MAKAUNIYAR KADDARA 50

 *Page 50*

……….Soaai AK yayi mamaki matuƙa da ganin abokansa waɗandama shi kobi takansu bayayi yanzun, hakama abokan harkar business ɗinsa dake anan Nigeria. Dole dai ya ware ya shanye mamakinsa ya shiga basu hannu suna gaisawa da tayashi murna, tare da masa ƙorafin ba’a gayyacesu ɗaurin aureba sa fatin da babu amarya babu ƴammatan amarya balle Uwargida. Murmushi kawai yakeyi bai iya cewa komai dan baida abin faɗar.

    Daga haka komai ya kasance a nutse cike kuma da birgewa. Dan abune na masu aji sam babu wata hayaniya. Anci ansha an sake taya ango da amarya murna da musu fatan alkairi, zuwa goma taro ya tashi lafiya kowa yana sam barka. Baƙi suka koma masaukinsu masu gidaje anan kano suka kama gabansu. 

     Sosai AK yaji daɗin fatin nasu kuwa. Dan koba komai ya haɗu da tsoffin abokansa da uzurorin rayuwa ya sashi mantawa dasu. Koda ya ɗan leƙa gidan nasu bayan sun tashi kasa zama yayi saboda hayaniyar ƴan biki, wai a hakanma wasu sunyi barci saboda gajiya, dole yayma su Baffah da Uncle Ahmad da suke nane da juna sallama ya gudo gida.

       Lokacin daya shigo gidan Farah tayi barci, dan haka shima kayan jikinsa kawai ya zare yay wanka da neman makwanci saƙe-saƙe fal ransa. Musamman fargabar zuwan su Mammah gobe idan ALLAH ya kaimu da Mahma ta sanar masa. Sam bayason Mammah tazo ta tada hankalinta a cikin wannan taron mutanen ƴan biki, shiyyasa tun ɗazun abin ke damunsa da ƙyar yaketa faman tausar kansa.

    Yau sukai niyyar tahowa Mahma ta sake lallaɓasu akan su zauna zaman shirya abubuwa yanda zasu iya tunkarar Baffah. Dan  sunyi aniyar tahowa su shiga garin danya da akace musu amarya take kafin su wuce kano. Hakan yasa Mahma kautar da hankalinsu har amarya ta isa ɗakinta lafiya sannan. Tasan dai idanma sunzo a gobe insha ALLAH aikin gama ya gama kuma.

     _______________________★

    Washe gari aka tashi da shirin gagarumar walima wadda daga ita kuma sai miƙa amarya Zinneerah ɗakin mijinta. Zinneerah data kwana a ɗakin AK ita da Adilah kuwa da zazzaɓi ta tashi, amma tanata daurewa dan har wasu ƴan sauran gyara da suka rage hajiya Falmata tai mata a daren. Tsabar gyaran data sha maranta har wani ciwo yakeyi mata. Haka dai ta cigaba da daurewa har hajiya Iya ta shigo ɗakin domin dubata. Dan Adilah dake fashin salla ma ko tashi a barci batayiba.

       Sun gaisa da hajiya iya take tattaɓata ganin duk tayi wani iri, “Kai Inno ai zazzaɓi ne a jikin nan naki, haka kika kwana da shi ma ko?”.

      Cikin ƴar shagwaɓar da suka sabama hajiya iyan ita dasu Jamal ta ɗaga mata kai idanunta na cika da ƙwalla. Sannu hajiya iya ta shiga jera mata, kafin ta taimaka mata shiga bayi dan ta samu tayi wanka. Koda tayo wankan ta samu ta shirya cikin atanfa sabuwa ƙal data amshi jikinta ɗas ta fito a amaryarta, Adilah kanta data farka sai yaba ƙyan datai takeyi, murmushi kawai Zinneerah keyi dan sosai take ganin girman Adilah ɗin kasancewarta ba ƙarama ba, sai dai kawai ALLAH ya bata ƙaramin jiki ga kuma yanayin inda ta tashi rayuwar turai, dan ita hausarma ba iyawa taiba tunda ba zuwa Nigeria ɗin Mammah take bari tayiba. Iya kacinta dasu magana da turanci, saiko AK dake iya jin yaren Mammah na larabci sukanyi, shiyyasa basa shiri da hajiya iya sosai saboda takaicin Adilah ɗin bata iya hausaba.

     Tea hajiya iya ta kawo mata a sha da magani ta sake kwanciya kafin lokacin walimar. 

★★★

      A katsina kam ko breakfast ɗin arziƙi basuyi zaman yiba suka kamo hanyar kano, lokacin da suka iso gidan anata kwasar mutane zuwa ƙaton hall ɗin da za’a gudanar da walimar. Yanda anguwar ta rikice da kai kawon motoci masu kwasar mutane yasa dole su Mammah suka fakin tun a waje, Mahma ce kawai ke dauriyar gaisawa da mutane, amma Mammah da Aunty Zakiyya sunata shan ƙamshi.

    Koda suka iso cikin gidan sun sami Baffah tare da baƙi, yana ko ganinsu yabar baƙin da uncle Ahmad ya nufosu fuskarsa ɗauke da murmushin daya sake fusata Mammah, aiko tayi kicin-kicin da rai tamkar zata fasa ihu. Sai dai batace komaiba bisa ga gargaɗin Mahma da sukasha.

      Duk yanda Aunty Zakiyya taso nuna halin nata ga Baffah kasawa tai, dan wani irin kwarjini yay mata da cikar kamala. Dole tai ƙasa da kanta tana gaisheshi da girmamawa. Shima cike da fara’a ya amsa mata harda tsokanarta.

     Yanda Mammah ta ɗauke kanta daga garesa haka shima yayi tamkar bai gantaba, cikin girmamawa yacema Mahma su shiga ciki. Murmushi tai masa, yay gaba suna binsa a baya har sashensa tacan baya da ƙofar falonsa ta ainahin bedroom ɗinsa take. Dan yasan acanne kawai babu wani hayaniyar mutane da hankalinsu zai kai kansu saboda wutar bala’i daya hanga a idanun Mammah.

     Kafin su shige ya aika Jamal da sukaci karo ya sanarma hajiya iya zuwansu, daga nan ya wuce a haɗo abinci a kawo musu. Mammah zatai magana cikin masifa Mahma ta dakatar da ita da idanu, dole taja bakinta tai shiru tana haɗiyar zuciya.

          Cikin ƙanƙanin lokaci hajiya iya ta ƙaraso tareda su Bahijja dake ɗauke da abinci, suna ajiyewa suka gaishesu suka fice. Mahma da aunty Zakiyya ne kawai suka gaida hajiya iya, Mammah kuwa sai da Mahma ta harareta sannan ta gaisheta da ƙyar. Hajiya iya bata damuba kam, dan ba yaune farauba.

         Yanda hajiya iyan ta nuna rashin damuwarta ya ƙara zafar Mammah ta fara magana a ƙufule, “Kabeer  miye wannan ke nufi?”. Tai maganar tana ajiye masa invitation card a tsakkiyar centre table. Uncle Ahmad daya shigo falon ne ya ɗauka ya duba ya maida ya ajiye. Kasancewar shima ɗan zafin kan ne a gadarance yace mata “katin gayyatar walimar liyafar cin abincin auren gudan jininmu mana”.

     Kallonsa tai rai a ɓace tana juya idanu, “Kai kuma bansa da kaiba mijin tace, kaji da taka matsalar kafin ka tsoma baki a ta wasu”.

        “Hakan na nuna miki cewar wadda ta maidani mijin tace ɗin tafiki komai, tunda ke kin kasa maida Yayana mijin tace ɗin saboda ƙarancin ƙyaƙyƙyawan nazari da kishin hauka dake damunki. In banda abinki Hindatu tayaya kike tunanin raba ƴaƴa da mahaifinsu ta ƙarfin tsiya? Ke waya rabaki da naki har suka bar duniya”.

         “Wlhy Ahmad ka kiyayeni, kasan na fika zafin kai”.

    “Anƙi kiyayar taki, kiyi duk abinda zakiyi”.

       “Zako kaga mizanyi ɗin, dan wlhy wannan auren kun ɗaura banza saina rabashi, in banda son zuciya taya yaro yana zamansa lafiya da matarsa zaku ƙaƙaba masa auren yarinya baƙauya mara galihu………”

       A fusace hajiya iya ta katseta da faɗin, “A rashin galihun nata shi ɗan naki ya gani yakeso, tunda har ya iyama yarinya ciki a waje ta haihu ita ƴar son naki bata haifaba. Hindatu ki kiyayeni wlhy, ina ɗaga miki ƙafa saboda ɗanki, amma inaga wannan karon saina fito miki a Amina ta, moddibo ne dai ya dawo gidansu kenan daga shi har ƴar uwarsa babu kuma yanda kika iya. idan buƙatar kasancewa kike dasu kema saiki dawo gidan ubansu ki zauna cikin kishiyoyin da kike gudu. Dan daga yau na yanke shawarar moddibo ya dawo ƙasarnan da zama kenan da iyalansa idan kin gansa a wata ƙasa sai dai yaje harkokinsa ko gaisheki ya dawo wlhy”.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button