Zare Da Abawa

Dasauri ta fita daga wurin tana rufe idonta hadu da danne kirjinta gefenda zuciyarta,taku takeji irin na kafafuwa yana taka kowane sashe na zuciyarta,
Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, me yake damuna?tafi awa daya a duqunqune kafin tasamu bacci yakwasheta washe gari komai asanyaye takeyinsa yau setakejin so kawai take ta ganta a naija wallahi da zata iyayin fiffike sedai su ummu suganta a naija batayi tunani sau biyu ba ta kira Abu,
SULAIMI yaya dai kira da sassafen nan, adiririce tace eh nakirane naimuku yagajiyan biki,Alhmdllh ya exam din kuma kungama ne ko yaya?,eh Abu kingama shiyasa nakiraka Abu Dan Allah indawo ranar Monday kafin result dinmu yafito,
Shi yana mamakin shirme irin na SULAIMI, cikin fada yace,waike wace iri CE?iye?to banida kudin da zakiyi wannan yawo kijira sekin gama hada komai naki daya danganci makaranta sannan ki dawo bana son shirme,
Haba Abu ni yanzu kwata kwata kunbar sona,shekara daya darabi banzo naga gida kuma yanzu nace zanzo kace a’a,se kuka yana magana bama tajinsa kashe waya kawai yayi ya kyaleta,
Tundaga ranar walwalarta ta ragu babu yadda meeela batayi da ita ba amma takasa shawo kanta daga ma ta dameta takesa samata kuka Abu ma yayita kiranta taki dagawa ummu cema suke waya shima muryarta akumbure wai basa sonta yanzu shine taketa fushi,
AFTER ONE MONTH AND SOME WEEKS
LAIMI pls what’s all ths for?kindawo tundaga Sudan bayan fin shekara daya ace bazaki kira kowa yazo ya daukeki ba akasa zaki karasa cikin gari? Bakya tunanin hukuncin da yaya haido ze dauka akanki (yayansu abdulhafiz),
Ke zaki bani lift idan anzo daukarki idan kuma bazaki bani ba let me know so that na nemi mafita tun lokaci be kure min ba, fuska ahade tai maganar,
Allah yabaki hakuri yar autan ummu da abbu,har cikin gida zan kaiki,
Ummu, abbu, yaa haido suna zaune a palo se ganinta sukayi da kaya niki niki ta ajiye su gefe malan garbati yabiyo da sauran zuwa tai har gabansu duka ta gaishesu sedai kalar mamakin dake kansu yahanasu amsawa,
Yaahaido face, laimi ya akayi haka bakisanar mana zaki zo ba waye yabiyamiki kufin jirgi kuma yadaukoki daga airport,?
Dagowa tayi zatayi magana takasa daga cewa yayaaa….. Sekuka tafada jikinsa, duk rikicewa sukayi suka shiga lallashinta dakyar suka samu tai shiru, haba yar autan abbu kiyi hakuri kinji tashi maza kije kici abinci kiyi wanka kiyi hakuri,
Se asannan tasake tashiga walwala dasu se zuba musu labari take dama laimi badai surutu ba suma se labarin biki suke bata da akayi batanan,
Ai ummu yau agidan yaa huda zan kwana inaso inganta wallahi,
Aikuwa dai dakin kyauta dama tanata jimamin kwana ita kadai yau mijinta yaje abuja yin wani aiki,
Tsalle tayi tashiga murna da sauri ta janyo akwatinta yaa haido dan Allah muje ka kaini,
Ganin ta sake bayaso ranta yakuma baci yasa yamike yace muje sallama taiwa ummu tawuce se dadi take.
Kuyi hakuri da wannan wallahi tun safe nake typing bansan meyasa nazama lazy ba yanzu. ????
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA
Story and written by SophieG
Hanjin jimina’s fans
SophieG novel group
Taskar Billy galadanchi ina miqa dimbin godiyata agareku,
Hakika masoyana ne kadai zasuringa bin littafina, sune kadai wadanda zasu ci Karo da kuskure acikin rubutuna sujani gefe suyimin gyara batareda sun muzanta niba, masoyanane kadai zasu bi littafina koda baiyi dadiba kokuma bashida ma’anar komai, duk inda masoyana suke masubin littafina ina miqa godiyata agaresu kuma ina fatan idan sunga kuskure atattare da rubutuna sukasance masuyimin gyara hanya mafi dacewa, wannan shafin nakune masoyan safiyyah galadanchi Allah yabar kauna ameen.
Page 4
Bansan me laimi take nufi da sababbin abubuwan data tsiro dasu ba sedai nalura duk bayan kwana biyu seta kira deen wai gaisheshi take gawani suna data sama mai wai swit bro,
Yakan dan biye mata sugaisa kuma ayi barkwanci irin Wanda yake ganin yadace atsakanninsu,sedai tana zuwa dawani shirmen yake mata sallama,
Yauma kamar kullum yaa huda na bacci bayan tagama kwadayin awaranda laimi tasiyo mata takwanta bacci,
Laimi ta kira deen Abu daya kesashi yadaga saboda bayida tabbacin dasanin yayarta take kiransa haka kokuwa bada saninta ba,
Hello sweet bro wai seyaushe zaka dawo niwallahi inaso inganka,
Laimi kibari yanzu ina aikine kinji, soyake yaimata sallama saboda yadda take maganar dawata haramtacciyar murya, sosae abin ke daure masa kai,
Ummmm banyaddaba seka fada….,dit dit taji alamar yakashe wayar, hmm kome zakayi bazan daina kusanto kaina dakaiba harse nacika burina,
Abubuwan da laimi ke masa sun daure masa kai sedai besan yazeyi da ita ba ta wani bangaren idan yana tunani seyace Ai jiya ba yauba yaki fada mata yaushe zedawo dan yasan yafadawa yayarta ita ce yadace yafadawa domin taimasa tanadi na musamman,
Washe gari karfe shida dasukayi salla basu kwanta ba,
Wai yaa huda mezamuyi yanzu nifa bacci nakeji,
Sweetdeen dinane ahanya yau dawowa zeyi,
Ai miqewa kawai tayi, eh yakamata amai girki mekyau, muje mufara,
Huda taji dadi ganin kanwarta na murnan dawowan mijinta danhaka suka shiga kitchen suna aiki harsun kusa kammalawa huda tace ,
Kai amma naji dadi zamu gama aikinnan dawuri,
Sabodame ,inji laimi,
Ahh sweetdeen Dina akwai takura nasan idan yadawo baze barni inhuta ba, kinga yanzu karfe shadaya wanka kawai zanyi in kwanta karfe daya da rabi kitasheni nasa kayana naisalla muje airport dan jirginsu 2:00 ze sauka,
Ummm, kawai tace dan tagane me huda kenufi,
Suna isa lokacin har mutanen jirgin sun gama sauka segashinan ya iso cikin tafiya irinta isassu masu ji da aji,
Yana sanye da kananun kaya Riga ja da wando baki wayarsa ce ahannunsa yana daddannawa da alama kira yakesonyi seji yai anrungumeshi,
Kamshin humran dake jikinta yasashi gano itace dagata sama yai kafin yasauketa yana bata kyakkyawan kiss akumatu,tana lafe jikinsa itadai laimi tana gefe haushi yadirar mata azuciya gaba tai dasauri tashiga bayan motar ta zauna, gani kawai tayi sun bude gefenta huda tace dan Allah sis kiyimana driving muzauna nida yayanki kinsan munyi missing juna,
Murmushin da iya labbanta yatsaya tayi kafin tafito takarbi key din motar ta zauna gefan driver suka shiga suma gabadaya huda ajikin deen take takai bakinta daidai kunnensa nahagu shikuma yana daidai kunnenta na dama
Tace sannu dazuwa sweet heart damuryarta me dadin saurare, yawwa baby dafatan kinshiryamin tarba me kyau?, dariya me dan sauti tace, kaima kasani ai,
Daidai lokacin sukahau highway din daze kaisu cikin gari,
Dagudu laimi ke tuqin haushinsu ya isheta amma ina sunma manta da ita se luv dinsu suke yarfawa,
Daidai wurin wani junction wani memota yazo bejira ta wuce ba yakutso kai saura kadan suhade sauke glass tai ganin masoyan basuasan tanayiba tayiwa me motar daquwa tace jar kaniyarka,
Har lokacin hiransu suke suna dariya,
Jakan yayarta ta dauka ta bude gidan tashiga batakobi takansu ba,
Dakinta tashige tarufo shi ta jima kwance zuciyarta kamar ta fashe Sega huda tana buga kofa, laimi kizo muci abinci, dakyar tace kuci kawai bacci xanyi idan natashi naci dakaina, batareda huda takawo komai aranta ba tace to sweet laimi,