ranar dana halarci school mahaifiyatace take fara tambayata abun da’a koyar damu idan mahaifina ya dawo shima sai ya dora da nashi tambayoyin. Mahaifina hade da mahaifiyata suna matukar alfahari dani ganin yadda nake kokarin zuwa makaranta. Sai dai kuma a zaman takewar rayuwa dolene kaci karo da mutane biyu na banza dana kirki. Abokan banzane suyi sular canza halayyata izuwa halayyar da suke ciki. Tun Ina dari-dari dasu har na kaiga sakin jikina a cikinsu. Da zaran mun halarci school bama daukar awa daya ba tare damun arce bayan gari yawon banza ba. Tafiya mukeyi ba yar karamaba dan zuwa kwarin daya daga cikin abokanmu domin shan kayan itatuwa. Kafin mahaifina ya ankara tuni wannan yawon banzan yayi karfi a zuciyata ta yadda sai ankai ruwa rana kafin a dakatar dani. Tabbas ni nasan da cewa mahaifina yana matukar sona amma duk da hakan bai hanashi yimin shegen duka ba domin bansan adadin dukan da nasha a dalilin yawace yawacen banzana ba. Sai dai kuma akwai wata dabi’ar da nake tattare da ita wadda hakan yasa nake yawan samun matsala da abokan nawa. Wannan dabi’ar tawa ta samo asaline tun wata ranar Monday kafin halayyata ta samu nakasu ta hanyar yawace yawacen banza. Musalin karfe 8 na safiyar Monday na fito daga gida a gaggauce ko karyawa ban samu damaryi ba domin gudun kar a dakeni a makaranta saboda nima kaina nasan a wannan ranar na makkara. Har nayi nisa sai kular abincin da nake rike da ita hannunta ya fita nan take taliyar dake ciki tayi watsa-watsa. Tabbas abun mamaki ya bani sakamakon ganin yadda kadangaru su tasa abincinnan daci. Ban bar wajan ba har saida su cinye abincin tas. Duk da cewa ayunwace nake haka na nufi makaranta ba tare da bayyana wata damuwa ba domin a cikin littattafaina akwai wata naira hamsin din dana dade da ajewa. Haka nayi hakuri har a tashemu break sannan na samu abun da zanci. Tun daga wannan ranar na kuduri niyar cigaba da tallafama kadangaru. Ako wace rana bana taba rasa yan kudaden kashewa daga abbana ko mahaifiyata wani lokacin kuna yayata zainab nake tunkara da bukatar ta bani kudin da zan dan kashe. Ta wadannan hanyoyin nake samun yan kudaden da nake sayan taliya domin ciyar da kadangaru. Tafiyayya nakeyi zuwa wani kango domin kaiwa kadangaru abinci badan komai ba sai dan kar al’umma su samin ido. Saboda abun yana matukar burgeni a yayin da naga sun dukufa cin taliyar. Gaba daya sai wannan al’amarin ya zamemin kamar wani bangare na rayuwata wanda idan ban aikatashi ba to ba yadda za’ai naji dadi. Haka naita gudanar da wannan aikin ba tare da kowa ya sani ba domin a wannan lokacin bani da wasu abokai na musamman. A yayin da halayyata ta samu canjine ta hanyar samun abokan banza sai wannan dabi’ar tawa ta fito fili. Amma ba kowane ya sani ba domin iya abokainane kadai susan da wannan dabi’ar tawa. Koda nakai kimanin 10 years sai na aje lokacin da zan rika kai masu wannan abuncin wato taliya kenan. Musalin karfe 7:30 na safiyar nake zuwa dakin abokina ANAS domin dafa taliyar da zankai masu. Musalin karfe 2 na rana kuma bayan an idar da sallar Azahar kudi nake cirewa daga aljihun domin siyan taliyar da zan kai masu. Da zaran naga yamma tana neman yi haka zan sake siyan wata taliya na aje masu idan magariba ta tunkaro sai naje na kai masu. Abun ba kadan yake bani dariya ba ganin yadda kadangarunnan suyi kiba kuma ni ba ma’abocin cin kadangare ba balle na rika yankawa inaci. Duk yawon da zanyi da abokaina bana taba yin sake wajan kai madu abinci akan lokaci. Idan har nasan zanyi tafiyar da zata haifar da rashin kai masu abinci akan lokaci to ba makawa sai naje garesu domin basu hakuri. Da zaran sunji sallamata sai su rugo zuwa gareni. Abun da nake ce masu idan zanyi tafiya shine “kuyi hakuri domin yau zanyi wata yar tafiyane kuma ina tunanin hakan zai iya haifar da rashin kawo maku abinci da wuri. Haka zasuyita gyada kai hade da buda baki ba tare da nasan abun da suke fada ba. Idan kuma a samu akasi wani uzirin ya hanani kai masu abincin akan lokaci haka zan basu hakuri hade da sanar dasu dalilin faruwar hakan. Ganin yadda wannan al’amarin ya game jikinane yasa abokaina suke nuna bacin ransu wanda a karshe suyi yunkurin kashe kadangarun gaba daya ta hanyar sa masu guba a taliya. Amma Allah bai basu ikon cin taliyar ba. A majalissa da muke zama akasin daya haifarmin da tsanar kadangare ya samo asali. Muna cikin zamanmu NUHU ya kira mai gyada. A gabanmu ya siyi ta 20 naira ya murjeta a gaban idonmu da kudurin cinyeta shi kadai. Ganin hakane yasa na nace akan sai naci gyadar. Cikin yanayin wasa muyita kokawa har mu kaiga fita daga majalissar tamu ta hanyar yin tafiya mai dan nisa. Ba yadda ya iya haka ya bukaci na bude hannuna domin ya samman gyadar. Wajan zuba min gyadarne a samu akasi wasu su zuba kasa. Sai kuwa wani kadangare ya rugo a guje ya dauki daya daga cikin gyadar data zuba a kasan. Nan take naga ran NUHU yai matukar baci wanda hakan yasa yayi ko karin kashe wannan kadan garan. Haka yabi kadangaran a guje domin ganin bayanshi sai Allah ya taimaka kadangaran ya afka wani rami to ashe kadangaran baisha ba domin ramin ba wani mai nisa bane. A gaban idona nuhu ya zura hannu ya kamo kadangaran. Ganin yadda yake neman ganin bayanshi ne yasa nayi kokarin dakatar dashi amma hakan bai yuwu ba domin bugashi yai da kasa. Tabbas ba kadan nayi mamakin ganin yadda kadangaran ya kunbura ba. Haka naja abokina mu tafi tun a hanya ya sanar dani shifa kanshi ciwo yakemai wanda hakan yasa yayi gaggawar tun karar gida. Ko cikakken 30 minutes da rabuwarmu ba aiba sai batun rasuwarshi ya karade gari. Ba kuma kowane yasan abun daya faru kafin rasuwar shi ba sai ni da abun ya faru a gaban idona. Bayan kwana ukku da rasuwar nuhu wato abokina kenan sai babban kalubale ya fara bibiyata. Cikin dare muslin karfe 2 naji matsin abu a kirjina wanda ban gane ko menene ba. Tsoran da najine yasa na kwalla kara ban kuma san lokacin dana fado daga kan gado ba. Cikin yanayin furgici na haska tocila. Ganin kadan garan da NUHU yayi kokarin kashewa a dakinane yasa nayi matukar tsorata. Wanda hakan yasa nayi kaura daga dakina zuwa dakin anti zainab. Da shigata saina tasheta daga bacci hade da cewa anti wallahi tsoro nakeji. Haka ta tilastamin akan saina sanar da ita tsoran da nakeji amma naki domin nasan muddun nayi gaggawar sanar da ahalina wannan batun to ba makawa sai an samu wanda zaiyi kokarin hallaka wannan kadangaran. Kuma na tabbata hakan zai iya haifar da sular hallaka rayuwar wasu daga cikin ahalina hade dani kaina. Kuma ni faruwar hakane banaso. Ganin yadda naki sanar da itane yasa ta kyaleni mu kwanta tare a gado daya. Ban saniba ashe akwai sauran rikici a gaba. => 14 Ba karamin tashin hankali na shigaba a dalilin kasancewar wannan kadangaren a tattare dani. Bani da wata sakewa domin aduk inda zan tsunci kaina dolene shima wannan kadadaren ya kasance a wajan. Idan ina cikin abokaina ko wasu mutanan da ban baya kusanto inda nake saiya koma can gefe. Wallahi har fargabar zama ni kadai nake domin har hawa jikina yakeyi. Aduk lokacin da naji yahau jikina ba karamin zabura nake a guje ba. Domin har faduwa nashayi wajan gudu wanda hakan yake sawa naji ciwuka a hannayena hade da kafafuwana. Bana taba yadda na kwana ni kadai domin a dakin anti zainab nake kwana. Bacin ran kwanan da nakeyi tare da itane yasa tayimin mugun duka alhalin kuma ba laifina bane domin duk laifin wannan ad- dababben kadangaren ne. Duk dukan da anti zainab zatamin baya taba damuna domin ko zubar da hawaye banayi ni dai kawai na gwammaci ta ganamin duk wata azabar da taga dama maimakon na kwana tare da wannan kadangaran a dakina. Koda ta gaji da ganina a dakinta sai ta gargadeni dana daina kokuma ta sanar da abbanmu. Tun daga wannan ranar saina koma kwana a dakin abokina ANAS. Tsawon sati daya na dauka ina kwana a dakin anas sai mahaifina ya gane cewar bana kwana a gida. Duk da irin fadan da abbana yakemin baisa na daina kwana a dakin anas ba. Ganin hakane yasa abbana yamin dukan da bantaba tunanin fuskantar irinshi a fadin duniyar nan ba. Gudun karna sake fuskantar irin wannan dukanne yasa na bukaci abokina ANAS daya rika zuwa dakina muna kwana tare amma yaki domin shima cewa yayi abbanshi bazai taba lamuntar haka ba. Haka dai wannan kadangaran ya hanani sakewa. Hmm!! Lokaci daya kadangaran ya bijiromin da wani sabon iskanci. Dazaran na sayi wani abun da niyarci sai kadangaran ya rugo a guje zuwa gareni tsoran da nake tattare dashine yake sawa na saki abun ya fadi kasa nan take kadangaran zai hau abun daci. Musalin karfe 3 na rana na tunkari gida da kudurin cin abinci. Da shigata dakina sai kuwa nayi ido biyu da wannan kadangaran a saman marfin abincin da’a ajemin. Hakika nima nayi matukar mamakin ganin yadda kadangare ya addabi rayuwata. Kuma gashi idan na nemi takurama rayuwarshi to ba makawa sai na rasa rayuwata kamar yadda abokina NUHU ya rasa tashi rayuwar. Ganin hakane yasa na durkusa har kasa ina zubar da hawaye domin neman sulhu a tsakanina da wannan kadangaran. Cikin yanayin kuka nace “haba bawan Allah meyasa kake neman takurama rayuwata ta hanyar bibiyata, alhalin ban aikata laifin komai a garekaba? Abokinanefa ya nemi kasheka ganin hakane yasa na nemi ceton rayuwarka. Kuma ai ka dauki fansar abun daya aikatama meye zaisa kaci gaba da bina. Dan Allah idan har bazaka daina binaba to kadaina hawa jikina kuma ka daina kokarin tunkarar inda abincina yake. Kuma nayima alkawarin duk abun da zanci zan rabashi biyu daya naka daya nawa. Haka tunanin wannan kadangaran ya addabi zuciyata lokaci daya duk nabi na rame ganin hakane yasa iyayena suyi yunkurin tilastamin ta hanyar sanar dasu lalurar da take damuna. Ganin yadda naki yimasu cikakken bayanine yasa su dangantani da asibiti domin duba lafiyata. Abunda likitan daya duba lafiyata ya sanar da iyayena shine “ba wani abune yake damun danku ba illah yawaitama zuciyarshi tunani. Dan haka rage tunanin dake zuciyarshine kadai zai kawo mai sassauci. Anti zainabce ta tilastamin har saida nayi mata cikakken bayanin abun da yake damuna. Haka aita nemamin magani domin rabani da wannan kadangaran amma hakan yaci tura. Haka wannan kadangaran yaci gaba da bibiyata na tsawon shekara 14 amma da taimakon Allah a dalilin maganin da iyayena su dukufa nemamin sai Allah yasa wannan kadangaran ya rage bibiyata. Yana zuwa garenine lokaci-lokaci kuma idan ya tashi zuwa gareni tofa a duk inda nake Kwatsam zan ganshi amma baya hawa jikina. Yau kimanin shekara biyu kenan rabona da sake ganin wannan kadangaran. Matsowa kusa dani Aisha tayi fuskarta cike da murmushi. Budar bakinta sai tace “bani ya kamata kaba wannan labarin ba domin nice wannan kadangaran kuma nice sular afkawarka a cikin duk wani rudanin daka tsunci kanka a ciki. Zumbur na mike tsaye a yayin da naji fitar wannan furucin daga bakin Aisha. =>15 Tsoran da Aisha ta gani a tattare danine yasa tayi gaggawar rike hannuna. Fuskarta ba alamar wasa tace ko kadan ban nemi shiga rayuwarka domin na cutar dakaiba. Bukatar rayuwata da taka su zama dayane yasa nayita bibiyarka. Ganin yadda ka tausayamin a yayin da abokinka yai yunkurin cutar danine yasa ruhina ya aminta da kai wanda hakan yasa naita bibiyarka a suffar kadangare alhalin kuma ni aljanace. A duk lokacin daka kwanta bacci kai kadai ni kuma sai nazo na kwanta a saman kirjinka domin ba karamin dadi nakeji ba a yayin da sautin bugun zuciyarka yake ratsa kunnuwana. Kwatsam sai naga take-taken soyayya tana neman shiga tsakaninka da UMMY kafin ka gane cewar ita kanwarka ta jinice. Gudun karka takurama kanka wajan bibiyar ummey da sunan soyayyane yasa nayi kokarin dakatar dakai ta hanyar yima hannunka mai sanda ba tare dana fito fili nayima cikakken bayanin cewar ummey kanwarka ta jini bace. Bayanin da nayima a lokacin dana kiraka a wayane ya tunzuraka wanda hakan yasa kayima ummey bayanin abun dana sanar da kai na cewar ba aure a tsakaninka da ummey soyayyar da take zukatankuce tasa baku dauki maganar tawa da mahimmanci ba. Mahaifiyarka itace wadda ta fara gane alakar da take tsakaninka da ummey. Bukatar ganin farin cikin mahaifiyarkane yasa ka shirya tafiyar da zaka dauki dogon lokaci kafin ka dawo ga ahalinka badan komaiba sai dan ka rusa son da ummey takema a zuciyarta. A hanyarka ta dawowa ga ahalinkane nayi amfani da wannan damar domin kusanta kaina dakai wanda hakan yasa ka bani masauki a gidanku. Tabbas banyima bayanin komai dangane da rayuwata ba mahaifiyarkace kadai taji labarina. Amma ita a tunaninta kaima kana wajan alokacin da nake bata labarin wanda har hakan yasa ka daukarmin alkawarin kasancewa dani na tsawon har abada sakamakon tausayamin din da kayi batasan cewar duk shirina bane domin ba kai din bane. Batun mutuwatama ba gaskiya bane domin kai kadaine kaga haka saboda shima duk a mafarki na nunama faruwar hakan. Dan haka zan nisanta dakai na tsawon har a bada bazan sake bibiyarka ba domin na fahimci akwai tsoro a tattare da kai. Sai dai kuma akwai sauran kalu bale a gabanka domin tun daga lokacin daka dawo gida iyayenka hade da kanwarka ummey ba wanda yaji furucin komai daga bakinka. Nan take naji kaina ya daure na kalleta a sufane nace Aisha ban fahimci abunda kike nufi ba. Cikin yanayin tausayawa tace “Dan Allah kayi hakuri nasan nayi matukar rikitar da kai. Ba kuma komaine yasa na aikata hakanba sai dan bukatar mallakarka a matsayin abokin rayuwata. Ganin inna aikata hakan banyima adalci bane yasa na yanke shawarar fadama gaskiya. Durkusawa tayi har kasa sannan ta dago kai ta kalleni tace “kayafemin akan karyar da nayima akan cewar UMMEY kanwarkace domin ba wata dangantaka a tsakaninka da ita wadda zata hana ka aureta domin gaba daya abun daya faru a wannan al’amarin duk shirinane domin har kawo yanzu ummey batayi aure ba. Na aikata hakane domin na maye gurbinta. Tabbas ummey tana matsanancin sonka domin bata da wani muhimmin tunanin daya wuce naka. Na bude baki zanyi magana bat ta bace. Ko cikakken munti daya da bacewarta ba ai ba sai naji karar bude kofa ummey na gani hannunta rike da abinci a plate. Da zuwanta sai ta aje abincin a gabana sannan ta zauna a kusa Dani. Yanayin kallon da naga tamin ne yasani murmushi! budar bakina sai nace “ummey meye alakata dake. Zumbur ta mike tsaye cikin yanayin farin ciki ta fara kiran mahaifiyata “umma! umma!. Kizo yayi magana. Cikin kan kanin lokaci saiga mahaifiyata ta shigo hade da anti zainab yayata kenan. Cikin yanayin mamaki nace “umma wai me yake faruwane?? Cikin yanayin alhini zainab ta rungumeni tana jukan farin ciki. Bayanin da ummey tayiminne ya tabbatarmin da cewa maganar aljana Aisha gaskiyace domin ummey cewa tayi tun daga lokacin dana dawo gida bana iya furta kalmar komai. Shiru nayi na dan wani lokaci sannan na jinjina kai hade da cewa ashe dai Aisha da gaske take. Budar bakin zainab sai tace “wacece kuma Aisha? Fuskata cike da mamaki nace “kina nufin bakisan Aishar data zauna a gidannan ba kenan wadda na dawo tare da ita. Girgiza kai naga mahaifiyata tayi hade da cewa tabbas ba wata mace mai suna Aishar data zauna a gidannan koda kuwa na kwana dayane amma tabbas bakai ka dawo da kanka ba domin wata baiwar Allah ce ta kawo mana kai sakamakon ID CARD din data gani a tattare da kai kuma sunanta ya banbanta da wanda ka fada a yanzu domin cewa tayi hafsat shine sunanta kuma ko kwana batayi ba ta koma. Kaina a daure nace to amma umma meye alakata da ummey? Cikin yanayin mamaki ummey tace “kardai kace har ka manta da soyayyar da take tsakanina da kai? Girgiza kai nayi hade da cewa a’a ban mantaba amma akwai sarkakiyar dana tsunci kaina a cikinta. Banyi kasa a guiwa ba har saida nayi masu cikakken bayanin abun daya hadani da Aisha wanda hakan yai matukar kidimasu domin basu da masaniyar komai dangane da bayanin da suji daga bakina. Bayan na gane cewar akwai aure a tsakanina da ummey sai na nuna kaguwata akan ayi hanzarin daura aurena da ita domin gudun kar wata matsalar ta sake biyo baya. Wani kallo naga anti zainab tamin hade da cewa “kai kaji yaro da rashin kunya ai komai gaggawarka dolene kajira sai nayi aure sannan ayi naku bikin. Cikin yanayin dariya ummey taja hannuna muyi waje. Da fitowarmu sai na kalli ummey nace “wai dama har kawo yanzu ummey batayi sure ba. Murmushi naga ummey tayi hade da cewa kaga ya kamata ka mance da duk wata bakuwar rayuwar da kayi a baya saboda wannan itace asalin rayuwarka domin ba wani auran da anti zainab tayi. Ummey tayi matukar sabawa dani domin ko kadan batason na nisanta da ita. Makarantace da kuma bacci suke rabamu da zaran an tasosu daga school ba inda take fara yada zango sai a gidanmu ba kuma zata fito ba sai tare dani duk da cewa tsakanin gidanmu da nasu ba wata tazara bace mai nisa haka zan rakata har cikin gidan nasu. Bayan anyi aurena da ummey sai zuciyata ta kasa samun natsuwa sakamakon yawaita tunanin Aishan da nakeyi saboda har kullun bana cire tsammanin bazata dawo gareni ba wanda hakan yasa na kasa gane shin sonta nake ko kuma tsoranta nakeji. Alhamdulillah. Anan zan dakata da wannan labarin sai kuma mun sake haduwa a wani sabon labarin da zan kawo maku nan bada jimawa ba. Farin cikinku shine farincikina addu’arku itace garkuwa a gareni. Post navigation [ad_2]