HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

Kallonta kawai huda keyi hartakai karshen zancenta kafin ta Dora nata borin,

Eh naji ni jahilace idan abinda yakawoki kenan maza zoki fice kuma karki Kara zuwa inkinsan shizekawoki,

Mayafinta dajaka ta kwasa tace, zantafi kuma inajiran ranar tonuwar asirinku ranarda zata kwabe muku wallahi karki sake kinemeni, fuu tawuce ko yaa haido dake Palo bata kalla ba damamaki yakebinta da kallo,

Yasan halinsu yanxunnan zasuyi fada anjima sushirya danhaka baze Shiga tsakaniba su suka sani sedai yana mamakin yadda meela tawuceshi haka,

Washe gari Saturday  laimi tazo duk abinda tasaba seda tayi, tun bayan magrib ta dami deen yakaita gida kasancewar da motarta yaa haido yafita tashi tana gurin gyara se ya ajiyeta shikuma yafita, huda tadan sake yanxu cikinta wata takwas tacezata bisu basu musaba sedadi laimi keji ganin yayarta tadan sake.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA

Story and written by sophieG

 

Page 9

Amota se surutu suke ma huda amma takasa biyemusu zafi takeji azuciyarta kullum zuciyarta da kuna take wuni take kwana duk ranar da laimi tazo setaji yadda suke zubawa juna kalamai sedai tazauna tayita kuka yau takuduri kawo karshen wannan kazantar wannan Abu tasani baze taba yimusu dadiba sedai bazata rufe Ido asamu tangarda ba,

Wani dadi taji lokacin data samu iyayen deen agidan harkasa ta durqusa dukda nauyin cikinta ta gaishesu, mamansa hajiya Laura tace yi maza ki gyara zamanki noor wannan ai se ki takura babyn kuma kafafuwanki zasuyi ciwo, murmushi tadanyi kafin tagyara zamanta aka Shiga gaisawa dukansu se faraa suke Ana dan taba hira Sega ya haido yafito shima suka gaisheshi yagaisheda su maman deen anan dai aka dan taba hira har su hajiya Laura sukace zasu wuce dama daga wani guri suke shine sukace zasu biyo agaisa kuma balba nacan najiransu gidan yayarta hajjagana acan tawuni zasu daukota,

A’a umma bazaku tafi ba magana nake tafe da ita kuma ta shafe ku, inji huda,

To sukace suna gyara zama, laimi setayi dubin ita karama ce watakila sabani huda tasamu damijinta danhaka seta miqe zata fita,

Kidawo kizauna laimi nafi bukatar kasancewar agurinnan fiye da kowa dake nan ganin ki zekaramin karfin gwiwa yadda bazan rage ko kalma daya acikin maganganunaba,

Deen yagama shan jinin jikinsa duka da besan akanme zatayi maganan ba, asanyaye laimi ta dawo tazauna,

Seda huda ta kalli ummu tace,ummu Ashe haka auren yeka baki fadamin ba?, tajuya gun Abu, Ashe Abbu irin haihuwar da kukayi kenan?, kallon iyayen deen tayi tace, umma da abba kuntabbata danku yanada ilimin addini?, sekuma takalli yaa haido tace tana zubar da hawaye, yaa haido Ashe dan uwankama ze iya cin amanar ka?, duk bana bukatar amsoshin ayanzu ku saurareni kuji abinda yayanku suka aikata,

Dan matsawa baya tayi tajingina da kujera, duka wurin kallonta suke kansu yakulle,laimi tatashi dasauri zata gudu ita niyyarta tashige daki dantasan yau duka zatasha tagano inda huda ta dosa, wallahi laimi inbaki dawo kinzaunaba sena nunamiki ni yayarki ce kuma girman cikinnan baze hanani karairayaki ba, juyowa tai dafuskar kuka tana hada hannayenta biyu tamarairaicewa huda,

Nayi mamakin shaquwar sulaimi da zainul’abideen bayan dawowarta daga Sudan, sedai nasan dukansu mutanene masu son wasa kila wannan dalilin yasa suka shaqu,sedai abubuwa danaji nakuma gani sun girgizani tana kuka taci gaba,ummu ashe laimi da deen soyayya suke,ummu lokacin datake gidana badon Allah take zamacan ba bakuma danni ba ummu kullum sesun fita idannace zanbisu sesuce cikina menene wahala zanyi,ummu babu ruwan deen dawayar sa amma yanzu babu wani app dake cikin wayarsa dabashida password,kuma kokadan baya barin wayar kusa dani,ummu inajin tsoro,

Babu wanda yakeda bakin magana dukansu sun sandare laimi kuwa takasa tantance wane yanayi take ciki,shin kunyace,storo ne,kokuma nadama ce,

Meela tazo kawowa ummu sako daga wurin momynta tariski wannan zancen kawai seta sulale awurin babu wanda yasan dazuwanta kuka take sosae dama wannan ranar take gujewa sulaimi ashe tana kusa,

Huda kuka take kamar ranta zefita tace ummu ku tambayi yayanku ko wani abu nashiga tsakaninsu?munajin labarin abubuwa makamanta irin wannan hankalina yatashi domin soyayyar su batada alkibla seta zina,ummu Allah yasa kanwata bata zubar da darajarta ba inajin tsoro wallahi inajin tsoro,

Zuciyar ummu tagama rufewa batasan lokacinda tadamqo wuyan laimai ba, Maruka gudabiyu masu kyau ta zuba mata cikin kakkausar murya tace, fadamin zaman me kukeyi?, shiru babu amsa, wani Marin takuma kifa mata, kifadamin nace inbahaka ba wallahi sena kusa kasheki,kanta na kasa takasa magana jitake kamar zuciyarta zata fito dazaran ta bude bakinta, purse dinta dake gefe tajanyo kamar ta karfe haka take marinta tayi da purse din take hancinta ya bare da jini, awurin babu Wanda yai kokarin hana ummu, deen ma kansa akasa seyanxu abubuwa keta dawo masa innalillahi wa’inna ilaihirraji’un haka yaketa maimaitawa,

Kara tasake tana kokarin kwace kanta amma takasa kuka tasaki mecin zuciya,
Ummu wallahi babu abinda yataba shiga tsakaninmu, wallahi bantaba kokusanto kaina da zina ba, ummu dan Allah ku yarda da…. Tass tass saukan wasu Marin a fuskarta, karya kike kifadamin gaskiya, meye ma’anar soyayya da mijin yayarki?, ummu wallahi bamu tabayin zina ba, karya kike, cikin daga murya tace,
Ummu yaya deen saurayina ne tun Ada can baya,
Turata ummu tayi harseda tafadi kwance awurin, cikin kuka tasoma basu labari,

TUSHEN LABARIN

Yan matane su biyu dabazasu wuce shekaru sha uku ba sedai na lura kamar daya ta girmi daya, agaban babansu suke yace kowa tazabi makarantar datakeso ze canza musu,
Huda tace, Abbu nidai bordin skul nakeso, laimi tace nkuma day nakeso idan zanyi jami’a Abbu kakaini wata kasar,

Murmushi yayi yace to shikenan zamu fara process,
Tashi sukayi sunata Murna,
Bayan sati biyu aka kai kowaccensu makarantar datazaba sedai huda makarantar kwana FGC dake garin aka nema mata itakuma huda success skul aka kaita,

Lokaci na tafiya na lura akwai shaquwa da soyayya tsakanin huda da laimi kuma akwai girmama mawa, tsakanin huda da laimi babu shekara wata goma ne atsakaninsu dan haka atare suka taso komansu iri daya dakadan huda tafi laimi tsayi sedai laimi tafita haske, idan kagansu zaka zata twins ne,

Lokacin da suke ss3 lokacin aka kawo copers to anan ta hadu da deen yanuna yanasonta mutumne shi mecikar kamala bashida Matsala kokadan becika hayaniyaba sedai yakan yi wasa aduk lokacinda yake cikin nishadi, laimi tadan sake mai daga farko sedai zugar parrot tayi tasiri akanta,

Mezakiyi da teacher rayuwarku atalauci zata kare motar dakike ganinsa da ita ai babansane yasiyamai kuma kace kai alhajine yafi akan kace kai dan alhaji ne, wallahi karki biyemai kicimai mutunci yakyaleki, meela tayi kokarin fahimtar da ita lokacin dasuke class subiyu,
Ni meela bawai banasonsa bane kawai dai banason auren teacher kumakeni karatu zanyi ba aureba ammafa wallahi inason uncle deen sedai yanxu zantaka masa birki, duk zancen dasukeyi yanajinsu danhaka yakuduri baze kuma kulata ba tundaga ranar komagana baya mata har sukayi exam suka bar skul din,
Bayan sundawo aka nema musu karatu a Sudan itada meela suka tafi itakuma huda tasamu addmision a UDUS danhaka sukayi karatunsu semester dinsu ba atare yake tafiyaba danhaka huda tarigata kammalawa tazo Hutu takoma anan ne huda ta hadu da deen har akai bikinsu laimi bata dawoba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button