WATA TAFIYAR 3

Da Uncle Tahir ya fara cin karo a tsaye yana jiran karasowar shi,ɗan ɓata fuska ya yi, ganin yanda sai wani washe baki yake kamar bashi ya gama azal-zalan shi daya dawo gida ba jiya,ya na karasowa ya rungume shi “barka da dawowa ƙasarka ta haihuwa,da fatan ka dawo lafiya”
Shima dan sake fuska ya yi “lafiya Uncle,na same ku lafiya” daganan ciki suka shiga,har bakin kofar shiyan shi ya raka shi”kayi wanka ka ci abinci sai kazo mu yi magana dan suna babban falo kai kaɗai dama ake kira”
Gyaɗa kai kawai ya yi, sannan ya shige cikin.
Unguwan Daji,Gidan Ɗan Nanne
Ba ita ta buɗe ta ba sai da takwas na safe,saboda zuwa lokacin yawanci mutanin gidan sun ragu,tana buɗewa ta da sallama ta shiga ɗakin,zaune ta same ta kamar ko wani lokaci da sandanta a hannu,sai dai wannan karon yanda kasan mahaukaciya sabon kamu,dan yanda ta bar baza suman kanta ya sauko mata har gadon baya,ga idonta da yayi zuru zuru sai zare su take yi,alamun dai yau akwai rigima ke nan. A hankali ta ƙira sunan ta”Asma’u “banza ta yi da ita,ƙara kiran sunan ta ta yi nan ma shiru ta mata sai uban harara data maka mata,” Taso muke Nanne na kiran ki”
Jin ance Nanne na kiran ta yasa ta ja wani uban tsaki ta murguda mata baki,,sannan ta tashi ta fita abin da,
ɗakin ta fita bako ɗankwali akanta yasa da sauri tabi bayan ta,”Asma’u zo kisa ɗanƙwalli, tsaya in kawo maki”amma ina kamar ba da Ita ake magana ba, dan ma tuni ta shige shiyan Nanne, wacce ke zaune kawai sai ganin mutun ta yi tsaye a kanta”na shiga uku, ke me haka, kin tsayamin aka”
Hararan Nanne ta yi, ganin haka yasa ta gane yau ƴan iskan na kusa ke nan, “to Allah ya kyauta,ni ma wuri ki zauna” Sai da ta ja mata tsaki sannan ta zauna,kallon-kallo suka shiga yima juna tsakanin ta da Nanne,
Can dai da abin ya ishe ta,ta kalli Asma’u taga sai faman hararan ta take tana murguda mata baki”Allah ya tsine maku Albarka,ƴan shegu marasa kunyan fitsararru,ni dai ba haka jikana take ba, kuma in Allah ya yarda ba abin da za ku yi da ita,jikata tafi karfin shaidanu irin ku,”
Tsaki mai ƙarfi ta ja tana ƙara murguda ma Nanne baƙi,
Allah sarki tsohuwa, sai kawai ta fashe da kuka”debabbun Albarka,kukan ko a cikin jinsin Aljannu daga ganin ku ƴan Ta’adda ne ”
Shigowar Salma da Karima ne ya katse mata surutan da take yi, sai dai ba ta bar kuka ba da facen majina,
“A’a Nanne lafiya,waya taɓa ki” Cewar Salma.
Ita dai Karima kallon abin da Asma’u take yi kawai ta ke.
Cikin kuka ta ce “ni da waɗannan yan Ta’adda ne”
Gaba ɗayansu kallon ta suka yi,Karima ce ta ce”ina suke”ƙara fashewa ta yi da kuka tana muna masu Asma’u dake zaune ta daura ƙafa ɗaya kan ɗaya,
Gaba ɗayan su, lokaci ɗaya suka kwashe da dariya har da tafa hannu,suna nuna Nenne su nuna Asma’u,ita dai sai tsaki take tana yamutse fuska,
Tsawan da Baba Mudansir ya masu shi ya dakatar da su, dan shigowar shi kenan.
Millioniar Cutters
Zaune suke a wani ƙayataccen falo,su uku ne shine cikon na huɗun su,Uncle Nasir,,Uncle Tahir,Uncle Ahmad, sai shi,gaba ɗayansu zaune suke saman tebur dake ɗauke da kujeru, magana suke yi,,
Uncle Nasir ne ye”a gaskiya lokaci ya yi da ya kamata ace mun kawo karshen wannan abun,dan shekara uku ba wasa ba ne ”
“Maganar ka gaskiya ne,ni kaina matse nake da wannan lamari” Cewar Uncle Tahir.
“A gani na Aure kawai ya kamata mu yi ma shi,kaga ta hakanne za musamu cikar burin mu na shekara da shekaru” In ji Uncle Ahmad.
Gabaɗaya hada baki suka yi wurin kiran kalmar Aure,har dashi uban gaiya.
Cikin ɓata fuska yace”Uncle Aure fa, ta ya ya, a hakan”
Basu amsa yayi”saboda ta hanyar matar kadai zamu iya samun abin da muke so”
Gaba ɗayansu shiru suka yi suna nazarin maganar shi, Uncle Tahir ne yace”wacce irin mace ya kamata ya Aura,”kallon Haris ya yi “ko kana da wacce kake so ne?
Girgiza kai ya yi” Babu sai dai ko zan bincika”
“To in ma kai zaka bincika ko mu zamu bincika ma, ya kasance ko ma wacece,dole zai kasance wacce ba ta yi zurfi a karatun Boko ba,ba ta da wayau sosai, ba ta da cikken hankali,,ina fata kun gane,kuma ba na son a ɓata lokaci”cewar Uncle Ahmad.
” Ta yaya zamu samu irin wannan yarinyar,kasan yaran yanzun da shegen wayau”Uncle Nasir ya fada
“Ai shi yasa nace mara hankali”
Haris ne ya katse su”shi kanan zan samo irin matar da kuke so in aura,zan nemo irin ta a duk in da ita”yana kaiwa nan ya tashi ya fita.
To fa akwai magana kenan a ƙasa……
[ad_2]