HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

Hawayen idonta tagoge tace,Yaya yunwar ce banajin ta and inajin bakina babu dadi,
Haidar yace kamar harda Dan zazzabi bari inbaki paracetamol injection amma kafinnan ummu idan akwai hura ko kunu abata kafin ayi alluran,
Dasauri ta juya har tana tuntube tace bari in dama mata,

Bayan sati daya har zuwa lokacin suna jimamin mutuwa yara dai anyanka rago amma bawanda yabi takan naman sunan,
Tana zaune rungume da huda ta fito wanka tasameta tana kuka ta jijjigata tayi shiru se ta ajiye ta kan cinyoyinta tana shafa mai se gani tayi yarinya na bude baki tana daidaita bakinta jikin maman laimi,
Wayyo Allah yaa huda zatasha nonon kanwarta,tafada tana dariya,
Ummu da shigowarta kenan tace ohhh ni jikar mutun hudu laimi zaki koyawa yara shirme ko?,
Ba wani shirme ummu yarannan sunki mantawa da nono kiga fa basu mance yadda ake riqesu inzasusha nono ba,

Ummu tayi dariya tace to Ai yaran yanzu da wayonsu ake haihuwar su Allah dai yashiryar mana dasu,

Ameen inaga gobe zanje asibiti da sulaimi mura take kinji yadda kirjinta yake amsawa intana numfashi,to Allah yakaimu goben lafiya idan kundawo daga asibitin seki je gun kakarsu Ku wuni acan,

To ta amsa tana fito da kayan sawarta a asibitin,
Washe gari taje asibiti tana zaune suna jiran akirasu huda tasa kuka se lallashin ta take amma yarinyar taki yin shiru tabata ruwa da madara amma a banza,
Matan gurin suka soma surutu,wata tace sekin koyawa yaran ki kukan banza Ku yan matan nan nazamani haka kuke kubar yara nata kuka kamar ba naqudarsu kukayi ba wai sekuce bazaku basu nonoba karya fadi kokuma kunaso Ku yaye su dawuri wasu yaran ma a hannun me aiki suke baruwanku dasu,
Tanaso tai musu bayani amma ko saurarenta basayi kowa na tofa albarka cin bakinsa wata tace,
Kuma  abinda basu saniba ruwan nono na kara bude kwakwalwar yara sukasance masu saurin daukar karatu,

Wata magidanciya na zaune daga gefe tace kinga kwanto tagoyen in riqe miki sekibawa wannan tasha Ai renon yan biyu se an shirya barakallah sunada Sha’awa amma wallahi renonsu babban Abu ne,
To meye ma nacewa setayi musu bayanin ba itace ta haifi yaranba beside ma babu komai acikin nonon sedai su tsotsa banza kuma itaso so take ta nunawa duniya yaran basuda uwar data wuceta Dan haka kawai ta miqawa matar little laimi,
Za manta ta gyara tatura little huda cikin mayafi kafin ta dura mata nonon da ko nipple dinsa be gama fitowa ba,lols,
Sega yarinya na tsotsan empty breast amma tayi shiru laimi dai zafi takeji se rintse ido take,
Sun jima ahaka kafin aka kirasu koda ta leqa fuskar  little huda tayi bacci murmushi tayi kafin ta karbi little laimi da hannu daya ta shiga,

Ahhh hajiya sulaimi haka kuka yimin ko?,inji likitan,
Laimi tayi murmushi tace haka Allah ya kaddara dai,
Amma baki Dade da aureba kuma naji ance mijin yasakeki ina kika samo yara?,

Eh hakane yayan yaa huda ne jiya sati daya kenan da rasuwarta wannan ce mura kedamunta kadubamin ita,

Allahu alkhbar Allah yajikanta ya rayamana twins,
Ameen tace kafin yashiga tambayarta yadda yarinyar keyi tana bashi amsa yagama rubuta magani yabasu yace idan babu chanji ta dawo zuwa wani satin godiya taimasa Zata tafi yataimaka mata da daukar little huda har mota yakara ka ta kafin yace,

To hajiya sulaimi nakara zuwa da kokon soyayya ta ina fatan karki yimin irinna wancan karon kiki karbata saboda Allah nake sonki nabaki dama harki gama iddah seki bani number wayar ki,

Murmushi tayi tace to Dr. shammas zanyi tunani insha Allah nagode,

Shima godiyar yayi bayan ya karbi numbern yatafi,
Seda ta tsaya ta siya maganin kafin tawuce zuwa gidansu deeen,

Aiko maman deen tayi murnan ganin su tarasa inda Zata dorasu tasasu agaba tana kallo tana kuka balba da laimi ma se kuka suke seda suka gaji Dan Kansu suka yi shiru,

Laimi na zaune tana bawa little laimi madara Sega deen yashigo batama saniba se kallon babyn take tana murmushi tsayawa yayi yana kallonta tana sanye da doguwar riga tadan kama daga kirjinta daga kasa kuma ta bude babu Dan kwadi akanta bakin gashinta yasha kananun kalaba ya zubo har gefen wuyan ta wallahi banbancinta da huda kadan ne runtse idonsa yayi sosae karfin hali yayi yakara so dakin yana cewa,
Ahh maman yan biyu yau Ranar muce kenan mu akazowa wuni,
Dagowa tai tana kallonsa……..

 

Nagaji wallah.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA….page19…by SophieG.

 

Ina wuni Yaya deen,har muna shirin wucewa ma munyi ta jiran zuwanka baka dawoba,

Lafiya lau sulaimi aikine yariqeni wallahi,yanaga wannan tanashan magani?,
Mura ke damunta daga asibiti ne ma mukayo nan likita yace idan bataji sauki ba zuwa next week semu koma,
Dan bata rai yayi yace,yazaki kaisu asibiti baki fadamin ba?daga yau duk abinda yakamata nayi kudaina yi Ku fadamin koda zakuyi aiduka responsibilities dinsu akaina yake,
Kasa tayi da idonta tace insha Allah hakan baze kuma faruwa ba,
Yawwa,idan zaku tafi ki fadamin amma karki jira se anyi magrib tunda kekadaice,

Gyada masa kai kawai tayi yafita,hawayen datake maqalewa suka zubo,Allah sarki yaa huda kalli yadda deen yakoma saboda rashinki,Allah yabamu ikon jure rashinki yaahuda,

Miqewa tayi tashimfide little laimi tayo alwala,sallar la’asar tayi tasoma shirin tafiya balba tashigo,

Anty se ina naga kina gyaran mayafi?,
Wallahi zamu tafi ne balbasatu kinsan bawani iya driving nake da dare ba kuma gashi nikdaice zan kuma je naduba Meela yaa haido yace batajin dadi tun jiya,

Ayya Allah yabata lpy yanzu dai kibani 10mnt zankaiwa my life baby’s dinnan yagani koda aka haifesu bayanan,

Murmushi laimi tayi tace to muje na daukar miki daya,
Gaba tayi laimi nabinta abaya ta tsaya suka gaisa da sadeeq din kafin tadawo gida ta kwasa kayan su takai mota,

Ahh balba wannan uban kayan haka duk na takwarori na ne,gaskiya zamuje mutuwa sadeeq dinki godiya sosae,
Nima nayi mamaki aima yawuce namasa godiya kibarshi kawai,
Murmushi tayi tace,to Dan Allah kicewa Yaya zamu tafi kar dare yayi,OK ta amsa tana fita daga dakin,

Har mota yarakasu yanaji kamar kar yaransa su tafi amma haka yayi hakuri bayan yabata sauran kayan daya siyo na baby’s daza akara cikin barka koda yazo har antafi kaiwa,har bayan motarta seda yacika,

Salamu alaikum me ciki harkin fara kyiuyan rufe gida?,
Banason tsiya malama yayanki ne yafita be ruhomin ba nikuma idan namiqe jiri ke kwasa ta,

Subhuhanallahi sannu aigashinan duk kin rame Allah yaraba lafiya,ya Karin haurinmu kuma,
Hakuri mun gode Allah,muga baby’s dinnamu naga sunyi kiba,
Miqa mata huda tayi tana cewa,aikuwa dai masha Allahu,kekam babu wani amarci wata nawa da auren harkin kwasa ciki?,
Tambayi yayanki shine yacika zalama yadura min ciki dawuri banza kawai,zanga naki lokacin,

Aimu yan gidanmu bajarababbu bane dankisani,
Karya kike er iska kifito da miji mu wanke ki kawai tunda shi wancan bakin hali yahanashi angwancewa sadakinsa yatashi abanza,
Gwanda Dabe angwancen ba kinga isma’il babban Dan iskane ya iya romance daya angwancen nasan dole sena suma kun kaini asibiti,
Dariya meela ta tuntsire da yarinya kice ke matsoraciya ce kuma kinsha matsa?,
Matsa kuwa yarinya watarana har mantawa nake awacce duniyar muke,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button