WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 11

 ????WATA TAFIYAR????       Story & Written

                By

         Jiddarh Umar

????????????????????????????????

*????✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION????✨*

https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

 *“`We are the moonlight writers we shine all over the world.“????`* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم

~~~~~~~????????~~~~~~~

PAID BOOK

                      

               11

Ga mai buƙata zai turo 200 ɗari biyu ta wannan Asusun 2284905309,Hauwa bUmar Zenith Bank, 

Sai ki turo shaidar biya ta 08141644865.

Ko Katin Waya.

Da Bismillah ta fito,har cikin dankareren falon suka shiga,daga nan suka shiga da ita in da aka nuna masu a matsayin  bedroom ɗinta,sosai suka yaba da yanayin tsarin komai,Baba Mudansir ne ya fara mata nasiha sosai mai matukar ratsa jiki, kuka take sosai,daga nan sai matan ƴan uwan Baban ta,sosai aka masu sha tara na arziki sannan aka maida kowa har gida,kasancewar ƙarfe biyu aka ɗaura Auren yasa kafin ƙarfe huɗu gidan ya zama shuru.

Gabaɗaya hankalin ta a tashe yake domin kuwa wani irin tsoro hade da fargaba ne ya ke kamata,irin wannan babban gidan ace ita kaɗai ne zata zauna a cikin,ganin lokacin sallah La’asar yayi ne yasa ta tashi ta shiga ta ɗayan ƙofar da ta gani,ga mamakin ta  wani ɗakin ne shima harda kujeru da kayan kallo,”ikon Allah “ta furta a fili,ganin wani kofa ne yasa ta ƙara tura shi, wannan karon kam an dace domin babban banɗaki ne, domin ba ƙaramin kauyanci ta sha ba kafin ta fahimce yanda za ta yi amfani da komai. 

Duk bayan awa biyu wata mata wacce ta ke tunanin ƴar aiki ne takan zo ta tambayeta ko tana buƙatar wani abu,haka kuma da Magrib ita ta kowa  mata abinci, sannan bayan sallar Isha’i ta ƙara shigowa “ranki ya daɗe idan kina bukatar wani abu sai in kawo maki, dan yanzun zan wuce”

Kallon ta ta yi,akalla matar tana iya haihuwar ta,koma ta haifi wacce ta fita shekaru ” Mama ba anan kike kwana ba? 

Ɗan kallon ta tayi jin sunan da ta kirata da shi “A’a ba anan nake kwana ba,sai dai  da sassafe nake zuwa sai in wuce bayan sallar Isha’i”

“Kenan ni kaɗai ce zan kwana a wannan babban gidan? 

Ɗan murmushi tayi”ki yi haƙuri ƴa ta amma ba ni da hurumin da zan amsa miki wannan tambayar”

“Kamar ya? 

” Tunda baki da bukatar komai Uwar ɗaki na,mu kwana lafiya “ba tare da ta jira jin mai Asma’u zata  kara faɗa ba, ta juya da sauri ta bar ɗakin. 

” Innalillahi wainnailaihi rajiun,Allah na gode maka daka kawo ni  irin wannan gidan mai cike da sarƙaƙiya “banɗaki ta shiga ta kara yin wanka,Akwatunan ta ta buɗe ana huɗu ne ta samu kayan Barci,dan haka mai dan ƙauri ta zaba ta saka,addu’a ta yi ta shafa a jinta sannan ta haye gado ta kwanta.

Har bacci ya fara ɗaukar ta wuraren ƙarfe sha biyun dare ta fara jin kamar tafiyar mutane, kamar kuma ana bige-bige ana magana, tsoro ne ya kamata,gashi kuma bata kulle kofa ba,jin kamar ana zuwa ta ƙofar dakin da take ciki ne yasa cikin zafin nama da gudu ta sauko ta shige ɗayan dakin ta kullo ƙofar ta saka sakata,tsabar tsoro jikin ta har rawa yake,ta kusurwar ƙofa ta leka,wasu mutane ta hango su biyu suna magana ƙasa ƙasa, sai dai bata iya jin abin da suke faɗa, haka kuma bata iya ganin fuskar su kasancewar sun juya baya ne,sai dai kaman ɗayan yana sanye ne da kaya irin na ƴan aikin asibiti,tana kallon su har sanda suka juya suka fita,ajiyar zuciya ya sauke tana mai dafa kirginta “yau nikam na shiga uku,su waye kuma waɗannan,wata zuciya ce ta ce,to in kuma Angon ne fa, da sauri ta girgiza kai,kai ba shi bane,dan bata yanda za ayi yazo a irin wannan lokacin, kuma jikin ta bai bata yana cikin waɗannan mutane ba,ranar dai kam anan ta kwana kan kushin.

  ASUBA TA GARI AMARYA

Washegari da safe,kasancewar bata san yanayin gidan ba shi yasa koda ta yi niyan gyaran ɗaki ba wasu kayan aiki,kuma ita Allah ya gani tsoron fita take daga dakin,shi yasa lokacin da Mama ta iso,suna gama gaisuwa,ta ce “Ranki ya daɗe ko zaki iya  komawa can falon sai in kyara miki nan? 

” Ba damuwa Mama kawo kawai in gyara dama tun daxu naso in gyara amma ba kayan aiki ”

Rike baki ta yi “wane ni, dan Allah ki rufa min asiri,aiki na ne ki bari kawai in yi”

“To shi kenan,amma in kin gama ko zaki dan zazzaga dani inga yanayin gida? 

Dan shiru ta yi kamar mai wani nazari,, sai kuma tace ” To Ranki ya daɗe ”

Tana zaune tana kallon ta,yayin da  ta shiga duniyar nazari,to ina mijin da ta aura yake,wanda ko sunan shi yanzun  haka bata sani ba,ita  dai ta san ko wani Ango murna da doki yake da Amaryar sa a rana  ta farko,to amma shi wannan me yasa bata gan shi ba,kuma har yanzun da ake niman ƙarfe takwas na fase,to ko dai shi ne da abokin shi suka shigo jiya,amma kuma ai in shi ne bai kamata ya shigo da abokin shi har dakin barcin ta ba, sannan kuma in da shi ne,da  sunan ta ya kamata ya kira a lokacin da bai ganta kwance saman gado ba,sannan kuma ya ni me ta, amma kuma wannan duk bai ye haka ba,ita gaba ɗaya ji take kanta ya kulle,tunanin ta ya cushe, Mama ce ta dawo da ita daga tunanin data faɗa “Ranki ya daɗe na kammala,mu je ki karya sai in raka ki”

Kai kawai ta gyaɗa  mata,sannan ta tashi tabi bayan ta.

Abinci ne irin na yan gata ko in ce irin na ƴan gayu,amma duk da irin waɗannan abincin wanda yawancin ma bata taba ganin irin su,hakan bai sa ta sake jiki ta ci sosai ba, dan gaba ɗaya hankalin ta ba a kwance yake ba,sai yanzun ta gasgata zancen da ake cewa duk daɗin abu ko kyan abu idan har hankalin ba a kwace yake ba to baka gani kuma baka ji. 

Tana kammal ci, ta  ce wa Mama wacce ke ta goge gege “na kammala mu je”

“To ranki ya daɗe”

A hankali suke takawa tana nuna mata wure,”ranki ya daɗe nan ne Garden wurin shan iska,wannan kofar kuma in kika shiga ciki dakin motsa jiki ne,”ta wani kofa suka shiga”Wow Mama nan ina ne? 

“Nan Lanbun mai gidan ne, yawancin lokuta yafi zama anan lambu na biyu,”

“Kai amma wurin ya haɗu sosai” Zazzagayawa take a  wurin,dan cike yake da kalan itace masu matsakaita tsawo,waɗanda suka zuba Albarkatu ga sunan gwanin sha’awa kasance gaba ɗaya dasu aka yi ado wurin zagaye wurin,icen mangwaro,gwaiba,Apple,gwanda,da dai sauran su,sosai ta zagaya wurin,har zasu fita sai ta hango wani ƙofa makale da bangon wurin,wanda sai ka lura sannan kasan da ƙofa a wurin “Mama wannan ƙofar fa? 

” Ohh wannan kofar zai iya sadaka da waje ”

“Kamar ya”

“Ina nufin ƙofar yana fita waje ne,idan ka buɗe to kai tsaye bakin titi zaka ga kanka”

Gyaɗa kai ta yi,sun daɗe suna zagaya babban cikin gidan harta da harabar gidan sai da suka je, ita sam bata ma lora da masu tsaron  ba, waɗanda ke sanye da kaya kamar wasu ƴan sanda,harda police Dog suke yawo, sun kai kusan su takwas,gasu baƙaƙe mutane dasu,hmmm.

Cikin gida suka koma.

Yau tsayin kwanta biyu kenan a wannan gidan amma har yanzun shiru ba Ango ba labarin shi,tun abun baya damun ta har hankalin ta ya fara tashi sosai da lamar gidan,dan kullun da ƙarfe sha biyun dare sai ta ji wannan motsin da kuma maganganun,a kwana na biyun ne ta samu Mama a kicin tana aikin hada abinci rana, gaisawa suka yi,sannan ta ce “Mama ni kan me yasa ba ki kwana anan”

Dan kallon ta ta yi “saboda akan tsarin haka ne aka ɗauke ni”

“To ki dinga kwana anan mana”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button