WATA TAFIYAR 11

“A’a ba ni da hurumin yin haka”
Shiru ta yi kamar ba zata ƙara cewa wani abu ba,sai can kuma kamar wacce aka matse bakinta akan dole sai ta faɗa, tace”Mama wai ina mijana ne?
Kifi take wankewa amma jin abin da Asma’u ta tambaya yasa ta tsaya cak,sai kuma ta juyo gaba ɗaya tana fuskantar ta”ke da yake mijin ki ma biki sani ba, ballantana ni da nake ƴar aiki”
Kwabe fuska ta yi,cikin kosawa da sabon yanayin da ta tsinci kanta a cikin ta ce “to ni na gaji ne da zama haka,kuma kullun cikin jin tsoro na ke,ni gaskiya a maida ni gida” tana faɗan haka ta juya ta koma ɗaki cikin jin haushi,wallahi yau sai dai tsoro ya kashe ta amma sai ta fita da dare ta ga nema idanunta me ke faruwa.
Tana ganin ta bar kicin din, da sauri ta ciro wayar da ke sake a zanin ta, ta shiga lasawa,can kuma sai ta hau magana a hankali “Yallabai aƙwai matsala fa!!
Daga ɗayan bangaren ya ce”wani iri”
“Wai ta gaji gida zata koma, sannan ta fara korafen wai bata ga mijinta ba”
Dariya ya fashe dashi sosai “shegiya Mahaukaciya, ashe har ta san miji, to kar ta damu,nan da kwana kusa zan tura su in da ba a dawowa ita da mijin, sai su je can su karasa soyayya” ya ƙarasa faɗa yana fashewa da dariya,yayin da take taya shi “sannan ki ci gaba da saka mata ido a duk wani motsin ta ki sanar da ni”
“To yallabai”
“Zuwa dare de zamu shigo, dan haka sai ki kasance a shirye”
“Ok to sai kunxo yallabai” daganan suka sauke wayar, yayinda ita kuma taci gaba da aikin ta hankali kwance..
[ad_2]