Zee Baby Book 1 Page 20
************************************
*bayan kwana ukku*
tunda zee baby da Dr Sardauna sukayi fada da Alkawalin fita daga harakar juna yau har kwana uku to sun cika alkawali babu mai shiga sabgar kowa tun ranar zee ko kallonsa bata yada ta sake ba tayi watsi da lamarinsa kamar yada shima ya watsar da ita a salima idan sunji murya junansu kowa k’okianrin barin gurin yake shiyasa yanzu zee bata fiye zama parlo ba da dare dama dasafe kafin ta tashima ya tafiyasa gun aiki shiyasa basu fiye gamuwaba tun daga ranar har yau basu hada idanuba kowa yama zuciyarsa alkawalin hakan shiyasa ta maida hankalinta gun Mahabeer suke zuba soyayyarsu tana masa sangarta iri iri yana biye mata Dr Sardauna ya maida hankalinsa gun sweet babynsa dan tana bashi tausayi yanda take mutuwar sonsa, yaune wa’adin da malam kafi madubi yama Aunty amarya yaune zata amso magani da sharudan da zai gindaya mata, tun safe tacewa Daddy mamarta ba lfy yace ta shirya ya ajiyeta tace amotarta zata bai musaba, bayan sun gama breakfast taje ta shiryo, ghaisha na zaune aparlo Mahabeer na mata sallama yau ya makara da ya shiga gun zee ta tsayar dashi wai suyi hira sai daket ya lallabata ta koma bacci dama shine ya tasheta ya kawo mata tea tasha, Aunty amarya tafito rike da hannu nanah tace” Aunty ghaisha zan dubo mummy sai nadawo”kodai na tashi mutafi? ” wlh ki zauna gidan ba kowa. idan kin samu lokaci sai ki tafi”to agaishemun dasu kafin nazo nanah zo mu zauna kafada ta makale Mahabeer ya dauketa yana dariya tare suka fito da Aunty Amarya har motarta ya rakata yana rike da nanah ya ajiyeta sukayi sallama ya shiga motarsa ya nufi get Aunty amaryama ta shiga motarta tayi mata key ta nufi get…………✍????
[ad_2]