HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

Murmushi huda tai tace Ai nima haka nake tashi watarana musamman lokacinda nakeda cikin nan kuma yawuce watannin haihuwar sa har nakan zauna innemi deen yafiya seduk ya diriri ce,Allah yagafarta mana baki daya ameen,

Wai sulaimi kinsan wane suna deen yasawa yarannan?
Sulaimi tace sekin fadamin,
Dariya huda tayi tace dani dake yaiwa takwara,amma be fadawa kowa ba,
Dariyar jin dadi tayi tace wacce ce huda aciki,

Wannan karon kece babba,ahh lallai nayi Sa’a mugani takwarar tawa koda ni take kama,
Ahaf dole yarinya tayi kamada uwarta dariya sukayi suduka su naci gaba da hirarsu nidai Fita nayi naje inda abbu dake zaune da wani dattijo suna magana,

Alhaji ban fadama Dan natashi hankalinka ba nafadama ne sedan ganin be musa ba yakuma aiko da takardar saki har uku sekuma Dan adauki mataki sosae wannan abin Ai sirrinmu ne shiyasa bannemi alhaji Ibrahim ba nanemeka kai tsaye,
Mahaifin isma’il yana kwalla yai godiya yaja sandarsa yai gaba driver dinsa yaja mota suka tafi, yacire ran ze haihu aduniya segashi Allah yabashi isma’il yayi iya kokarin sa wurin bashi tarbiyya dabiya masa bukatunsa matukar basu fi karfinta ba amma seya zabi yasaka masa ta wannan mummunan hanyar shiyasa yaki aure babu yadda beyi dashiba amma yace besamu wacce yakesoba fatansa dai yanxu Allah yashiryar masa da gudan jininsa Dan hannunka baze rube kacire ka yar ba,

Ya matukar bawa abbu tausayi tsintar koda wani barene ba dankaba cikin irin wannan mummunar rayuwa yanada ban firgita da dimbin damuwa hadida shiga al’ajabi balle ace danka guda daya da Allah ya azurtaka dashi ya nayiwa isma’il fatan shiriya da adduar Allah yabawa mahaifansa hakurin jure Wannan kaddarar,ameen,

Har dare laimi da huda basu wani saki jiki ba yadda suka kwanta dazu saboda gano baby’s din nason kwanciya haka shike hanasu rigima haka suka kwanta yanxu sedai kowace nakan gadon ta ba hira suke ba sunyi shiru Dan kar yaran sutashi sudamesu dakuka,

Dangin mijin huda sukayo ayari guda Dan kawo kayan barka se suka nemi ganin yara da mamar su Ummu tace Ku shiga can dakin suna can yau zaman dakin sukeji,

Sunyi kwankwasa kofar dakin harsungaji sunji shiru Ummu tazo tace,Ai shiga kawai zakuyi kila tana ban daki ne,tura kofar tayi tashiga,akwance tasamesu daya idonta arufe daya kuma abude ga yaran se ihu suke suna kuka,

Kidemewa Ummu tayi tarasa ma mezata farayi,juyawa tayi tana kallonsu sukuma kowannensu gabansa se faduwa yake.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA….. Page 15…by SophieG.

 

Mom Hanan here’s ur page make sure kin shafa min kan Hanan da addu’a,bance kishafamin kan danki ba lol.

Kare kanta tashiga yi ganin baya fita koda kofar gidane kullum yana Palo zaune jiran fitowarta amma tayi musu Katanga irin wacce baze iya rusheta ta sauki ba,Ranar da Abu yasata tadawo gidan isma’il dagudunta tashige dakinta tasaka key ta rufe taimakonta daya keys din gidan ba arabasu ba danhaka bashida Wanda ze bude kasancewar kowace kofa key dinta Wanda akalla zasukai biyar biyar suna jikinta,

Kwananta biyu adaki banda kuka babu abinda takeyi yourgot dake cikin karamin fridge a dakinta shine yakasance abincinta,idan dare yayi kuwa uku take kasashi,kashi daya kuka,daya raya daren wurin neman mafita daga Allah,daya kuma bacci,

Tsoro ne Yakama shi ganin yar mutane tana kusan share sati adaki shi besan metakeci ba,dole yanemi yar mutane karta mutu adakin be saniba,
To taya zeyi yasamu ta bude,yarinyar ya lura tanada biyayya yasan basonshi take ba amma tana girmamasa amatsayinsa na mijinta to amma dashi baze fasayin abinda yayi niyya ba Dan akwai samu dayawa atattare da wannan lamarin kuma yayi alkawari koda da gawartane seya cika burinsa,

Zuwa yai kofar dakin yashiga bubbugawa,sulaimi Dan Allah ki fito kinema abinda zakici kar yunwa tai miki illah,kinsanfa kinada chronic ulcer don Allah kifito nayi miki alkawarin bazan miki komai ba,
Tana takure jikin gado tana bacci tajiyo bugun kofar sa gigicewa tayi gani take kamar ze balla kofar yashigo da gudu tayi sliding kofar wardrobe din gadon ta bude ta tashige takuma sliding tarufe tafi minti talatin aciki se gumi take seda taji takun takalminsa yabar kofar dakin San nan tafito,

Haka dadare yadawo yaringa mata magiya tabude ga abinci yasiyo mata dakyar tabude bayan tadauki bed side lamp daniyyar dayayi yunqurin tabata ta rafkamasa aka se yaga sama tadawo masa,lol,

Yana ganin ta bude yai saurin ja dabaya yana ajiye mata disposable dinda kebab meat yake ciki da ledar happy hour,zuwa tayi ta dauka ta koma dakinta yadda takecin naman kamar bata taba cin abinci ba duniya,
Seda taci dayawa tatura sauran fridge,
Kullum haka yake mata kwana biyu danhaka tadan rage tsoron tana fitowa yau har girki tayi musu sukaci,daga baya  yazo yana zama kusa da ita yasoma bata labari masu ban dariya tun tana Dari Dari da zamansa kusa da’ita harta sake sukanyi hira sama sama,

Daganan yafara da Dan kiss ganin be wuce nanba yasa ta kyaleshi amma yau karamin yaki suka gwabza,kokarin fita take daga gidan kota halin kaka batareda ta damu da babu kaya ajikinta ba tafi muradin fita ahaka wata kila idan Abu yaganta ahaka ya yadda da ita,

Yaa huda,yaya haido da meela ne sukazo dubata dasauran kayanta da ba akawo ba nasawa dakuma na gadon ta saboda shagon dasuka siya seda suka binciko a store dinsu,
Tsaye sukayi jin yadda ake daga murya sosae daga cikin gidan da alama ma muryar laimi kuka take,

Ki yadda kibiyamin buqatata ta hanyar danakeso hakan shine kwanciyar hankalinmu nidake,

Wallahi bazan taba shiga cikin tsinuwar Allah da mala’iku da gangan ba,idan ta hanyar sunna zakayi na yadda ka kwana akaina amma bazan taba yadda kakusance ni ta baya ba sedai idan da gawata zakayi,

Aiko sedai nayi da gawarki Dan zan iya kasheki saboda biyan buqata ta,

Yadda zuciyar yaa haido tarufe ko gabansa baya gani sosae iya karfinsa yasa yai kofar mummunan bugu atake ta balle afkawa palon sukayi,laimi naganinsu tazo dagudu dasauri huda tacire hijab din jikinta ta samata tana sakin kuka sosae ta rungume kanwarta meela dakin laimi taje tadauko mata Riga da zani da hijab suka Daura mata,

Shi kuma gogan akidime yararumi jallabiyarsa yazura yana muzurai,
Kallonsa kawai haido yayi yace,Akwai Allah kuma yanaji yana gani wannan shi ba azzalumin sarki bane muna jiran takardar sakin laimi domin wallahi tagama zama dakai,yana gama fadar haka suka fice laimi se kuka take suma se kuka suke har haidar hawayen tausayin laimi yake yadora laifin gaba daya akansa domin shine yabada karfin gwiwa aka aurar da ita batareda sun zurfafa binciken waye mijin ba,

Wayace kukawo min wannan matar gidana?,maza maza tafice min tunban illatata ba,
Abu kasauraremu kaji me zamu Fada ma maganar batayiwuwa a tsaye se an zauna,
Murya adage yace,Nace ba agidanaba,
Dasauri,laimi tatareshi Abu semubarta mijinta yaringa kusantarta ta baya?,meyin abinda al’umar annabi ludu sukayi kuka bawa yarku batareda kunyi bincike ba,
Bazamu yadda takoma ba kuma dolene yasaketa saboda mungani yau da idon mu,

Ummu dake tsaye jin hayaniyarsu tafito hawaye suka zubo mata masu zafi komawa dakin kawai tayi tazauna tana kuka,

Abbuma jikinsa yayi sanyi sosae bekara tabbatarwa ba sedayakalli yadda laimi tarame tabushe idonta duk ya zurma zuwa yai ya rungumeta yana lallashi yana shafa kanta amma takasa daina kukan,
Nasutashi a gurin ba driver din Ummu yashigo yamika takarda wai inji mijin laimi,
NI ISMA’IL NA SAKI MATA TA SULAIMI SAKI UKU.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button