YAR WAYE

Xaune su momy Rayhana da daddy suna xancen yanda xasu nufi wannan kauyen dake cikin jahar gombe.momy kuka takeyi hadi da cewa”daddy baxan yarda ba gaskiya a rabani da Afral,duda ina son “yata,don haka daddy kayimun alkawari kowani halin kaga ” yar ka baxaka yi kokarin tona cewa”Afral ba diyar mu bane…
Buda baki daddy yayi xaiyi magana dai² suka ji an banko kofan dakin,a firgice suka dago kai,ganin Afral bakaramun daga masu hankali yayi ba.
Kafin momy tayi magana tuni Afral cikin wani irin murya daji kasan mutum yana cikin matsanannacin tashin hankali.
Momy….daddy…mai nakeji?mai kunnuwana suke ji mun?momy ni ba diyar ki ba ne Kaman yanda naji kin fada?
Momy it is true that I’m not your biological daughter?
Wani duhu² Afral take gani amma takasa shiru har sai da ta gama jero masu tambayo yin.baya tayi xata fadi,nan da hanxari daddy da momy Rayhana sukayi saurin taro ta…..
More typing…
More comment
Maman teddy ce…
[12/29, 9:55 AM] mmn tedy: *TYPING…*
*2/12/2020*
*YAR WAYE???*
_*pure love and symphaty story*_
*Story and written by:*
Ayshatou (maman teddy)
Facebook@maman teddy.com
*wattpad*
Ayshatou(maman teddy)
_Banyi labarina don inci xarafin wani ba,sai don in fadakar,nishadantar,wa”axantar,kuma na faranta ran dukkan wani masoyin Ayshatou…_
*DEDICATION*
Dedicate to you my fans????wannan pagen nakune,kuyi yanda kukeso da shi…????????????????????????
*GARGADI*
_Ban yarda wani ko wata suyi amfani waken juyamun labari ba_????
*__________________________________*
*A kullum burin Ayshatou bai wuce taga ta faranta ran masoyan ta ba,????love you more my dear fans…*????????
*Episode* 20 – 21
*~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~*
Momy ne ta jawo Afral hadi da xaunar da itah jikin ta,kuka sosai momy keyi,nan ta fara cewa” Afral bana son ganin damuwa a tare da ke plz you have to stop cry…momy haka ne ni ba “yar ki ba ce? Daddy ba mahaifina ba ne? Ba daddy na bane momy??? Afral ke magana cikin matsanan cin kuka,Wanda momy bata da amsan da xata bama Afral din.sai hawaye…
Shi kanshi daddy sai da ya goge kwallan idon shi,don yau ya gama tausaya ma momy da Afral din.
Haka suka dinga kuka ba mai lallashin wani.itako Afral ji take kaman ta mutu ta bar duniyan gaba daya ta huta.
Ahhh…ahhh…maxajen nawa ne agidan yau? Lale marhaban,ahhh su Umaru ne da Ammaru sannun Ku da xuwa.
Hajiya kaka take cewa” cike da farin cikin ganin en jikokin nata.
Murmushi sukayi hadi da cewa”hmmm yau dai munxo ganin er tsohuwa ne,muga lafiyan ta.
Hajiya kaka ne tace”kai Ku rufamun baki,ni nan da kuka ganni na fiku lafiya,irin abincin da nake ci ba kwaci,kun tsaya bin na zamani da duk an kashe da sinadarai.
“Ammar ne cike da biye ma ” yar tsohon yace”haba hajiyan mu jube mu fah,gadagau muke,don lafiya har yy mana yawa mah…
Maganan da Ammar yayi shiya sa Umar dariya sosai,don duk insun xauna da Hajiya kaka sai anyi dariyan lamarin nasu,Ayi fada a shirya,a haka kullum suke.Amma a haka in Hajiya kaka bata gansu na kwana biyu ba,ta dinga magana kenan.musamman Umar da yake da sunan mai gidan nata.
Dariya sosai Umar keyi…Hajiya kaka ne tace”hmm kai kanka mai gidana kayi dariya ai,hmm toh yanxu dai kuje Ku huta sai mu xauna Muyi hira,don yau na gaji, kiran iyayen Ku xanyi akan Ku fitar mun da matan da xaku aura.jiku duka kun haura shekara 30, amma ba kwa ko maganan Aure.toh yau baxa ku koma ba, sai naji kwakwkwaran magana ga iyayen Ku…toh Hajiya wannan xuba haka? Mai da wukan,don ni tuni nasamu Wanda xan aura.
Ammar yace”hadi da yin ma Hajiya kaka murmushi.
Cike da rashin gamsuwa da maganan Ammar Hajiya kaka tace” anyah kuwa da gaske Kakeyi Ammar? Nifah nasanka da shegen son mata,kace yau wannan gobe wancan,har gomma Umaru na.
Murmushi Ammar yayi hadi da kallon Hajiya,nan yace” hmm Hajiya da gaske fah nake wlh inna xauna inah fada maki yanda nake son ta sai mu bata awan ni bana ma ba.
Kai Mara kunya rufe mun baki,wlh Ammar baka da kunya mai gidana ba haka yake ba.Hajiya kaka tace”hadi da kallon Umar da yake danna wayan sa,kaman bai San suna yi ba.
Toh Hajiya na lura kaman kishi ki keyi,amma koda kishi xai kashe ki sai na nuna maki hoton ta yau.sai dai Umar din ya biki shima Ku mutu tare.duka Umar ya kai mai hadi da cewa”kai toh bari in fada maka duk kyaun budurwan naka baxa ta kai Hajiya na ba,don da tsohon xuma ake magani…Hajiya kaka ne tace “kyaleshi Umar ya nuna mun Wanda yake ikirarin tafi ni.
Dariya Ammar yayi hadi da cewa” shiyasa kullum nake jin ki a raina ya kaka,bari kiga my shining star,my beauty,Angel….kai duk ya isah, ni dai nuna mun yarinyan.bama ganan banxa ba.murmushi Ammar yayi hadi da cewa”toh Hajiyan mu bari ki ganta.
Kauda kai Umar yayi don shi yanxu yarasa ya xai fara tunkarar ta,Wanda ya dade da son ta a birnin xuciyan shi,kullum da soyayyan ta yake kwana yake tashi,Wanda kullum yake mafarkin ta xama uwar “ya’yan shi…nan take lokaci guda ya fada duniyan tunanin ta.Wanda yasa ko su Hajiya kaka ba yajin irin draman da sukeyi da Ammar ‘din.
Hajiya rufe idon ki,kiyi addu” a don kyaun ta in kika gani sai ya firgita ki,don ba irinsu a nijeriya,kin gako baki saba gani ba.mtsswww Hajiya kaka tayi tsaki hadi da cewa”ni bana son shashanci in xaka ban kaban in baxaka nuna mun ita ba,ka kyaleni kawai.murmushi Ammar yayi hadi da cewa”eyyah Hajiya kiyi hakuri kar kishin ki ya fito sarari mana,ke din ae har yanxu ta daban ce.haka yayi ta xolayan Hajiya kaka sannan ya bata wayan nashi,hadi da nuna mata hoton Amrah.
Hajiya kaka batasan lokacin da bakin ta ya subuce ba tace”kai masha”Allah,a inah take? ‘YAR WAYE??? kuma.hmmm Hajiya a Zaria take,Hajiya ne tace”kai masha,Allah.mai gida na farouqu kai fah ina taka matan? Kai kuji mun tsohuwa da shishigi,toh ni bani da wata Wanda na keso a yanxu.Hajiya ne tace”toh ai shi kenan Allah ya Baku mata duka na gari,Wanda xamuyi alfahari da su nan gaba.hada baki sukayi wurin cewa” Ameen.mikewa Umar yayi hadi da cewa”Hajiya na bari mu shiga daga ciki.toh farouqu yanxu nima xan shigo…barin sitting room din Hajiya sukayi hadi da nufah dakin su da yake permanate na sune.bin Umar da kallo Hajiya tayi hadi da cewa”a xuciyan ta,tabbas a Kawai abunda ke damun farouqu,shiru tayi hadi da cewa”komai nashi kalan na mahaifiyan shi,murmushin sa,miskilancin,yawan alkhairin sa,kwallah ne ya ciko idon Hajiya kaka, nan ta daga hannu hadi da yima mahaifiyan farouq din addu’an duk inda take allah ya bayyana ta,inkuma ta mutu ne Allah yaji kanta,yasa duk abun da Hajiya tayi mata ta yafe mata…
Xaune feenart take a dirning ba kunya, da su dadyn farouq hadi da shi kanshi farouq din.don xasuyi break fast ne. addu’a Umar yayi kafin ya fara cin abincin.
Kallon Juna momy kubrah da leenart sukayi,don xuciyan su fari take kal yau,don sun San bukatan su ya biya ya gama.
Haj.kubrah kuwa cewa”take a xuciyan ta ai yau Umar ko kwana kake akan buxu kana saukan alkur’ani kullum yau sai wannan maganin ya cika…
Haka haj.kubrah su kayi break fast cikin jin dadi tana cin abincin ta hankali kwance,haka ma leenart, don har wani shige mawa Umar din take,shi kuma sai shareta yake,yana wulakanta ta,don wani abun raga mata yake yi saboda momyn na shi…anan daddy yake kara mai maganan company Wanda yace” mai nan da 1 week xa”a bude companyn insha,Allah…
Murmushi Umar yayi hadi da cema wa”daddy Allah ya yarda daddy.haka suka dinga cigaba da firansu na kasuwancin su da sauran abubauwa,don komai daddy xai yi sai ya nemi shawarar Dan nashi,don shi daddy irin mutanen nan ne hoxlar Wanda basa tsaya mawa abu daya,sai gashi Dan nashi ya biyoshi har ma yana Neman yafi uban na shi.daddy ne kan ya tafi yace” mawa Umar yaje yayi tunanin sunan da xai sa ma companyn na shi.a haka sukayi suka rabu da daddy akan xai tunanin sunan da xai sa mawa companyn…