WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL

WATA TAFIYAR 4

Kai kawai ya gyaɗa mashi. 

godiya ya shiga yi mashi. 

“Maza shiga gaba mu je”

Ba tace komai ba ta zagaya ta shiga gaban motar,kasancewar tasan da mutun a bayan motar, kuma shima bai yi motsin da za tasan da shi ba,har bakin  juction din ya ajiye ta “dan Allah Asma’u ki karasa gida,kin ga ba karami tashi hankalin Nanne da Baba ya yi ba”

Ita dai ba tace komai ba,sai juyawa da tayi ta gangara cikin unguwar abinta,

Ƙaramin tsaki ya ja, “Allah ya shirya ki”

Ta bayan shi ya ji an  amsa da “Amin”

Dan juyowa ya yi,”yallabai na gode sosai fa”

“Ba damuwa,amma ƙanwar kace? 

” Eh, yallabai ”

“Naji kace tana da matsala,wacce irin matsala gare ta”

Ajiyar zuciya ya sauke”dogon labari ne yallabai, sai dai in ce maka kawai,tabin hankali,dan yawancin lokuta ta fi yin abu kamar mai hauka”

“Tana da Aure ne? 

” A’a sun rabu da mijinta, saboda ta dalilin shi komai ya faro,dan da kyar aka samu ya sake ta”

Shiru yayi kamar ba zai kara cewa komai,sai kuma ya ce”ta yi karatu kuwa”

“Eh, ta yi school of health” 

dan shiru ya ƙara yi, yana nazari. 

“Yallabai lafiya”

Da sauri ya dai daita kan shi “lafiya klau”

Jinginar da kan shi yayi,ya na sakin wani irin murmushi  wanda da wuya ka fahimce manufar yin ta,hummm lallai wannan shine babban damar shi,gaskiya ta yi ta ko ina,na tabbatar za ka yi murna da wannan Little Bro,,hummm,zan so ganin me zai faru, dole ne ya auri irin matar da su Uncle suka zaɓa, dole ne ma wannan.

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button