HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

Sukam tsakuran abincin kawai sukayi musamman deen suka shige daki love suka dirza kamar ba gobe, se bayan ishai suka fito lokacin laimi tagama hasala tana zaune tanacin indomie da sardine ga dafaffen kwai da cinyar kaza tasoyu agefe ga kuma fresh mango juice agefe (gaskiya raina yabiya),taji lokacin dasuka fito amma batako kallei gefen dasuke ba, taduqufa dacin abincinta segani tai huda tasa hannunta tanaci cankuma tadeba takaiwa deen abaki yadda indomie din taji kayan lambu yasa ya hangame bakinsa ta zubamai duk a idon laimi ruwan indomie din yataba gefen bakinsa nan huda takai harshenta ta lashesu,

Anzo gabar da bazata iya jura ba afusace tamiqe tabar gurin dakinta tashige tana banko kofar da karfi,

Bin bayanta dakallo sukayi anrasa me bakin magana, ita huda mamaki take meye ya tunzura laimi ta fice haka ko magana batai musuba, to Kodai samata hannun datayi a abinci ne to ai bayau tasabayimata haka ba kuma ranta betaba baci ba to meye ze bata ranta yanzu, kallon deen tayi da alamar tambaya,
Kauda kansa yayi danshi yaga take taken laimi amma baze yadda yayarta tagane ba kodan kare lafiyar ta wannan abin bakin cikinbesan dame ze aunashiba,

Muje mu lallashi sweet sis yace yana riko hannunta da murmushi afuskarsa.

Follow me on wattpad @safiyyagaladanchi16
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA

Story and written by sophieG

Page 5

Sunyita buga kofar taqi budewa secan wani tunani yazo zuciyarta tace, anya bazasuyi saurin gano me nake nufi ba?, yakmta na canja salo, dasauri taje ta bude murmushi huda tayi tace haba little sis meye haka kuma kiga yayanki fa yadawo ko gaisawa bakuyiba,

Dakyar ta matso kwalla tana kallonsa tace sannu dazuwa,
Shi dariya ta bashi ma sa’ar huda ke wannan kuruciyar,yawwa little sweet sis yaa hudace ko metaimiki?,

Ai dukanku ne hardakai, riqe baki yai yana zare Ido yace memukai miki?,

Kune kuka barni da yunwa hardare nadafa indomie na kunzo zaku cinye kuma kunata soyayya agabana kunsani jin kunya, dariya huda keyi kamar me tace to kiyi hakuri zomuje kikarasa cin abicinki kizo abude jakar tsaraba dake,

Tanacin indomie suna hira hartagama se satar kallon deen take,

Washe gari ummu tayi kiranta a waya tace, sulaimi kidawo gida haka tunda mijinta yadawo karki takurasu,

Haba ummu wane irin takura ni bayanzu nakeso na dawo ba,
Ke kina haukane? Mijinta nagari zakije ki tsaresu maza kihado kayanki gobe kidawo kinaji na ko?,
Eh tace tana kumbura murya dabaki,

Wunin ranar da kunci tayishi tunani yazo matatakira deen, lkcn dayaga kiranta seda yaji gabansa yafadi haka yadaure yadauka,
Cikin muryar kuka irinnan shagwaba tace,
Sweet kaga ummu wai sena koma gida gobe nace bazan koma ba wai Dole Dole gobe zan dawo kuma ni bangaji da ganin ka ba,

Tunani yadanyi itama hudan tazama wata raguwa ba abinda ta iya yanzu daga bacci se kwadayi dama yana tunanin samo mata yar yarinya dazatana tayata ayyukan yalura kamar laulayi take kafin cikin yayi kwari sedai maganarta ta karshe wai bata gaji daganinsaba tasashi shiga duhu, amma dukda haka zeje inda ummu yace ta aramusu laimi zuwa nadan wani lokaci,

Haka kuwa yayi jin yace batadan jin dadine yasa ummu yadda murna fall zuciyarta Sata samu jika, harda hado masa kayan kwadayi dataje cikin gari ta kwaso,

Shima yai godiya yawuce,
Lokacinda ya koma gida yafadawa laimi ummu ta yarda tsalle ta ringayi ganin tasamu Dama dan haka tashirya plan dinta cikin kwanciyar hankali, takira Abu wai kawarta zatayi aure shine takeso tabata kudi dan bazata iya Shiga kasuwaba saboda yaa huda batajin dadi dubu ashirin yaimata transfer tun ranar Sunday da dare ta siya kati ta bank ta ajiye,
Washe gari tunda asuba ta tashi tayi wanka ta shafa powder da kwalli tasa doguwar Riga armless shiga kitchen,
Mamakin tashinta dawuri haka yakama huda da deen amma suka share,

Yana zaune a office  dinsa Sega kiranta ya shigo dafe kansa yayi yace na shiga uku wannan yarinya metakeso ta maidani ne?, kindawaga yayi harseda taimasa miss call hudu Ana biyar ne yadaga amma cikin sanyin murya ta gaidashi tace ya aiki ya amsa lafiya lau,

Dagaske take magana wannan Karon, zainulabidin takira sunansa,
Seda ya gyara zamansa ya amsa, ma’am, wannan zalunci kayi kome?,
Bata rai yayi yace bangane ba sulaimi, mekike nufi?,
Cin amanata kayi kasan yaa huda yayata ce kuma kaje ka aureta,

To laifin wa?,kinga mubar zancen niyazama tarihi awurina?,
Nikuma be zama ba haba deen yazakayimin haka kasan kuwa yadda nakeji azuciyata?,
Soyayyarka tayimin mugun kamu irin Wanda zan iya rasa rayuwata akanka,

Asanina keba jahila bace, mekikeshirin yi haka sulaimi, kada kibari shedan yaribaci zuciyarki,
Kamar yadda kabari kai yaribaci taka zuciyar harkaci amanata ko?,
Nifa haushi kike bani idan kina cewa naci  amanar ki, kinmanta yadda mukayi?, to idan kin manta Nina banmanta ba, kisake tunani kiga acikinmu waye yaci amanar wani,

Nidai duk ba wannan ba abinda nakeso kawai kanema mana mafita,

Afusace yai magana, haba sulaimi idan ido ze bata yabata a tsakar ka mana, wannan wane irin dance kike idan hankali ya bata nemo shi ake bawai abi son zuciya ba kisani abinda kike shirin aikatawa babban kuskure ne kuma wata rana zakiyi Dana sani,

Bazan taba yin danasaniba saboda Akan gaskiyata nake kanemo mana mafita domin nasan kaima kanasona kamar yadda nakesonka,

Laimi ni banason ki bana kaunar yanxu a matsayin budurwa ta kokuma mata, inamiki sone irin na kanwar matata dan haka ki kyaleni da wannan zancen,

Deen wallahi karyane bazan yadda haka sona ba ayanzu,

Eh kece bazaki yadda ba a yanzu HUDA ITACE RAYUWATA inamata so irin Wanda baze fadu da harshe da fatar baki ba, huda bawai rabin jikina bace itace dukkanin jikina, itace jini da tsoka da ruwan jikina aduniya babu Wanda yataka mizanin data taka azuciyata, laimi kidaina wahalar dakanki akaina domin duk wani Abu dazakiyi bazesani naci amanar matata ba,

Jin zancen take kamar yana yayyanka naman jikinga zuciyarta kuwa kamar Ana wasan kwallon kafa acikinta saurarensa take hawaye masu zafi nazuba daga idonta ta tabbata daruwane sukayi zafin da zuciyarta tayi to za a iya Dama kunu dasu, runtse idonta dakyar tabude bakinta tace,

Nabaka lokaci kayi tunani bazan taba fasayin abinda nakesoba deen wannan muradi ne na zuciyata kuma inada muradi akansa ka tabbatar kayi tunani me kyau irin Wanda nakeyi domin mukasance cikin farin ciki da aminci a tsakanin mu,

Kashe wayar tayi ta shiga kuka, kuka mecin rai da zuciya, kukan dabatasan dalilinsa ba, kukanda batasan Akan me takeyinsaba sedai tanajin abin menauyine dazuciyarta bazata iya dauka ba haka ta zauna dakin har shabiyu na rana tashi tayi zata daura girki sanin huda nacan tana baccinta na fama, dan murmushi tayi tace, Allah yasaukeki lafiya yaa huda,

Bangaren deen kuwa hularsa yacire yana Kara jingina bayansa da kujera yadauki kafafuwamsa yadora kan table yaiwa kafafuwan daya kan daya yana girgizasu, innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Yarinyar nan ta dagula masa komai bemasan ta inda ze faraba, korarta zeyi daga gidansa? ,wata zuciyar tace matarka zataji haushi,kararta zankai gidansu? ,wata zuciyar tace zaka haddasa kiyayya tsakanin yan uwa masu cikeda kaunar juna, to ko lallabata zanyi tayi hakuri abubuwa da garaje basa tafiya daidai bazan kuma yimata zafi Akan maganar ba fatana Allah yabani  ikon dazan kauda wannan tunani daga zuciyarta kodan lafiyar matata abar kaunata dakuma babynmu,
Cigaba yai da aikinsa ganin yasamu mafita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button