Labarai

2022 Shekarar Yin Sulhu Ce Da Neman Zaman Lafiya, Inji Ganduje

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce sabuwar shekarar 2022 kamata ya yi ta zama shekarar neman sulhu da zaman lafiya tsakanin ’yan siyasar Jihar da ma na kasa baki daya.

Ya ce alamomin sulhun da suka fara bayyana tsakanin kusoshin siyasa a Jihar babbar nasara ce, kuma suna nuni da cewa saura kiris a kafa wani babban tarihi a siyasar Jihar.

Ganduje na wadannan kalaman ne a cikin sakonsa na sabuwar shekara, kamar yadda Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar a wata sanarwa ranar Juma’a.

A cewar Gwamnan, “A cikin ’yan watanni masu zuwa, za mu tsammaci ganin sauye-sauyen da za su bunkasa Dimokradiyyar cikin gida a jam’iyyunmu, ta hanyar fitar da nagartattun ’yan takara, wadanda kuma za su zama shugabanni nagari.”

Kamar yadda Aminiya ta rawaito saidai Ganduje ya nuna damuwarsa kan yadda ya ce al’amuran tsaro na dada tabarbarewa a kullum, kari a kan wahalhalun tattalin arzikin da ’yan kasa ke ciki.

Amma Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa duk da tarin kalubalen, inda ya ce gwamnati mai ci ta Shugaba Buhari na iyaka kokarinta wajen sauke nauyin alkawuran da ta dauka.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta karasa dukkan manyan ayyukan da ta fara don inganta rayukan al’ummar Jihar, musamman ma na yankunan karkara.

A ’yan makonnin nan dai, alamu na nuni da cewar a akwai yiwuwar Gandujen ya yi sulhu da tsohon maigidansa, kuma tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bayan sun shafe kimanin shekara biyar suna zaman doya da manja a siyasance.

An fara ganin hakan ne tun lokacin da Gandujen ya je yi wa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar kaninsa, sannan wasu kusoshin gwamnatinsa su ma suka rika tururuwar zuwa.

 

 

 

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button