NOVELSUncategorized

NAJEEB 13

Ciki ta shiga inda ta iske Mum da Granny a falon, “gaida mum tayi cikin girmamawa “mum tace sannu ibtisam ya hannun? 

Ibtisam tace Alhmdlh Mum da sau’ki, “kallon Granny tayi da take kallonta cikin tausayi  “tace Granny Yadai? “granny tace sannu ya hannun naki? 


Ibtisam tace Alhmdlh da sauk’i, “Granny tace ai naga idonki da Fuskanki ansha kuka, sannu Kinji? “jeki watsa ruwa kiyi wanka za kiji dad’in jikin ki, Kinji?

Ibtisam tace toh, “tare da shiga cikin d’aki, inda ta iske Zarah kwance ta lullube da blanket, “alaman tana jin sanyi “Ibtisam kallon Ac tayi wanda yake a kunne, “tace toh ki kashe AC d’in mana kaman dole, kin kunna AC kuma kin lullube cikin bargo, “jin muryan ibtisam na Mata magana yasa ta waigo tare da fad’in “har kun gama love d’in???

Ibtisam tace love kuma? Dawa? 

Zarah tace da wanda kika tsaya, “uhm ni Wlh kin Fara bani mamaki keda Bros, “sai kiyi ta nuna kaman bakwa shiri, Ashe soyayya kuke zubawa. 

Tsaki ibtisam taja tare da fad’in shirmen banza ” ni zanyi soyayya da wannan yayan naki? Allah ya kyauta Wlh, sai kace maza sun k’are a duniya 

Zarah tace uhm adai ta rufe rufe, ana boye boye, “duk zurfin cikin mutum abunda yake boyewa zai fito Wlh.

Ibtisam tace Wlh Zarah kina da matsala, “in rasa wanda zanyi soyayya dashi sai NAJEEB, uhm Allah ya kyauta, “Bari kiji koda maza sun k’are ace shi zan aura, toh gwara in mutu Banyi aure ba, Tabdi Allah ya kyauta, ai gwara in mutu da in aureshi Wlh, mutum sai miskilanci da mugunta, ya iya. 

Zarah tace wannan shine yasa nace ke dashi kun dace, “saboda halinku yazo d’aya, “Kinga indai miskilanci ne ke dashi kunyi anko S…… 

Plz ya isa haka, ki daina danganta ni dashi, halina da nasa ba d’aya bane “zarah tace uhm ni banga amfanin rufa rufa ba, toh miye Abun boyewa Dan kuna soyayya? 

Tsaki ibtisam taja tare da shiga toilet, “domin tasan maganan Zarah inta tsaya saurara rai kawai zata bata mata, ga hannunta na ciwo, “ga surutu mara amfani Tana mata “koda mutuwa zanyi in akace saina aureshi zan rayu ba gwara na mutu ba, “mutum miskili, mugu, wanda bai San darajan mutane ba, tsaki ta kuma ja tare da fad’in aikin banza kawai, “ya tashi ya k’ara famamin hannu, “ insha Allah sai an d’aura maka hanne Wlh, sai dai ka mutu, lokaci d’aya kuma ta saki murmushi tare da fad’in zanso inga yanda zaiyi in aka d’aura auren, “ni tausayi ma take bani kar yaje yaita ma y’ar mutane mugunta, tunda baida imani. 

Koda ibtisam ta fito daka wanka kwanciya tayi akan gado itama, “Wanda zarah tayi nisa cikin bacci, domin ibtisam ta dad’e a toilet, dan dakyar ta samu ta iya yin wankan, domin hannunta yana mata zafi daga ta d’aga, “itama bata dad’e ba bacci yayi gaba da ita. 

Granny da Mum suna zaune suna fira saiga Dad ya fito cikin shiri, “gaida Granny yayi cikin girmamawa tare da fad’in gobe ne tafiyan mu yola d’inko? 

Granny tace insha Allah, toh amma shi najeebun kunyi magana dashi ya amince? 

Dad yace mama mune iyayensa, bai isa ya ketare abunda muka zartar ba, “dole yabi, “koda baya so, granny “tace Allah ya tabbatar ya taimaka, “goben ma tafi da wuri 

Mum na jinsu bata ce komai ba, “sai dai ta kud’ira cikin ranta, zatai ma Granny magana, dan gaskiya bazata Bari a cuta d’anta ba, “yaron daya taso a waje, sai a aura Mai y’ar kauye, “kuma wacce baya so, “dama yana son auran ne, Toh da ance dasauki, “shima Dad in banda rashin adalci Ina Najeeb zai Kai matar da ake son aura mai, “ai yasan ba ajin Najeeb bace 

Dad dinning ya nufa inda itama Mum ta tashi ta nufi dinning din, abinci ta Fara zuba ma mijin Nata, “Mum tace ma Granny in Kawo miki abinci ne mama? 

Granny tace a’a, “Bari Nima yau in gwada zama a danis d’in nan, “Mum dariya tayi k’asa k’asa, “shiko Dad murmushi yayi 

Tashi Granny tayi ta zauna akan dinning, Mum tayi serving d’inta, “Granny ta Fara cin abinci Tana ta mutsul mutsul, “lokaci d’aya tace Kai nifa wannan Dinis din zama akanshi babu dad’i, “tashi tayi ta d’auki abincin ta koma kujeran falon ta zauna, Tana fad’in yauwa, ga inda mutum zai zauna yaji dad’i nan, “amma Danis in ka zauna kaman kahau kujeran da akwai ruwa akai, “kwata kwata babu dad’in zama, “Mum dariya tayi Sosai, “shiko Dad dakewa yayi.

Granny tace Wai ina yaran nan ne? 

Mum tace May be suna can suna bacci 

Granny tace miye kuma my e? 

Mum tace ina nufin hala suna bacci 

Granny tace oho na gane yanzu.

Najeeb kam tunda ya shiga cikin gidan part d’inshi ya nufa, inda ya kwanta tare da lumshe ido, “tunanin ibtisam ya farayi, “kwata kwata baya son yarinyar ko kad’an, “danya Lura bata da kunya, tsaki yaja tare da fad’in haka yaran Nigeria suke most especially inka Fara sake musu, “and suna ganin kaman su wasu ne, “daga sunga sun Fara fira da saurayi, tad’i kenan, sai su Fara nuna Sun isa , that ibtisam karamar yarinya amma har an barta tana kula samari, “yanzu sai aji ana zatai aure, “komai take dashi da mijin zaiyi wani abu da ita oho, “Kai shima guy din da yake zuwa wajanta, bashi da hankali, “ko uban Mai zata bashi oho, lokaci d’aya yaja tsaki,  domin shi kwata kwata baya son saurayin ibtisam, baya son kabir, duk da ba saninshi yayi ba, but guy din bai mishi ba, tunda yaga yana zuwa tad’i wajan wannan karamar yarinyar ibtisam, wacce bata da kunya, “d’aukan wayanshi yayi tare dayin dialing wani number, naji yasa a kunne yana fad’in “get ready by 8pm I will come and pick you” yana fad’in haka ya kashe wayan “ba tare da yaji amsa daka wacce yake ma maganan ba. 

Bayan Dad ya kammala cin abinci, “ya tashi tare da fad’in zan fita, “inada meeting, “sannan ki fad’ama su Zarah admission ya fito duka sun samu, jiya nayi waya da Bc, yace Sun samu amma suje su duba. 

Mum tace Alhmdlh, sai zuwa makaranta kenan yanzu. 

Granny taja tsaki tare da fad’in, “Aikin kenan, boko boko, “Wai Mai yasa bakwa maganan yima yaran nan aure ne sai dai maganan boko, kullum? “yanzu ku gani ga wane bai ishi wane tsoran Allah ba, “kenan abunda miskili yayi baisa Kun saduda bako? 

Dad yace mama, Zarah da ibtisam yara ne k’anana K…. “salati Granny ta saki tana fad’in na shiga uku ni Aminatu, “yanzu su takwarar tawa ce yara k’anana? Lallai kam, ” ku yanzu bakwa ganin tsufansu koh? “gaba d’aya yara Sun zama manyan mata, duk jikinsu ya fashe, gaba d’aya komai nasu ya bud’e, sannan kace yara k’anana ne? “Wlh yanzu su ibtisam da zarah inda a kauye ne da sun ajiye yara biyu, suna da cikin na uku. 

Mum bata san lokacin data sake da dariya ba, “su itbisam dinne za’ace suna da yara biyu, da cikin na uku Hhhhh, kwata kwata kwaya nawa suke? Yaran da basu Kai koda 18yr ba , “mum cikin ranta tace sai yasa yara k’anana inka gansu a kauye saika d’auka tsofaffi ne, gama misali da Hanne, wacce karamar yarinya ce, amma ta yamutse ta koma kaman tsohuwa ,”shine za’a wani kawo ma NAJEEB, “tunda shi bai San abunda yakeyi ba, yana saurayi a aura Mai bazawara. 

Dad tashi yayi ya fita, ganin haka yasa Mum tace mama ina son bada wani shawara. 

Granny tace name fah? “Allah yasa akan maganan auran yaran nanne su zarah 

Mum tace a’a “akan maganan Najeeb ne. 

Granny tace inaji, “Mum tace mama kin daiga abunda Najeeb yayi ma babanshi akan maganan auran da ake so yayi, inaga Najeeb bai dace da hanne ba…..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button