Hausa Novels

Zee Baby Book 1 Page 11

*????????11*

….Kafin nayi wani yinkuri naji an murda kofar da sauri na koma bayan kofar na labe yana shigowa tun daga parlo yakejin kamshin turarensa hanyar bedroom d’insa ya nufa ai tanaga ya karya kwanar da zata sada shi da bedroom d’insa ta fito ta zuba da gudu hankalinta atashe karo taci da Mahabeer ya rikota ” my zee menene duk kika tsorata haka rumgumesa tayi ” Yaya Mahabeer wancan mugun ne nawa barna duk na fasa masa wayoyinsa da turarukansa da kayansa duk na yankasu wlh tsoro nake kar ya kasheni hankalin Mahabeer atashe ya kamo fuskata ” haba my zee ya zaki rika shiga zabgarsa yana dokarmun ke ya ilataki kinsan kimanin kudin wayoyinsa da kika fasa shagwabewa nayi ” to Yaya Mahabeer kasan irin wahalar da ya bani yau kawai fah dan nayi shaye shaye ” wlh nima zamu bata dake idan kina shaye shaye ” bari na shiga gida kar yafito jikinta ta janye tayi part dinsu da gudu parlo ta shigo tana maida numfashi gun ghaisha ta nufa ta fada jikinta rumgumeta ghaisha tayi ” momy kirage rashin ji kinji? ” to ummi naji ummi muje bedroom dinki nayi wanka nayi sallah ” to taku fah? shiru tayi Daddy yace ” momy bakijin yunwa?

” inaji bari nayi wanka da sallah ta Mike ta nufi bedroom d’insu saida ta murza key akofar khaleesat na zauna saman kujera zee ta kalleta ” my khalisat me kikeyi? murmushi tayi ” bakomai Amarya yayamu dariya zee tayi ta nufi bathroom ta sallo wanka ta fito daure da towel abaya ta saka ta shimfida darduma tayi sallolin da ake binta magarib da isha tajima tana neman gafara gun Allah ta Mike ta cire abayar tasa kayan bacci Riga da wando dogaye har kasa, akwatinta ta nufa, ta kwashe kayan mayanta ta boye dan tasan tabbas zai nemesu ” my khalisat muje parlo mana kin wani gumshe ad’aki mikewa tayi suka fito kusan Daddy ta zauna ta kwantar kanta kafadarsa ” Ammin zanci Shawarma? ” to momy yanzu kuwa zakici wayarsa ya dauka ya kira Dr Sardauna amma wayoyin duka akashe mamaki ya kamshi “Najib maza kiramun Dr yazo ina kiransa” to Daddy kanwata ina wayata?? idanu ta zaro ” wai bro kaje tana Swimming pool wlh namanta ta tana k’asan kujeran farko ” ok yace ya fice zee ko duk hankalinta atashe yake jin za’a kirawo Dr Sardauna, bangaran Dr

Sardauna ya shiga da niyar ya kara cin ubanta ya korota yana shiga yaci karo da irin tijara da zee baby tayi masa idanu yazaro waje wayoyinsa ya nufa ya sunkuya ya daukesu duka yaga har abdan bazasu moruba gaban dressing mirror ya zo ya tsaya yana jinjina kai turare ko daya bata bariba kwalaben duka ta fashesu d’akin tsabar kamshi kar yayi mura saida ya toshe hancinsa ya kalli saman bed d’insa yada tawa tsadadan zanan gadonsa filla filla wardrobe ya nufa abude duk rabin suit d’insa masu tsada da kyau da shadodinsa da jallabiyoyinsa tayi musu kisan gilla gasunan saman bed azube murmushi ya saki yana, ciza lips d’insa na k’asa iska yake busowa mai zafi daga bakinsa ” gud hatsabibiya gud tantiriya gud zee baby aikinki yayi kyau mutika amma zakiyi nadama mara anfani kinci bashin Faisal Almahadee Sardauna duk sunanane ni daya zaki biya barnar da kikayi zan azabtar dake ta fanni da bazaki taba manceniba zan gagauta ramuwa ta hanyar da zan dasa miki dafi mai zafi azuciyarki duk da ba hali na bane wlh sai namiki hore ta hanya mai nisan gaske zaki sanine zan gagaguta hakan ne kafin guri ya ya koremun insha Allah cikin gagawa zan hukuntaki narigada na gama gano wacece kedin wlh banajin akwai abunda na tsana sama da yarinyar nan amma zakici uwarki sai na hadasa miki ciwon zuciya dani kike maganar murmushin bakin cikin dauke kan fuskarshi ya shiga bathroom Mahabeer da ya shigo Dr bai fito ba ya Rika bin d’akin da kallo daya bayan daya yaga irin uwar barnar da zee baby

tayima Sardauna hankalinsa ya tashi tabbas yasan bazai yafe mataba abun zuba shara ya dauko dakansa ya kwashe duka tulin kwalaban da ta fasa na turare da maiyuka ya kwashe kayansa da ta yanka kaf cikin rawar jiki ya gyarawa Sardauna d’akinsa tsaf yaje d’akinsa ya dauko wani zanin gadon mai msifar kyau da tsada shikansa tamkar katifa dan laushi dukda Dr yanada amma yaki taba nasan lokacin da yazo Sardauna ya fito da kallo yakebin Mahabeer har ya gama ” Dr namu don Allah kayi hakuri wlh zan biyaka wayoyinka yaje ya daukosu babu mamora” Faisal karka hukunta ta da horo mai tsanani yarinyace duk fah 17 year take ciki don Allah kayafe mata ko nasamu nutuswa wlh bansan irin horan da zaka yimataba jikinsa ya goge ya saka jallabiya ruwan toka yana murmushi yazo ya rumgume Mahabeer ” babu komai na barta tunda kace yarintace zan barta ai ko dan kai Mahabeer yaji dadi sosai” Nagode Dr Sardauna Najib ne yayi sallama ” bro Daddy na kira kai ya daga Najib ya fice tare suka fito Mahabeer bedroom d’insa ya shiga Dr Sardauna ya nufi part dinsu Daddy, da Sallama ya shigo parlon ai tanjinshi ta boye bayan Daddy ko da wasa bata dago kantaba kusa ghaisha ya zauna ” Daddy gani? ” Dr Sardauna kanwarka takeson shawarma don Allah samo mata ” to Daddy muje da ita sai tazabi irin wacce takeso tana bayan Daddy tace” Ammin abarima nakoshi bazan kai kaina ga halakaba Daddy barna fa namasa dariya Daddy yayi ” barna me momy ” Daddy bari to naje na sayo mata kala ukku sai tazabi wacce tafi so ” yauwa Allah ma Albarka ” amin Daddy kiss yama ghaisha ya Mike nanah tazo gunsa ” ina zuwa daukarta yai suka tafi Aunty amarya na dariya ” momy ke sai tsokana da tsoro ko dagowa tayi tabi Sardauna da kallo yanada yake takunsa gwanin shawa tamkar bai dauki mutum ba akafadarsa ghaisha dariya tayi” momy uwar rigima gunta ta koma tayi kwance jikinta” ummi yau gunki zan kwana? ” to naji Nawwara tazo ta zauna kusan zee ” aunty kinmun kwacan mama ko dariya tabasu sosai bai jima sosaiba ya kawo mata Shawarma Mahabeer sai godiya yake masa zama yai amma ko da wasa baima kalli inda takeba itama bata kalleshiba dan tasan gabar ci tayi ta koshi abunta tana zuba surutu dan tasan ba yada ya iya da ita ana muk’ewa yayi ya musu sallama ya fice baki ta tabe ” Allah raka taki gona dakazo muka ganka ko ajikinsa ya fice Mahabeer yace” babu ruwanki dashi zainab kibar daukan magana gurin da akafi karfinki baki ta turo Daddy yace” wasan da take masa shiru mahabeer yai dan har yanzu bai yada da yafiyar Sardauna ba Hafeeza ta Mike ” sister tashi muje mu kwanta ” Tab jeki ba yanzuba hira sukaci gaba da yi kowa saida yaje ya kwanta ta tisa Mahabeer GABA sai sangarta take masa yana biye mata sai karfe daya, na dare yasa mu ya lallabata da tace bazata kwana da su Hafeeza ba Dr Sardauna yabiyo dare ya kasheta saida Mahabeer ya rantse mata yace yafe mata ta yada, sakuyi sallam ya rakata har kofar bedroom yace gobe yasayo mata layin Nigeria don surika shan soyayya ko yana kamfani gun aiki da haka yasa ta shige d’aki shiko ya tafi lokacin Dr Sardauna ya jima dayin bacci tana shiga taje gun da ta boye kwayarta ta dauko tasha ta kunna wayarta tana tikar rawa da ihu Dole su Hafeeza saida suka farka tagumi sukayi suna mamakin wannan hali na zee saide yau bata jima ta bingire ana saman carpet sai bacci wayar natayi ita daya khalisat ta sabko ta kashe mata wakar suka koma bacci,

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button