Hausa Novels

Zee Baby Book 1 Page 16

” my zee babyna har karfe ukku saura maza jeki kiyi kizo da gudu ta shige bedroom d’insu su Nisha na kwance suna sharara barci ita da hafeeza khalisat na zaune da waya hannuta “ke ko dan bacci rana bakiyi ta cire rigar jikinta ta d’aura towel ta shige bathroom ruwan gumi ta hada tayi wanka harda na tsarki dan bakaramar zuba tayiba fitowa tayi tasa Abaya digowa ta shimfida dadduma ta tayar da sallah azuhur, koda ta gama tajima tana istigifar da neman gafara Allah tana rokon Allah kada yakawo abinda zai sake hadata da Dr Sardauna tayi Adu’a akan Allah ya saka mata duk cutar da yamata adu’a ta shafa ta Mike ta cire Abayar siket ta saka kadan ya wuce gwiwa da Riga karama mai yankeken hannu ko brezia bata sakaba dan kem suke kuma dama bata fiye saka brezia ba gashinta ta saki bata daureba ta fesa turare tasaka janbaki kalar lips

d’inta pink jinta take wasai tunda tayi wanka tayi sallah s’aide jikinta babu karfi khalisat tace” wlh kinyi kyau murmushi tayi ” nagode ta fito har yanzu batada kuzari dan de tanason Nuna jarumtarta Dr Sardauna na manne cikin idanunta yana sakar mata murmushi har yanzu parlon ba kowa sai Mahabeer kusansa ta zauna ta fara zuba masa shagwaba” my zeena kinyi kyau dayawa please kibar irin wannan kwalliyar sai bayan auranmu kinci abunci?? ” Allah my heart ban ciba kuma banajin yunwa daide lokacin Dr Sardauna ya shigo da Sallama ya hade cikin 3quarter fari da wata jibgegiyar rigar sanyi baka sai zuba uban kamshi yakeyi yayi masifar yin kyau takunsa yake cikin kasaita ai tanajin muryasa ta fada kan Mahabeer ” my heart wlh karabani da Dr Sardauna aikuwa gadan gadan kansu yayo Mahabeer ya boyeta bayansa ta tura kanta bayansa shiko yana kallon Dr Sardauna da yayi kicin kacin da fuska yanufo gunsu Mahabeer ransa ab’ace ya dagama Dr Sardauna hannu ” dallah malam dakata wai ina zaka ne kana nufin agabana tana jikina na boyeta zaka zo ka bugeta wlh da na wanwanke ka da mari yaushema ka ganta da har tashiga harakarka ko dan ka ilatamun matata kuma ko bakomai yanzu Auntyn kace wai me tama ka tsaneta kamar ba jininka ba ai ko darajata taci my zee babyna me kika masa ne?? har yanzu nufosu yake ransa ab’ace kanta ta dago karaf idanunsu ya sark’e da juna kallon Dr Sardauna take cikin wani yanayi shima ita yake kallo face ta had’e ta dauke idanunta daga kallonsa ta kauda kanta dan tayi Alkawalin fita daga harakarsa har Abadan dan alakarsu babu alheri gashinta da ya zubo ya rufe mata fuska gurin kauda kanta daga kallon Dr Sardauna Mahabeer ya shiga gyara mata ya daure mata kallon Mahabeer tayi gashagwab’e tace ” my heart kace kar ya iso garemu wallahi dukana zai yi kuma ni insha Allah na fita daga zabgarsa dan haka kamana tsakani dashi wai kawai fah dan na………………✍????

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button