BAKAR INUWA 47

Chapter 47
47
…………So take tabi umarninsa ta buɗe amma ta tabbatar bazata iya kallonsa ba riga ba. Sai tayi kamar zata buɗe sai ta maida ta rumtse da ƙarfin tsiya.
Tayi haka kusan 3times amma ta kasa. Cike da mugunta ya saki murmushi yana saka hanunsa guda ya janye nata data tokaresa da shi.
Wani irin ƙuuuu! Cikin Raudha ya bada sautin da har Ramadhan sai da yaji lokacin da taji saukar lips nashi akan nata daketa ƙyallin lipsgloss mai ƙamshin
strowbarry. Shi kam da yayi da niyyar tsokana duk yanda yaso janye nasa lips ɗin sai yaji bazai iya ba, cikin rashin ƙarfin jikin da ke tare da shi ya sake
manneta da mirror ɗin tare da rumtse ɗayan hanunta dake cikin nasa ya manne jikinsu waje guda yanda har numfashinsu ke fita da ƙyar….
Ya riga ya mata matsewar da rawar jikin nata ma baya tasiri, sai zuciyarta dake mugun gudu a ƙirjinta har yana iya jiyowa. Randa su Anne sukazo yayi
kissing nata sai dai ba irin na yau ba. Na yau babu sassauci, kai tsayene, cike da salon daya sata shagala tuni tsoronta ya gudu saƙonsa ya fara shigarta
ɓargo da jini. Itama tanada lafiya, duk da abinda takeji sabo ne gangar jikinta bataƙi amsaba, dan ta kai shekarun da zata iya buƙatarsa. Sai dai rashin
sabo ya sake tabbatar da ruɗaninta, dan lokacin daya janye bakinsa kasa tsaiwa tai a kan ƙafafunta. Babu shiri ta sake ƙanƙamesa. Bazata iya ɗagowa ta
kallesa ba, sannan ƙafafunta ma bazasu iya tsayawa akaran kansu ba, dan jikinta babu abinda yakeyi sai mazari.
Duka hannayensa biyu ya dafe kan mirror ɗin da suke jingine, kansa na bisa kafaɗarta, idanunsa duka a rufe suke saboda abinda ke faruwa a cikin nasa
jikin. Lallai yasan ya takaloma kansa, ya kira ruwa yau. Yana zaman-zamansa da lallaɓa yanayinsa gashi nan ya takaloma kansa ruwa wajen neman tsokanarta ya
tsokanoma kansa abinda ke kwance shekara da shekaru.
Sunayen ALLAH ya shiga ambata a zuciyarsa da son janye jikinsa da sauri, sai dai Raudha data dabaibayesa sam ta hana yuwuwar hakan garesa. Sai ma ƙara
ƙanƙamesa tai dan bata fatan ya ganta a yanayin da take. Sake gwada janyewa yay itama ta sake ƙanƙamesa. Dole ta sashi buɗe ido yana kallon kansa da bayanta
ta cikin mirror. Murmushi ne ya suɓuce masa, sake duban idanunsa da suka kaɗa sukai jajur yayi alamar fitinace kwance a cikinsu. Hannunsa ɗaya ya ɗaga da
jikin miron ya kaisa kanta ya ture hular data saka, a take gashinta dake ɗaure ya bayyana. Yatsunsa ya tura ciki baki ɗaya ribbon ɗin ta fice duka.
Babu abinda ke fita a bakin Raudha sai kalmar innalillahi…. Har ƙarshe, ga hawayenta na zarya a kan ƙirjinsa. Murmushi ya saki da sake yamutsa gashin
nata da yakeji kamar su yini yana wasa da shi. Cikin wata irin shaƙaƙƙiyar murya da bata taɓa cin karon ji da ga garesa ba ya fara magana…
“Ustaza wannan ba mafita bace, idan kika bari naje matakin ƙarshe sam bazan saurarekiba sai na tabbatar da sadakina bisa kanki yanzun nan harda ribar
baby insha ALLAH..”
Baima kai ƙarshe ba tai saurin sakinsa da son tureshi, sai dai hakan bamai yuwuwa ba, dan duk da halin da yake ciki ai goma tafi biyar albarka. Yanda
tai ɗin ya bashi dariya, sai dai halin da yake ciki bana dariyar bane, yayi imani kuma da inhar aka cigaba da kasancewa a haka babu makawa a yanzun nan
bazai iya ƙyale yarinyarnan ba, duk da ƙoƙarinsa na son yin hakan. Kaɗan ya matsa ta samu hanya, ai da gudunta ta fita har tana bigewa da ƙofa…. Shima
zaune ya kai jagwab saman stool ɗin mirror bayan ya ɗauke book ɗinta dake a wajen. Ya dafe kansa zuciyarsa na matuƙar gudu kamar zata fito… (Mike damunka
Ramadhan? Mikaje ka takaloma kanka wajen shegen tsokale-tsokalen neman ayi?) a zuciyarsa yake maganar, sai dai sam babu nadamar abinda yay tattare da shi.
Sai ma a fili daya furta ‘Oh Ramadhan ka lalace, da sa’ar autarku kake wannan abun ko kunya babu.’
Sai kuma murmushi ya suɓuce masa, ya kai hannu a wuyansa, “Ni Ramadhana zazzaɓin ma ya dawo” yay maganar a marairaice yana wani langaɓe kai gefe cike da
tausayin kansa…. Tuna abinda ya gani ya sashi saurin juyawa ga mirror ɗin, book ɗinta ya ɗauka ya buɗe, sai kuma ya miƙe yana bin rubutun da kallo. “Kai
ina..” ya faɗa a fili yana girgiza kansa da miƙewa riƙe da littafin. Bakin gado ya koma, ya ɗauka ɗaya daga cikin wayoyinsa yay snapping rubutun, littafin
ya ajiye ya cigaba da danne-dannensa. Tsahon mintuna biyu ya kai wayar kunensa.
Daga can cikin tsokana Bappi yace, “Ɗan gatan ALLAH ka warke kenan?”.
Murmushi yay yana sake ƙoƙarin control ɗin halin da yake ciki. “Oh Bappi nida nake kwance cikin ciwo kake kira ɗan gata?”.
Dariya Bappi ya karayi daga can. “Ɗan gatane mana tunda ciwon naka na ƴan gatane. Bakaji bahaushe yace mura ciwon ɗan gata ba”.
Dariya sosai shima Ramadhan ya sanya a wannan gaɓar Bappin na tayasa. Sai da suka nutsu Ramadhan ya fara magana serious. “Bappi wani abune ya ɗan
rikitani yanzun nan. Amma na turo maka saƙo ta email ka duba yanzu dan mu tabbatar”.
Bappi ma daya koma serious ɗin yace, “To ALLAH yasa dai lafiya?”.
“Lafiya lau Bappi duba dai”.
Bayan kamar mintuna uku sai ga kiran Bappi ya shigo, lokacin yana ƙoƙarin saka kaya a jikinsa. Dakatawa yay ya ɗaga wayar. “Ramadhan ina ka samu wannan
hand writing ɗin?”.
“Iri ɗaya ne ko bappi?”.
Ramadhan ya amsa tambaya da tambaya. Daga can Bappi yace, “Tabbas babu wani babbanci, kenan wanda ya turo takardar nan kamar yanda mukai hasashe yanada
kusanci damu?”.
“Bappi kasan rubutun waye kuwa?”.
“Shi na ƙagu naji Ramadhan ”.
“Ameenatu!”.
“Aminatu? Kana nufin Aminatu dai matarka?!”.
“Ita kuwa Bappi. Yanzu naci karo da shi a book ɗinta na makaranta, shiyyasa gaba ɗaya kaina ya kasa ɗauka nima dan na shiga ruɗani”.
“Uhhm to kaga wannan maganar bata nan bace ba, idan ka fita office gobe idan ALLAH ya kaimu zanzo kawai”.
“Bappi na sameka a gida mana anjima”.
“No Ramadhan akwai haɗari. Satar fitarka tayi yawa, ina tsoron magauta su fara fahimta su cutar da kai ta wannan hanyar. Dolene ka canja takunka”.
Fuska ya ɓata, dan gaskiya akace bazai dinga zuwa gidansu akai-akaiba an cutar da shi. Wannan takura har ina dan ALLAH.
★Hajjaju Raudha kam tunda ta fice tana can ɗaki duƙunƙune a bargo. Ji take kamar ta tona tsakkiyar gidan kawai ta shige ta huta. Bawai bata san minene
aure ba, domin tanada zurfi a ilimin addininta, shiko musilinci ya fiddo mana komai dangane da aure cikin hikima da rahamar UBANGIJI. Matsalar kawai shine
komai yana zuwa mata baƙo ne. Bata saba ba, bata taɓa gani anayi ba. Bata karatun littafi sai ranar da Bilkisu ta bata, ko karatun tanayine cike da kunyar
wasu wajajen idan tazo a lokacin. Gidansu na hutawa ko tv babu, wama yake da lokacin zaman kallo, yo fitinar Abbansu ma tasa idan rashin kuɗi ya ciyosa ya