HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

Haka sukaita barkwanci har yamma laimi tabaro gidan,

Bayan sati biyu deen yana zaune a office dinsa abin duniya ya isheshi kokari yake yagama da matsalar laimi amma abin ga citura, kiranta ne yashigo wayarsa dasauri yadaga,

Sweetheart lokaci yayi wane mafita kasamo mana?, tambayar datai masa kenan lokacin daya daga dan murmushi yayi yace,haba laimi kina sonane haka kike wahalar dani?,ina sonki bazan taba daina sonki ba ko awancen lokacin nafada miki sedai yanzu yakamata ace muyi hakuri saboda akwai katanga me karfi a tsakanin mu,kingane?,

Alhamdulillah abinda nakesonji kenan kanasona,nibana ganin akwai wani katanga a tsakanin mu kafahi…,

Kiyi tunani saubiyu mana laimi, yakatseta, keyakamata ki fahimce ni ko a addinan Daba musulunciba baki taba ji ko ganin namiji ya auri yan gida daya alokaci daya ba kuma uwa daya uba daya,

Nibabu ruwana da wannan kawai dai,

To shikenan zanyi tunani akai,
Yafada mata hakane saboda kansa yayi zafi yafi minti biyar ahaka kafin zuciyarsa ta raya masa abubuwa da dama.

My people karkuga kamar korafina yayi yawa banaso kuna yawan complain Akan page din yayi kadan sekunyi hakuri hannuna keciwo wollah. Tnx.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA

Story and written by SophieG

Inagodiya sosae da adduo’inku agareni wayanda suka turo saqo har wayanda sukakirani domin jin lafiyata da adduar samun sauki agareni nagode Allah yabar kauna ameen.
Wayanda basuda labari kuyimin uzuri na rashin jina kwana biyu banji dadi bane.

Page 8

Lokacinda suka isa gidan dayin sallamar su huda tai dinning inda taga su ummu nacin abinci Irish tagani da soyyyan kwai take yawunta suka tsinke gaidasu take tana debar nata a plate dukansu babu wanda yasamu bakin amsawa se kallonta suke cikeda mamaki,
Ledar dake hannunta tamiqawa laimi tana mata nuni da hanyar kitchen saboda abincin dake bakinta tama kasa magana,
Haushinta yakama laimi tace, waimeye haka?, mezanyi dawannan kibude bakinki kiyimin magana,

Tea dake gaban ummu ta janyo tadan kurba kafin tace, kiyi Sauri ki Dora mana yunwa nakeji, mamaki ya Kara kamasu laimi ta fizgi ledar tanacewa, ai shikadai kika iya zanso ganin wannan babyn me mahaukacin cin tsiya,

Dariya ummu tayi tace, abincin haidar kika cinye fa noor ,bata amsasu ba taci abincin ta seda taji tadawo daidai sannan ta kora da tea tamiqe kitchen tanufa can ta samu har laimi ta Dora tafasan naman,

Yawwa yar kanwata Allah yaimiki albarka yabaki miji nagari Wanda ze soki fiye da kansa,
Ameen laimi ta amsa tana murmushi,
Yawwa waike bakida saurayine naga keko irin wayarnan da yanmata keyi da samarinsu ke bakya yi, murmushi kawai laimi tayi tana kunna blender domin niqa attarugu dazata dafa indomie dashi,

Uhm?, dake fa nake magana huda tacewa laimi, sedai kafin tayi magana amai yazomata dasauri tai kofar baya awaje tsuguna duk seda ta harar da abinda taci,

Kema dai yaa huda bakida dangana daga zuwa kinga Abu kinkwasa kindurawa cikinki aigashi yanzu kina amai, itadai bata samu bakin magana ba haka tagama aaman tawanke bakinta laimi ta riqo ta takaita Palo,
Ummu tace meyasa Meta kuma?,amai tayi laimitace tana shigewa kitchen  sauke naman tai tadora mai yanayin zafi tafara suya seda ta kusa gamawa ta Dora indomie dinta,

Au wai bacci tayi?, laimi ta tambaya, eh wallahi Nima se juyowa nai naga ta bingire wannan ciki dai Allah yaraba lafiya, ameen laimi tace zata juya taji huda tace,

Laimi haryanxu baki gamaba yunwa nakeji sosae,
Nagama mana bari inkawo miki, zama taayi taci harseda taji cikinta yayo sama kafin tayi bacci agurin, suna zaune laimi da ummu na hira ummu tace wai kekam laimi bazaki fito da mijiba?,ummu waganni dazece yana sona babu inda nake zuwa,
To Allah yakawo nagari, ameen

Can darana Sega laimi tashirya tace zasu fita da meela tazo daukar ta ummu tace Allah yakiyaye,

Tunda naga deen naji ba dadi Ashe tare zasu fita tace meela,
Zuwa sukai wuraren shaqatawa sunata hiransu namasoya abin dai ba acewa komai se yamma suka dawo,

Ranar sedare yadawo ya daukesu bayan ummu tacewa laimi ta shirya wani satin tadawo ai huda tasamu sauki cikin yayi kwari,batasoba amma Dole tace to,

Tagama hada kayanta tsaf gobe zata wuce duk rayuwarta ajagule take zata bar habibinta abincin idanuwanta da xuciyarta, tana kwance adakinta segakiransa tana dagawa yace
Kisameni kasan bishiyar mangoro ta kofar baya,
Kit yakashe wayar miqewa tayi taje inda yafada mata cikin kujerun robar dake wurin tadauka daya tazauna ta facing dinsa,

Yanzu laimi tafiya zakiyi kibarni?, zanyi missing  dinki wallahi,
Nima wallahi zanyi missing  dinka se hakuri ai,
To yanzu yakike ganin zamuyi?, hakuri zamuyi sedai insha Allah duk weekend zanna zuwa nawuni se in koma gida kuma zaka iya zuwa muje yawo duk ranar dakake free,

Murmushin jin dadi yayi kafin suzauna sunata hiransu har magrib,

Bayan laimi ta koma gida huda na iya kokarinta wurin kula dagidanta dakuma mijinta soyayya suke dirza kamar ba gobe(nidai na daina binsu domin dauko rahoto kar Inga abinda yafi karfin idona) ,
Duk weekend kuwa laimi tana gidan kasancewar bata kyiuya yasa duk tazo zeta gyara gidan ko ina dan yanzu cikin huda yakai wata bakwai ba komai take iya yiba,

Yauma ranar asabar laimi tazo da yamma suna zaune inda suka saba zama suna hirarsu huda taji duk zaman Palon ya isheta bari tadan fito kozata iya zama suyi Hiran tare, kasa fita tayi zuciyarta nazafi tayi tsaye agurin kamar andasata,

Shiru tayi tana sauraren yadda suke zubawa juna kalaman soyayya,

Nifa wallahi laimi jinake kamar incewa ummu tabarki kidawo nan zanfijin sanyi azuciyata in naganki kusa dani,

Kai sweetheart yanxu duk kokarin danake ina zuwa duk asabar da lahadi?,

Huda jitayi batasan inda take ba kasa take ,sama take,aduniya ne kokuma ta na lahira ne, dan muntsilin kanta tayi ta rabbatar aduniya take dagudu takoma cikin gida dakinta tawuce direct takwanta kangado se kuka har aka kira sallar magrib tana kwance tana aikin kuka tama kasa tashi tayi sallah, haba wannan shaquwar tayi yawa ya Allah kasa iya kalaman soyayyar ne ya Allah kasa basu jefa kansu cikin halaka ba, wayyo Allah yar kanwata meyasa zakiyimin haka duk soyayar dake tsakanin mu kika zabi kici amanata, duk tarbiyar da iyayenmu suka bamu amma kika zabi ki kunyata su,nasan ma deen yagama da ita tunda sunsan babu aure atsakanin su watsewa kawai zasuyitayi, dakyar ta lallashi zuciyarta tayi sallah, bayan sallahr ishai laimi taimusu sallama tawuce bayan takammala girki,

Haka rayuwa tacigaba da gudana sedai gaba daya sun kasa gane kan huda tadaina rawar kai Akan deen tadaina zama inda yake duk da bata hanashi kanta sedai abubuwa da Dama sun sauyu awannan lokacin, tarage zuwa gidansu kamar yadda tarage sakewa laimi fuska laimi tayi complain  ummu tace wata kila cikinne kesata haka,
Dole sukayi hakuri,

Haba huda meyasa kikemin haka dan Allah kinsan yadda zuciyata take idan inaganinki haka wallahi son danakemiki yawuce misali kitausaya min mana,

Daurewaa tayi tace
Haba my deen nasanifa bbakomai kamin tausa jikina ciwo inasonayi bacci, dadi ya mamaye zuciyarsa,

Yau Friday meela tazo gidan su laimi,

Laimi abinda kikeyi jahiline kadai zeyi haka bakida abinda yafi dacewa dake dayafi aure amma kintsaya haukan luv da Wanda bakusan ma dalilin dayasa kukeyinsa ba duk wandayaji labarin wannan soyayyar taku tunani daya zezo masa zaman zina kukeyi banza kawai me kazamiyar zuciya,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button