Zare Da Abawa

Sulaimi zoki zauna zanyi magana dake,
Jikinta yayi sanyi ta zauna gefenta tana yin kasa dakanta,
Sulaimi nasan duk duniya yanzu bakida wacce tafini bakida wacce Zata baki shawarar da zatafi wacce zan baki,bakida wacce Zata karfafa miki gwiwa fiye dani,
Badan mu nuna miki mun isa dake ba sedan mukare miki mutuncin ki kitaimake mu kada ki watsa mana kasa a ido kinga inyaranki suka girma zasuyi alfahari dake kuma su soki irin son dazasuyiwa uwar data kawo su duniya Allah yayi miki albarka,tafada tana shafa kan laimi,
Dagowa laimi tayi hawaye duk ya wanke mata fuska tana murmushi tace,insha Allah ummu bazan kuma yin laifi irin wancen ba ummu bazan kuma bijirewa umurnin Ku ba,na amince koda yaune Ku aurar dani ga deen nayi alkawarin yimasa biyayya kamar yadda naga kinawa Abu na,
Nasan zaki iya Ai Allah yashige mana gaba,and dama inaso namiki magana akan aurenki da isma’il banji dadin yadda kikaje haka kika dawo ba laimi mace komai kuncin datake ciki bekamata tahana mijinta kanta ba kin kwaso zunubai masu dinbin yawa sulaimi,
Yamutsa fuska tayi tace,ummu niba zunuban Dana kwasa saboda be nemaba ko ranar aina fada muku Ai se in bakiji bane,
Sulaimi ranar dakikaxo kikace yana dukanki menagani ajikinki?,
Ummu kinga abinda kika gani just kawai wasane fa shine kadai abinda ya iya sekuma abinda yarabani dashi,
Jinjina kai ummu tayi tace Allah ya karemu kitashi Ku tafi Dan kudawo dawuri,sallama sukayi mata kafin su fita,
Oyoyo ga amarya to nidai ayi sauri ayi auren nan kanna haihu Momy tahanani zuwa biki,inji meela
Murmushi kawai laimi tayi ta gaisheda haidar ya amsa shima yana murmushi kafin yashiga tsokanarta,
Amarya zoki fadamin yaushe kikeso ayi bikin dakanki zaki saka date din,
Yaya waceni dasaka date?kune dai zaku saka kuda kuka jajibo auren,
Dariya yayi yace babu komai Ai mun gama magana da Abu sha biyar ga wannan watan za adaura auren kayan dakinki kawai zakizo muje kizaba Abu yace asauya miki,
Dariya tayi tace Allah yakaimu,ameen meela ta amsa tana cewa kaji yar gatan Abu amma wannan karon Ku shirya mana dinner gaskiya bamasan biki abushe,
Wane irin dinner a auren bazawara?,kudai Kubari kawai adaura auren,
Haidar ya kallesu yace zan shiga ciki kuyi maganar abinda yadace seku fadamin,
Yana shigewa daki meela ta miqe dakyar ta dauko bowl a fridge ta miqa mata ingo shanye duka gara kifara tsimuwa tunyanzu,
Hararanta laimi tayi tace,karki bani abinda zeja akusa kasheni fa Dan naga shikadai kika sani keda yaa Haidar,
Dariya tayi tace Ai bayanzu zan baki wannan ba se ana gobe za akaiki yarinya kedai kifara da wannan tukunna,
Haka sukayi ta hirar su har yamma laimi tawuce,
A zahiri ya razana dajin ba tunda mahaifin sa yazo masa dashi kuma wai har anbiya sadaki,
Kaina ke saurare deeni domin har an saka date din bikin,
Shi bemasan meyake cikiba da alama ma ahankalinsa baya jikinsa dakyar yabude bakinsa yace Abba duk abinda kukeso nima shi nakeso insha Allah babu matsala daga gefena,
Allah yai muku albarka katashi katafi ka mu ma kaje gidansu kaji ko akwai abinda sukeso zasuyi,
Gyada masa kai kawai yayi yawuce dakinsa,kicewa kan gado yayi yana kuka anfama masa ciwukansa,wai shine zeyi zaman aure bada hudarsa ba.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA…. Page23…by SophieG.
Follow me on wattpad@safiyyahgaladanchi16.
Wannan shafin sadaukarwa ne ga masoyana.
Babu laifi dinner din yakayatar anci ansha karfe goma aka soma watsewa ganin haka haidar yace suma su wuce gida ango yatafi da amaryarsa sedai yaje gidansu da ita domin mahaifiyar sa tai musu nasiha,
Haidar yace kawo twins nan za akaisu inda ummu idan tagama hada kayan su kwana biyu daidai kinhuta se akawo su,
Take taji hawaye nazuba daga idonta tunda aka haifesu ba ataba rabasu ba seyau,
Zatayi magana haidar yarigata,kiyi sauri mana dare keyi,shi da meela suka karbi yaran yai musu seda safe,
Wata irin kunyar deen ta shige laimi amotar ma ta kasa kallonsa se tattaro mayafinta take tana rufe kanta da fuskarta,
Yayinda shi kuma abubuwa suka taru sukai masa yawa,nasiha sosae umma tayi musu jikinsu duk yayi sanyi laimi se kuka take acikin mayafi,
Gidansu suka nufa motoci biyar suka take musu baya na abokanan ango da yan tsirarun kawayen amarya,
Siyan baki akayi kafin surufe da adda’a,
Sunfi minti goma awurin bayan wucewar kawaye da abokanan ango,miqewa deen yayi yaje yarufo gidan yadawo,
Dakyar yace,kitashi muyi sallah,
Babban akwatin dake gefe ta janyo da kyar tasamo hijabi kafin tashiga toilet tayo alwala tun a can tasako hijabin tazo suka gabatar da sallahr nafila,
Komai jiki a sanyaye yakeyinsa nama yakawo musu amma laimi ko tabashi batayiba dukda yunwa dake addabarta,
Toilet yashiga yacire kayan jikinsa yasako jallabiya fara me gajeren hannu yazo ya kwanta,
Can karshen gadon ta rakube ko kayan jikinta bata cire ba kuka take ahankali Dan tunawa da itace yanzu take auren mijin yayarta,
Yadade idonsa arufe beyi bacci ba ganin Bob din dakin akunne shirun da yaji yasashi kallonta yaga bacci take awahale,miqewa yayi zekashe yar mutane yatuno da nasihar abbansa,
Deeni sulaimi amana ce agareka kakula da ita yadda kake kula dakanka,yadda ka kula da yayarta koma fiye dahakan,inaso kabawa Mara da kunya,
Juyawa yayi yafita daga dakin,dakinta yashiga yajanyo akwatunan lefenta yasamo doguwar Riga ta bacci me kauri yadawo dakin,daf da ita yaje ya zauna zaune ya miqar da ita yacire hijabin jikinta kwanto da ita jikinsa yayi yaji jikinta da zafi,girgiza kansa yayi kawai ya zuge zip din rigar tafarka kunya ta dabaibaye ta da sauri ta riqe hannunsa,
Banason musu,kadai yace yayi kasa da rigar yasa mata rigar baccin itadai idonta na kasa,miqar da ita tsaye yayi yakarasa cire rigar,cikin dauriya ta balle bra dinta ta cikin rigar ta cire hannun bra din da sauri yatura hannunsa takasan rigar yazaro bra din ya kwashe kayan yasa su a wardrobe,
Wutar dakin yakashe yadawo yakwanta yana sata ajikinsa ahankali yace,
Lafiyarki kuwa?naji jikinki dazafi,
Lafiya lau kawai tace tayi shiru Dan bacci takeji sosae,
Shima shirun yayi yana Dora lips dinsa awuyanta numfashinsa me zafi nakashe ko INA najikinta Neman baccin tayi ta rasa gaba daya ta shiga shauki,azuciyarta tace,aiga irinta nan babu yadda banyi da ummu ba abubuwan nan zasu yimin yawa takiji,
Ganin zezautar da ita kawai setayi dabara acikin baccin tayi juyi Wanda yasa taraba jikinta da nasa,se asannan tasamu bacci yadauketa,
Da asuba koda ya farka yaganta awahale yanajin saukar numfashi ta yasan zazzabi take alwala yaje yayi yatafi masallaci bedawoba seda haske yasoma fitowa tun a hanya yakira Haidar,
Ango lafiya dai kira da asussubar nan?,inji haidar,
Sulaimi CE ke zazzabi ko zaka taimaka kazo kadubata pls,
Insha Allah bari ganinan zuwa,
OK to sekazo,
Koda yakoma dakin yasameta kwance da alama tayi sallah, se juyi take tana dafe da kirjinta,
Girgiza kansa yayi yakoma yadauko madara a fridge yadawo,
Haidar kuwa dakin meela yashiga yace,maman baby zanje gidansu sulaimi yanzu deen yakirani wai batada lpy,
Subhuhanallahi meyake damunta ko duk amarcin ne?,
To gsky bansaniba zanje dai inga idan zamuje asibiti ne to zandawo inshirya,
To Allah yabata lafiya,ameen ya amsa yana fita,