Yadda na riƙa haɗa jinina da zoɓo ina siyarwa mutane -Wata mata mai cutar ƙanjamau
Wata mata mai ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki (HIV) watau ƙanjamau ta bayyana cewa ta haɗa jininta da zoɓon da take siyawar domin ta sanya wasu mutanen su kamu da cutar.
Matar ta bayyana hakan a wani shirin gidan rediyon Wazobia FM mai suna MarketRunz a daren ranar Laraba. Jaridar The Punch ta rahoto.
Mai gabatar da shirin ya nemi masu sauraro da su kira waya su bayyana abinda suka yi a kasuwa wanda mutane basu sani ba wanda kuma ba su ji daɗin aiwatarwa ba.
Matar ta bayyana dalilin da ya sanya aikata wannan ɗanyen aikin
Matar mai siyar da zoɓon ta bayyana cewa:
“Naje asibiti wata shida da suka wuce inda aka gayamin ina ɗauke da cutar ƙanjamau.”
“Na fara sanya jini na cikin zoɓon da nake yi na siyarwa sannan na siyarwa da mutane da dama.”
“Na ɗebi jinina da sirinji sannan na haɗa shi da zoɓo. Da ni ma’aikaciyar jinya ce amma bayan an tabbatar ina ɗauke da cutar ƙanjamau dole na bar aikin.”
Matar ta bayyana dalilin da ya sanya aikata wannan ɗanyen aikin
Ban ji daɗin abinda na aikata ba amma naji daɗi ba zan mutu ni kaɗai ba.”
“Yanzu na kai wata shida ina yin wannan taɓargazar sannan ina fatan ubangiji zai yafe min.”
Sai dai, binciken da jaridar The Punch tayi, ta gano cewa ba’a ɗaukar cutar ƙanjamau ta hanyar ruwa ko abinci.