Hausa Novels

Zee Baby Book 1 Page 15

Tafi gidan ya rage sai mata Najib dama tun karfe bakwai ya fice Aunty amaryama tana shirin zuwa gidansu a parlo suke azaune suna hira Nisha tace ” wayyo hutu zai kare monday sai makaranta zee baby dai sama sama take amsawa dan tun da tayi idanu hudu da Dr Sardauna ta rasa nutsuwarta uwa uba kamshin shiyasa yanzu take gudun duk abinda zai hadasu yauma tsau tsayine jikin Nisha ta shige ta lumshe idanunta ahaka suke hirasu sama sama jin bacci ya fara zomata ta Mike dama ita baccinta sai bayan azuhur ne take tashi ” my dear na tafi gidan Daddah nakira ummina muyi hira idan mun gama na kwanta can kurya gadon mai rumfa na kwashi bacci sai bayan azuhur zan farka ko zaki eh muje amma ni nan zan dawo idan anjima ” ok muje hafeeza ma ta Mike suka tafi suna hirasu lokacin da sukazo part d’in Daddah mai ran karfe har ya tafi masallaci itama Daddah tana shirin tafiya dan dama karfe goma suke tafiya masallaci duk ranar juma’ah nan parlo suka zube suna hira har Daddah ta tafi masallaci ta barsu zee tayi takiran ummi Raiyan bata samunta ta kira Mahabeer ma ta fada masa shima ya kirata bai sameta dama mafi akasari awannan lokacin ba’a fiye samun taba sai zuwa yamma ko da sasafe Dr Sardauna yana fitowa ya shiga wata jibgegiyar mota kirar venza,2019 baka sudik ya shige yamata key kafin ya isoma mai gadi ya bude masa get ya fice aguje wayarsa ya dauka ya kira mashakurah sukasha hirasu ta soyayya har ya isa hospital din tunda yazo jama’a yake dubawa marasa lafiya, sai goma da rabi ya Zauna zaune yake cikin kawataccen Office d’insa Wanda ya gwaraye da ni’imattacan kamshi da sanyin Ac sai sigari yake zuga yana waya “bandar kaifa bakada mutumci wlh na kusa aure ka daure kazo dan bai wuce saura wata daya da kwana ashirin da biyar ba ok karshan watanan ko? Ahmed shegen mutum bashida niyar aure fa inaga sai NASA an masa na Dole Ahmed ne ya murda kofar ya shigo Dr Sardauna ya kallesa ” kajimun dan iskan mutum ka ganshi bari na baka shi wayar ya ba Ahmed yana kaimasa duka ya amsa ya kara akunne ” wai shegen mutum wai yaushe zaka shigo ne Dr fa aure zaiyi ah ni inajiran wata yarinyane zan gwada sa’ata mutumin na hango zaune awani kayataccen wuri daga gani ba kasar bakar fata baceba ” wlh Ahmed akwai abunda na aikatawa wata yarinya ya dameni bansan inda zan gantaba amma yar Nigeria ce kuma garinmu daya da ita tunda na aikata hakan hakkinta ke bibiyata na kasa sukuni amma zanyi kokari nazo karshan wata Dr yace nazo muyi maganar anutse” subhanallah bandar me ka aikata haka?” maganar sai na diro Nigeria batayi a waya ” ok Allah kawoka lafiya ” Amin bani Dr Sardauna wayar yana Dr sukaci GABA da hirasu sun jima Dr na masa tsiya wai yafadi gaskiya ko kwartanci yama yar mutane yace duk abar maganar har yazo k’asar abin ya faru bisa kaddara ne haka sukayi sallama cikin kaunar junansu Ahmed yace” kai dan iskane shine baka nemana yau kwana biyu bamuga junaba ba fa? ” yi hakuri kasan aiki yasha kaina ya jikinka??” ba sauki Dr Sardauna don girman Allah kasa baki bro Mahabeer yabarmun zee baby wlh Allah ji nakeyi kamar zan rasa raina da kallo Dr Sardauna yabi Ahmed sai kuma ya bushe da dariya yana nunasa da yatsa ” dallah malam kamun shiru ba abin dariya bane temako nake nema zee baby nada saukin kai wlh idan bro ya barmun ita nasan zata soni saboda ina da zubin namijin da takeso” yi hakuri Abokina ba abin tada jijiyar wuya bane ya fada yana buso hakin sigari baki da hanci yana lumshe lumsassun idanunsa” yanzu yada za’ayi tashi kaje gun bro Mahabeer yana gun aiki kanemi alfarama yau ranar juma’ace gashi garin ya hade da hadari ruwa bai sakoba idan kaci sa’a yabar ma to sai musha biki amma da kamar wuya fah kadai je ka gwada jarumi ya fada yana dariya yana busa ma Ahmed hakin sigari a fuska ” wai meyasa kafiye wulakanci kafasan banason hayakin taba ko?? ” uban waye ya gaiyatoka hospital DINA an busama ya fada yana karama sa hayakin duka ya kaimasa ” Allah ya isa mugu kawai yanzu zan samesa a kamfani kuwa?? ” yes zaka samesa ya fada yana duba wani shegen agogon hannusa mai masifar kyau mik’ewa Ahmed yayi ya bashi hannusa wani shegen kallo Dr Sardauna yama Ahmed ” bazan gaisa dakai ba sai ka wanke hannuka ya karasa fada yana dariya dukansa Ahmed yakai Dr ya cafe hannu Ahmed ya murde da karfin tsiya cikin mugunta sai yasaki kara Dr Sardauna ya bushe da dariya mugunta ” yaro ni sa’ankane zaka dokeni ahir dinka da kallo Ahmed yabishi ” wai me yasa kafiye mugunta saboda Allah yanzu me nama ka kakeson mun illa sakinsa yayi yana dariya ” yi hakuri Abokina ya Mike ya rumgumesa muje na rakaka gun motarka dariya Ahmed yayi ” ai haka kake idan kayi mugunta tare suka jero har harabar Hospital din saida Ahmed yashiga mota ya tafi ya dawo duk inda ya wuce gaishesa akeyi miskilancin ya dawo hannusa kawai yake dagawa kofar wani room ya hadu da Ruma sai wani feleke takeyi ya dauke kansa fuskarsa amurtike zai wuce ta gaishesa ” Doctor dama kai zani kira Dr Nabil yace an gama kai ake jira ka fara tiyata kai ya daga ya shige Office dinsa baki ta tabe ” wlh sai na malaki wannan hadadan gayen shirin shiga tiyatar yayi ya kara zugar sigari sai karfe goma shadaya da mintina goma cif ya shiga tiyata yarone ma karami dan kimanin shekaru goma Adu’ar nasara yayi kamar kullum idan zaima mutum tiyata sai yayi Addu’o’i kafin ya yanka mutum,,

goruba Road *Kai kadai gaiyya magawata kamfani* na hango masha Allah jama’a sai shige da fice akeyi a motoci. Wasu amashin waso akafa Office Daddy na fara lekewa yana zaune kan wata hadadiyar kujera da mutane sai lisafi suke ya kalli wani dan matashi ya bashi kudine masu uban yawa ” maza kaima manager yana Office fitowa yayi nabi bayansa wani hadadan Office muka shiga sanyi da kamshi ya bugi hancina Mahabeer nagani zaune saman wata lumtsumeyiyar kujera shida wani kyakyawa bakine amma bayada makosa duk da Mahabeer yafisa kyau zai kai sa’ansa daga gani abonkinsa ne da sallama ya shigo Hadeem ya amsa Mahabeer waya yake da zee sai dariya yake dan shagwaba take zubama sa shigowar mutumin yasa ya tsinke Kiran suka gaiza ya bashi kudin ya amma ajikin wata na’ura ya zubasu total suka nuna masa million biyune kashe ya dago ya kallesa ” million biyu ko?? ” eh Manager slm ya masa ya fice Ahmed ya shigo da sallama Mahabeer ya amsa fuskarsa sake ya nuna masa kujera ya zauna Hadeem yace ” ina kabaro Dr Sardauna?? kai ya sosai ” ya shiga tiyata cikin jin kunya kansa k’asa yace “bro Mahabeer dama temako zakamun kar na rasa raina dan Allah ka barmun zee baby na auran please jahadee zakayi wallahi ina mugun sonta ko rashin lafiya danayi kwana biyu da suka wuce wlh akantane don Allah ka duba lamarin bro idanu hadeem ya zaro yana kallon Ahmed da kokari Mahabeer jiyayi kansa na juyawa maganganun Ahmed sun masa mugun zafi har wata zufa yake yana cikin tunanin ne yaji Ahmed ya rumgumesa yana kuka da rokonsa yayi hakuri haushi yacika Mahabeer bai san lokacin da ya wanke Ahmed da mari yana huce yace “wallah………

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button