Al-Ajab

Wani lokacin ƴan iskan maza sun fi iya soyayya, Fatima Umar

Wata budurwa ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna Fatima Umar ta bayyana irin mazan da su ka fi iya soyayya.

 

Yayin da mata da dama ke neman maza natsatstsu da hankali, ita ra’ayinta dangane da maza wadanda su ka fi lakantar soyayya.

 

Budurwar wacce tayi wallafar tare da hadawa da wani hotonta wanda ta dau kyau, ta bayyana cewa maza ‘yan iska sun fi iya soyayya.

 

A cewar Fatima, wani lokacin maza ‘yan iska sun fi iya soyayya maimakon maza masu natsuwa.

 

Kamar yadda ta wallafa:

 

“Wani lokacin ‘yan iskan maza sun fi iya soyayya.”

 

Tabbas wannan wallafar ta dauki hankali kwarai, inda wasu ke ganin gaskiya maganarta, wasu kuma na ganin akasin haka.

Ga bidiyon ayi kallo lafiya!

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button