LabaraiTinubu

An Sace Min Duk Takardun Shaidar Karatuna – Tinubu

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya shaida wa Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC cewa duk takardun shaidar karatunsa sun salwanta.

Tinubu ya shaida wa INEC cewa wadansu mutane da har yanzu bai iya gano ko su waye ba sune suka sace masa takardun shaidar kammala karatuttukansa a lokacin da ya yi gudun hijira ya tsere daga kasar.

Tinubu, wanda tsohon gwamnan Jihar Legas ne, yana daya daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar National Democratic Coalition (NADECO) da suka yi gudun hijira a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa, Marigayi Janar Sani Abacha.

Ana iya tuna cewa Abacha ya murkushe malamai, masu fafutuka da sauran manyan masu fada a ji da suka yi adawa da mulkinsa.

A cikin bayanan rantsuwa da ya shigar a takardun bayyana manufar neman takarar Shugaban Kasa ga Hukumar INEC, Tinubu ya ce “na yi gudun hijira daga watan Oktoban 1994 zuwa Oktoba 1999.

“Amma lokacin da na dawo na tarar cewa an yi awon gaba da kadarorina ciki har da duk takardun da suke nuna cancantata da shaidar kammala karatuttukan da na yi.

“Kuma har yanzu ban iya gano wadanda suka yi min wannan aika-aika.”

Tinubu wanda ya tsallake sashen shigar da bayanan karatunsa na Firamare da Sakandire a fom din da INEC ta gabatar, ya bayyana cewa ya halarci Jami’ar Chicago da ke Amurka a tsakanin 1972 zuwa 1976, inda ya samu shaidar digiri na farko a fannin Tattalin Arziki.

Ya kuma ce yana da digiri a fannin Kasuwanci da Gudanarwa, da kuma wata takardar shaidar Satifiket ta nazarin Kula da Asusun Al’umma.

Da alama dai sabbin ikirari na Tinubu sun saba wa wanda ya gabatar a baya, musamman a shekarar 1999, lokacin da ya tsaya takara kuma ya lashe zaben gwamnan Jihar Legas.

A wancan lokaci Tinubu ya ce ya yi Firamare a Makarantar St Paul Children’s da ke Ibadan daga shekarar 1958 zuwa 1964; yayin da ya yi karatun Sakandare a Kwalejin Gwamnati Ibadan (GCI) daga 1965 zuwa 1968.

Sai dai biyo bayan raddin da aka yi masa, tsohon gwamnan ya rike bayanan karatunsa na Firamare da Sakandare lokacin da ya sake tsayawa takara a shekarar 2003.

Ya yi ikirarin cewa daga karatun da ya yi a Ibadan, kai tsaye ya wuce Kwalejin Richard Daley da ke Chicago a Amurka a tsakanin 1969 zuwa 1971.

Kazalika, a karshe ya ce ya halarci Jami’ar Jihar Chicago da Jami’ar Chicago.

Sai dai wani fitaccen lauya a Najeriya, Marigayi Gani Fawehinmi ya kalubalanci bayanan shaidar karatuttukan da Tinubun ya gabatar, yana mai cewa babu kamshin gaskiya a ciki, amma daga bisani Kotun Koli ta yi watsi da karar.

A nasa bayanan da ya gabatar, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce digiri na biyu da ya kammala a shekarar 2012 shi ne mafi koluluwar shaidar karatu da yake da ita.

Asali  Aminiya

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button