HAUSA NOVELZare Da Abawa

Zare Da Abawa

Laimi har karfe biyun dare takasa bacci saboda zulumi amma kamar daukewar ruwa abin bezo ba dakyar bacci yadauketa washe garima tatashi bawani ciwo feldine tadauko Tasha tana cewa gwanda na Kara danne shi Akan yazomin yanzu bawanda ze kuladani gidannan,

Leqowa tayi tana kallon ko ina a Palon taga bakowa dasauri tafito tadauki wayarta a Palo harzata wuce taga yaa haido na shiqowa da akwatuna masu matukar kyau dagani kayane aciki ganin yadda yasa karfinsa yana jansu, shagala tayi da kallonsa sejitai yace,
Ke dan ubanki banhanaki fitowa daga dakinnan ba kika bari nakaraso wurin sekin gwammace kida da Kara…, wuf yaga tabace sekarar rufo kofa yaji dariya yayi yace se shegen tsoro,

Tana Shiga dakin tarufo kofar harda murza key, zama tai tashiga kiran deen, yana zaune office dinsa kiranta yashigo, gabansa ne yai mugun faduwa yakasa dagawa setunani yake har wayan ta tsinke, wata zuciyar tace Dama ka dauka kila hakuri zaka bata tagane kuskurenta yana cikin wannan tunanin Sega kiranta Yakuma shigowa,

Dagawa yayi gabansa na tsananta bugawa,

Haba baby kardai kacemin dan wannan abin dayafaru haryasa zuciyarka ta karaya, to wallahi baka cika namiji ba kasharesu danni kokasheni zasuyi bazan taba daina sanka ba,

Shiru yayi yana kallon wayar yama kasa cewa komai besan dawane suna zekira laimi ba kashe wayar yayi kawai ya aijiyeta kansa yadau zafi haka yajibge aikin gabansa.

Zaheeda
Pretty meena
Zara bint wannan shafin nakune kukadai.

Kuyi hakuri da wannan kaina ke ciwo har cikin idona wallahi thank you.
[12/24, 10:54 PM] SophieG❤: ZARE DA ABAWA… Page 12…by SophieG.

Tab…wai me deen yake nufi wallahi yayi kadan Dole nema yadaga wayarnan muyi magana,kiransa takumayi amma ko kallon wayar beyiba sekarar shigowar massage yaji bebi takaiba yai ayyukan dayake ganin su zasu fishsheshi,se kusan 5:00 yakama hanyar zuwa gidansu,

Azaune yasami huda balba na mata kalaba,zama yai kusa dasu yanajan kalaban guda daya da murmushi afuskarsa yace, wannan kitson beyi kyauba gasu manyamanya,

Huda ta tabe baki tace, aidai ba akanka yakeba bakasan yanakejiba wannan zaman danayi na qagu tagama min nakai kwance,

Allah yabaki hakuri guzuma, kutaimakeni yunwa nakeji tunda nakarya rabona da abinci,

Balba tace gashican kitchen zakaganshi a kula pink,

Sedare suka koma gida bayan umma tahadasu da abinci,

Yana Palo zaune yake duba massage dinda laimi taturo masa,

Kasani kabani kunya, ashe kai ragon namijine haryaushe dan wannan abin zakabari ya tsorata ka?,wallahi kadawo hayyacinka yazakabari arabaka da zuciyarka?,in kuma lkace karabu dani to kasani sena kullama tuggun da bazaka iya warwareshi ba,

Dafarko gabansa yafadi amma dayatuna akwai Allah se hankalinsa yakwanta, badan karya dasa kiyayya a tsakanin yan uwaba daya nunawa yayarta amma dai ajuri zuwa Rafi…,

Haka kullum laimi ke damunsa da kira dakuma massages amma betaba kulataba haka nan tana zaune adaki bata fita ko’ina yaa haido ya hana, yayinda ummu da Abby ke fushi da ita basa kulata kokadan amma dayake rudin shedan yaimata yawa bata damuba, Ana haka taga anata shirye shiryen biki agidansu amma batasan kobikin waye bane kuma babu fuskar tambaya,

Sati biyu kenan da faruwar abin meela ta kirata a waya,
Yar iska kingama fushin?, laimi tace tana dariya,
Bangama ba,
Kifito waje ganinan Sauri nake kikarbi ankonki,
Da mamaki laimi tace ankon bikin wa?,
Bikina mana kiyi sauri jirana ake,
Fitowa tayi takarba basuyi wata hiraba meela ta Kara gaba,

Dakin ummu tashiga kanta akasa tanuna mata kayan kafin tace Ashe meela aurenta za ayi shine bansaniba,
Batareda ummu takalletaba tace, waye to ze kira mahaukaci a al’amuransa tunda hauka kikeji aidole tanisanceki karkizo ki kwace mata miji,

Maganar tasosa zuciyarta amma seta tuna da soyayyar da mahaifiyarta kemata yanzu gashi baruwanta da ita,
Take zuciyarta takarye tomeyake damunta haka, lallai ta haukace tunda takeson mijin yayarta, lallai Dole duk masu miji sugujeta tunda ta iya soyayya damijin yayarta,
Rungume ummu tayi tana kuka tace ummu nahaukace kuyimin addu’a ummu kugafarceni dan Allah wallahi nadaina bazan kuma son mijin yaa huda ba,
Itama ummu rungumeta tayi tana bubbuga bayanta to shikenan ya isa daina kuka kinji tashi Allah yaimiki albarka, kishirya kikoma gidansu meelan harse angama bikin,

Massage din laimi nayau dasafe yafirgitashi tace wai zataje wani yaimata ciki wallahi tace shine danhaka yatashi yasami yaa haido har office dinsa yafadamai Yakuma nunamai massages dinta tun nafarko,
Batareda yayi maganaba yadauki wayar yafice daga office din deen nata magana yana cewa katsaya ai abi komai a hankali, amma kosaurarensa bayayi yaja motar segida deen nabinsa abaya Abby yasamu yadawo a Palo ya dannawa laimi kira dasauri tafito yace tazo har kasa ta durkusa a agabansa, miqawa Abby wayar yayi yace wayan deen ce kaga sakon da laimi keturamai wannan shine nayau da safe, abbu inabaka shawara ka aurar dayarinyar nan inabahakaba seta kasheku da bakinciki,

Riqo kafarsu tayi danjin xancen aure tafirgita, wallahi abbu nadaina kutausaya karku aurar dani,

Mari ya haido ya kwadamata yace kinyi kadan wallahi ba ahaifekiba, shiru sukayi jin abbu nawaya yana cewa,

Eh alhaji Ibrahim kacewa mahaifin isma’il afara shirye shirye kawai inyaso se a hada Dana haidar kawai ranar Saturday din,
Yana gama fadar haka yakama gabansa,
Ya haido yace wallahi abbu yamin daidai shegiya mekamada yan Ethiopia naga karshen iskanci yau,
Magiya tashigayi tana riqo kafarsa don Allah kataimakenj zankawo Wanda nakeso wallahi,

Deen dake tsaye yadafe kansa domin be so hakaba yaso abi ahankaline, haidar ma fitayai yabarta awurin dasauri takarasa wurin deen tace, kataimakeni kayafemin don Allah kace karsumjn wannan auren wallahi banaso,

Wayarsa kadai yadauka Akan kujera yafita, ummu dake tsaye jikinta a sanyaye takoma daki saboda azahirin gaskiya bataso hakaba sedai babu yadda zatayi Allah yasa shiyafi zama alkhairi,

Kuka tayi awurin seda ummu tazo tadagata suka Shiga dakin ummun,

Ummu nabonu na lalace auren Dole zaamin,
Kiyi shiru baki bonu ba kinji kiyi hakuri zoki kwanta karkanki yayi ciwo,
Kwanciya tayi tana sauke ajiyar zuciya har dare yayi ko abinci takici,

Suna kwance tacewa ummu ita mararta tafara ciwo, Lipton ummu tabata tace Allah ya sawwaqe,
Tun abubuwa basukai ko inaba tafara juyi tana kuka dassuri ummu taje dakin abbu tace laimi fa ba lafiya ciwon Mara yazomata,
Allah ya sawwaqe kadai yace yacigaba da karatun jaridarsa,abbu kasan fa yadda takeyi harda suma,
To ta mutu mana baruwana ai takusa aure dama shitakeso,

Ganin ransa abace yake yasata fita takoma gun laimi, kwance tasameta ta banqare duk jikinta yabaci da zanin gadon, wayarta tadauka takira haidar tace yazo da allura laimi batada lafiya, to kawai yace takashe wayar,

Kasancewar beyi nisa da gidaba yasa shizuwa dawuri, daga bakin kofa yatsaya yace, to ummu ta gyara jikinta mana bazan iya tabata da wannan kazantar ba,

Banason haka aliyu zakamata ne kokuma nakaita chemist, ummu meyai zafi haka zanmata, hannunsa yasa yakifeta dan kamarma ta suma ko motsi batasonyi yadda ta banqare baya yasa jinin Shiga rigarta tabaya, cikeda kyankyami ya zuge zip din skirt dinta yai mata alluran, yace kitasheta taiwanka daruwan zafi dan bada dadewaba zatayi bacci alluran harda nabacci,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button