NOVELSUncategorized

NAJEEB 22

Hauwa ta kalli Aisha tace nifa kin San ba iya wannan lesbians din nayi ba, kar inje in kwafsa 

Aisha tace tsaya in baki ki kalla, “d’auko wayarta tayi ta kunna Mata video tare da bata, “baka jin k’aran komai saina nishi sama sama tare da shhhhh sai kuma dariya 


Jin k’aran yana ma ibtisam wani iri yasa ta tashi da sauri tabar d’akin, “ganin haka itama Zarah ta mi’ke ta bita waje. 

Ganin Sun fita hauwa tace karmu lalata y’ay’an mutane fah. 

Aisha tace ai irinsu haka suke, farkon zuwansu waje suyi ta Abu kaman na Allah, Bari kiga nan gaba, zaki sha mamakin su, Idan suka saki jiki, yanzu duk na munafunci ne, kowa da kike gani dan iskan kanshi ne, sai dai na wani yafi na wani, sannan mu namu ne ya fito, akan masuyi a boye fah, ai gwara mu 

Hauwa tace kai gwara masuyi a boye fah, “Allah zai iya shiryar dasu, muma muna fatan shiriya 

Dariya suka saki, “hauwa taci gaba da kallon video din Tana fad’in Kai Wlh wannan Abun ko wahala, gaba d’aya baya burgeni 

Aisha tace Kedai kawai kiyi dan kud’i malama 

Hauwa tace amma wannan mutumin da zaki had’amu ko d’an iska, ace shi so yake yaita kallo…. 

Kofar da aka bud’e ne yasa suka d’aga Kai, wata yarinya ce ta shigo cikin d’akin tasha riga da wando gaba d’aya dressing d’inta y’ar musulmai bazata iyayi ba, amma abun mamaki sai naji suna kiranta da Zainab Zee,. 

Hauwa tace shegiya zee, Dama tare zamu? 

Aisha tace eh tare zaku,.

Zee kai hannunta tayi kan nonon Hauwa Tana fad’in Bari in fara tabawa tun daka nan. 

Hauwa tace Wlh ke y’ar iska ce, nifa ban wani iyaba sai yasa nake kallon video 

Zee tace toh Abu Mai sauk’i, Bari muyi a nan, Kafin muje can. 

Aisha tace a ina? Kunga ku tashi ku tafi tun Kafin ya kirani,kuje can kuyi a gabansa 

Tashi sukayi suka fita su Duka harda Aisha data rakasu 

Bayan ibtisam ta fita gaba d’aya gefen hostel d’in ta Bari, inda ta zauna akan wani bishiya, “lallai rayuwar jami’a Abun tsoro ne, dole kabir yaita mata kashedi sai yanzu take Lura da abunda yasa yake mata kashedi har take mamaki take ganin ya canza ba kaman daba, Ashe da gaskiyan shi. 

Gaba d’aya ibtisam taji bata son zama dasu hauwa da Aisha cikin d’aki d’aya, ajiyan zuciya ta sauke tare da fad’in lallai yanzu wannan abunda muke gani wai sunan muna cikin hostel ne, “in muka fita waje kuma fah? Tab gwara nan dinma zaifi gaskiya

Tana nan zaune wayarta tayi k’ara d’auka tayi taga ummi ce, “sawa tayi a kunne tare da fad’in Ummi Ina wuni 

Ummi ta amsa da lafiya kalau ibtisam ya karatu? 

Tace Alhmdlh Ummi, “Ina Granny da Abba?

Ummi tace Abbanki yana kasuwa, “Granny kuma gaba d’aya ta addabi mutane akan kin tafi karatu, “kullum mita daka an zauna taita fad’a an Turaki karatu. 

Ibtisam tayi dariya tare da fad’in kai Granny ko rigima, “Tana kusa ne ki bata wayar mu gaisa? 

Ummi tace bari inkai mata wayar “koda ummi ta shiga d’akin Granny bacci taga tanayi, dan haka ummi tace ma ibtisam tana bacci sai dai inta tashi sa gaisa din

Ibtisam tace toh ummi, tare da fad’in Ummi dama ina son inyi miki magana 

Ummi tace name? Ina jinki 

Ibtisam tace ummi yanzu Ina matukar bukatar babban waya, saboda duba internet in an bamu assignments in duba a ciki, “ummi tace hakane zanyi ma Abbanki magana. 

Ibtisam tace ummi Kabir yace zai kawo min waya, shine nace mishi a’a amma ya dage Wai sai Yaban, harya nuna rashin jin dad’inshi akan nace a’a. 

Ummi tace karki damu bari abbanki ya dawo, zan Mai magana, “sannan shi KABIR in banda abunshi ina shi ina k’ara siyan miki wata waya, mutumin da yake hidiman aure ga gini, wanda ya baki ai Tana nan, zanyi magana da Abbanki in yaso saiya baki wannan, amma bai kamata yasai miki wata ba 

Ibtisam tace toh ummi, saina jiki

Ummi tace toh, tare da fad’in ina zarah? 

Ibtisam tace Tana d’aki, ni na fito waje insha iska ne 

Ummi tace ok sai anjima tare da kashe wayan 

Zarah ce ta k’araso inda take tare da fad’in Ashe nan kika zo, kika makale, inata nemanki 

Ibtisam tace eh nan nazo.

Zarah zama tayi kusa da ibtisam tare da fad’in kai Wlh yau garin babu dad’i wani iri nake ji 

Ibtisam tace ko baki da lafiya ne? 

Zarah tace lafiya na kalau, kawai dai ina jin kaina wani iri ne yau, “gashi inada lecture 4

Ibtisam tace Kinga Muma muna dashi 3 ga time ya kusa 

Ibtisam tace Zarah wlh ni yanzu tsoran su Aisha nakeji 

Dariya Zarah tayi tare da fad’in tsoran Me kuma? 

Ibtisam tace naga iskancinsu yayi yawa, nifa a duniya Ina tsoran abunda zai taba mun budurcina na, burina in kaishi gidan miji, saboda in samu y’anci da kuma girmama wa a wajan miji,”amma su Kinga har fad’a suke suna bin maza ga bin mata Kai Abun nasu yayi yawa, sai yanzu nake gane abunda Granny ke fad’i ashe gaskiya ne “tace anama matan jami’a kallon y’an iska 

Zarah tace Hmmm Abun dai sai a hankali, sai dai muce Allah ya shirya, amma abunsu Hauwa sai addu’a ,”su gaba d’aya basa jin kunyan fad’a wajan kowa cewa suna iskanci, wlh duk alaman karshen duniya ne, an maida zina kaman ado 

Ibtisam tace hakane wlh, alaman karshen duniya ne, dama ance zaka ga mutum na zina akan titi, toh gashi nan muna gani, wanda sai yanzu na Lura da abunda ake nufi da akace za’a ga mutane suna zina akan titi Mai imani ne zaice su matsa gefe, kin San yanda na Lura? 

Zarah tace a’a 

Ibtisam tace bawai ganin mutum zakayi akan titi a kwance suna cin junansu ba, a’a, irin abubuwan da ake nufi shine, zaki ga mace tayi zina bata jin kunyan fad’a tayi, sannan kiga mata a jere a titi suna jiran abokanan shashancin su, dan suyi zina dasu, toh kinga wannan shine ake cewa zaki ga mutane na zina akan titi, wlh duniya ta gama lalacewa, “Allah dai kawai yasa mu dace, ya tsare mana imaninmu 

Zarah ta amsa da Allahumma Ameen, “tare da fad’in duniya kenan, kai Allah ya kyauta. 

Ibtisam tashi tayi tana fad’in bari kiga inje in shirya time ya kusa,na shiga lecture 

Zarah tace nima bari inje in shirya domin 4 za muyi saimu fita gaba d’aya 

Tashi sukayi suka nufi d’akin, babu kowa a ciki suka shiga suka shirya, ibtisam wata doguwar riga tasa sannan ta yafa wani Gyale medium a saman kanta, duk da babu makeup a fuskanta tayi kyau Sosai, “ita kam Zarah jallabiya tasa suka fita Bayan Zarah ta d’aukesu a hoto 

Rufe kofar d’akin sukayi da key tunda dukansu Suna da key 

Kai tsaye inda su ibtisam za suyi lecture suka nufa, inda suka iske salis a ciki 

Ibtisam tace salis kai kullum saika riga kowa zuwa? 

Yace Wlh gwara in riga kowa, kin San Dr jibril baya wasa fah, yanzu sai ya fadar da mutum 

Ibtisam dariya tayi tare da fad’in Allah ya kyauta 

Salis Ya amsa da Ameen “tare da kallon Zarah yace Kai ibtisam amma wannan sister d’inki ce koh? 

Ibtisam tace eh 

Yace haba kaman tayi yawa wlh 

Zarah tace amma na fita kyau koh? 

Salis yace kai Anya kuwa? Gaskiya bazan iya zaba ba, dan dukanku ba baya ba 

Duka dariya sukayi, suna cikin fira mutane nata shigowa domin baifi 10mnt su Fara lecture ba 

Time na cika dai dai saiga Dr jibril ya shigo ciki, yana shigowa saiga Aisha, tsayawa tayi tana kallonshi domin tasan bazai barta ba.

Baiko kulata ba balle ya Mata magana, ganin haka yasa ta juya dan tasan ko zata mutu bazai Bari ta shiga ba, tsaki taja tare da fad’in gashi Nayi late dama ni naje aka dan Sosa min In samu kud’in 

Dr jibril Fara lecture yayi inda ya nuna Zarah tare da fad’in stand up 

Tashi tayi tana kallonshi, sannan ya kalli ibtisam itama yace ta tashi 

Itama mak’ewa tayi 

Idonshi nakan Zarah yace yau na taba ganinki a nan, sai yau kika fara zuwa or what? 

Zarah tace a’ah sir, ni Ina karantar low ne, kawai na zauna ne Kafin time din lecture d’ina yayi 4.

Kai ya d’aga alaman ok, “kallon ibtisam yayi wacce itama shi take kallo, “yace and you Kema Mai kikeyi a nan? 

Tace ina lecture ne, “yace you mean kina department dinnan ne na medicine? 

Tace eh cikin sanyin murya. 

Ok yace tare da fad’in su zauna 

Bayan ya kammala lecture yace ma ibtisam ta sameshi a office d’inshi yana son ganinta, “yau kwata kwata 30mnt yayi ya fita domin an kusa kiran sallah la’asar 

Ibtisam bayan ya fita ta kalli zarah dake zaune tana danna wayarta, tace plz muje ki rakani inji mai zaice min. 

Zarah tace wa ?lallai kije ke d’aya, nifa yanzu sallah zanje inyi daka nan inje lecture, “Nasan shima yanzu ko Kinje saikin jirashi ya dawo daka masallaci 

Salis dake bayansu yace ibtisam, idan Kinje ki rokeshi ya baki text din da bakiyi ba, domin 20mrk ba wasa bane 

Ibtisam tace kana ganin zai yarda inna rok’eshi?

Salis yace Am not sure zai yarda, but try May be ya yarda, tunda mutum ne kuma yasan Allah 

Zarah tashi tayi tana fad’in bari inje inyi sallah, in tafi lecture 

Koda ibtisam ta fita itama taga Aisha ita da wasu mata a zaune suna ta surutu, kuma duka firan akan in sunje club ne ga yanda zata kaya,”ibtisam tace suko kunya basaji, “club din da babu abunda ake sai iskanci da shaye shayen giya 

Aisha ce ta katse mata tunani da fad’in ibtisam har kun fito?

Ibtisam ta saki murmushi tare da fad’in eh yanzu muka fito, “naga kinzo kin koma. 

Aisha tace Aiko na shigo korana zaiyi wlh, baida mutunci ko kad’an 

Sauran matan da Aisha take fira dasu suka zuba ma ibtisam ido, “wata Mai suna kubra tasha attachment brown da wando an matse tace wannan fah? Ban taba ganinta ba sai yau 

Aisha tace d’akinmu d’aya sannan course d’aya muke karanta 

Kubra tace OK, amma shine bakwa zuwa club tare 

Aisha ta kalli ibtisam tace Kinji abunda take cewa, wai bama zuwa club tare 

Ibtisam murmushi kawai tayi, “amma cikin ranta tace Allah ya rabani da zuwa club, kuma ina muku fatan shiriya, ku tuba ku daina…

Kubra ce ta katse ma ibtisam tunani da fad’in ibtisam koh? 

Ibtisam tace eh 

Kubra tace Sunan yamin dad’i, Sunan larabawa 

Ibtisam murmushi tayi tare da fad’in ngd 

Kallon AISHA ibtisam tayi tace plz zaki rakani wajan Dr jibril. 

Aisha tace ni? Rufamin asiri Mai zakiyi a wajansa? 

Ibtisam tace yace yana son ganina 

Aisha tace toh fah, Allah yasa dai lafiya, kodai shima d’an hannu ne, ya gani ya kyasa? 

Kubra ta saki dariya tare da fad’in uhm kibar lecturers dinnan, suna da iskanci, “amma Dr jibril ban tunanin zaiyi haka fah. 

Aisha tace ke ba’a shaidan mutum wlh, “yanzu mutum zai nuna Shina Allah ne anjima kiga ba haka bane, rayuwa kawai Ayi sha’ani kawai 

Kubra tace nikam ibtisam muje in rakaki, inje inji gulma komai zaice miki 

Ibtisam kam kunyar jerawa da kubra take, domin irin shigar dake jikinta, Wanda mutumin kirki dan musulmi bazaiyi ba, “amma babu yanda ta iya dole ta bita suje tare tunda tana neman dan rakiya, musamman da taji ana fad’in kodai dan hannu ne shima, “sai taji ta tsorata dan dama tasan ana cewa lecturer suna iskanci da student d’insu in ta’ki yarda sai su fadar da ita a course d’insu 

Har office din Dr jibril suka isa, da yake kubra tasan office din, nocking sukayi yace yes coming 

Bud’e kofar kubra tayi ta Fara shiga, ibtisam na bayanta kallo d’aya zaka mata ka gane jikinta yana d’ari d’ari 

Karatun al’qur’ani yake saurara

Ganin Sun shigo yasa ya kashe karatun tare da kallon kubra yace lafiya? 

Tace sir cikin d’ari d’ari na rakota ne. 

Yace OK you can leave 

Fita kubra tayi da sauri 

Ibtisam kanta na k’asa idon Dr jibril na kanta ganin yanda ta tsorata ba tare da ance wani abuba, inda zaiyi ihu da karfi zata iya zabura 

A hankali yace you can sit 

Zama tayi akan kujeran daya nuna mata 

Yace ya sunanki? 

Tace Amina, but ana cemin ibtisam 

Yace OK 

Tare da fad’in mai yasa kika fita a lecture Rannan da zan bada text, ko mark dinne bakya so? 

Da sauri tace a’ah 

Yace so tell me why kika fita? 

Tace saboda ban San abunda zan rubuta ba, sai yasa na fita, ranan shine farkon shigana lecture 

Yace amma ai an dad’e ana lecture why baki Fara attending ba sai ranan? 

Tace akwai problem din da yasa ban fara attending da wuri ba, sai daka baya aka yarda inzo 

Yace which problem? 

Shuru tayi tana d’an nazari, can tace “sir is family issue 

Murmushi yayi tare da fad’in oh ok sorry for asking you 

So yanzu kinyi missing 20mrk kenan right?

Ibtisam tace plz kayi hakuri ka bani inyi, tunda ranan na fara attending kuma kona rubuta I will fail, that is the reason da yasa naga gwara kar in rubuta din 

Idon Dr jibril na kanta yana kallon yanda take magana, ba kaman daba da take kaman a tsorace, “yanzu ta dan sake 

Yace OK zan baki text, but not now kizo gobe by 5pm sai in baki.

Da sauri ta d’ago ta saki murmushin da yake k’ara Mata kyau, tare da fad’in “nagode sir

Yace karki damu you can go 

Tashi tayi cikin murna ta fita.. 

Dr jibril da ido ya bita yana murmushi. 

Koda ibtisam ta fita taga kubra tsaye tana jiranta. 

Bayan ta fito kubra ta kura mata ido tun daka sama har k’asa 

Ibtisam tace lafiya irin wannan kallon? 

Kubra tace ina son insan koya miki wani abune, “Sai yasa nake kallonki inga Ina ya taba .

Ibtisam tace auzubillah “wlh kinyi mishi sharri domin ba haka yake ba, kuma ko maganan banza baiyi min ba, “infact ma magana yayi min akan Mai yasa da yace zai bada text na fita? “shine na fad’a mishi dalili, har yace zai ban text din inyi, “ni Bama yanda nake tunanin ana fad’a akanshi Nayi ba, mutum ne mai sauk’in Kai a yanda na Lura raini ne kawai baya so, “sannan yana kama kanshi ne da shaidanun student masu kaima lecturer tallan kansu.

Kubra tace uhm ibtisam kenan, daka had’uwa dashi yau yau har kin Fara bada shaida a kansa haka? 

Ibtisam tace ba haka bane, kubra Ina son ki gane wani abu, koda yanzu kika had’u da mutum indai kuka zauna kukai maganan minti biyar Zaki dan iya fahimtar Waye mutum da kuma irin abunda mutane ke fad’a akanshi 

Kubra tace toh ba girin girin badai, “Allah yasa Dai kar nan gaba inji kina tsine Mai, kina fad’in Ashe haka yake 

Ibtisam tace insha Allah bazaiyi abunda za’ace tir ba, domin koda Yana aikata wani mummunan Abu, yanayi a boye Toh Allah zai iya shiryashi tunda a boye yakeyi “amma wanda yakeyi a fili shikam sai dai ace Allah ya kyauta, mutum ya dinga Abu baya tsoran kowa, baki’i uban kowa ya gani ba, Kinga wannan yayi nisa baya fatan shiriya,”kuma shaidan duniya itace ta k’iyama daka ranan da mutum ya mutu za’a turo mala’iku suzo suji abunda mutane ke fad’a akan ka 

Idan mutane na fad’in oh an rage mugun iri, ka bani 

Inko aka samu ana yabanka ana fad’in mutumin kirki, koda kana aikata sabo a boye babu wanda ya Sani, sai Allah to Allah zai yafe ma mutum tunda wannan tsakanin Allah da bawa ne, kuma sirrin da Allah ya rufe babu Mai tona shi 

Kubra tace Allahu Akbar, “Ashe ibtisam din malama ce? 

Ibtisam tayi murmushi tare da fad’in daliba dai, muna koya ne 

Tafiya sukayi daka wajan inda suka nufi d’akin su ibtisam din, suka iske Aisha na zaune tana waya 

Ita dai ibtisam zama tayi tana jiran gobe tayi taje Dr jibril ya bata text din, d’auko littafi tayi ta Fara karatu 

Bayan Aisha ta gama wayar ta kalli kubra tace ya kuka kaya dashi? 

Kubra tace korana yayi da muka shiga 

Aisha tace ita d’aya kika bari? Maiya mata?

Ibtisam dake karatu tace babu komai, tare da bata labarin abunda ya faru

Aisha tace kodai yana miki wayau ne nan gaba ya fito da mayyatarshi, dan naga nashi Abun kaman da salo yakeyi 

Ibtisam tace Wai Mai yasa kuke mishi mummunan zato ne? Dan Allah ku daina Wlh babu kyau, tunda baice komai ba Kubar mishi mummunan zato, ku dinga kyautata zatonku akanshi plz 

Aisha tace lallai ibtisam ke yarinya ce baki San mai duniya ke ciki ba, kin ganni nan, “babu irin iskancin da ban sani ba, “sannan babu wani salo dana miji zai kawo in kasa gane inda ya dosa, “kuma Wlh zaki ce ni Aisha na fad’a miki, wata rana saiya fito miki da manufarshi 

Mutumin da baya wasa, baya sakar ma kowa, in bakayi text d’inshi ba, kokai Waye kayi missing kenan, ‘amma ke har yace kije office d’inshi sannan ya yarda zai miki, uhm akwai wata a k’asa Dai

Ibtisam cikin ranta tace Wai Mai yasa mutanan da suke aikata sabo suke ganin kaman kowa ma haka yake.

Lallai maganan da malamin su ya taba fad’a musu gashi yau ta tabbatar, in mutum yana Abu sai yaga kaman kowa ma irinsa ne, sai yaga kaman kowa ma yana irin abunda yakeyi,” mutumin kirki shine wanda yake ganin kowa kaman na kirki ne, na banza yana ganin kowa na banza ne. “Amma a fili sai tace nidai bayyi min Kama da mutumin banza ba 

Kubra tace bazaki gane ba, gaba muke miki tunani kuma zakice mun fad’a 

Tashi kubra tayi tana fad’in bari inje in dawo tare da kallon Aisha tana fad’in “anjima 8 akwai birthday din fatin d’akinmu ta fad’a miki kuwa? 

Aisha tace eh ta fad’amin Zanzo

Kubra tace OK tare da kallon ibtisam tace Kema Ina inviting d’inki Tana fad’in haka ta fita 

Aisha ta kalli ibtisam tace ina fatan zaki je koh? 

Ibtisam tace Kai Anya kuwa 

Aisha tace a cikin skul ne ba wani waje ba 

Ibtisam tace OK tunda cikin skul ne Zanzo nida Zarah 

Aisha tace OK saimu je tare gaba d’aya 

Koda zarah ta dawo ibtisam tace su shirya zasu birthday din wata cikin skul din za’ayi 

Zarah tace ok, amma fah ni bana son shiga iri irin wannan Abun. 

Ibtisam tace nifa da Farko nace ba zani ba, saida akace a skul za’ayi 

Zarah tace ok.

Ibtisam da zarah sun shirya duka cikin dogayen riga, ita Zarah doguwar rigan atamfa tasa, ita kam ibtisam jallabiya sunyi kyau Sosai duk da ba makeup sukayi ba, sai dai ita Zarah ta shafa powder 

Bayan sun gama shiri, suka zauna jiran AISHA Dan tare zasu, dan ita ibtisam ba sanin d’akinsu kubra din tayi ba.

Aisha ce ta shigo cikin riga da wando, tare da fad’in ku muje, na tsaya amsan abune 

Fita sukayi, har bakin gate Aisha ta tsaida mota suka shiga 

Ibtisam tace kunce cikin makaranta? 

Aisha tace eh amma a cikin gidan wanda suka Kama d’akin waje za’ayi… 

Ibtisam bata k’ara cewa komai ba, har motar da suka shiga Aisha tace ta tsaya a nan. 

Fita sukayi Aisha ta biya kud’in suka shiga wani Gida inda d’akuna ne Kala Kala a kalla yakai 30 daka ganin dai gidan d’akin dalibai ne, “baka jin k’aran komai saina kid’a da ihun Mata ana rawa, ko wacce ta tsuke cikin shiga mara kyau 

Ibtisam da zarah kallon juna sukayi 

Samun waje sukayi suka zauna inda suke kallon irin rawan da sukeyi, gaba d’aya babu maza sai mata, ibtisam tana cikin wannan tunanin saiga maza sun Fara shigowa kaman ana turosu kuma duk dalibai ne mazan student 

Nan wajan ya k’ara kacamewa da ihu, inda maza da mata suka fara rawa cikin rashin kamun kai da fitsara 

Suna rawan a manne da jikin junansu, basa kojin kunya. 

Yayin da wasu ke zaune a gefe suna shan shisha wasu kuma suna shan codeine kuma duka student Abun dai babu kyan gani 

Zarah ta Katse ma ibtisam tunani tare da fad’in jiba birthday din babu ko tsari, wannan Aiba birthday bane, ni ko cake ban gani ba 

Ibtisam tace uhm, kawai dai sun had’a party suyi rawa, “ni tashi mu koma dan ban son kallon wannan iskancin wlh 

Zarah tace a’ah mu tsaya Kinga dare yayi saimu fita muda yawa, mu zauna a nan iya kacin mu kallo 

Ibtisam tace Allah ya kyauta 

Zarah ta amsa da Ameen 

Haka suka zauna suna ta kallo ashe anyi cake, an ajiye ne a ciki lokaci d’aya aka d’auko birthday girl ta yanka nan suka saki ihu ana tafi 

Su ibtisam na nan zaune saiga kubra tazo, tace zan kuka zauna? “kuzo kuyi rawa mana. 

Ibtisam tace a’a barmu kawai a nan 

Kubra tace haba miye haka? Duka fa nan student ne babu bare, plz ku tashi mana, janyo hannun ibtisam tayi wanda dole yasa ta tashi sannan ta janyo zarah itama, tare da fad’in muje kuyi rawa 

K’aran wayan ibtisam ne yasa ta janye hannunta daka na kubra tana kallon wayar cikin tsoro ganin sunan Ummi ne a cikin wayar tana kiranta, “gashi wajan k’ara yayi yawa, “janyo Zarah tayi suka fita daka wajan amma still k’aran kid’an har waje 

Saida sukayi nisa da wajan sannan ibtisam ta tsaya “Zarah tace miye kike ta jana lafiya? 

Ibtisam tace ummi ce ta kirani ban San mai zata cemin ba, gashi wajan k’aran kid’a yayi yawa, “bari in kirata inji mai zata ce 

Kiran Ummi tayi, “ummi ta d’auka tare da fad’in ina aka shige aka ajiye wayar? 

Ibtisam tace ummi wayar na silent ne tunda na fito daka lecture Ashe ban cireta a silent ba 

Ummi tace ok, Nayi magana da abbanki, gobe zai bada wayar ta Mota a Kawo miki, zaiba driver din number d’inki saiki je ki amsa 

Tace toh ummi tare da fad’in nagode ummi na.

Ummi tace akwai abunda kike bukata? 

Tace a’a ummi bana bukatar komai, ina Granny? 

Ummi tace bari inkai mata 

Ummi taba granny waya, ibtisam tace Granny shine ko kirana bakyayi a wayarki koh? 

Granny tace yaushe zan kiraki yanzu kin zama y’ar jami’a Kema zaki fara fitsara irin na miskili, in kira a fad’amin ba dad’i 

Ibtisam tace Granny lallai kince wani abu, Sharrin da zakiyi min kenan koh? 

Granny ta tsuke baki tare da fad’in ke yanzu kin fison zama a wani gari koh?”zaki sa aita miki kallon y’ar iska, ni wannan Abun kunyar har Ina, haba takwara ta ki dawo gida mana in anyi bikin naku keda kabirun sai kici gaba a dakin ki, Kinga babu wanda ya gani balle yace 

Ibtisam tace Kai granny wai Mai yasa kike haka ne? Ni ginka sai anjma 

Granny tace ai kyace sai anjima tunda ba’a son gaskiya, zan kira kabirun ai inji dalilin da zai yarda yace kije wani gari karatu tunda shi baida kishin kanshi 

Ibtisam dariya ta saki tare da fad’in Kinga Granny sai anjima tare da kashe wayar 

Zarah itama dariya tayi tana fad’in Granny ba dama hala mita take miki 

Ibtisam tace Wlh kuwa, mitan na’ki aure kin San ita magananta kenan, ta matsa inyi aure ansa rana amma duk da haka bata kyaleni ba, ita wannan bokon ne dai bata so, na rasa dalili tsohuwa sai jaraba.

Zarah tace nikam wlh abunda Granny take fad’i gaskiya ne, ai kinzo jami’ar Kinga irin abunda akeyi a cikinta 

Ibtisam tace Aiba duka aka taru aka zama d’aya ba, akwai na Allah Sosai, amma y’an iskan ne sukai kaurin suna 

Zarah tace Allah ya kyauta Kinga mu wuce skul kawai, dan bazan koma ba tunda mun fito, machine suka samu suka hau 2 in 1 domin Sun dad’e suna jiran Abun hawa basu damu ba, sai yanzu shine suka haye machine din guda d’aya su biyu 

Har cikin skul ya kaisu inda suka sauka suka biyashi sukai d’akinsu, suna shiga kiran kabir na shigowa wayar Ibtisam tace Wai Allah ya soni 

Washe gari kaman yanda Dr jibril yace ma ibtisam hakan ko akayi 5 dai dai ibtisam ta nufi office d’inshi tayi nocking ya bata izinin shiga 

Bayan ta shiga ta gaidashi cikin girmamawa 

Ya amsa tare da sakar mata murmushi yace you can sit 

Tana zama wayarta dake hannunta ya fara K’ara, k’okarin kashe wayar ta Fara yace you can answer it 

D’auka tayi tare da sawa a kunne 

Sallama aka mata tare da fad’in nine akaba sa’ko IN baki gani garage kina ina? 

Ibtisam tace ina ABU plz ka taimaka ka Kawo min ban San ko inaba a cikin zaria ba 

Yace kai gaskiya kiyi hakuri kiyi tambaya sai kizo ki amsa, kuma kiyi sauri dan nan da awa d’aya zan juya Kano. 

Ibtisam tace toh kaban nan da lokaci kad’an zan tambayi inda garage din yake inzo 

Dr kabir idonshi nakan ibtisam Bayan ta kashe wayar yace Mai zakiyi a garage? 

Tace sa’ko aka aiko min dashi, daka Kano, gashi yace bazai dad’e ba zai koma and…. 

Sai kuma tayi shuru 

Yace and? 

Tace nothing sir am ready for the text 

Tashi yayi tare da daukan key din motarshi yace muje tare dayin gaba 

Binshi tayi da ido tana kallonshi, tare da tunanin Ina zamu???? 

Ganin yakai bakin kofa bata ko motsa ba, yace I said let go 

Tashi tayi da sauri ta fito ya rufe office din 

Tafiya ya fara tana bayanshi har wajan daya faka motarshi k’iran Benz, yace shiga muje 

Bata shiga ba sannan batai magana ba, domin ita dai bata san ina zasu ba inta shiga, sannan akan wani dalili zata shiga motarshi? 

Dr jibril yace Amina Mai yasa idan akayi magana sau d’aya bakya d’auka sai an k’ara repeating din magana?

Tace sir kawai naga ban San inda zamu bane sai yasa 

Yace zanje in sai dakine 

Da sauri ta d’ago ta kalleshi cikin mamaki 

Ganin irin kallon data mishi yasa yayi dariya tare da fad’in calm down am joking,”just enter d car 

Ganin bata da niyan shiga yaga alaman tana jin tsoro yace shine matsayin text d’inki, and in baki shiga ba zanyi failing naki 

Bud’e kofar tayi ta shiga Tana tunani iri iri a ranta 

Shiko ganin ta shiga ya tada motar yabar skul din 


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


Ibtisam kam bata sake ba domin a tsorace take dashi, tana tunanin Ina zai kaita daya d’age saita shiga cikin motarshi, kodai abunda su Aisha suke fad’i gaskiya ne. …

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button