HAUSA NOVELYAR WAYE

YAR WAYE

Koma cikin gida nayi inda na baro Amaratu na wanke²,binta nayi da kallo,fara ce amma wahala yasa takoma baka kirin.hakoranta na bi da kallo inda suka wani irin jah,gashi so greenish abun ba kyan gani,tana wanke²n tana Sosa kai don akaduba kan shi kanshi ba arasa kwarkwata ba.don tsagon kitson datti har manne wa yake kaman swingum…

Saukan duka taji da bulala,jikake zau,zau…zau…
Ihu Amaratu keyi hadi da bama Ummu hakuri, amma ko sauraranta batayi ba.sai duka Kawai takeyi.tun Amaratu na kuka har tayi shiru sai hawaye don Ummu cewa take in bakiyi shiru ba wlh baxan bar dukanki ba.tun daxu jubi Dan wanke²n da ki kayi kin tsaya iskani,toh ubanki zanci.
Maxah ki wanke don minti biyu na baki,ki shirya ki wuce makaranta.
Haka Ummu ta wuce tana cigaba da bambami…

Bin jikinta Amaratu tayi da kallo inda gaba daya ya farfashe sakamakon dukan da Ummu maryam tayi mata.a haka da kyar ta karashe wanke² hadi da dauko hijabin makarantan ta saka,ta nufi wajen Ummu maryam..Ummu na xan tafi.
“Amaratu tace” Dan gwarar mata tayi da dumamen tuwon jiya a gurin.
Durkusawa Amaratu tayi hadi da dauka tanufi xaure.da sauri² take cin abincin don yau tasan xata daku a makaranta,don ba karatun latti tayiba.
Bayan tagama cin abincin ne ta maida kwanan cikin gida hadi da nufan hanyan makaranta.
Sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta Isah makaranta…
Yau taxi sa’a ba malaman su farfajiyan makarantan don haka da gudu tayi cikin aginsu,wato primary 6.
Da sauri wata kawanta Wanda take saude ta matsa mata wuri hadi da cewa”maxa ki xauna an an Amaratu,yanxu muguwan malaman nan xata shigo….
Toh saude matsamun.
“Amaratu tace” hadi kokarin xama.
Da xaman su wata malaman su ta shigo nan ta dauke su English bayan tagama masu karatun ta ne ta hau tambayan su.ba Wanda yabata amsa sai amaratu,koda ta bata amsa sai malama murja ta yamutsa baki hadi dacewa”kewai wata irin kaxama ce?jiki fah da Allah,kullum cikin kaxanta uniform kaman na me kwanan siminti.ba wanka ba wanki?
Duk randa kk kara xuwa mun a haka sai na xane jikin wlh.
Malama murja tace”hadi da fita waje…
Saude ne tace”kin gani ko Amaratu bata yabamaki na kinyi kokari ba amma ta haumaki fada.don haka karki kara bata amsa a aji intayi tambaya, ki barta da dakikan en ajin.
Murmushi shi Amaratu tayi ba tace ma saude komai ba.a haka aka tashi break.bayan sun koma ne wani malami ya shigo hadi da cewa”duk Wanda bai biya kudin comon entrance ba ya tashi ya wuce gida ya amso,don yau sauran kwana 6 afara.
Da sauri Amaratu ta mike hadi da barin ajin da sauri,dariya en class en suka hau.don kowa yasan ita ce dama bata biya.
Daka masu tsawa yayi hadi dacewa” kuyimun shiru….

 

Koda Amaratu ta nufi gida Ummu maryam ta cidda tana kokarin daura abincin sayarwan rana.
Mai ya dawo dake?
“Ummu ta tambaya” fuska daure ba annuri.
Ankoro ni kudin common entrance ne.
Amaratu tace hadi da kallon Ummu.
Tsaki tayi Ummu had a da cewa”hmm ai ko xaki shekara ba ilimi,don naira baxan bayarba.ace makarantan gomnati ma sai an biya kudi?toh cire uniform en ki wanke mun kayan can.
Toh Amaratu tace”hadi da nufan dakin Ummu ta cire kayan ta hadi da nufi wurin kayan wankin.

 

Haka washe Gari Amaratu ta shirya ta nufi makaranta.
A ranan ma tasha toxarci don malaman su murja sai da taxane ta hadi dacewa”ace naira 50 na common baxa kuiya bayarwa ba?toh karki kara xuwa daga yau…
Haka tanufi aji tana masifa da cewa”xaman kauye bai yi ba,don basu San darajan ilimi ba Sam…

Haka Amaratu ta nufi gida jikin ta duk tsami yake mata.don bata kwana ba abuge ta ba a rayuwanta.don yanxu ma har tasa ba.
Tun a kofar gida tacikaro da wani gibgegen mota.bin motan tayi da kallo abunka da Dan kauye,kan tace”toh motan waye wannan?ganin bata da amsan tambayan ta yasa ta kutsa kai cikin gida.
Muryan Ummu taji tana kuka hadi da masifan ta tana cewa”wlh ba ki Isah ba.don baxan taba yards da mgn nki na cewa”Amaratu ba ‘ya na ba ne.in ba ‘yana bane to ‘YAR WAYE??? Ummu ta fada cikin kakkausar murya…
Cike da natsuwa da aji doctor najwa tace”er Alhaji mana?kinsan waye ubanta?toh ubanta wani kusa ne a gomnati,Wanda ko gomna a kace maki yayi karki mamaki.don haka tambaye na iyayenta da kk yi kona fada maki ba xaki iya xuwa inda suke ba.don sunfi karfi,ko a ‘YAR AIKI baxasu ajiye ki ba.
Don haka bai dace kurinka wannan haukan ba,ni a yanxu kaman na taima ke kine.don yarinyan ki na can tana shan ruwan gora,tayi wanke Dana dutse.ta xagaya kasashen da take so.kuma kisani wannan duk makirci na ne.don haka shine kadai xaisa inrama abun da Alh.Mohammad yayimum shi da matarsa.
Don haka kici gaba da axabtar da ensu.yanda yaka mata plz….

Dogon tsaki Ummu tayi hadi dacewa”WAYA gaya maki xanyarda da ta tsiniyan gudanki?toh Amaratu ‘ya ta CE.
Murmushi doctor Najwa tayi hadi dacewa”tohm ga wannan shaida CE.nasan xaki yards yanxu.
Wani camera doctor najwa ta kunna mawa Ummu, nan take ta fara tuna komai daga bin yanda Najwa tayi exchanging en Amaratu da wata ‘ya da batasani ba…
Kuka Ummu tasa hadi da xakin Najwa ta uwa ta UBA.kuma ni maryam in Allah ya yarda xan ne mo mawa Amaratu iyayen ta,koda a birnin sin suke.

OK doctor najwa tace hadi da fita gidan.dajin motsi yasa Amaratu saurin boyewa.bayan fitan ta Ummu xama tayi tana kuka,itako Amaratu kuKa tayi ma’ishi sannan ta fito hadi da hada wanke²ta farayi.
Ummu da ta fito da mamaki tace”Amaratu yaushe kika dawo?
Yanxu ne Ummu..
“Amaratu tace hadi da cigaba da wanke²n ta.
Ummu ne tace”Amaratu sun koreki ne ko?
Dagowa Amaratu tayi hadi da cewa ehhh Ummu.
OK inkin gama kixo kici abunci,gobe xan baki kudin ki kai masu.
Dasauri Amaratu tace” Ummu xaki bani kudin?
Dariya Ummu maryam tayi hadi dacewa ehhh mamana xan baki ki kai masu.
Godiya ta hau yi ma Ummu.
Ummu ko murmushi tayi hadi da nufan kicin…

Tun daga wannan rana wani irin soyayya n Amaratu take shiga xuciyan Ummu hadi da tausayinta,haka Ummu ke ta kokarin fahimtar wani ABU dangane da Amaratu amma ba tagane komai ba.

 

Waye Ummu maryam???
Ummu maryam cikakkakiyan er asalin gombe ne,a nan en uwanta dangin ta gaba daya ke rayuwa.
Ummu maryam tayi aure ne a garin gombe inda ta auri mijin ta mai suna ml. sani.sunyi xama na soyayya da jin dadin rayuwa. Inda tun tana da cikin Amaratu Allah yayi mai rasuwa sakamakon accident…
Tundaganan Ummu ta shiga cikin damuwa,Wanda har wata daga cikin yayunta na gombe ta dauke ta xuwa cikin garin gomben don ta haihu a can.
A haka cikin Ummu ya Isah haihuwa inda aka dauke ta aka kaita wani asibiti mai tsadan gaske mai suna al madina.a nan Ummu ta haifo diyarta,inda bayan tagama wanke ta dawo kauyensu da xama.Wanda ta cigaba da sana’anta,don tace”baxata kara aure ba tun daga kan mal. sani.
A haka taci gaba da rayuwanta da Amaratu,koda take tsanan ta ma Amaratu ta nayi ne don kar ta lalace,ace mata er mace..wannan kenan.

 

________________________________

Haka Ummu ta ba Amaratu kudin common inda aka turasu cikin garin gombe,don anan suke xanawa.kullum Ummu xata bata na mota.don yanxu soyayya ne Ummu ke muna mata sosai.Wanda ita kanta Amaratun ke mugun kaunar mahaifiyan na ta.

Bayan Amaratu sun fito daga makaranta xa suyo kauyensu.taxo tsallaka titi ne don tasamu abun Hawa.
Wani bakar mota ne taxo da gudu nan take ta banke ta.Allah ya kiyaye tayi saurin kaucewa Dan haka sai ta fadi a kan titin.
Bude motan su kayi,wasu alhaxai ne su uku Wanda daga ni duniya ta yarda da su.
Ganin su Amaratu yasata saurin mikewa tana goge jikin ta.
Hmmm wannan musabbabin labarin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button