ALKALI NE 1-END

ALKALI NE Page 41 to 50

Da gudu Raheena tayi d’akin ta tana mai cike da farin ciki, da kyar tayi sallolinta abinci ma a d’aki taci ta kosa dare yayi sosai ta kira Ra’eez dan ta amshi lambarsa a wajen Dadynta. 

**

Ra’eez bayan ya kammala abubuwan da yakeyi ya kakkab’e gadonsa ya kwanta, rungume filo yayi yana jin kewar Iyayensa, tun dawowarsa gidan da aka gyara komai ya koma d’akin Abbunsa da zama, domin yana matuk’ar son gadon Abbunsa, babu abinda aka canza hatta da filo da katifar duk sune na kusan shekaru takwas, zanin gadon kawai ya canza shima na Ummunsa ya d’auko yasa, duk lokacin daya kwanta a gadon yana mai jin dad’i, sai yake jin kamar yana tare da Abbunsa ne. 

K’arar wayarsa ce ta dawo dashi daga tunanin da yakeyi, d’auka yayi yana bin wayar da kallo har ta tsinke, dan besan lambar da ya gani ba, sake kira akayi amma be d’auka ba, sai da aka kira sau ukku kafin ya d’auka. 

Shiru yayi ba tare da yayi magana ba. Mak’e murya Raheena tayi cikin shagwab’a tana fad’in haba Yayana sai da na kira sau ukku sannan zaka d’auka. 

Murmushi Ra’eez yayi dan ya fahimci mai magana. Raheena tace koda yake laifina ne da ban baka lambata d’azu ba, amma kuma ya kamata ace ka d’auka tun akira na biyu. 

Gyara kwanciya yayi yana fad’in kin kira waya sai surutu kikeyi baki fad’i sunanki ba. Cikin shagwab’a tace kai Yayana nasan dai ai ka d’auki muryata? Ra’eez yace ai ni ko wata mukayi da mutum ba lallai bane na rik’e muryarsa ba. 

Murmushi tayi tana fad’in Raheena ce fa. Ra’eez yace Raheena? Wace Raheena fa? Yanzu kam kukan shagwab’a tasa hada birgima asaman gado, duk yana jiyota sai ma murmushi da yayi. 

Gyaran murya yayi yana fad’in Malama zan kwanta naga alamar bakida abun cewa. Cikin sauri tafe Raheena da kazo gidan mu d’azu a Surelere fa. 

Tab’e baki yayi yana fad’in Allah sarki ashe kece? Nasan dai ban baki lambata ba shiyasa nayi mamaki. Raheena tace awajen Dady na amsa ai. Ra’eez yace to yayi kyau ya ‘yan gidan ki gaishe mani da su. 

‘Dif ya kashe waya yana sakin murmushin mugunta. Raheena kuwa saurin cire wayar tayi tana binta da kallo, sake kira tayi amma a kashe. Wurgar da ita gefe tayi tana mai jin haushi, amma bakomai zata jure komai matuk’ar zai amince da ita, tasan ma yana da saukin kai zai amince da ita. Bargo ta jawo tana murmushi.

*** 

Washe gari wayar Raheena ce ta tashesa abacci, dan bayan yayi sallar asuba ya kunna wayar ya kwanta bacci ya d’aukeshi. Saurin tashi yayi yana kallon yanda gari yayi haske sosai, wayar ya kalla yaga lambar jiya ce dan beyi saving ba. 

Hannu yasa ya d’auka akaro na biyu da ta sake k’ara. Gaishesa tayi tana fad’in Yayana ko bacci kakeyi ne? Murza ido yayi yana fad’in wallahi kuwa gashi har na kusa makara, gaskiya nagode maki. 

Dad’i ne ya kamata ta sake kank’ame wayar tana fad’in naji dad’i kuma zan rik’a tada ka a koda yaushe dan bana so ka makara. Murmushi yayi yace nagode, bara nashiga wanka. 

Da sauri tace da ina kusa dana had’a maka ruwan. Ra’eez yace hakan ma nagode. Kashe wayar yayi ya nufi band’aki. 

Raheena kuwa fad’awa tayi saman gado tana murmushi, saurin tashi tayi ta jawo hijabinta domin tayi sallah, dan alokaci zatayi sallar asuba, ahakan ma saboda suyi waya da Ra’eez yasa ta tashi wajen k’arfe takwas, dan Raheena akwai sallah a makare, wani lokacin sai ta kai k’arfe tara batayi sallar asuba ba. 

Tashi tayi tana fad’in dole nasa alarm ko dan narik’a tashinsa sallar asuba, da haka zan saye zuciyarsa, idan na tashesa nima zan daure nayi sallar sai na koma bacci kafin alarm d’in 7:30 yayi na sake tadasa yayi wanka. Murmushi tayi tana kabbara sallah. 

***

Komai beci ba ya rufe gidan ya nufi gidan su Rumaisa dan ya saba saiya fara duba su kafin yawuce wajen aiki. 

A tsakar gida ya iske su suna karyawa koko da kosai, Rumaisa kuma tana had’awa da shayi dan bata shan koko. Da sallama yashiga. Amsawa sukayi Mama tana fad’in yanzu nake fad’in Rumaisa ta kawo mani wayata na kiraka naga shiru baka shigo ba. 

Zama yayi yana fad’in wallahi yau makara nayi Allah yaso ma Raheena ta tashe ni da… Kwarewar da Rumaisa tayi ne yasashi yin shiru yana kallonta. 

Mama tace kiyi ahankali mana Rumaisa. Shayin ta d’auka tasha tana goge hawayen da suka taho mata wanda babu wanda ya gani sai Ra’eez. 

Murmushi yayi dan ya fahimci dalilin kwarewarta. Juyawa yayi yana gaishe da Mama. Bayan sun gama gaiswa Rumaisa ta gaishe sa. Harara ya buga mata yana fad’in shine ko ki tashe ni ko? Duk’ar da kai tayi fuskarta a d’aure. 

Mama tace Rumaisa kawo masa kofi ya karya kafin yawuce. Ra’eez yace Mama na kusa makara gara dai na tafi kawai. ‘Daure fuska Mama tayi tana fad’in tashi ki kawo masa kofin. 

Murmushi yayi dan yasan halin Mama bata son ya fita beci komai ba. Tashi Mama tayi ta koma ciki ta barsu a waje. Zuba masa tayi ta mik’a masa kular kosan. 

Amsa yayi yana kallon yanda tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka. Murmushi yayi yana girgiza kai yace K’anwata waya tab’a mani ke kuma? Zama tayi tana kok’arin maida hawayen idonta. 

Kosan ya kai baki yana kallonta sai juya kosan hannunta takeyi. Murmushi yayi yana fad’in ke shayi zaki sha ni kuma kin had’ani da koko saboda son kai ko? Kauda kai tayi bata ce komai ba. 

Ra’eez yace wai bazaki kulani ba ne yau? Turo baki tayi tana fad’in kaje Raheena ta baka. Dariya yayi yana fad’in lallai sunan yayi maki dad’i, daga fad’ar suna so d’aya shikenan har kin haddace, ko kina so na had’aku kawance ne? Tab’e baki tayi tana fad’in Allah ya kyauta. 

Girgiza kai yayi yana fad’in kada ki sake kiranta da Raheena domin Yayarki ce. A zabure Rumaisa ta tashi tana dira k’afa tayi d’akinta. 

Dariya yayi sosai yana girgiza kai, abincinsa yacigaba da ci aranshi yana jin wani sanyi yana ratsa masa zuciya ganin yanda Rumaisar sa take nuna kishinta akansa, yana matuk’ar sonta amma har yanzu ya kasa fad’a mata, yana jira ta kammala karatun ta kafin ya fad’a mata amma a yanzu baya jin zai iya jiranta, domin yana buk’atar mai kula dashi, dole ma ya fito mata da abinda yake zuciyarsa shekaru da yawa. 

Bayan ya kammala yayi ma Mama sallama. Fitowa tayi tana masa addu’a, kud’i ya aje yana fad’in Mama yau sakwara nake son ci. Mama tace badamuwa za’ayi maka, kun gaisa da Madu ko? Ra’eez yace lokacin dana shigo yana band’aki sai dai idan na fita yanzu. 

Mama tace to Allah ya tsare ya baka sa’a a duk abinda kasa gaba, Allah ya kareka daga sharrin masu sharri. Murmushi yayi cikin jin dad’i yace amin Mama. 

Mama tace ina Rumaisar fa? Ra’eez yace tana d’aki kila wani abun takeyi. Mama tace to sai ka dawo. Fita yayi yana waiwayen d’akin Rumaisa. Sai da suka gaisa da Madu ya bashi kud’i yana ta masa addu’a kafin ya tafi. 

Asibiti ya fara biyawa ya duba Ummunsa kafin yawuce wajen aiki, koda yaje ya iske har Alhaji Barau yazo, kai ya jinjina yana fad’in lallai yau na makara da yawa. Ciki yawuce yana gaisawa da mutanan da suke waje. 

Lokacin daya shiga ofis d’in Alhaji Barau tare da bako ya iskeshi, risnawa yayi ya gaishe su. Alhaji Barau yace Ra’eez ko dai bakayi bacci jiya da dare bane? Murmushi yayi yana fad’in wallahi makara ce kawai nayi. 

Alhaji Barau yace Mr. Kallah kaga sabon lauyen da nake fad’a maka. Da sauri Ra’eez ya kalli wanda aka kira da Mr. Kallah, domin duka sunayen wad’an da suka zalunci Abbunsa babu wanda bai rik’e ba. 

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button