NOVELSUncategorized
RAINA KAMA (BOOK 3) 22

BOOK 3 ????????2⃣1⃣
……………..Kusan mintuna 7 da fitar Nurses d’in doctor yay Knocking, Galadima ya amsa ba tare da ya ajiye wayarba, doctor ya shigo abinsa, Nurse d’aya da sukai akin d’azun Na biye dashi.
Galadima ya d’ago yana kallonsu fuska babu walwala, Dan shifa yafara gajiya da wannan shigi da ficin, amma baice komaiba.
Doctor daya d’an tsargu yace, “Afuwan ranka ya dad’e, dama ina ganin yakamata tafara cin abincine, Dan ruwan da muke saka matane dama yake taimaka mata, to yanzu kuma zata fara shan magunguna insha ALLAH”.
Galadima yad’an sauke numfashi yana fad’in “ok, to amma yaranfa? za’a iya kawosu yanzu?”.
“eh to, sunkai nawa?”.
Yatsu uku Galadima ya d’agama doctor, dukda yayi mamaki saiya danne abinsa, musamman dayaga munayar y’ar k’arama da ita. yace, “Ranka ya dad’e dadai and’an k’ara mana lokaci koda kwana biyune, har yanzu zancen danake maka ba’ason abinda zai cika mata hayaniya a kai”.
Jinjina kai Galadima yayi kawai, alamar gamsuwa.
Daganan Doctor yay d’an dube-dubensa ya bama Galadima Drugs d’in Munayar akan Nurse zata dinga zuwa tana bata kullum.
Doctor Na fita shima ya ajiye wayarsa kusa da ita ya fito, d’akin da Nuren yake ya shiga, yana zaune Aunty Mimi Na bashi abinci a baki, Galadima yad’an hararesa yana fad’in “k’aton banza kacika shagwa6a”.
“Uhmyim” Nuren ya fad’a yana ta6e baki da rama Harar da Galadima ya masa.
Ita dai aunty Mimi murmushi kawai take da wannan rigima tasu dabata k’arewa, dama can inhar Nuren da Galadima Na waje sai kayi dariya, Dan kafin su rabu sai anyi kusan fad’a goma.
Galadima yace, “Ya jikin?”.
“Aini kam Alhmdllh, yanzu kawai maganar gaskiya amin aure, inda Na mutufa shikenan, kukan kwana uku zakuyi a wuce wajen, amma in mat……”
Hannu Galadima yakai zai bige bakinsa, yay saurin duk’ewa, Aunty Mimi ta sanya dariya, Galadima kuwa kwafa yay yana kallon Aunty Mimi, “oh ALLAH, maimakon kimasa fad’a dariyama kike masa? Wannan yaron wlhy fitsararrene, idan kunk’i masa aurenan zai iya zuwa yayi baku saniba ma”.
Nuren ya gyara zama yana hararsa, “Yo angaya maka ni irinkane, soyyaya Na cin zuciyata k’asaita ta hanani fad’e, Malam mufa dama munsan komai, munzuba idone muga yanda wasan zai k’are”.
Murmushin da Galadima bai niyyar yibane ya su6uce masa, ya mik’e da fad’in, “Duk iskancin da kamin ninaso, tunda nine nazo dubaka, idan nakuma zuwa d’akinnan kace ba sunanka Nureddin ba”.
“Ahaf, yo dama sunana Sameer ne?”.
Galadima bai kulashiba, ya kalli aunty Mimi daketa musu dariya, “Auntyna yakamata a sanarma gidansu ta farka, naga har yanzu babu Wanda ya iso”.
Murmushi Aunty Mimi ta masa, ta ajiye plate d’in datake bama Nuren Abinci tana cewa, “babu damuwa, mu barsu har zuwa yammar, tunda kaga har yau basu bada damar a shigaba”.
“Ok, hakan yayi”.
Harzai fice aunty Mimi tai saurin cewa “Abincinfa?”.
Kansa ya girgiza mata yay ficewarsa.
Nuren dake murmushi ya kalli Aunty Mimi yana fad’in “Auntynmu soyayya nacin Guy d’inan yak’i fahimta”.
Dariya tayi “Nuren kenan, ingaya maka sarai yasan yana sonta, shegen son girma da miskilancine kecinsa, amma ai naga alamar yanzu an wuce wajan”.
“A haba? Aunty da gaske?”.
“kwarai ma kuwa Nureddin”.
Hannu yabata suka tafa, yanajin wani sanyi a ransa, da sakama Muftahu albarka a zuciyarsa, danya zama aboki kuma d’an uwa Na k’warai.
Fitowar Galadima yaci karo dasu Yassar, ya fad’ad’a murmushinsa, shima yaran sun shiga ransa sosai, k’arasowa sukai gareshi, cikin girmamawa duk suka gaisheshi, ya amsa da kulawa.
“ku bakwa gajiya da yawo?”.
Soshe-soshen kunya suka farayi, Marcel yace, “ai daga gida muke, munzo muk’ara ganin jikin Aunty da Uncle ne”.
Galadima yad’an murmusa yana tura hannayensa duka a aljihu, cikin d’an lumshe ido yace, “kushiga to kugansa”.
“Uncle! Auntynfa? Ta farka itama?”. ‘Ahakam ne mai maganar’
Galadima ya jinjina kai. Yace, “ta farka Ahakam, amma tana barcine”.
Gaba d’ayansu farin cikine ya bayyana a fuskokinsu, kai kace y’ar uwarsuce ta jini, da wannan farin cikin suka shiga d’akin da Nuren yake, shikuma yakoma inda Munaya take murmushi d’auke a fuskarsa.
Dad’an hanzarinsa ya k’arasa gareta, ganin ta farka, zama yay a kujerar suna kallon juna, murya a sanyaye yace, “Kin tashi?”.
Da idanu ta amsashi.
Ya shafa kanta yana fad’in “Sannu, yanzu ina ke miki ciwo?”.
Fuska ta d’an yatsine, ta nuna masa hannunta da kanta.
Cikin tausayawa Yakuma mata sorry, sannan yace, “mizaki ci?”.
Kanta ta girgiza masa alamar babu komai.
Ya d’an 6ata fuska yana fad’in “Ban yarda ba, kinga kuwa yanda kika rame?”.
Murmusawa tayi, itama ta masa alamar wai ya rame shima.
Baki yad’an ta6e, amma baice komaiba ya d’auka wayarsa dake kusa da ita yay kiran Muftahu akan abinda za’a kawoma Munayar kozata d’anci.
Itadai kallonsa kawai takeyi. Ya yanke wayar yana kallonta shima da d’age mata gira d’aya alamar kallonfa?.
Dukda taji kunya saita yamutse fuska irin miye abin kallon anan.
Galadima yay wani miskilin murmushi cikin murya k’asa-k’asa yace, “Really?”.
Ta lumshe idonta alamun tabbabatarwa.
“zaki maimaitamin idan kin warke yarinya”. Yay maganar da wata siga harda cije lips.
Munaya ta kauda idonta tamkarma bata fahimci ina ya dosa ba.
A ranardai haka kowa ya yini cikin farincikin farfad’owar Munaya, gashi anbarsun sunshi sun gagganta, saidai anata musu gargad’in banda hayaniya, tausayin ta duk ya kamasu. Innaro harda hawayenta, aka saka bakin Zane ana sharewa da jemasu Alhaji balala ALLAH ya isa, harda cewa sai an koma kotu an sake sabuwar shari’a an kar6oma jikarta hak’inta.
Shi Galadima ma abin dariya ya bashi matuk’a, yadai had’iye yana duk’ar da kai baiyiba, wannan tsohuwa akwai abin dariya wlhy.
Munubiya kam rungumeta tayi taita hawaye, itama Munayar nayin nata.
★★★★★★*★★★★★★
Bayan kwana hud’u da farfad’owar Munaya jikinta yayi k’yau Alhmdllh, Dan tana samun kulawa ta kowanne 6angare, ciwukan jikinta ne kawai basu gama warkewaba.
Aunty Mimi da Laraba na a d’akin, Dan kowa ya tafi, suna zaune d’auke da su Abdurraheem da ake kawowa su yini yanzu, sai dare a koma dasu.
Munaya tana zaune ne a gadon datake jiyya an saka mata filo ta jingina, abincin da aka zuba mata taketa faman jujjuya cokali a cikinsa, tasaba kullum Galadima ke bata abincin, gashi yau tun safe da’aka kirashi ya fita bai sake dawowa asibitinba har yanzu, dukta damu, da taji motsin tahowa za’a shigo d’akin saita zata shine, sai anshigo taga bashi bane sai haushi ya kamata, Munubiya data fahimceta tsaf taita gumtse dariya har suka tafi, su Aunty Mimi hankalinsu gaba d’aya yanaga yaran, basusan mitakeyiba.
Turo k’ofar da akayi ya sakasu kallon k’ofar gaba d’aya, dan k’amshin turarensa yafara musu sallama kafin shigowarsa, wayace manne a kunnensa yana magana a hankali, hannunsa d’aya cikin wandon aljihun Ash color d’in shaddarsa daketa maik’o, Munaya daketa sauke k’ananun ajiyar zuciya tunda taji k’amshinsa tad’an saci kallonsa, shima idonsa a kanta, gira ya d’aga mata, tai saurin janye idonta tana tura baki kad’an.
Murmushi yayi ya zauna a bakin gadon kusada k’afafunta yana cigaba da wayarsa, yayinda yakema Amaturrahman da aka kwantar kusada ita wasa, yaran sund’an fara wayo, Dan idanuwa k’yar suyita kalle-kalle, kwanakinnan da suka dawo shan nono sunyi y’an k’u6ul-ku6ul dasu abin sha’awa.
Munaya dai tafara tura abincin da k’yar, sai wani faman had’e rai takeyi, shidai Galadima dariya na cinsa a rai amma baiyiba, saidai ya saci kallonta ya maida idonsa ga Amaturrahman data rik’e d’an yatsansa gam daya saka a d’an hannunta, kaikace tasan minene.
Sudai Su aunty Mimi da laraba suna cigaba da hirarsu, Dan laraba na bata labarin halinda su Abdurrahman suka shiga a kwanakin da Munaya bata farfad’oba ne.
Galadima ya ajiye wayar yana d’aukar Amaturrahman da fad’in, “O my lil princess I miss you”. Ya k’are maganar da sumbatar kumatunta, sannan ya juyo suka gaisa dasu aunty Mimi dake kallonsa shida babyn tashi abin sha’awa.
Cikin tsokana aunty Mimi tace, “Ai dama shirin kiranka nake danna kula my k’anwa bazataci abincin nanba sai kana kusa”.
Galadima ya juya yana kallon Munaya data waro ido tanajan mayafi ta rude fuska Dan kunya, dama aunty Mimi suna kula da ita kenan, itakam taga idi.
Galadima yace, “A lallai Aunty Mimi da gaskiyarki fa, kamarma kuka tayi?”.
“kad’an dai ya rage tayishi my k’ani, tun d’azun ina lura da ita, rabin hankalinta naga k’ofa”.
Laraba da Galadima sukayi dariya, ya kuma kallon Munaya data kasa d’ago kai ta kallesu.
Galadima ya had’iye dariyar dake Neman kufce masa, ya ajiye Amaturrahman d’in yana matsowa kusa da ita, Murya k’asa-k’asa yanda su Aunty Mimi bazasujiba yace, “Any problems my Princess?”.
Munaya ta saci kallon su Aunty mimi, ganin basa ganinta saita tura masa baki kad’an tana matso k’ananun hawaye.
“O my God”. ‘ya fad’a a hankali yana d’ora tattausan hannunsa saman nata, cikin wani salon daya saka tsigar jikinta tashi ya kar6ar spoon d’in. Babu shiri ta sakar masa.
Yakuma k’asa da murya yana d’ebo abincin da fad’in, “nifa kibarmin shagwa6arnan kokuma humm”. ‘ya k’are maganar da ciza lips yana jifanta da wani kallon mai cike da sirrika’.
Waro idanu Munaya tayi tana kallonsa baki bud’e. Abincin ya zuba mata yana kashe mata ido d’aya.
Kunya ta kamata, Dan wlhy Galadima bashida kunya ko kad’an, kad’an daga aikinsa ya aikata duk abinda yazo masa a rai d’in, danta San halin kayanta sarai.
bata k’ara yarda sun had’a idoba har yagama bata abincin, ya d’akko d’an Basket d’in da drugs d’inta ke ciki yana dubawa.
Aunty Mimi data kasa hak’uri ta mik’e tana tawa, “Oh ni Haneefa, dama abinda ya hanaki cin abincin kenan da gaske dai tun d’azu kiketa cuna baki my k’anwa”.
Munaya tai saurin jan d’an gyalen dake yane bisa kanta ta rufe fuska saboda kunya dataji, Aunty Mimi ma akwai iya 6aro zance, kuma ta Fiske abinta.
Laraba tayi y’ar dariya itama tana bin bayan Aunty Mimi suka fice, itakam dai birgeta sukeyi sosai, komai nasu a nutse.
Galadima dake binsu da murmushi ya juyo da kallonsa ga Munaya yana fad’in, “Saiki bud’e fuskar, dama haka kikeso su fita a barki daga ke sai mijinki ko?”.
Babu shiri Munaya ta janye mayafin tana d’an hararsa da kwa6e fuska tamkar zati kuka.
Ya ta6e baki da d’aukar ruwa ya zuba a cup yana mik’a mata, kauda kanta tayi gefe kamar bata ganshiba.
Mik’ewa yay ya koma kusada ita sosai yana sakata jikinsa, “Haba dai yalla6iyan yalla6ai miye na fushin to?”.
Munaya ta ture fuskarsa tana fad’in “Ni babu ruwana dakai, ka koma inda ka fito”.
Yace, “Oh God Babie na sorry kinji, wani babban uzirine ya rik’eni, yanzu dai ga maganin kisha, sai amin hukuncin laifina”.
Munaya ta matso hawaye sannan ta bud’e bakin ya zuba mata maganin ya bata ruwan tashanye, yakuma zuba wani, ahakadai tagama sha.
Dawowa yay tagabanta ya zauna yana murmushi, “Dad’ina dake shagwa6a, amin murmushin mana”.
Kauda kai Munaya tayi gefe murmushi na kufce mata.
Galadima ya dawo da fuskarta suna kallon juna, cikin k’ank’ance idanu yace, “ko kefa sweedy na, kindai hak’ura ko?”.
Kaita jinjina masa tana wani far da ido.
Hannunta mai lafiyar ya sumbata, yace, “Thanks My Queen, Saura wanka ko?”.
Munaya tai k’asa dakai saboda kunya, danta zata ya manta da maganar wankan da Doctor yace tafarayi yau indai zata iya. Murmushi Galadima yayi, dan kunyar tata na sakashi a shauk’i.
Kanta a duk’e tace, “Nidai kabarni zan iyayifa da kaina wlhy”.
Baice uffanba ya mik’e zuwa k’ofar ya saka key, yazo yawuce cikin bayin dake a d’akin. A sace ta bishi da kallo harya shige, ta lumshe idonta wani farinciki nabin sassan jikinta.
tsaf bayin yake, dan kullum cikin gyaranshi ake, hakama kayan ammafani irinsu boket, buta da sauransu komai need yake, ruwa ya saka danya d’anyi zafi dayake akwai wuta, ya fito yabarshi.
Har yanzu idon munaya a rufe suke.
Saukar Numfashin Galadima da k’amshin turarensa kawai taji a kan fuskarta, ta bud’e ido da sauri, Ashe yana gab da ita, motsawar datayi saiyazama kawai fuskarsu ta manne da juna, hakan yabashi damar aikata yanda yaso cikin sauk’i.
Batada za6in daya wuce mik’a masa ragama gaba d’aya, danya cancanci abindama yafi haka a gareta.
Tsawon mintuna biyu ya d’ago suna kallon juna, kasa daurewa Munaya tayi ta rufe idonta, yay murmushi gefen baki yana hura mata iska a saman idon.
Dole na bud’e idona nakuma sakasu cikin nasa, a hankali ya furta “I love you so much my Munaah”.
Murmushi na masa mai kashe ga66an jiki, na matsa kad’an ina bashi Sumba a kumatu, lumshe idonsa yayi yana sauke wani nannauyan numfashi, ya d’ora kaina a k’irjinsa, daddad’an k’amshin turarensa ya shige hancina, nima na lumshe idanu ina shak’a da godema ALLAH. muduka nutsuwa ta musamman ta sauka a zuciyoyinmu. Wayata datai ring ce ya sani d’agowa daga jikinsa na zauna sosai ina kauda fuska saboda kunyarsa.
Ganin Samha Ce na d’aga wayar cikeda farin ciki.
Galadima mik’ewa yay shima ya lek’a ruwan daya saka, ganin yayi zafi saiya kashe ya juye, surkawa yay, saida yaji yayi dai-dai sannan ya fito yana cire bottoms d’in rigar shaddarsa, hankalin Munaya baya garesa, shiyyasa batasan miyakeyiba, sai ji kawai tayi an amshe wayar tareda yin sama da ita. Da farko ma tsorata tayi, zata saka masa ihu yay saurin cemata “Shiiiii!!”.
Ajiyar zuciya na sauke na kallesa, ya kashemin ido d’aya. Murmusawa nayi ina janye idona daga kallonsa, dan naga lamarin nasa na Neman fin k’arfina, koya manta a ina muke oho? harda su cire rigafa.
Nidai wannan wanka anyisane kawai dan banida yanda zanyi, dan dana nema yin gardama saiya had’e fuska yana hararata, dole nabarsa yayi yanda yakeso, ya d’auramin towel ya kamo hannuna muka fito, Muduka Kallon Amaturrahman mukai daketa wutsil-wutsil da k’afafu.
Na zauna a bakin gadon shikuma ya jawo kujera ya zauna yana rik’o hannuna mai ciwo, fara’ar dake a fuskarsa dukta d’auke, alamar ransa yana 6aci inhar ya tuna tushen ciwon.
Cikin son kauda masa damuwarsa nayi murmushi ina d’ora hannuna mai lafiya saman nashi dake rik’e da mai ciwon, d’ago ido yay muka kalli juna, nad’an juya idanuna ina fad’in “yafi k’yau a haka ko?”.
Hararata yayi kawai baice komaiba.
Nayi k’aramar dariya.
Yiyay tamkar zai matsa hannun nai azamar janyewa ina d’ane gadon gaba d’aya dayin y’ar k’arar tsorata, kad’an yarage na haye Amaturrahman.
Murmushi yayi har hak’oransa na bayyana. yace, “ga tsoro ga tsiwa”.
Nace, “naji dai ba komai”.
Bai kuma cewa komaiba, sai murmusawa da yay, da kansa ya shafamin mai ya canjamin riga, dukda kakkauda fuskan kunya danaitayi, shikam ko a jikinsa, kai tsaye yake lamarinsa kuma hankali kwance.
A gurguje please????????.
*******
Satina Uku a Asibitin aka sallameni, jikina kam sai godiyar ALLAH, dan na warke sarai, saidai y’ar ramar danayi, dakuma ciwon kai dake yawan addabata inhar waje yacika hayaniya.
Tunda na dawo sai kuma kewar Galadima ta tasoni gaba, su Fauziyya nata shirin komawa gidajensu, sainaji inama harda mu????.
Tunda na fito asibiti Aunty Salamah takuma k’aumi wajen bamu kulawa, musamman ma ni, dan ita Munubiya ina asibiti akaita mata nata.
Tunda aka sallami Munaya daga asibiti ta koma gida sai yaji zaman k’asarma dukya gunduresa, ganin zai saka kansa a damuwa saiya had’a inasa-inasa yabar k’asar, itama Munaya rana tsaka yazo mata da zancen komawar.
Addu’ar fatan alkairi kawai tamasa, da kuma sak’on magungunan Abie, a ranar yaso shiga su gaisa da baba mai kanwa, amma sai akaje wai bayanan, d’ansa yaje kaisa wani k’auye nan kusa gaisuwar Mutuwa da akayi.
……………………….★
Su momma sunyi farin cikin dawowarsa garesu cikin k’oshin lafiya, sai dai y’ar ramar da yayi.
Shima wani matsanancin farin cikine ya kamashi ganin jikin Abie ya k’ara k’yau, yanzu har mitsa hanunsa yakeyi sosai, ga doguwar hira da akanyi dashi batareda ya k’osa ba, ranar sunsha hira sosai, har saida doctor d’in Abie yace subarshi ya huta sannan Galadima ya tafi gida shi da Momma, ranar Aunty Mimi aka bari wajen Abie tunda ita tasan komai.
Sabuwar hira Momma da Galadima suka kuma dasawa a gida, dukkan abinda yafaru yabata labari dallah-dallah, dukda Aunty Mimi tabata dama, Momma harda hawayen jin dad’i, ta rungume Galadima tana saka masa albarka shida matarsa da yaransu.
Babu kunya ya ringa amsawa cikin tsantsar farin ciki.
Yanzu kam koba komai hankalinsa ya kwanta, ya maida hankalinsa ga dukkan aikinsa da sana’oinsa da suke samun kud’in shiga akan jiyyar mahaifinsa.
Shiri yake a gaggauce saboda kiran da Doctor d’in Abie yamasa tun a daren jiya akan yanason ganinsa yau da sassafe.
Yayi k’yau cikin Orange d’in Suit, sai k’amshinsa yake mai dad’i, cikeda salon birgewa yake sakkowa daga steps d’in benen yana waya, bayin daketa aikace-aikacen k’imtsa falon duk suka zube suna gaisheshi.
Hannu kawai ya d’aga musu ya nufi hanyar fita a hanzarce yana cigaba da wayarsa, ya d’ora briefcase d’insa saman motar yasa key ya bud’e, bag d’in yafara ajiyewa gefen mai zaman banza sannan ya dawo ya bud’e ya shiga mazaunin driver ya tada motar ya fice.
“Muftahu kabari zamuyi magana daga baya dai kawai”.
Daga can Muftahu ya amsa da to babu damuwa.
Ajiye wayar Galadima yay ya maida hankalinsa ga tuk’insa, yayinda sashen zuciyarsa ke tunano masa hirarsa da Munaya ta daren jiya, kwana biyunnan idan yamata maganar dawowarta saitai ta masa yawo da hankali, yarasa dad’inmi zaman can d’in yake mata? Ai wankan jegon ya isa haka, shima yana buk’atar zama da iyalansa koya samu nutsuwa tamkar kowanne magidanci, k’aramar tsaki yaja yana furzo isaka daga bakinsa, mata kenan, wataran su baka zuma, wataran su caja maka kai.
Da wannan tunanin ya k’arasa asibitin, wayarsa kawai ya d’auka ya fita a motar, kai tsaye Office d’in Doctor Ajay ya nufa, yay Knocking aka bashi izinin shiga, (Abu Na CCTV suna kallon shige da ficin kowa) Doctor Ajay ya fad’ad’a murmushi sa yana mik’ewa, hannu suka bama juna cikin Musabaha suna gaisawa, Doctor ya nunama Galadima wajen zama.
Bayan sun zauna Doctor daketa faman murmushi yace, “Sameer wani abun farin ciki ne nasamo a daren jiya, shiyyasa nakasa sukune saida Na kiraka a daren domin buk’atar ganinka”.
Galadima dai kallonsa yake baice komaiba.
Dr Ajay yaci gaba da fad’in, “Wato wani Doctor ne mai suna Dr Erfan Fahad Sajaad, d’an k’abilar Kashmir ne, Likita ne babban masani ta fannin irin matsalolin su Abie, yanzu haka yana k’asar England akan wani aiki, nakai watanni 6 inason ganinsa akan matsalar Abie amma ban samu damaba, saboda matuk’ar Busy dayake, sai a daren jiya nasamu magana dashi, bakaji farin cikin dana samu kaina a cikiba, dan mun tattauna sosai akan matsalar Abie, yanzu haka yabamu date d’in dazamu sameshi can Kashmir a asibitinsa”.
Alhmdllh Galadima yaketa ambata a zuciyarsa tunda Dr Ajay yafara bayaninsa, cikeda farin ciki yace, “Doctor lallai nayi farin ciki da wannan albiahir naka sosai, ka wuce matsayin likita kawai a garemu saidai d’an uwa”.
Murmushi Dr Ajay yayi, suka rungume juna shida Galadima kowa yanajin dad’i a ransa.
Galadima ya fito d’auke da wannan farin ciki sukaci karo da Akash a hanya.
Akash yace daddyn Triplets kenan, kwana biyu ka 6uya?.
Hannu Galadima ya bashi yana fad’ad’a murmushinsa, yace, “Sorry my friend ka ganni dai yawo kamar ruwan sama, idan bani anan aganni acan, ya aikin?”.
“Gashi munata fama, ya naka?”.
Galadima yace, “Alhmdllh”.
“Wai sai yaushe zaka dawo mana da Mummyn triplets ne? ga bikina yanata matsowa, bafa zan muku alfarma ba”.
Murmushi Galadima yayi, ya dafa kafad’arsa yana fad’in “kwantar da hankalinka, ai babu yanda za’ai bikinka babu mu a wajen”.
Aksha yace, “Ato kun wanke kanku, daga ina ka fito haka cikin farin ciki?”.
Bayanin komai Galadima yayma Akash, dan baya 6oye masa komai gameda ciwon Abie.
Shima ya nuna tsantsar farin cikinsa kuwa, kafin suyi sallama kowa ya nufi inda zaije.
Waya yaciro yana lalubo number Munaya…………….✍????
Zan iya cewa yanzu zaku dinga rashin ganina, wlhy ammana haihuwar da tilas saina kasance a wajen a kullum, amma inhar Na samu time zaku dinga ganin posting, dan yauma banyi tunanin zanyiba, amma saigashi ALLAH yabani iko bayan dawowata daga asibiti, nima kaina Na k’agara nagama Na huta kuma Ku huta????????♀, I love you all????????????????❤????????
ALLAH ya gafartama iyayenmu????????????