HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

Se bayan kwana biyu yasamu damar tura mata saqon tana zaune rungume da pillow tana karatun wani Hausa novel mesuna zurfin ciki se dariya take sakon yashigo,
“Ki fada abinda kukeso kikuma turomin account number dinki zan tura miki”

Tsaki tayi ta ajiye wayar,shibakonta ne dabazezo suyi magana ba ze turo mata massage,
Cigaba tayi da harkokinta har yamma Sega wani sakon,

Ki turomin account number din ina cikin banki zantura miki kafin nawuce lokaci Na tafiya,

Ummu meyasa wai deen baze iya zuwa yatambayeni ba se yaita turomin massage nifa banason haka sekace wani mace daze ringa yimin yanga,
Ummu takalleta rai abace,banason iskanci sulaimi mutun matar sa ta rasu ace za a aura masa kanwarta aidole yashiga damuwa nasan baze iya zuwa gidannan ba yanajin nauyi,
Kibashi amsa ta massage din kema,

Shiru tayi kafin ta janyo wayar tatura mai saqon,
“Ni banida bukatar komai amma sunce su naso ayi dinner kawai” tatura tarreda account number din,

Dubu Dari biyar yatura mata kafin taturo massage yace,
“Ku shirya abinda zaku rabawa mutane kawai zan kama hall dakaina,abincin daza’aci da decoration duk zanyi and balba zatazo kuzabi kayan dazaki saka zan turawa Hafiz yana Dubai har dinkawa se ayi a can ranar Friday ze dawo”

“Angode Allah yakara budi”
Haka kawai tatura masa da saqon ta kwanta tana kallon su laimi dasuka zubar mata da sheo rack duka se ihun su suke ga kayan wasa ko ina duk sun hargitsa dakin,

Tana zaune a dakinta ummu tashigo riqe da wani Abu a jarka medan girma da wata roba da murfinta,

Karbi wannan kikai toilet kina hadashi da ruwa masu dumi kiyi tsarki duk lkcn dakikahiga bayin,
Wannan kuma kiringa damawa da madara kinasha sau uku arana,

Kallon ummu tayi fuskarta kamar zatayi kuka tace,ummu wayannan abubuwan bazasu yimin yawa ba?ni wallahi kar naje yakusa kasheni,
Wai meyasa kika zama Mara kunya ne?,dalla kiyi yadda nace,haka kawai tace tafita,

Har gida haidar yaje yasamu deen bayajin dadin yadda yake ganin su nesa dajuna yadauki soyayyar duniya ya dorata kan yar kanwarsa yana bukatar yaganta cikin farin ciki koyaushe yanaso yaga mijinta yana kula da ita fiye da tunanin su,

Bisimilla mana mushiga ciki,inji deen,
No base mun shiga ba nan ma ya isa,
Gaisawa sukayi kafin deen yace to muje can mu zauna magana a tsaye bazatayiyu ba,

Zama su kayi kan kujerun roba suka gaisa kafin haidar yashiga magana,

Ba shishshiga zanyiwa rayuwarka ba amma inada damuwa gameda yadda naga kuna shirin gudanar darayuwarku kaida laimi,ita yarinya ce kobayan haka ita macece a abaude take kafita hankali dasanin yakamata,banaso naga rayuwarta cikin wani hali na rashin walwala,
Babu wata jituwa a tsakaninku kudai gakunan,babu wani Abu daze nuna wayannan suna shirin zama ma’aurata,to nidai banajin dadin irin haka,huda bata duniya mutuwarta bazata hanamu gudanar da rayuwarmu ba musamman bangaren bautar Allah addu’a kawai zamu cigaba dayimata,nasan akwai nauyi amma kuyi kokarin sasanta kanku,

Murmushi deen yayi yace,haidar nagode sosae hakika masoyinka ne kadai ze nuna ma daidai yayinda kake kokarin kaucewa nagode sosae Allah yabar zumunci,
Babu komai Ai barin wuce ka gaishemin dasu ummu kasan yanzu uwar gida bazata baru ita kadai agida ba ko aikima ba kullum nake fita ba,
Dariya deen yayi yace sannu romeo,
Yana dariya yashiga motarsa yatafi,

Ana gobe daurin aure laimi na zaune da yan matanta agefen ta suna wasansu wayarta tayi ringing,ganin shine yasa tayi mamaki a sanyaye ta daga wayar ta gaisheshi yace,ina waje and kizo min da takwarorin ki,

Hijab kawai tasa ta dauke su dakyar bayan tasaka musu hula gashinsu duk a hargitse Dan basa yadda ataba gashin,

Suna zuwa tasameshi a corridor yana zaune kan kujera yana ganin su yamiqe yakarbi little huda yana cillaata sama itama se kyalkyala dariya,
Laimi ta zauna tana cewa,Yaya bazamu yadda ba wannan nuna banban ci ne Allah kuwa yazaka tsallake babba ka dauki karama,
Dariya yayi yace Allah yabaku hakuri ni banama saurin gane su wallahi,
Dariyar itama tayi tace huda tafi kiba kuma itace mummunar takwarata tafi kyau,

Tab…ban yadda ba sedai suzo kyau daya,
Da haka dai suka dan taba hira kafin yamata sallama yace zuje mota ta karbo dinkunanta da kayan su little huda dazasu saka suma,

Godiya taimasa suka shiga gida tana nunawa ummu kayan,
Ki ajiye su nan dan dakina da dayan dakin mutane sunyi yawa banaso suga kayan dazaki saka,
To tace ta bude wardrobe din bango ta tura su tasa padlock ta rufe,

Washe gari karfe goma na safe aka Daura auren Zainul’abideen Muhammad Usman da Sulaimi musaddiq Abduljalal,

Ango yasha sky blue din shadda se basarwa yake,daganan gidansu yaje suka sha hotuna shida dangin sa su umma baki har kunne,

A bangaren amarya kuwa itada yayanta sunsha ado ita tasa farin lace da sky blue din mayafi,
Su little huda ma sunsha fararen doguwar Riga da sky blue din band da takalminsu ma blue kalaba guda uku akayi dakyar,bansan yadda zan fassara muku kalar kyaun dasukayi ba,

Bayan isha’i suka yi shirin zuwa dinner,
Laimi tasa pink din lace skirt da Riga head dinta ash cloche dinta da takalmi ash,deen ma yasha ash din shadda da babbar Riga yayinda su little huda laimi tasa musu doguwar Riga pink da ash din band da takalmi har safan kafansu ash tana rungume da little huda deen kuwa yadauki little laimi.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA….. Page 21….by SophieG.

Follow me on wattpad @safiyyahgaladanchi16.

 

 

Neman bacci tayi tarasa tayi juyi hartagaji idan ta rufe idanuwanta babu abinda take gani se mutane hudu,yaa huda,deen da twins dinta,

Idan ta auri deen tazauna dashi za ayi tunanin dama haka takeso kodan ta taba yin soyayya dashi ne,idan taki auren shi wasu zasuce dama ba auren takeso ba tunda ko auren farko kinzama tayi Wanda tasha jin surutun abakin mutane,tanason yayanta ta kuma tabbata idan tana gidan mahaifin su zasu fi samun kulawa fiye da tunanin mutane bataso tasakeyin wani laifi makamancin wancan danhaka ta tsayar da zuciyarta wuri daya akan magana daya dakuma yarda daya yakuma aminta da abubuwan dazuciya da kwakwalwarta suke karantawa da hango mata,juyawa tayi ta gyara kwanciyarta bacci me dadi yadauketa ba ita tafarka ba seda mafarkin datayi yakare lokacin har gari yasoma haske,
Miqewa zaune tayi tana tunano mafarkin da abinda tagani acikin sa,
Yaa hudarta tagani cikin shiga ta mutunci da kamala tana mata murmushi Wanda bata taba ganin irinsa a fuskarta ba ko lokacin da take Raye,itama murmushi tayi tana kara samun karfin gwiwa juyawa tayi takalli little huda data farka se surutunta take irinna yara,

Yarinya yunwa ta tasheki ko?,to bari Momy tayi sallah kinga na makara ga yayarki ita kotashin batayiba nalura sekin fita zama jaruma,ta karashe maganar tana Dan matsa kumatun yarinyar dasu kayi kamar zasu fashe Dan kiba,
Kamar tasan wasa take mata itama tasoma dariya tana wasa da kafafuwanta,

Wanka tayi tayo alwala kafin tayi sallah,seda tabawa yaran abinci sukaci sundau lokaci sosae Dan yanzu suna rarrafe uban barna suke sunacin abinci suna ja mata aiki,
Karfe goma nasafe ta fito da huda abayan ta tagoya laimi kuwa tana hannunta dakin ummu tashiga tasame azaune tana dannan Waya bayan ta kashe wanka sallama tayi ummu ta dago tana kallonta bayan ta amsa,bata zauna ba ta gaisheta kafin ta fada mata zasu je gidan yaa haido,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button