HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

To kiyi sauri kikawo wani mijin yadda zakifi jin kina lulawa sararin samaniyar dadi,amma fa ko yayanki ba baya ba,

Dariya sukayi suduka laimi tace Allah yabarku tare,Bari kiga mutafi inyaya yazo kigaishesa idan nasamu tym zanzo miki wuni,

To shikenan insha Allah zan fada mai bari inzo amma Dan kamani na miqe tsaye,

Ahh yanzu ke bazaki iya tashi tsaye dakanki ba kice har wanka yimiki ake,laimi tafada tana miqar da ita,
To meye Dan yamin wanka tunda mukayi abinda yafi wanka Ai wannan bakomai bane,
Shegiya Mara kunya nikiyi sauri kona fice,

Kayane aleda huda ta bata karbi hajiya Momy CE ta siya mana nidake tace mudinka,

Allah sarki nagode sosae zankirata ma Ai se anjima,

Bayan kwana biyu shammas yadanno mata kira kanta yayi hira sosae bayan ya tambayi jikin little laimi ba laifi tadan sake dashi,

Lokacinda yaran suka cika wata shida sunyi girma sosae kiba kuwa kamar anjika yeast anbasu ga uban kyiuya basa yadda da kowa se laimi da ummu se kuma babansu amma ko balba sesun ga tajima agidan suke yaddabta dauke su,
Zuwa lokacin soyayya tashiga tsakanin shammas da laimi soyayya me karfi haryana mata zancen turowa,

Shiryawa tayi taje gidansu deen Zata karbi saqo taje gidan meela wuni Dan ta dameta da mitar taki zuwa ita kuma yaran ke hanata sakewa basa tashi kukansu sesunga mutane kokuma bakon gida yanzu zasu fara tura mata hannu ariga wai zasu sha nono dansunga in sunyi irin haka tana saka musu abaki suna tsotsar banza amma yanzu tadaina tunda sun fara girma amma sunki mantawa,
Bayan ta karbi saqon tayi juyin duniya motar taki tashi danhaka takoma cikin gidan,
Meya dawo daku sulaimi inji deen,
Wallahi motarce taki tashi kuma ba laifin battery bane kamar laifin daga key starter ne se an gyara,

OK muje in saukeku idan kun gama seki kirani namaidaku gida,
To tace tayi gaba cinmata yayi suka jera yanacewwa,waike bakyajin nauyin yarannan ne kingoya daya ga daya a hannu,
Dariya tai tace basuda nauyi sosae Ai,

Abba ke kallonsu daga nesa wani Abu yaji yadarsamai azuciyarsa,inama yarannanan zasu amince banbanci tsakanin margayiya da sulaimi kadan ne,

Suna shiga gidan suka hadu da haidar yana goge mota,yadda suka jero dukseyaji Sundance amma benunaba suka gaisa tayi ciki,

Abba shiryawa yayi yaje gun abbu bayan sun gaisa yanuna mai bukatar sa,
Ahhh alhmdllh wannan Ai abin ayi murnane insha Allah babu wata matsala cikeda jin dadi abba yace,se a fadamin sadaki yanzu nabiya,
Babu banbanci kabayarda daidai nafarkon,anantake yabayar suka watse cikeda farinciki,

Ajikin motar shammas nahangosu shida laimi suna hira fuskarsa kamar zeyi kuka,

Haba sulaimi Ashe babu idda akanki kika bata min lokaci dayanzu munyi aure wallahi gaskiya banji dadiba,

Kafin ta amsa shi taga motar Abu ta dannonkai bayan yashigo yayi wurinsu ya gaisa da shammas kafin tambayeta waye shammas cikeda kunya kanta akasabtayi masa bayanin kowace shi,

Juyawa yayi gun shammas yace,don Allah Yaro kayi hakuri bansan dakaiba na karbi sa dakin wasu danhaka yanzu da sadakin wani akanta inafata zakayi hakuri kadauki dangana nagode,

Shigewa yai yabarsu a tsaye bakin laimi asake yayinda idanun shammas sukayi jajir Allah yagani yaso sulaimi sosae tsakanin da Allah.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA……page20….by SophieG.

 

 

Sulaimi nasoki tsakani da Allah bakuma zan taba daina sonki ba har numfashi na nakarshe,Abu daya zanyi daze nuna nimai kaunarki ne shine natayaki yiwa iyayenki biyayya kada ki sake kibijirewa umarnin su domin su ne ake Neman gamawa dasu lafiya daga karshe ina Neman gafararki adan zaman damu kayi koda nataba yi miki wani laifi kiyafeni,

Babu abinda take se hawaye,murya narawa tace,kada kayi saurin karaya kayi hakuri kabani tym zan fada musu nikai nakeso sumaidawa waccen sadakinsa,

Kul dinki sulaimi nahaneki bazan zamo silar lalata auren da Allah yakeso ya kulla ba kiyi hakuri wannan itace kaddarar mu danhaka mu dauketa hannu bibbiyu kikuma sanar dani lokacin bikin idan antsayar,motar sa yashiga yayi mata sallama yatafi anan yabarta tana kuka sosae dakyar taja kafafuwanta tashiga gidan a Palo tasamesu taje kusada Abba ta zauna,

Kafin tayi magana yarigata,kufara shirye shirye banaso adau lokaci amma nabaki dama kuyi shirinku cikin tsanaki yayanki na zuwa idan bakyason kayan wancan gidan se kifada masa akawo wasu yaso wayan can se a siyar,

Abbu meyasa Baku tambayeni ba?,bawai naqi zabinku bane a’a inagudun fadawa mummunar rayuwa ne irinta gidan isma’il Abu Dan Allah karku sakani yawon gidajen aure da kuruciya ta kutaimakeni Ku barni da shammas inason sa,dakyar take magana hawaye nazuba a idonta,

Sulaimi wannan auren ba kamar wancen bane na tabbatar zakiyi alfahari dashi kiyi hakuri kada ki watsamana kasa a ido mijin dazaki aura a yanzu shine mafi dacewa dake kitaimakemu ki taimaki yayanki ki taimaki margayiya yayarki kikuma taimaki zainulabideen,

Dawata irin razana ta miqe tsaye jikinta rawa yake kamar wacce tahau bori dagudu tashige dakinta takulle bata samu damar karasawa gadon ba tazube akasa tana kukan rashin yar uwarta kuma tana ganin kamar taci amanar yar uwarta idan ta auri mijinta,kuka tayi me isarta kafin tajanyo wayarta tashiga kiran meela,

Tana kuka ta labarta mata abinda ke faruwa amma seji tayi meela tace alhmdllh laimi dukanmu muna farinciki da wannan al’amarin kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki ki aure shi Dan Allah kuma Dan yaranki su girma agaban uwa da uban su sutashi cikin sodakaunar yan uwansu kada ki rarrabasu Dan Allah,

Shiru tayi gaba daya meela takashe mata jiki,dakyar tace zanyi tunani gobe ma zanzo,

Sallama tayi tana kara bata hakuri da karfafa mata gwiwa,

Ummu tajuya tana kallon abbu idonta taf da hawaye,abbu dole ta firgita,
Shima idonsa yayi ja yace,Zata sauko ummu mubata lokaci kiyi addua kawai,

Hawayenta ta share tace Allah yaimana jagora ya amsa da ameen kafin ya janyeta daki nikam ban bisuba.

Kuyi hakuri da wannan pls.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA…page22…by SophieG.

 

Follow me on wattpad @safiyyahgaladanchi16.

 

Shi namiji ne dayake bukatar kulawa da soyayyar matarsa,baya tunanin matar da batason sa zata iya daukar dawainiyarsa ,besan ta ina zefara ba lokacin da sulaimi takasance mata awurin sa,besan ya zamansu a matsa yin mata da miji ze kasance ba,besan ko sulaimi zata iya da lalurorinsa ba,
Atunaninsa huda ce kadai ze kwana akanta kuma ta tashi dawuri tashiryasa da abincin dazeci a office batareda ta nuna gajiya wa ba,huda itace macen dako bata furtaba zaka gane tanasonsa duk abinda yakeso shi takeso koda batada ra’ayi akansa,
Huda ce kadai yake ganin zata iya da sharuddansa wurin nuna masa soyayya,
(Yo Ashe soyayyar ta deen har sharudda ne da ita?ikon Allah),
Besan me zeyi ba ayanzu nauyin haduwa yakeji da sulaimi kawai ya amince besan ta ina zefara ba,shidai baze iya magana da ita awaya ba sekawai yayi deciding yatura mata saqo yaji me zasu buqata wurin bikin,
Dafe kansa yayi yana tunanin yanzufa seya hada lefe gakuma gyaran gida duk a satin biyunnan,
Miqewa yayi ya nufi gidansa da rabonsa dashi tun ranar da aka kwaso kayan huda zuciyarsa na masa wani irin kuna,baze gaji dayimata addua ba shine kadai soyayyar daze nuna mata,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button