HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

To Ai numfashi na normal ne tunda bani daya bace,
Kila kema twins zaki Haifa mana,
Rike baki tayi tace,rufamin asiri renon twins da wahala wallahi su huda sun ishemu,

To Ai shikenan zamu gani bazaki wuce sati biyu ba,
Eh mana Allah dai yasaukeni lafiya naga,barinje in shirya ka kaini nadubo balba,
Meya samu balba din?,
Dazunnan umma takirani baka nan wai balba tasamu miscarriage suna asibiti ma,
To kiyi sauri kidaukowa twins hula gashinsu duk ya yamutse,

Shirin ta tagama yi tafito tasamu twins zaune da Leda agabansu,nama sukeci gasashhe da hakoransu guda hudu basama iya cin naman,
Yanzu fisabilillahi shine seka basu naman dansu lalata kafasan bazasu iyaciba kuma bazasu yadda na taba ba,

To kibar musu mana muje na siya miki wani suma kuka suka sa shiyasa yabasu saboda banason kuka ko kadan,

Kallonsu tayi tace kutashi mutafi to,kamar badasu take yiba danhaka tace,to huda muntafi mota bye bye,dagudu suka miqe basumabi takan naman ba inda takalminsu suke sukaje suka dauko laimi da deen se dariya suke,

Daga asibiti gidansu yakaita ta gaida ummu tajima ba taje ba,

Sulaimi kidawo gida haka,kalle kifa duk kin kumbura gashi bakida me aiki,tunda haihuwar ta kusa kicewa mijinki kinaso kidawo gida,

Ummu ni wallahi cikin nan babu abinda yake hanani yi dukda yanada nauyi amma ko kumburin nan danayi banajin ciwon komai,
To shikenan Allah ya saukeki lafiya,ameen ta amsa tana dauko ledar nama tace Ummu zo muci,

Girgiza kai ummu tayi tace,kibada himma kece kwadayayya yanzu,
Dariya kawai tayi taci abinta,sedare suka koma gida,

Yau da safe ta tashi tanajin nauyin cikin yakaru amma bata damu ba,tana fito da inners dinsu masu datti zata wanke,

Na hanaki wankin nan kinki kibari ko?,deen yafada yana harararta,

Inace wankin nan a machine ne?,daurayewa kawai zanyi na shanya kuma babu abinda nakeji zanyi abina,
Girgiza kai yayi yace,Allah yabaki Sa’a sena dawo,
To Allah yakiyaye,
Ameen yace yana fita,

Zama tai ta wanke su duka a machine ta matse su ta dauraye,bucket biyu tacika masu girma ta dauka se tsakar gida tabar su little huda a Palo suna wasansu duk sun zubo da throw pillows suna goyawa,

Shanya kayan tayi duka a igiya,sedai takasa miqewa daidai yadda take da,dakyar takoma dakinsa takai bucket din toilet,tana ji tana gani takasa fita daga dakin,wasu ruwa kebin kafarta kokarin daga kafar tayi amma takasa durqushewa tayi agurin tana runtse idonta sosae saboda yadda taji bayan ta naciwo,

Lallai wannan shi ake kira naquda,yanzu ita ya zatayi ta dauko wayarta ma takira wani,
Ganin dagaske haihuwar ce jin wani Abu na kokarin ratsa ta tasaka hannunta ta fige zanin jikinta tana addu’a da ummunta tafada mata,

Ko ita karar datayi seda ta firgita ta,se uban gumi take hadawa,miqa hannunta tayi ta dauko babyn tadora acikin ta tana jin yadda yaketa kuka,
Ashe abin be tafiba,wata sabuwar azaba tazo mata,kawai seta fashe dakukan dabashida hawaye second baby yafito se kuka yake shikam tama kasa dauko shi daga kan zanin se sauke numfashi take batamasan me zatayi ba,
Tana cikin tunani Sega twins dinta sun shigo dagudu da wayarta a hannun laimi tana cewa cikin hausansu,

Mamma anbugo,
Hamdala tayi dasauri ta karbi wayar sukuma lokacin dasuka lura da jini malemale akasa suka kurma ihu dagudu suka fita(Yaro baya kaunar ganin jini ko wani babba yagansa hankalina tashi yake),
Ummu kawai takira tana dagawa tasa mata kuka,
Subhuhanallahi laimi lafiya?ko naqudar CE?,
Ummu na haihu nikadai a gidan kinji kukan yaran ma,

Alhmdllh twins muka samu kuma?,jirani ganinan zuwa yanzu,
Haidar takira yaimata kwatancen gidan bula yakaita,
Allah yataimaketa gidan abude yake tashiga,duk abinda yakamata tayi ta gyara babyn da mamansu,
Yaran duka maza ne asibiti sukaje haidar yaduba su dakyau suka koma gida laimi ta Debi kayanta Dana twins dinta suka wuce gidan Ummu,

Se lokacin ummu takira yan uwa tasanar musu da haihuwar,deen dadi yakashe shi da mari gidansu yaje ya dauko ummansa sukaje ganin karuwar dasuka samu,

Koda sukaje a Palo suka samu laimi tana bawa babyn mamma,tana ganin umma kunya ta kamata.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA…page26..by SophieG.

 

Yarasa meyake damunta tundazu yake tambayarta amma taki tai gaya masa se kuka take ga dare yayi,tun shekaranjiya yagano ta rage walwala gashi yazo mata da albishir amma gaba daya ta birkice masa,
Wani haushi ne yakamasa cikin tsawa yace,
Dalla d’aga daga jikina inbazaki fadamin abinda yake damunkiba haka kawai kisani gaba kinamin kuka nayi tamabaya kice min babu komai,

Gefen daya tureta nan tai kwanciyarta tana kukanta,shima juyawa yayi ya kyaleta tagaji tayi bacci,
Da takai cin ta yayi bacci,
Tun asuba data tashi tayi komai yadda ta saba tabar mai dakinsa wanka tayi tayiwa twins dinta kafin tasameshi dining yana kar yawa,

Dan Allah Yaya yau inaso naje gidan Yaya haidar inda meela,

Allah yakiyaye kawai yace yafita suna binsa abaya itada twins seda yafita ta dawo breakfast tayi ta shirya suka fita,koda ta karasa twins sunyi bacci haka ta kinkimesu tashiga gidan,
Zaune ta samu meela tana shayar da babynta kamarma yayi bacci,

Bayan sun gaisa meela taga kawar tata bata walwala kamar yadda tasaba,
Sulaimi lafiyarki dai?,
Tana hawaye tace wallahi ba lafiya ba,
Zama meela ta gyara tana kallonta a firgice Dan ita ta zata matsalace tsakanin ta da deen tace,meya faru?,

Sulaimi ta goge hawayen fuskarta, yau kwana biyar kenan nakejin motsi acikina kuma marata na ciwo,tsoro nakeji kila wani ciwon ne Yakama ni banaso na mutu nabar twins dina bansan Waze kulamin dasuba hankalina yatashi,

Meela kasake tai tana kallonta tama rasa mezatace wannan wace irin wauta ce da sulaimi?,
Mtswwwwww… Taja dogon tsaki,wallahi kintayamin da hankali nima shikenan daga kinji motsi aciki sekice ciwo ne ya kama ki?,
Yaushe rabonki da period?,
Ni tun bayan rasuwar ya huda da wata hudu nayi shine na karshen ban kuma yiba,amma ban damuba tunda nakanyi Rabin shekara ma banyiba,

Ni seyanzu ma naga alamun masu ciki ajikin ki,anya ba ciki gareki ba?,kalli yadda kikayi haske da kiba,

Meela bawani ciki fa ni banji canji ajikina ba bawani laulayi kuma,
Eh duk da haka dai bari INA zuwa,

Dakinta tashiga takira deen,
Zamuzo asibiti ne ko kana can?,
Inanan mana waye ba lafiya?,
To sulaimi CE dai tazo da shirmen ta wai batada lafiya tana tsoron wani ciwo yakamata motsi takeji a cikinta kuma mararta na ciwo,

Subhuhanallahi kawomin ita ganinan INA jiranku yau babu patients dayawa,
To gamunan zuwa,

Meyasa kika fada masa?,inji sulaimi,
To seki kirasa kifada mai bazaki ba,
Hijab dinta tasaka zata dauki huda meela tace barsu nan zuwaira nanan Ai tunda ba jimawa zamu yiba,

Fita sukayi tana kiran deen Dan tafada masa amma yaki dagawa,tatura masa massage amma OK kadai yamata reply dashi,

Bata damuba tasan yadda zata shawo kansa idan sunkoma gida,

Suna zuwa suka shiga office dinsa yamiqa mata roba karama me murfi yace,shiga toilet gashi kiyi fitsari kukawo min,jikinta a sanyaye taje tayi takawo mai yakarba ajiye gefe yace ta kwanta kan gadon dayake duba marasa lpy,

Idonta yaduba da tafin hannunta,kafin ya daga rigarta yadan matsa,jinjina kaiyayi yadauki fitsarin yafita bayan yasa gloves yana cewa kujirani,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button