YAU DA GOBE 13-14

“Ahankali yace to ummi bara naje d’in”saina dawo!to babana Allah yatsare”Yana murmushi yace ameen had’e da kallon zarah yace baby namiki tsaraba tunda broth d’inki bayanan?”
Eh Yaya wlh ice cream nakeso nakwan 2 bansha Shiba…ohk “yafad’a Yana ficewa..
Da kansa yyi driving d’in”Yana isowa yyi horn”get man yabude Masa get yadanna hancin motarsa ciki…Yana Gama parking yafito…yahango Abba zaune kan resting chairs dake haraban gdn.. directly yanufi gurinsa…bayan sun gaisa Abba yyi ajiyar zuciya cikeda fargaba yace ALIYU!da sauri Dr safana yakalli abba jin ya ambaci ainahin sunanshi”yasan maganar Mai mahimmanci ce”Ina neman alfarma agurinka amatsayina na k’anin mahaifin ka”Wanda ayanzun nine matsayin mahaifin ka duk duniya!cikin gamsuwa Dr safana yad’aga Kai Yana cewa hakane Abba insha Allah zanyi komeye kafi k’arfin neman alfarma guna saidai kabani umarni kawai..Abba yyi murmushi had’e da cewa Allah yayimaka albarka….nasan zakaji abinda bakayi zatoba abakina”inaso Aliyu ka auri sumayya y’ar amaryata”ba masoyi tarasaba ah ah!akwai wasu dalilai masu karfi”ko itama batasan da zancen Zan Mata aureba”inaso inbaka aminceba kamun bayani wlh bazanji haushiba.. sbd adah da Sadiq dake sonta Zan had’a su”to Amma mahaifiyar’sa sbd kishin Maryam tace muddin ya amince zata tsine Masa”kaga kuwa inbaka amince bazanji haushiba sbd d’an dana haifa da cikina an hana yamun biyayya duk da kaidashi duk d’ayane agurina…Ina saurarenka meye kagani??”
Dr safana jin maganar Abba yyi tamkar ankwad’a Masa guduma akansa “yarinyar daya tsana akeson lik’ama aurenta”Kuma suna soyayya da Sadiq? Wata zuface taketo Masa”dakuma yatuna da rukky sai yaji wani irin yanayi marar musaltuwa…Abba ya girgiza Kai Yana kallonsa “kafin yace inhar zaka amince ka aureta bbu laifi dg baya ka auri ita yarinyar dakuke tare”kobaka auri sumayya ba gsky banison ka k’ara wani lokacin bbu aure….cikin k’arfin hali had’e da b’oye halin d’aya tsintsi kansa yace bbu komai Abba Allah yasa hakan shiyafi alkhairi…
Cike da mamaki Abba yace ameen and beyi zaton zai aminceba jin yyi shiru..”tashi tsaye Dr safana yyi had’e da cewa Abba na wuce Saida safe”
baki washe abba yace to my son nagode k’warai”kaji Allah yyimaka albarka”cikin k’aka’ro murmushi Dr safana yace ameen Yana tafiya har ya iso Gurin motarsa yashiga ya ja yabar gdn…Abba yyi murmushin samun nassara…
#########
Cikin damuwa had’e da b’acin Rai”Dr safana keyin driving d’in”sai yanzun yyi nadamar ki’nyin aure da wuri”inda yanada aure bbu Wanda zai lik’a Masa wata wlh…tsaki yaja afili yace laifinkine rukky!kekika jamana”yafad’a Yana canza akalar motar zuwa gd”sbd gaba d’aya bayada kuzarin zuwa wajen rukky”Kuma itama yanzun haushinta yakeji sbd aganinsa itace sanadin komai…cikin damuwa da jin haushi yawuce part d’insu ko gun ummi be shigaba.
Da kyar yyi shafa’i da wuturi yakwanta. Yana ganin miss call din musty Dana rukky yyi burus dasu…da k’yar bacci yyi awon gaba dashi… yyinda ummi ke fargaba sbd tasan tabbas besan maganar tunda ko shayin dayace adafa Masa bezo yakarba b’a ,balle ice cream d’in daya ce zai siyama zarah..saidai ummin ta duk’ufa da adduar zabin alkhairi agurin ALLAH!
*Washe gari*
Dr safana be shigo gdn ba sai 7:40 am”a dining area yasami su ummi yagaida ita”zarah ma tagaishesa tana k’ok’arin masa tuni akan ice cream d’in ta “saidai ganin mood d’in sa yasa taja bakinta ta tsuk’e “aranta tace yau y’an hospital sun shiga ukku”
Ummi ta dubesa ganin be zaunaba tace kazauna kayi Karin Mana!
Cikin wani yanayi yace ah ah nak’oshi, yafad’a Yana dubar zarah fuska a’daure yace ke tashi zamuyi mgn..sum sum zarah tabar Gurin da sauri…Zama yyi kan d’aya dg cikin kujerun table d’in”murya asark’e yace pls ummi Ina cikin damuwa!Abba yabani umarnin zai auramun yarinyar nan y’ar amaryar wlh ummi bana sonta…tamkar gaske ummi tace subahanallahi”baka santafa kace?”Toni meye nawa aciki “bagara kayi aurenba “daka zauna jiran wannan yarinyar da har yanzun bata Gama karatun da ubanta yace ba… marairai ce murya yyi had’e da cewa dan ALLAH ummi kimasa mgn yajanye wlh yarinyar batamunba”zaro ido ummi tayi had’e da cewa”lallai ka isa meya hana sadda yasanar maka kace bakaso saini zaka turako?”to bari kaji tun kana k’arami alh Usman kesonka da shagwaba ka”sai Dan yanzun Yana umarni ke bazaka iya Masa biyayya”ayanzun tunda mahaifin ka yarasu kanada uban daya fishine?”ni inaji ajikina insha ALLAH auren nan alkhairi ne! na haneka da cewa baka sonta ko bata maka”sbd da yawa abinda mukeso muka k’wallafa ranmu akanshi ba alkhairi bane”Wanda Kuma bamaso shine yafi alkhairi agaremu…itama ai basonka takeba ko?”sbd haka ita wacce kakeson ubanta namaka yawo da hankali nan gaba inya gadama yabaka ka aureta…shiru kawai Dr safana yyi Yana sauraren ummi ta inda take shiga batanan take fitaba”yalura tana son auren d’ari bisa d’ari.. ahankali ummi tace ni aganina babana kayi hakuri kayi biyayya insha Allah zakaci riba”karik’e yarinyar nan da gsky inaga shiyafi maka”inkuwa ka kafe to saidai kaje da kanka kasanar Masa bakaso ,amma ni bazan iya ba”inkuma har kasanar Masa natabbata k’imar dayake kallonka da ita ta zube…ajiyar zuciya Dr safana yyi had’e da cewa shikenan! yafad’a atakaice Yana ficewa abinsaa…ummi tayi murmushi tace ai wlh gara ka aureta da ama lik’ama jidda da uwarta ke suntirin turowa”saidai nasan muddin hjy jamilah taji wannan mgn akwai aiki agaba…
Bangaren Abba kuwa yasanar ma ma “Wanda yatsaba ma sumayya amatsayin mijin aurenta”mama kuwa taji dad’i sbd ta yaba da hankalin Aliyu”sannan Abba yace karta sanarma sumayya shizai gayamata da kansa in ankwana2… sannan da kansa yaje gun baba Iliya yasanar Masa komai da Kiran da binta tayiwa mama game da zuwan su baffa habibu…
*bayan kwana5*
Musty ne zaune aroom din daya sauka “yanata aikin kallon pics d’in zarah dake awayarsa….mamaki yakeyi kusan kwanansa nawa kowa nakiransa agdnsu amma banda ita”contact yashiga ya lalibo *my heart* yyi calling d’inta…zarah na bacci ma Gurin 12 na safe” Kiran yatayar da ita!tana duba wayar taga my broth”turo baki tayi had’e da hararar wayar tace kaida ka manta dani meye na kirana?”katsewa tayi yasake Kira”d’agawa tayi”yasaki ajiyar zuciya aboye”kafin yadaidaita muryarsa yyimata sallama!ta amsa hade dayin shiru”lumshe ido yyi sbd dama muryarta kawai yakeson ji”baby dama ummi nikeson mgn da ita nakirata bata shiga”dit ta kashe wayar cikin jin haushi”wato bama ita yakira yaji lafiyarta kenan “ai ummin nada waya saika kirata “amma bada wayar zarah ba, tafad’a tana kashe wayar baki d’aya…
Dr safana ne zaune a office nasa yyi zurfi atunani”sbd ganin da gaskedai aura Masa marar kunyar yarinyar nan za’ayi(sunan dayake Kiran sumayya dashi) tunda jiya Abba yakirasa yasanar Masa ansaka ranar auren nanda wata 3″d’azun Kuma ummi tace ana gidan zasu zauna yasiyi fili dake bayan gdn yaturo ciki amusu b’angarensu sbd taga kalar zaman dasukeyi… gashi ko rukky besanar mataba “balle amininsa Nasir…sak’a da warwara kawai yakeyi….Wai kanka d’aya safana?”cewar Dr Nasir daya shigo yanata sallama amma ,yyi zurfi atunani bejishi ba…ajiyar zuciya Dr safana yasaki “had’e da cewa zauna inasan ganinka Ina cikin matsala wlh”yafad’a azuciyar sa na k’una… subahanallahi!to Ina jinka Allah yaka mana da sauk’i”cewar Dr Nasir Yana kallon SAFANA..