WATA TAFIYAR COMPLETE HAUSA NOVEL
WATA TAFIYAR 7

Gaba ɗayan su a lokaci ɗaya suka sauke a jiyar zuciya” Kai Allah dai ya rabamu da wannan takadirin yaron”uncle Tahir ya faɗa.
“Allah dai yasa mu gama wannan aikin lafiya da shi,dan ni wallahi tsoron shaiɗancin shi nake yi” uncle Nasir ya ce..
Shi dai uncle Ahmad yana jin su bai ce komai ba,sai wani irin murmushi da yake yi wanda shi kaɗai yasan ma’anar yanshi,wanda idan da zaka lura zaka fahimta tabbas ko ma menene yake sakawa a ran shi,to ba Alhairi ba ne.
[ad_2]