HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

Kuka ta kara sakewa lokacinda takammala karantawa,Ku kanta dabiyu ne,na daya tasamu ta rabuda fasiki,nabiyu kuma tazama karamar bazawara,

Nasiha Abu yaimata akan takama kanta saboda yanxu tashiga iddah taji tsoron Allah,

Muryarta a sarke tace,ni Abu babu iddarsa akaina,sekuma kuka,kullum da mummunar hanya yake zuwa nazo nan kunki saurarata bansan yazanyiba Allah ne kadai yataimakeni,

Ba abin mamaki bane Dan haka sukace arufe babin zasuje su kwaso kayanta
Anan kuma huda ta soma naquda cikin daya wuce wata goma agigice suka kwasheta sukayi asibiti bayan sun kira deen akan yadauko kayan baby zasu hadu a asibiti.

 

……………….
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA…. Pg 17…by SophieG.

I’m sorry!
Yeah I’m sory cos I know it’s gonna touch your hearts and that’s how it’s that’s why it’s lyk this????????,
I like touching your hearts and i’m very sory for that,thankyou.

Hajiya maimunatu kudubamin yarana sun mutu wallahi basa motsi kitaimakeni,
Duk ta dabirce se hawaye take,

Hajiya maimunatu takaraso tana kai kunnenta daidai hancin laimi,
Wayar laimi dake kusa da ita tashiga Neman agaji vibrating dinda take yasa laimi miqewa da sauri tana dafe babyn dake jikinta,
Subhuhanallahi wallahi baccine yakwashe ni yaa huda kema kinyi bacci……
Maganar ta ta maqale ganin idon huda akafe ko kiftawa batayi dasauri ta miqe su Ummu sukabi bayanta,babyn jikinta ta ajiye gefe ta sauki babyn dake jikin huda ta shiga jijjigata amma ko motsi batayiba,hajiya maimunatu ta taba jikinta yayi sanyi kalau babu alamar rayuwa atareda ita,
Addua tashiga yi tashafe ta sannan taja baya tana fadin innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,

Ja dabaya kawai laimi tayi tana girgiza kanta idonta yayi ja sosae ga hawaye ya taru a ciki amma takasa zubar dasu,

Jin kanta take kamar ba aduniya ba wai gawar yar uwar tace agabanta tama kasa magana kallon mutanen dake kaikawo kawai takeyi mutanen dasuka kawo barkan tuni suntafi suna kuka kamar ransu haka duniya take babu ciwon komai Allah yakarbi ranta babban abin tausayi shine yaran bazasusan dadin uwar su ba Allah sarki,

Duk inda sukayi tana biye dasu har aka fito da gawar akaimata wanka aka yimata sutura se kallonsu take kamar ma batasan me takeyiba,kasancewar darene yasa akace abari seda safe akaita makwancinta,
Adakin Ummu aka ajiye ta ananma laimi tana zaune kusada gawar huda kuma har zuwa lokacin hawaye ko kadan bezuba daga idontaba,

Deen kuwa tamkar saukar aradu haka yaji zancen mutuwar hudarsa sumansa uku daga ya farfado seya kuma sumewa dakyar aka samu kansa,cikin darennan dukansu suka dunguma zuwa gidansu laimi balba tafada jikin laimi tana kuka me tsuma zuciya amma ko motsi laimi batayiba se kallon gawar huda take shima dai deen kuka yake kamar wata mace haka suka kwana jugum jugum
Se asuba yaa haidar yajiya Aida gashi har meela dakayan bacci sukazo Meela kuka take kamar Zata mutu itama,

Seda akazo fita da gawar laimi ta rirriqe yaahaido,
Ina zakukaimin ita?,kuduba dakyau bata mutuba lafiyarta qalaufa kuma hira muke bacci yadaukemu kuduba wallahi bata mutu ba,yar uwata nasona bazata tafi tabarni ba nida twins ba karku daukemin yaa hudata,
Janta meela tayi tace,laimi kiyi shiru karki yi sabo zo ki zauna,
Zaunar da ita tayi kusa da twins dasuka sha madara suke ta bacci abinsu,kallonsu takeyi harbata so ta kifta idonta,

Jijjigata Ummu tashiga yi,
Sulaimi kiyi kuka don Allah kiyi kuka,ki zubar da hawayen kar kema wani ciwon Yakama ki kimutu ki barni kiyi kuka Nace amma ko gezaun laimi batayiba,mari ta kifa mata tana cewa kiyi kuka laimi kiyi kuka nace,Ummu kukan yaki zuwa zuciyata CE dai nakeji kamar Zata fashe,
Rungumeta Ummu tayi tana cewa kitaimakeni Dan Allah laimi kiyi kuka kar zuciyarki ta fashe kiyi kukan kozakiji sassauci,
Hawayenda ke maqale a idonta tunjiya ne suka zubo yau sunyi zafi sosae se lokacin tasamu damar yin kuka tunda da durqushe cinyar Ummu ta sheqe dakuka takasa sauke numfashinta tamkar yaronda yayi mummunar faduwa,batada niyyar sauke numfashi Ummu ta dagota segani tayi hawaye nazuba kirjinta yayi sama kamar ranta zefita dasauri tadauko robar ruwa a fridge ta tuttule mata su afuska numfashi ta kawo tadurqushe agurin tana kuka,
Ashe hirar dasukayi akan mutuwa yaa huda yakusa barin duniya tundaga nursery one suke tare komansu iridaya segashi yanxu tatafi tabarta shikenan ita tayi ban kwana da farinciki janyo yaran tayi tarungumesu tana cigaba da zubar da hawaye,
Allah yajikan mahaifiyar Ku yakai haske kabarinta insha Allah bazaku taba yin kukan rashin uwa ba kuma babu Wanda ze rabani daku,

Yayi ban kwana da cin abinci balle kuma shi bacci,kodaya bayaji Ko agurin da ake zaman makoki kallon mutane kawai yake yana tunanin yadda zecigaba DA rayuwa batareda hudarsa ba,
Seya tuna Ranar karshe dasuka kusa yin fada saboda a kwanaki Ku karo suka kusaci taringa Neman gafararsa kenan to aranar karshenma haka tasa shi agaba Dan Allah yayafe mata haryarufeta da fada bayason haka dukda nauyinda cikinta yayi be hanata gayyatosa zuwa shimfidarsuba kuma batanuna gazawarta ba tunda tasamu ciki bata taba jure bukatar sa ta gamsar dashi irin na ranarba,aiko tasha albarka,
Wasu hawaye suka zubo masa yai saurin gogewa,

Juyin duniya anyi da laimi taci abinci takici itafa batajin yunwa kawai akyaleta se aukin kyankyamawa baby’s din madara da ruwa bata bari adaga dasu ko nan da can idonta sunyi zuru zuru ko ruwa bata nema ba hardare se 12tayi bacci yaran na gefenta,

Washe gari har jirjiri take gani atake ulcer dinta yatashi wasu abubuwa take jin ana tsira mata akirji ga cikinta na masifar ciwo nan tafara juyi tana dafe kirjinta se numfashi me zafi take fitarwa,

Gigicewa Ummu tayi lokaci daya ta zabge wayarta ta janyo jikinta na rawa takira haidar amma be daga ba sau hudu amma shiru,
Barin dubashi awaje tace tana fita dasauri bata damu da mazan dasuka cika wurinba tundaga nesa ya hango ta yatashi yana dosarta,

Ya akayi Ummu lafiya dai kika fito a hargitse haka?,INA kakai wayar ka inata kiranka?,a silent take banjiba,to taimakeni ga laimi can najuyi babu lafi….kafin takarasa fada yayi gaba abbu nabinsa abaya ko takalminsa be tsaya sawaba,idon deen akansu ganin sun shiga gidan dagudu ga Ummu abayansu yasashi miqewa shima yashiga,

Samun haidar sukayi rungume da laimi yana hawaye yakasayin komai ita kuma se hawaye take tana girgiza kai,
Dan Allah sis karki tafi kibarni kinga mukadai muka ragewa Ummu, yadda yake kuka kamar ba likitaba yasa matan dakin kidimewa suna ganin kamar bazata tashiba kenan,
Deen kallon ummu yayi yace ummu bakince ulcer bane yake dakinta?,gyada masa kai tayi alamar Eh,
Deen ya girgiza kansa yafita segashi yadawo daukeda gwangwanin madarar ruwa peak me sanyi yace karbi nabata tasha.

 

I just like touching ur heart,
Allah yajikan huda ameen,
Kuyi hakuri haka labarin yake nagode,
Ammafa kusani nima typing nake INA hawaye nataba tawa zuciya.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA…..page18…by SophieG.

Miqewa zaune tayi danjin abubuwan sun lafa mata bayan tasha madarar tana goge zufan daya tsattsafo mata,

Deen yakalleta yace,sulaimi meye nazama da yunwa?,shize dawo miki da huda?,kokuma sokike kema wani ciwon Yakama ki?,yanada kyau kiyadda da kaddara idan anmutu ba’a dawowa kuma dukanmu zamu mutu bazamu dawo ba kedai kawai ki yimata addu’a shine soyayyar dazaki nuna mata,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button