WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 1

“Nanne me na mata, naga ko zaman kishi ba mu yi da ita ba, kuma na riƙe mata ya’yanta amana,amma shine za ta nime rayuwata bayan ta rabani da mijina al halin ba sa tare, me na mata dana cancanci irin wannan hukuncin? Ta karasa faɗa tana kifa kanta saman cinyar Nanne, tana rusa kuka mai matukar tayar da hankali. 

Tabbas Asma’u abin tausayi ce,wacce ta cancanci da a tausaya mata,abu ɗaya ne kawai yaƙe taimakon ta wanda ya ke kare ta, ya kuma hana su cin nasara a kanta, wanda da tuni sun kashe ta sai dai labaran ta,dan da bakinsu suka faɗa a lokacin da aka kaita wurin wani mai magani wanda a lokacin ne aka fara samun nasara a kansu har aka samu suka fara magana, nan suka faɗa wacce ta turo su, sannan su ba komai suke so ba illa rayuwar ta kawai suke buƙata,duk irin wahalar da suke sha a wurin malamai amma sun ƙi fita, kamar yanda suka kasa cin nasara a kanta, domin Asma’u yarinya ce mahaddaciya Alkur’ani,wanda duk wannan bala’in da take ciki,karatun Alkur’ani baya taba barin bakin ta,hakanne ke hana su cin galaba akan ta,idan sun so sukan daura ma mutane tsanarta, ta hanyar saka mata rashin kunya na tsiya,dan wani bi zata zauna rumui-rumui ku yi hira da ita,amma idan yan iskan na kusa, idan ta fara zuba rashin kunya sai kaji kamar ka tsine mata albarka saboda takaici,dan wani bi idan abin ya motsa in tanayi har wani watsar da miyau gefe za ka ga tanayi, irin dai na tatattun marasa kunya,ga mai hankali idan yaga hakan yakan mata fatan samun sauki da shiri ya,domin duk wanda ya san Asma’u a da ya san wannan ba halinta ba ne sam,amma ga mutanen wa’yanda basa tuna baya, sai dai su bita da zagi da tsinuwa,ajiyar zuciya ya sauke, wannan duk tunanin Baba Mudansir ne, wanda tun dazu yake tsaye bakin kofa yana jinsu,dan basu ma san da zuwan shi ba, ganin kukan nasu ba mai ƙarewa ba ne,yasa ya shiga kawai. 

“Ni kam wai yaushe za ku gama kukan nan ne? Ya fada yana ɓata fuska. 

” Ɗan nan duk randa Allah ya nunamin Fettel ta dawo mutun kamar kowa”

“To yanzun ita ba mutum ba ce? 

” To da dai sauki,tunda yanzun zaka ganta a mutum zuwa anjima ta koma kamar wata Aljana, ko mahaukaciya,kaga ta ina zan kira ta mutum ”

Girgiza kai kawai yayi”Ke Asma’u ɗaga ta”

Ɗagata tayi tana gyara zama, sannan cikin dashasshiyar muryarta ta ce “Babana ka tashi lafiya”

Murmushi yayi “ya kukan banza, gaya nan kinsa mana uwa kuka” Ita dai ba ta ce komai ba sai dukar da kai da tayi. 

Cikin sanyin murya da lallashi ya shiga yi masu nasiha ita da Nanne.

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button