HAUSA NOVEL

YANCI NA 1

YANCI NA 1 TO END

8/30, 9:40 AM] ???????? ???? ???? ???? ???? ????????????: * *’YANCINA PART ONE (1)* *
.
Acikin Garin Bauchi, Gidan marayu wanda ke rufe sai kuma d’aid’ai kun jama’an da suke zuwa ziyara dakuma ganin marayu domin su samu subayar da d’an abun dasuke dashi ko Allah zai basu lada suma, Cikin gidan, wata baiwar Allah ce, wacce ta manyanta domin zata kai shekaru daga daya har zuwa hamsin(50), rike da wata jaririya ta zura mata ido, sauran mai’katan suna faman kimtsa yaran da basu da wayon, yayinda wasu kuma suke wasanninsu, gwanin sha’awa, wata yarinya yar kimanin shekara bakwai(7) ne tazo aguje rike da duwatsu a hannunta, ta kumbushe su acikin yatsunta tamkar za’a daketa a kwace, biye da ita kuma wani yaro ne shima bazai wuce shekaru bakwai d’inba, suka nutsu gaban dattijuwan yana kokarin kwacewa yayinda take tusawa ajikinta tana cewa “wayyoni! Wayyoni!! Wayyo hajiya kice ya sake min hannu, zafii” dattijuwan ta kallesu sannan ta tsuke fuska tana cewa yarinyan “mairo!, a rayuwanki yaushe zaki nutsu? Yanzu meye zakiyi da duwatsu kullum saikin d’ibo na hanaki kinki yadda, yanzu innace zan dake ki saiki fara zaro ido”, aikuwa mairo ta tsaya cak ta zubar da duwatsu sannan takoma gefe ta zauna shima yaron yabita zai zauna hajiya tace mishi “dawo nan ka zauna!, gaggaren yaro kawai” shikam komawa yayi inda yafito, yayinda mairo ta ke jira hajiya ta tashi, tafi awa d’aya kafin tamike tashige daki, dasauri mairo ta tattare duwatsun sannan ta tusa su a aljihun dogon rigan kantinta wanda yasha dattin kasa, ta tabbatar ta boyesu yadda hajiya bazata ganeba sannan takoma ta zauna, alokacin indo daya daga cikin masu rainon marayun take kallonta tana dariya, aranta tana mamakin halin naci irinna mairo.
.
Hajiya kamar yadda sunan take, itace babbar ma’aikatan dasuke rainon marayun gidan, suna bata girmanta iya gwargwado sannan macece mai tausayi saidai tana da zafin rai, tana da nuna gwaninta yayinda masu ganin marayu suka zo, musamman cewa gidan ya kunshi kananun yara dayawa, tabbas duk wanda yaleka gidan yasan cewa gidane wanda yara basu da galihu duk da gwamnati na kokarinta don ganin ta taimakesu haka wasu daga cikin al’umman sukanzo, yara ne farare kyakyawa inka gansu abun sha’awa, wasu akan tsince su ne akan hanya ko na kauyuka, wasu hatta acikin bola ana ciro su sai akawosu, wasu akan hanya ake tattaro su akawo su, saidai taimako yasa yaran suntaso cikin kwanciyan hankali, suna samun wadataccen abinci, sutura saikuma acikin gidan anware musu aji inda suke karatu, tundaga aji daya na nursery izuwa primary da secondry, akan samu masu taimako a gwamnati sai su tura mazan kasan waje yayinda matan ake kokarin aurar dasu, sunfi auruwa a tsakanin yan’uwansu marayu Mairama yar kimanin shekara bakwai (7), tun tana jaririya aka kaita gidan, inda wata mata ta kawota cewar ta tsinceta a hanyan alkaleri dake garin bauchi, ankawota a cunkushe cikin tsumma, daga gani bata wuce kwanaki biyar a duniya ba, hakan yasa aka mata register sannan aka rada mata suna maryam, saidai hajiya dasauran ma’aikatan suke kiranta mairama, hakan yasa ta taso da sunan, yarinya ce fara tana da kyau, kaman sauran yan’uwanta, da kunshin gashinta wanda yake da yalwataccen tsayi, tanada gagara, dakuma wayo, sai dai batada surutu sai neman tsokana, tafi magana da jiki akan bakinta, hakan yasa ma dayawa daga cikin ma’aikatan suke sonta, suke kuma jin dadin zama da ita. Ganin cewa hajiya ta shige cikin gida yasa tamike takoma inda tafito gun wasan su taje, lilon wasan yara ne dawasu tarkace dai wanda aka siya musu don debe musu kewa, ta zo gefen yaron sannan tace “umari kaga kasa hajiya ta harareni meyasa?”, baikulata ba ya damko ta sannan yafara lalumen cire duwatsun tuni tasa kara, wanda duk fad’in gidan babu mai kaunar jin wannan karan, tsantsan damunsu dayakeyi indo ce tazo dasauri, tana kokarin rabasu anma saida umari yakwashe duwatsun sannan yace “dutse na nefa”, yana fada hawaye na zubo mishi don indo dukanshi tayi akai, ganin haka yasa mairama ta ce “meyasa zaki dukeshi? To nima ki dukeni” bata kulata ba tajanye umari, sannan tajuyo tanunata da yatsa ” ke annoba ce wai? Kullum acikin gidan sai anrabaki da wani, kinsan duwatsun sa ne wayace kidauka?
.
Yarinya sai bakin hali” jin haka yasa mairama ta cuno baki takoma gefe tazauna, saukan numfashinta kawai akeji, ma’ana kuka takeyi, Har magrib tayi mairama na zaune bata motsa agun ba, duk yaran sunshige cikin gidan don suyi alwala suyi sallah, manyan kuma sunwuce masallaci, yanmatan ma sun wuce fanninsu, tana zaune bata mike ba, ga sanyi na damunta domin jikinta k’akk’arwa yakeyi, Hajiya daga ciki bayan ta idar da sallah taje dakin cin abincin su inda yaran kowa yazauna a inda yake zama ansaka mishi kwanon abincinsa, yayinda jariran kuma ake basu madaran ruwa, taga kwanon mairama, “ina mairama?”ta furta tana kallon ma’aikatan, a lokacin ne suka lura bata nan, tuni indo ta tuna cewa da yamma ga abinda ya faru, ba tace komi ba tafito dasauri alokacin har tafara bacci ta kudundunu tamkar bargo, d’aukanta tayi cak tanufi cikin gidan da ita, hajiya tanufota tana matsifa, “ke kinsan halin ta sarai, bawai baki sani ba, tunda kinsan kinmata fada dole ki koma kiyi baiko ko ta kwana muku agun, ko kin manta haka takeyi ne?, kin kuma san itace shalelen malam manager don dazaran yazo za’a fada masa kuma kinsan sakamakom ki bazai yi dadi ba” tana gama fada ta dauki torchlight ta fice, indo dai sai faman kokarin canjawa mairama kaya takeyi, alokacin tafarka, nan ta saka mata rigan bacci ta daura mata sannan tajawo hannunta, d’akin cin abincin suka je, ta ajiyeta agun sannan takoma tazauna addu’anta mairama taci abincin nan kafin hajiya ta cinye ta da matsifa, kowa zaiyi abu baza’a damuba anma idan mairama ce toh antabo musu shalele, domin akanta sunsha cin albarkan arziki da mutunci. Tasaka a baki tamkar tana tauna flagyl, itadai indo kallonta take, inta d’ibo sai ta bata, ahaka taci rabi, sannan tamike , “Ina zakije?”
.
Indo ta tambayeta , bata amsata ba sai tattare riganta data farayi tanufi d’akin kwanansu, sallanta ta dungura, a iya iyawanta datayi,nan tabi lafiyan gado, hajiya dai data leka taga tana bacci ne tabar d’akin, Kiran sallan asuba ne yamikar da ita, domin a fannin matan mairama ce take tashinsu, kiran farko take mikewa, domin wataran ko isha sai an tasheta tayi takoma, tana tashi tamike, tafara jan kafafun na gefenta wanda kansu d’ayane, wasa kulya tafara mata dasauri tamike, haka ta ringa tashinsu daya bayan daya, daga mintsini sai tasa bakinta a kunnensu ta fara hurawa ko ta musu wasan kulya, daya bayan daya suka mike, ta tsallakesu sannan tajawo kujera ta saka agefen kofan sannan tahau ta murd’a ta bude, fitowa tayi tanufi dakinsu indo basu bud’eba kuma dama basu cika budewan ba basu son tashi sallah, hajiya ce take kokarin tashi da wuri donhaka ta dauko dan dutsenta ta hau buga musu kofan, “le indo ! Le indo!! Kitashi, kutashi asuba tayi!, liman yana kiran masallaci kuje !” Tsabar takaici indo da hanzarinta ta bude kofan jin zata bude tana kokarin murd’a kofan yasa mairama rugawa da gudu takoma dakinsu sannan tarufo kofan, Indo cikin takaici tace “wannan yarinya ba abun muyi magana ba, yanzu hajiya tace mun takurata, yar kutumar wa, da asuba ai ko liman baya tashi a bacci amma kiran farko zata fara tashin mutane, ni nagaji da wannan iskancin” Hansat wacce itama ta mike don bakin ciki tace “maganinta zamuyi don taga tana saurin bacci, yanzu muhanata bacci sai karfe goma na dare hakan ne zaisa tana lattin tashi,” Ahaka suka gama gunaninsu itadai mairama tasa yan dakinsu sunmike bawanda yakoma, abunka da yara nan suka hau wasa, su ba da sallahn ba su bada bacci ba, saida hajiya tazo ta sakasu a layi, d’aya bayan d’aya sukayi alwala sannan ta shimfida musu sallaya sukayi salla yayinda mazan suka fice dama d’akinsu daban ne,
[8/30, 9:40 AM] ???????? ???? ???? ???? ???? ????????????: * *’YANCINA PART TWO (2)* *
.
Bayan sun idar wasunsu sunkoma yayinda wasu kaman mairama suke zaune, idonta a bushe take, tazauna tana karanta adduan da umma ta koya musu na safe da maraici, layi dad’d’aya take koyamusu ahaka suke rikewa, karfe shida hajiya tafice takoma daki don tasamu tadanyi bacci , alokacin indo sunfito zasu karbi lura da yaran, tunda indo ta shigo dakin mairama na gefen katifa taki matsowa balle a bugeta, aikuwa indo sai aika mata harara take, masu girkin safe ne suka fara shigo da d’umamen tuwon dazasu karya dashi, wanda al’ada ne da tuwo suke karyawa, mairama na zaune aka gama zuba musu suka faraci, ga yunwa na cin cikinta ga tsoro, ganin dai zaa cinye kuma tarasa, yasa ta mike tazo tazauna tasa hannu kenan tajefa lomar tuwo daya indo ta make kanta, “kin wanke hannu?, ba anhanaki cin abinci haka ba?” Tuwon ta hadiye dakyar kunshe da bakin ciki, tana kallonta, “Da Allah rufemin idon nan, ido kaman na mayya, daga anmiki magana saiki fara kallon mutum kaman zaki cinye” sunkuyar da kai tayi, tafara jan numfashinta kukan zucinta takeyi, ta tsame hannunta sannan tamike, hansat dama tashirya musu ruwan wanka har tafara yiwa wasu, ta kwala mata kira, haka kuwa tafita aka mata wanka, tadawo tazauna hansatu tashafa mata mai da layi yazo kanta, sannan tasaka mata rigar kanti, kayanta kala bakwai ne , biyu atamfa sauran biyar din rigan kanti, tafito tanufi aji, inda aka fara koya musu karatu kamar kullum. Manager, sunan ma’aikacin dayake kula da shiga da fitan marayu, agunshi ake register in ankawo yara tare da yan sanda, sannan idan za’a karba raino kokuma mallaka(adoption), kamar kullum yana zaune a ofishinsa, masu kawo ziyara sukanzo su shiga suga yara sannan subada dan abunda ya sauwaka. Yauma kamar kullum yans zaune sai gashi wata mata tashigo, tanada fara’a sosai da dan matsakaicin jiki bazata wuce shekaru talatin (30), suka gaisa sannan tace masa “Nazo ziyara ne, ko zan samu naga yaran?” “Ae hajiya, toh anma matsalan suna aji ne yanzu, saidai jariran yaran da wanda basu fara zuwa ajin ba” “Ae badamuwa muje nagansu din” Haka yakira daya daga cikin ma’aikatan gun sannan aka nufi cikin gidan da ita. Sun shigo ciki inda hajiya ta tarbeta cikin murna da farin ciki, anan tafara gabatar mata da yaran da sunansu, kuka tafarayi don tausayi, hajiya tayi murmushin tausayi sannan tace ” gashi bansan sunanki ba balle nata bada ban baki” “Sunana Fatyma, anma akan kirani da adda ” “Toh adda ai hakuri zakiyi, mu da muke zaune dasu muke ganinsu kullum me zamu ce?, kananun yara basuda iyaye kusa dasu, wani idan ankawoshi mukansha wahala kafin yasaba domin kuka yakeyi baya shiru”
.
Adda tadan share kwallan da yafara zubo mata sannan ta daga ido takalli wani yaro yana kwance daga nesa tamike tanufi kanshi sannan tace “wannan fa?” “Wannan imran sunanshi, da aka kawo shi kasusuwanshi duk sun karye, baida karfi, inkin lura da fuskanshi ai tsoho ne, shekaranshi biyu anma kinga ko zama bayayi, kullum yana kwance, andai kaishi asibiti amma kinsan abunda ba asalin iyaye ba bakowa zai damu ba, baya magana, baya komi ” Kafin ta idda magananta jitayi adda na jan hanci tsabar kuka, tadauko jakanta taciro tissue tafa goge fuskanta, sannan tace “insha Allah zandauko likita yaduba mana shi, irin wannan ku zakuna fada sai asanar inbahaka ba ana cikin gari bakowa zaisan halin da ake ciki ba” Hajiiya ta amsa da “toh, kinga akwai kurame, har da guragu, duk suna ajiye” Suna kan maganan adda taji an bankad’eta da gudu aka wuce, mairama ce ta tsaya gaban hajiya tana cewa “hajiya zanyi fitsari!” Tana fada tana kokarin cire wandon jikinta, dasauri hajiya ta rusuna ta tayata cirewa sannan mairaman takara komawa da gudu tafice, adda tace “wannan fa?” “Lu’u lu’un mu kenan” adda tayi murmushi sannan tace “naga alama, don naga alamun daga sunan dakika kira ta dashu” “Wlh adda badaga nan bane, kawai dai tafi sabo ne da mu” alokacin mairama tashigo tad’auko wandon tahau saman katifan sannan tafara sawa tana zurawa adda ido, can dai tace “hajiya wannan yar gayun tazo ne itama yau?” “Ae, meyene?” “Toh hajiya meyasa suke zuwa? Basu kwana damu saisuna tafiya?” Tasa kafa d’aya saura daya tana kokarin sawa “Saboda ba nan bane gidansu” “Toh , ainima nan ba gidanmu bane, tunda a aji malam yakoya mana acikin gida yace akwai mama, baba da kuma yara, toh hajiya nan gidan yaran munkai dayawa-dayawa faa” Adda ta kyalkyale da dariya ganin yadda mairama tazage tana surutu, har dimple din fuskanta yana shigewa, itakuma ganin adda na mata dariya takoma bayan hajiya tana riketa, hajiya tace “tunda kinsa wandon yanzu ki koma aji kafin azaneki” harta juya tafice sannan takara dawowa dagudu “hajiya toh wannan bata kawo mana komi bane?”
.
Sannan takalli adda tace “ina ledan kayan dadin?”. “Kayan dadi kikeson ci?” “Ae, duk wanda yazo yana kawo mana kayan dadi, toh kuma banga naki ba” Hajiya ce ta janyota tare da tura ta waje, tana cewa “karki kuskura kidawo nan” Adda kuwa sai dariya takeyi, bata juya ba saiga mairama takara lekowa “sai anjima anty” ganin hajiya ta juyo yasa takoma aguje Hajiya takoma zata zauna nan adda tace mata zata wuce, tafito don rakata sauran ma’aikatan sai godiya suke har suka nufo gun manager , nan tabude booth din motarta, matrix baka tasha tint, tasa ma’aikatan suka fara shiga da kayan, wata katuwar ghana must go ne na atamfofi, saikuma carton na taliya guda biyar, carton din caprosonne guda biyar, sai ledan cheese, suka shiga dashi suna godiya sannan tace zata wuce sun gode mata sosai sannan tashiga tawuce gida. Mairama tana aji anma hankalinta duk yana kan bakuwar data gani yau, kullum sukan sami baki kuma suna sonta don kiriniyarta anma bata taba jin takara kallonsu irin na wannan addar ba, saitanajin kaman ta dade da saninta da haka har suka tashi ta dauki dan littafinta ta rungumo sannan tanufi cikin gida. Fatima Usman shine asalin sunan Adda, haifaffiyar garin bauchi ce, takuma yi makarantarta a bauchi tun daga nursery izuwa jami’a atbu, takaranta quantity survey, tasamu tafita da first class wanda a wannan shekaran a department dinsu ita kadai ce mace mai first class, mahadacciyar al quran ce tanada basira da kuma nutsuwa, mace ce mai tsantsan hakuri, ta kad’aice rayuwarta wa Allah swt, har Allah yasa tagama atbu, tagama da wata biyu ta tafi camp taci sa’a anyi relocating dinta zuwa bauchi. Wata rana tafito daga gida sanye da hijabi dogo har kasa sanye da liqab wanda shine shiganta a kullum, tana neman adaidaita sahu sai kuwa taci sa’a ga wani, nan da nan tashiga tare da cemasa “g.r.a ” yace “toh” harsun wuce sai napep ta tsaya masa akan hanya nan yafito da sauri, yayinda taciro wayanta taduba taga lokacin sallah na neman kurewa, bayan yagama dube dubenshi yaleko sannan yace “hajiya barin tare miki wani kawai , mai na yakare” Bata ce komi ba tasauko ta tsaya tana jira ya tsayar mata da wani, wata mota ce prado baka ta tsaya agabanta, yasauke glass din anma bai ce mata komi ba, ganin ya tareta bata ganin hanya yasa takara matsawa, shikuwa bai motsa ba har saida mai keken yanema mata wani sannan tahau, yana fara tafiya bakar motan tafara binsa, can dai mai keken yalura yace “hajiya wancan mai motan mu yakebi”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button