AL'AJABI

AL’AJABI part 1

AL’AJABI part 1
Tsaye yake ya dafa tebirin dake gabansa tare da
rankwafawa kansa na kallon tebirin dake
gabansa, kallo daya zaka yi masa kasan a cikin
damuwa yake.
Ya dago kansa tare da matsawa yaci gaba da
takawa ya fara safa da marwa a cikin faffadax
ofis din nasa, tsawon lokuta ya shafe yana kaiwa
da komowa ya rasa me ke masa dadi.
A tsayen ya zura hannunsa ya zaro wayarsa dake
al‘jihu ya lalubi lambar wanda yake son kira tare
da karata a kunnensa ya taka a hankali izuwa
kan kujerarsa ya zauna, hannunsa daya na rike da
wayar yayinda dayan hannunsa ke dafe bisa
tebirin dake gabansa.
Hello!! ya fada dai-dai sanda aka daga wayar
sannan ya dora da cewa “ Ranka ya dade yarinyar
nan fa har yanzu bata zo ba ina tsammanin ma
ba zuwa zata yi ba, gaskiya na gaji ga yamma na
dada yi kuma na gaya maka uzuri gareni ga
yamma na dada yi.“
Cikin rarrashi wanda ake yiwa wayar yace “
Ahmad kayi hakuri ta taho go slow ne ya riketa
amma yanzu zata karaso.“
Ahmad din ya kara bata rai ya kauda wayar daga
kunnensa ya ajiye wayar bisa tebirin dake
gabansa ya kwantar da kansa jikin kujerar ya
zubawa kofar shigowa ofis din ido, sai daya shafe
wasu mintuna ashirin din babu alamun wani
zaizo sbd takaici runtse idonsa yayi kamar barci
yakeyi sai dai a zuciyarsa 2nanin irin fadan dazai
rufeta dashi kawai yake.
As-salamu-alaykum.
Wata zazzakar murya tayi sallamar data saka
Ahmad saurin dago kai tare da gyara zamansa
yana me kallonta har izuwa sanda ta zauna tana
me fadin “gani na iso“.
2nanin da yake tayi a baya sai yayi saurin kawar
dashi domin kallo daya yayi mata yasan tafi
karfin wulakanci ko a tozartata ba karamin
kwarjini gareta ba, zunzuru2n kyau kuwa ba‘a
magana lallai Allah yayi halitta.
ya fada a zuciyarsa.
Amma dai kinsan kin bata min lokaci ko??
ya fada yana dubanta.
ba tare da alamun nadama ba tace “ Eh nasani “.
To me yasa?? koda dai ance wai go slow ne ya
rikeki??
Ya tambaya ba tare daya dubeta ba shima.
Tayi saurin girgiza kai tace “ gaskiya karyane
hasalima ban taba hawa titi fayau irin yau ba, ni
din ce kawai ban taba hawa titi fayau ba motoci
irin yau ba, ni din ce kawai ban gadamar fitowa
da wuri ba.”
A karo na biyu ya sake dubanta da sauri ya danyi
shiru na dan lokaci sannan ya kawo gwauron
numfashi ya gyara zama yace ” Ance min in jiraki
za’a miki dan interview na yan mintuna kuma a
daukeki aiki a baki ofis kai tsaye, koda bansanki
ba amma nasan tabbas wanda ya tsaya miki
babba ne don ban taba ganin inda akai hakan ba
sai akanki don wasu da wuya suke neman aikin
basu samu ba wata kila hakan ne yasa kike wani
ji dakai kina gadara aikin ma ba wani damunki
yayi ba.”
Ta tsuke baki sanda ya kawo karshen zancen
nashi tace ” Gskyne ba damu na yayi ba kusan
ma ince maka tilastani akai sbd ansan nice zan
taimaka muku ba kune zaku taimaka min ba,
batun wanda ya tsaya min kuwa koda a fadar
shugaban kasa ya nema min aiki ba wanda ya
isa ya hana bare nan.”
Tayi nuni da ofis din a wulakance.
Ahmad ya sake binta da kallo a zuciyarsa yace “
Wannan tafi ni bala’i.”
Ya gyara zamansa tare da jawo laptop din dake
gabansa ya mayar da hankalinsa gareta jim
kadan ya dago kai yace ” Meye sunanki?? “
Kanta na duban tebirin dake gabanta tace “
HUMAIRA “.
ya danyi shiru kadan kamar me sauraron kara jin
wani abu daga gareta, jin tayi shiru yasashi ture
laptop din daga gabansa ya dubeta yace “
Yakamata kiyi min adalci, kin bata min lokaci a
zuwanki amsa tambayar ma sai kin sake bata
min wani lokacin??”
Au wai kana nufin full name?? To sunana
HUMAIRA ISMAIL.
Ta fada tana me kallonsa.
Ya jawo laptop sanda yayi tsaki kasa-kasa.
Meye level din karatunki??
Ta amsa da cewa ” Masters degree “.
Yayi saurin dubanta cikin mamaki a ransa ya
sake maimaitawa ( masters ) tab!!!!!
Wacce jami’a??
Ya sake tambayarta kansa nakan laptop din.
Ta dan kauda kanta kadan tace ” oxford
university- ENGLAND.”
Bai san sanda ya sake dubanta ba cikin mamaki,
A yarinya dole kiyi girman kai!! Ya fada a
zuciyarsa.
Yayi saurin kauda kada ta fahimci halin da yake
ciki yace ” kinzo da takardunki ne??”
Babu bukatar zuwa dasu 2nda ba maular aiki
nake ba dazan rinka yawo da takardun
makaranta.
Bala’i!!!! Lallai wannan tafi ni masifa.
Ya danyi shiru zuwa jimawa yace ” last question!!
Relationship??”
Tayi shiru kamar bata jiba ya sake maimaitawa
da hausa da fadin ” budurw, bazawara ko matar
aure?? wannan abu ne da dole a sani a duk inda
mace zatai aiki a duniya.
Fuskar Humaira tayi saurin canjawa izuwa yanayi
na damuwa tace ” Don Allah kasa UNKNOWN
kawai.”
Ahmad ya hade rai cikin takaici ya shafa kansa “
Wai ke wace irin mutum ce don Allah ?? Ya kike
meman kisani ciwon kaine?? baki ma san ke
budurwa ce ko bazawara ko matar aure ba?? “
Tayi saurin gyada kai tace ” Eh bani da tabbacin
zama daya daga cikinsu.”
Ahmad ya mike cikin tsawa yace ” wallahi
karyane hakan baya taba yiwuwa dole a samu
kina daya daga cikin wadannan azuzuwan “.
Ta mayar masa da martani da cewa ” ba wani
dalili da zaisa inyi maka karya 2nda ba aljanna
zaka bani ba don haka karka kara karyataniakan
abinda baka sani ba.
Ta dubeshi hawayen dake idonta suka yi
gaggawar zubowa ta dora da cewa:
” Na rantse da Allah idan nace maka ni
budurwace nayi karya!! Idan nace maka ni
bazawara ce nayi karya!! Haka idan nace matar
aure ce ni karya nake!! Ni kaina bansan da sunan
da zan kira kaina ba.
Ahmad wanda fusata ta sashi mikewa yayi saurin
komawa ya zauna idonsa ya zaro sbd mamaki, da
AL’AJABI zuciyarsa ta fara sake-saken tayaya
ma hakan zata faru??????????????????????????
???????
AL’AJABI part 2
NA A.A. muhammad
with==>Aßu Fer’ezerh
Ahmad yaci gaba da kallonta kawai har yanzu
mamaki ne cike fal kuma rubuce a fuskarsa,
Abinda ke yawo a zuciyarsa shine:
Babu alamar wasa a tare da ita, hasalima
hawayene ke zuba bisa idanunta a halin yanzu
kuma gashi ta rantse, Tabbas hakan na nuni da
cewa har cikin zuciyartane abinda take fada.
abin AL’AJABI mafi girma da kunnuwansa suka
taba jiye masa kenan.
Tunani daya da yayi wanda ya kore 2nanin da
yakeyi a baya shine: To kodai don ni namiji ne
yasa ban fahimci abinda take nufi ba??
Tabbas shine dalilin.
Ya bawa kansa amsa dai-dai sanda ya dubeta
tare da zaro wasu takardu dake gabansa ya dora
a gabanta yace ” Yanzu dai shikenan kiyi hakuri
ki daina kuka ga kundin takardun da kike bukata
a aikinki bari nasa masinja yayi miki jagoranci
izuwa ofis dinnaki, daga yau kece babbar me kula,
da adana bayanai na wannan ma’aikatar ALLAH
YA TAYA RIKO.”
Yakai karshen maganar dai-dai sanda ya waiga
tare da kiran sunan masinja, BALA!! BALA!!!
Da sauri ya karaso tare da dukawa yace
“Yallabai”.
Ahmad ya dan kwantar da kansa bisa kujerar da
yake zaune yace ” Kuje da ita ofis no: 11 ka
hadata da sakatariya zanyi mata waya.”
Da sauri bala masinja ya amsa da ” To Yallabai “
Ya wuce yayi gaba.
Humaira dake zaune ta mike ta jawo jakarta
wadda ta dade da dorata bisa faffadan tebirin
dake gabanta, ta debi takardun da Ahmad ya
bata ta zuba a ciki tare da gyara zaman bakin
glass din dake da fadin rufe idonta daya matukar
kara mata kwarjini.
Ta dan bishi da kallo kawai ta juya ta nufi kofar
fita daga ofis din, Yayi saurin cewa ” Koda ba
yanzu ba ina fatan na sami labarin rayuwarki
wanda ta yiwu ya warware min rudanin dana ke
ciki.”
Tayi saurin dakatawa tare da dawowa da baya a
hankali tace ” Idan har ba kana yin haka bane
don ka gano hanyar karya zuciyata ba to na
rokeka ka bari, ka kalleni a humaira kawai karka
takura wajen binciken wacece ni sbd ba abune me
samuwa a wurinka ba, Ta dan kara daga
muryarta tace ” Bakina bazai taba iya furta
labarin daya faru dani a baya ba kamar yadda
kwakwalwata ba zata juri tunano hakan ba, idan
kana son mu zauna lfy dakai karka kara taso min
da wannan zancen.”
Takai karshen zancen cikin tsawa a dai-dai
lokacin data canja gaba daya kamar ba ita ba.
Taja da baya ta fice da sauri.
Ahmad ya bita da kallo lkc guda ya mike izuwa
tagar ofis din ya hangeta ta glass kai tsaye wata
tsaleliyar mota kirar TOYOTA PRADO ta dosa ta
bude motar ta shige, motar tata tabi bayan
tsohuwar HONDA CIVIC wadda bala masinja keja
don yi mata rakiya.
Ahmad ya kauda kansa daga wurin ya fara
takawa a hankali cikin ofis din, Yarinyar nan fa ba
karya takai tayi takama ko gadara, kallo daya
yayiwa motarta yasan ta fito ne daga gidan masu
akwai, to amma meye mummunan abinda ya faru
da rayuwarta har yasata shiga yanayin da take
ciki?? menene musabbabin hakan??.
Abin nema ya samu don haka wlh sai na sani
kota halin kaka.
Ya fada a fili, ya juya ya rufe laptop dinsa tare da
jawo bakar jakarsa ya zirata a ciki, jakar tasa na
hannunsa yayi waje.
Kai tsaye motarsa ya nufa yabi tsaleliyar hanyar
data nufi kudu, a ransa ya darsa cewa ya fasa
zuwa inda yayi niya 2nda yamma ta riga tayi.
Duk da sanyayyar wakar mawaki justin bieber
dake tashi a hankali cikin motar tasa baisa ya
manta da abinda ke ransa ba.
Mintuna Ashirin ya kwashe ya gangaro cikin
katafariyar unguwar tasu, rukunin gidaje na
NEWCLAX QTRS. tsararriyar unguwa ta gani da
fada.
Worn daya yayi a bakin tafkeken koren gate din
ya fara budewa a hankali bisa jagorancin wani
siririn matashi wanda yayi saurin cewa ” sannu
da dawowa “.
Ahmad ya gyada kai tare da fadin yauwa.
Ya wuce da motar yayi parking dinta a harabar
gidan ya wuce izuwa cikin, shigowarsa falon keda
wuya yaji kyas!! Alamun daukar hoto, yar
kyakykyawar budurwar ta tuntsire da dariya tace
” gaskiya yaya hoton nan yayi kyau, bari a kara
maka daya.”
Ya dan harareta kadan yace ” ke baki da wani
aiki saina daukar hotunan mutane a waya ko??”
Ya karasa ga daya daga cikin kujerun dake
zagaye a katafaren falon, momi dake zaune kanta
na kallon TV din dake jikin bango ta juyo gareshi
tace ” Ahmad an dawo kenan??”
Wallahi momi sai yanzu,
Ya fada cikin ladabi.
Dai-dai lokacinne saudat ta dire farantin juice
dake hannunta ta tsiyayo lemon a dan karamin
kofi ta mika masa, Ya amsa tare da cewa ” Thank
U my blood sister, yau dai kina da kirki “.
Ta juyo tace “yau kawai??”
Ya gyada kai yace ” iya yaune kawai “.
Ta juya ga momi dai dai sanda ta karasa ga
kujera ta zauna tace ” momi kinji shi ko??”.
Momi ta mike tare da cewa “zaku fara surutun
naku kenan? to bada ni ba bari na shiga ciki
lokacin sallah ya gabato.”
Shigewarta sashin nata keda wuya Ahmad ya
dawo kujerar da saudat ke zaune yace ” yauwa
ina da tambaya watakila keki sani don nidai nayi
iya tunanina na kasa ganowa amma fa gsky zaki
gaya min pls”.
Tayi murmushi tace ” fadi muji idan na sani “.
Ya gyara zama yace ” Tayaya mace zata zama
ba budurwa ba, ba bazawara ba, kuma ba matar
aure ba?? Sannan da wane suna za’a kirata?? “
Saudat ta danyi shiru can tace ” waye yayi maka
wannan tambayar?”
Ya girgiza kai tare da cewa ” ba ruwanki kawai ki
amsa min idan kin sani “.
Saudat ta kyalkyale da dariya tace ” Amma yaya
anyi saurin juya 2naninka daka kasa gano amsa
me sauki irin wannan, mace na iya zama ba
bazawara ba, ba budurwa ba, ba matar aure ba
IDAN……….!?¿¿
Good morning….
*** AL’AJABI PART 3
.
Hakan na iya faruwane kawai idan fyade akayi
mata, kaga ta tashi daga budurwa, kuma ba
bazawara bace sannan ba matar aure ba. Ahmad
yayi shiru cikin salo na nazari jim kadan y girgiza
kai yace ‘ gaskiya baki fada dai-dai ba wacce aka
yiwa fyade ai ta zama bazawarako??” Saudat tayi
shiru kawai tabishi da kallo, tabbas ya ta gsky
kuma ba dai-dai ta fada ba. Ahmad yadan
harareta kadan ya tashi izuwa kujerarsa yace ” ke
dama idan ba danna waya ba me kika sani??”
Saudat tace ” to ai ko ba komai nayi kokari 2nda
nayi tunanin abinda kai baka yiba.” Ahmad ya
kauda kai yace ” kinyi tunani amma useless ne “.
Tabishi da kallo tace ” kasan abinda za’ai? “. Ya
girgiza kai alamar A’a.
.
Tace “bari mu tambayi momi 2nda ita tsohon
hannu ce ta yiwu ta sani sai ta fada mana,” Ta
yunkura da nufin kiran sunan MOMI, Ahmad yayi
saurin dakatar da ita yace ” KE! rufa min asiri,
bar don Allah. ” Ta kwantar da kanta jikin kujerar
ta kyalkyale da dariya tace ” Amma dai yaya duk
sanda ka samo wannan amsar don Allah nima ina
jira sbd ina son nasan yadda akai hakan zata faru
don nidai ina ganin da kamar wuya…..” Ahmad ya
mike rike da jakarsa yace ” kada kiyi saurin
karyata abinda baki sani ba, kiran salla ake bari
na shiga ciki nayo alwala. ” Tabishi da kallo
kawai har ya shige dakin nasa, ta juya ta kwanta
bisa doguwar kujerar tare da cigab da danna
wayarta.
.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Leave a Reply

Back to top button