HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

Da spoon tajuya mata takawo mata, malama hannu zakisaka kulin yafi shiga ciki,
Wanko hannunta tayi ta juya mata shi, yadda kulin da zogalen suka kama hannun laimi yasa huda riqo hannun kai bakinta dasauri laimi ta janye tace wai menene haka?, hannun zan sude, haka kawai zaki sudemin hannu wannan cikin naki yasa komai sekiyi yadda kikaga Dama kikaiwa mijinki yajuya da hannunsa seya baki ki sude mai,
Nidai kibani naki dan Allah, miqa mata hannun tayi tana mitar kinzama rigimammiya wallahi,
Sude hannun tayi kafin taci kwadonta,
Duk abin take so shi laimi ke mata,

Yau tunda sassafe suka tashi da shirin zuwa gida, kaza tadauko wai dashi taza karya insunje laimi ta soya mata, girgiza kai kawai laimi tayi tace Allah yasaukeki lafiya babu abinda kika iya seci.

Team laimi kuzo nashiryamana party zamu ragargaje mu ashhake, lol.
Luv u oll.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA…page 10…. By sophieG.

 

Deen duk amuzance yake jin kansa yakasa zama acikin gida hakan yasashi fita kawai yaje gun gateman din gidan yazauna tunani yake ta ina ze soma yiwa huda bayani kuma ga iyayensa sunyi fushi dashi, ahaka yaraba dare har kusan 11:30 yana gurin kafin yatashi yashiga gida bayan yagama cewa aransa zebawa huda gym tadan sauko daga fuahin datakeyi,

Abangaren huda kuwa kwanciya kawai tayi tashiga tunanin halin rayuwa, yanzu ace mijinta ne yake soyayya dakanwarta to mesuke nufi dama dan uwanka ze iya cin amanar ka har haka, dukda haka tagodewa Allah datayi saurin ganowa domin namije mugun ice ne amma tayi alqawarin seyagane kuskurensa,

Wanka tayi tayi kwanciyarta adakinta batareda tanemi deen dinba,
Koda yashiga dakinsa begantaba yasan bazatazo ba kuma bega laifintaba haka shima yai kwnciyarsa sedai dakyar yayi bacci setunanin ta yake,

Washe gari se karfe8 yatashi yayi wannka yasa manyan kaya yafito se kamshi yake, a Palo yasameta tana kallo amma kojuyowa batayi ta kalleshi ba nan yazauna yafi minti talatin agurin amma batayimasa magana ba, hakan yasashi tashi yafita se gidansh yaje yasamu iyayenshi babu Wanda yasake mai fuska,

Gaishesu yayi suka amsa adaqile kafin abbansa yashiga surfamai masifa,

Ashe bakada hankali?, idan har zaka iya soyayya da sulaimi bayan kana auren yayarta to zaka iya soyayya da balbasatu, wannan wace irin kazamtacciyar rayuwace?,

Ummansa dai batayi maganaba secan tace, kafada mana tsakanjnka da Allah babu abinda yashiga tsakaninka da yarinyarnan,karfa muzo muyi shiru abin kunya ya tabbata,
Kansa akasa yace wallahi umma babu komai babu abinda nayiwa yar mutane kodanake saurayi banyi zinaba balle yanzu danakeda aurena,

Murmushi tayi tace to Alhmdllh,nan yashiga basu hakuri wallahi Sharrin shedan ne sugafarta mai kuma sutayashi bawa huda da iyayenta hakuri,

Babu ruwanmu tsakaninka da matarka sekasan yadda zakayi kabata hakuri ta sauko, shiru yayi kafin yece to umma ataimakeni abani balba har Allah yasauki huda lafiya seta dawo,
Shiru umma tayi tace kaje zamuyi tunani,

Haka ya dawo gida jikinsa babu kwari anan kofar gidan yaita zama har yamma seda akayi laasar yashiga gidan leqawa yayi dakinta yaji alamar kamar tana wanka abayi danhaka yafito yanufi dakinsa tunda yashiga befitoba sedazashi masallaci salar magrib har ishai yai acan kafin yadawo gidan kwata kwata bayajin yunwa danhaka benemi abincin bama, yaizamansa adaki yana kallo badan yana fahimta ba, sekusan shabiyu yace bari yaje yadubo huda,
Akwance yasameta amma batayi bacciba, samunkansa yayi da hawa gadon shima yakwanta yana janyota jikinsa, dan matsawa tayi tana raba jikinta danasa sake janyota yayi yana tambayarta murya ahankali,

Meya hanaki bacci?, shiru tamasa yace kinajina fa?, nanma batayi maganaba, kitaimakeni kiyimin magana shirunki ze iya zama illa agareni nayarda nayi laifi duk abinda kikaga Dama kiyimin danki huce amma bada nesanta kanki dani, wallahi huda inamiki sondabana yiwa kaina Sharri shedan ne kawai don Allah kiyi hakuri, dasauri tadago tana kallonsa jin saukar hawayensa abayanta,

Tausayinsa taji, mijinta bajarumi bane watarana mace seta fishi juriya komai nasa a sanyaye yake, dan turo baki tayi tace, to meye nayimin kuka ninace banyafe maka bane?, nidai gaskiya kadainamin irin haka sekace banamijiba Abu kadan se hawaye?,

Kara qanqameta yayi, tace naji yawuce amma yanadakyau duk abinda zamuyi mucire sonzuciya mukawo tsoron Allah agabanmu, yanzu da rudin shedan yajaku aikata zinafa?, kuceme?,
Inason kanwata da ace kaganta kafin aurenmu dazan iya barmata kai ta aura saboda ita idan zatayi Abu gaba gadi takeyinsa bata tunani saubiyu raguwace ta gaske nasan yanzu tanacan tanajinyar jiki dan wallahi yaa haido baze kyaletaba,

Godiya yashiga zuba mata daga karshe yace meya hanaki bacci,
Ashagwabe tanunamai cikinta tace, babynkane daga nakwant shikenan seya ringa kicking,
Dan kashe mata Ido yayi yace yayi missing babansa ne bari Inga lafiyarsa Anan yashigayin yan abubuwa tonidai bantsaya ganiba nafice a jaka,

Sulaimi duniya tayi zafi, tana kwance duk jikinta ciwo yake, tunani take, anrabata da saurayinta andaketa kuma an hanata fita?, da wanne zataji?, kuma kowa na fushi da ita Allah yagani bazata taba daina son deen ba sonsa ajininta yake kuma kota halin qaqa seta mallakeshi yama za ayi ayimata irin wannan rashin adalcin,Dama antambayeta ne tayarda tabarwa yayarta tunda ita yafara so?, amma sema akafitomata ta hanya me tsauri danhaka Dole ta dau mataki,

Miqewa tayi daga kwancen datake tana duba jikinta inda aka faffasa mata, fuskar kuka tayi tace Allah ya is…. Shiru bata karasaba jin yadda mararta ta murda Dama wata uku kenan Rabon datayi al’adada, yarfe hannu tashiga Yi tace afili,
Wayyo nashiga uku shikenan tawa takare mutuwa zanyi babu Wanda zekuladani yau.

 

Forward ever backward never,
Never give up laimi muna bayanki se inda karfinmu yakare,

Team laimi kuyi hakuri da wannan dan yau naje unguwane kuma se magrib dinnan nadawo nagaji kuyi manage zuwa jibi zaku jini da yardar Allah kuma don Allah duk wanda nabatawa yagafarceni idan nataba masa laifi nagode.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA… Page 11…by SophieG.

Dakyar huda ta iya tashi da safe duk jikinta ciwo yake ga bacci a’idonta tagaji sosae kuma ga nauyin ciki,hakanan dai ta tashi tun asuba wanka tafarayi tayi sallah kafin tashiga kitchen Irish da kwai tasoya tadafa ruwan shayi takawo dinning, dan kokari tayi tasa brush daga tsaye ta share inda zata iya, 7:30 tagama shikuma lokacin yafito yagama shirinsa tsaf,janta yayi sukaci abinci yanata Sauri kafin yagama memakon yafita setaga yashiga dakinta, hijab yadauko mata da wayarta,

Deen ina zamu?,
Gidan umma zan kaiki bazaki iyayin girkiba kuma gaki kekadai,
Tab… Bazaniba Allah ni kunya nakeji,
Kallonta yadanyi da mamaki kafin yace, kinajin kunyarta kikayi wannan?, yafada yana nuna cikinta,
Kunya ta kamata dasauri ta cire idonta daga nasa, hannunta yaja suka fita bayan sun rufe gidan,

Be shiga ba ya ajiyeta daga waje takarasa ciki,
Da mama ki umma ke kallonta tana gaisheta,
Lafiyalau noor tashi dai ki zauna banason wannan durquson kinga kinyi nauyi yanzu, murmushi kawai huda tayi,
Meyafaru kikazo da sassafennan, babu komai umma shine yace zekawoni nan can gidan ba kowa,
Allah sarki to sannu, kinsamu balba batanan yau taje karbar notification sukam seyanzu Allah yayi,
Allah yataimaka nasan bajimawa zatayi ba tazo muyi hira,
Murmushi umma tayi kafin tace,
Huda me deen yaimiki naga idonki yakumbura kuma yayi ja karkiji tsoro ko kunyar fadamin,
Wallahi umma bakomai bacci kawai nakeji saboda jiya bansamu nayi bacci sosae ba,
Deen dinne yahanki bacci da takurarsa ko,
A’a umma kawai banajin dadine senakasa baccin,
Aiho to zoki kwanta Allah yaimuku albarka yasaukeki lafiya, ameen ta amsa tana cire hijab din jikinta,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button