HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

OK Allah ya sawwaqe bari muje musiya maganin,
Koda suka isa gida dakansa yahada mata ruwan dayafi nadazu zafi tayi wankan kuma ba laifi ta Dan ware,abincin sukaci suka zauna zaman kallo tayi pillow da cinyarsa,kallonsa tayi tace,
Yaya deen,
Amsawa yayi yana kallonta,tace
Kana sona?,
Tambayar yabashi mamaki amma seya waske yafada mata gaskiya yace,

Sulaimi tun ranar Dana Dora idona nafarko akanki nafara sonki bakuma zan daina sonki ba har duniya ta nade inasonki fiye da tunanin ki,
Aurena da huda kaddarace kuma akayi daidai da itama inason ta tun ranar Dana fara ganinta kyawawan halayenta suka kara sawa soyayyar ta taimin yawa da wata ce daban na tabbatar bazata yadda da abinda mukayi mata harta bar abin yawuce ba Allah yajikanta yasa muhadu a gidan aljanna,

Ameen ta amsa da Dan guntun hawayenta,

Share mata su yayi yace,sulaimi Dan Allah kikoyi koda rabin halin huda ne duk abinda nakeso shi takeyi bana gundurarta idan kinaso mutafi daidai sulaimi idan na nuna miki soyayya ta ki nuna min fiye da ita,kin gane?,
Gyada masa kai tayi yace to bari inbaki example mugani,
Pecking dinta yai a chicks, dagowa tai ahankali tahade bakinsu,wani kalar kiss take mishi daya kusa zautar dashi hryana Neman rasa nutsuwarsa,

Karatun da isma’il yakoya mata ne,lol.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA….PAGE 25….BY SOPHIEG.

 

Y’ay’ana abin alfahari na,wannan shine littafin na Wanda ban taba tunanin ze samu karbuwa yadda yasamu ba,abinda yake sani nishadi shine yataba zuciyar duk wacce ta karanta haryana cin karo da ainahin wayanda abubuwan ke faruwa dasu dagaske,har yanzu yana samun makaranta kuma dagaske yana taba zuciyarsu yadda nakeso nagode sosai,dont worry I’ll soon touchbur hearts again.

 

 

Yau CE ranar dasuka cika sati daya da aurensu tana zaune a dakinta tarasa me zatayi,deen yafita danhaka tajanyo akwatinta ta kwantar dashi,zip din sama ta bude hadi da zaro wani littafin Hausa mesuna,Gidan gadara,
Har tayi kwanciyar karatu taji ana buga kofa,hijab dinta tasaka taje tana tambayar wanenen,

Bula ne driver din hajiya,dasauri ta bude yan biyunta tagani hannunsa murmushi tayi ta karbi huda yashigo har Palo ya ajiye laimi yaimata sallama yafita,megadinsu yashigo dakayan su,yaran se suka lafe a jikinta atake sukayi bacci,tana zaune se kallon gashinsu take yadda duk ya hargitse taji ringing din wayarta,ummu CE ta kirata bayan sun gaisa tace,

Kinga naturo bula da yayanki ko?,wallahi sunhanamu rawar gaban hantsi yara wata bakwai amma bakinsu yasoma budewa?,dakyar mukayi kwana bakwai dinnan hanamu bacci suke wata rana harse abbu ya koromu yadawo aiki yagaji amma su hanamu bacci kuka suke suna kiramin mamma shiyasa yau nace aidai yakamata sudawo Dan kun huta dai ga sunan Allah yabaki ikon reno,

Ameen tace,amma ummu kibar min yara babu kitso ko kina kishine kinga sunfi ki gashi?,dariya tayi tace,duba kan huda kiga zakiga kalaba guda daya ranar Dana yimata atsaye nakwana,keni se anjima bacci nakeji tun asuba suka tasheni,

To se anjima ummu,
Kafin ta ajiye wayar Sega kiran deen,dagawa tayi tana sallama,
Baby kishirya ganinan zuwa zan kaiki gidansu meela Ashe tun jiya ta haihu da safe shine babu Wanda ya fada mana,

To shikenan ga twins nan ma ummu tadawo dasu wai tagaji,
Dariya yayi yace to aimun gode seku shirya ganinan zuwa,

Gashin kanta ta taje tasaka mayafi twins dake bacci kawai tasa musu hula,tana zama yana shigowa,seda ya tsaya ta tsotse bakinta dakyar ta samu ya rabu da ita,
Kallonsa tayi tace seka cinye bakin ka huta ko?tunjiya ka hanasa zama lafiya,

Hannunta kadai yaja suka fita,
Awaje ya tsaya aka kawo masa baby yagani dubu biyar yasa a rigar yaron takoma dashi,

Fisabilillahi yanzu meela seki haihu bansaniba arasa Wanda ze fadamin,

Wallahi meela jiyannan banajin dadi ne bleeding fa na ringa yi sedare aka samu ya tsaya Toni hankalina be bani baki saniba sedazu nacewa haidar banganki ba yace ummu tace kar afada miki Dan tasan fitowa zakiyi kuma be kamata ace kinfara fita ba aure sati daya dukda haka nace gaskiya afadamiki shinefa ya kira abideen yafada masa,

To shikenan Allah yaraya mana,kubani ruwa masu dumi zan hadawa yarannan friso,
Ga sunan a flask,
Wuni sukayi agidan se daf DA magrib suka koma,

Sallah tayi tadafa musu taliya sukaci tayi wanka tama yaran deen ma yayi yafita zuwa gidansu,
Akasan rug ta kwanta huda ta hau kanta ta zauna laimi kuwa ta hau cikinta se wasansu suke itadai tayi shiru tana jinsu Dan haryanzu tanajin jikinta,
Kwankwasa kofar akayi dasauri yaran suka rarrafa zuwa kofar saboda son yawo ne dasu,

Wata yar yarinya tagani bazata wuce shekaru ashirinba dadan cikinta daya soma fitowa,ja dabaya tayi fuskarta da fara’a tace bismillah kishiga mana,

Shiga tai DA sallama laimi ta amsa ta janye twins dake kokarin tare mata hanya,tace kizauna barin kawo miki ruwa,
Har sauran taliyar ta kawo mata da mango juice,
Allah sarki nagode sosai kamar kinsan nakasa cin abinda na girka wannan kuwa ina ganinta haryawuna ya tsinke,

Dariya laimi tayi tace to seki bada himma,seda kuwa ta cinye ta tas tace,

Sunana ameena parrot,lol,watana Na bakwai kenan anan unguwar nashigo gidannan saudaya gurin tsohuwar matar gidannan wacce Allah yaiwa rasuwa sekuma naji labarin rasuwarta saboda nalura tana kirki kuma naji labarin ta haihu to kuma bansan unguwar dasuke ba ga mijinta yabar unguwar balle inje indubo yaran last week naga anyi taro shine akace amarya za akawo,kiyi hakuri amma dai ke kanwar matar data rasu ne ko wallahi kuna tsananin kama,

Murmushi tayi tace eh ni kanwartace gakuma yaran data bari nan,
Masha Allah, Allah yaraya su,ameen tace,sunana sulaimi yaran ma sunan mu sukaci,
Dariya tayi tace to barin wuce megida yanzu ze dawo gida nane yake kallon naki daga kinfita,
Insha Allah nima zanshigo,

 

Sanda yadawo twins sunyi bacci itama se gyangyadi take,seda yayiwa yaransa dake bacci kan katuwar katifar dake malale adakin addu’a sannan yahau gadon,
Zakayi wanka ne?,a’a yace yana hade bakinsu,

Numfashi take saukewa ahankali tace,abideen waikai baka gajiya ne?,haka fa kake da yaa huda kana dawowa seka janyeta daki,

Dariya yayi yace,ki yarda dani ba abinda nake mata befi muyi saubiyu asati ba hiararmu ta masoya muke ko muyi bacci sometimes be wuce haka danake miki se romance kawai,Ai bana wahalar da mace ni,

Bargo taja tace to seda safe bacci nakeji,
Da kirjinsa yaimata pillow yace nima inajin baccin Ai,

Ba karamin yabawa laimi yayiba wata rana harse yaga kamar tafi huda ma,
Yadda take kula dashi haryakanyi mamaki abinci sau uku bata gajiya gayaranta ma tana kula dasu sunyi kiba sosae daga ita har yaran da mijin musamman ita kamar zata fashe,

 

Har sukayi wata shida da auren ummu sedadi yakeji ba agaba jin kan su ba sema soyayya datake ganin suna nunawa juna.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA…. Page27…by SophieG.

 

 

Kamar agano wannan cikin naki shikenan ya kunno kai kalli girmansa,deen yafada yana kallonta,
Dariya tayi tace,nima abin yana bani mamaki musamman ma Wannan kumburin danakeyi kamar zan fashe amma fa banajin nauyin jikina,

Banyadda bakyajin nauyin jikinki ba duk Wanda yaganki haka yasan kinajin jiki ji yadda numfashinki ke fita da bibbiyu,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button