Zee Baby Book 1 Page 21
Ban garan Aunty amarya ko bayan sun dawo zamanta tayi tace bazata komaba sai dare Asiya tamata sallama ta tafi itako tanan sai bayan sallah isha tayi shirin tafiya uwarta ta kara jadada mata yada zata kula da sharunda da malam ya fada mata, zaune suke aparlo zee da Nisha da khalisat sai hira shirme zee take musu hafeeza sai dariya take musu yada nisha ta biye mata Mahabeer ne ya shigo da sallama zee ta Mike ta tarosa harda riko hannusa “my heart wlh nayi missing d’inka “my zeena nima nayi missing d’inki sosai da fatan kina lfy? ” lfy lau zama sukayi nisha ta gaishesa da su hafeeza ya amsa fuskarsa asake “Ya Mahabeer bari kaga pic d’in da mukayi nisha bani wayata idanu ta zaro”au kina nufin baki dauko ba wlh tana part d’in Daddah harata nayi na Mike “Ya mahabeer tsaya na amso da gudu ghaisha ce ta fito ta zauna mahabeer ya koma kusanta ya zauna yanama zee magana ta tsaya amma ta fice da guda”Allah my heart sai na amso akofar parlo tajita tayi karo da mutum male male ta fada saman faffadan kirjinshi wani irin mugun shock ne ya debesu atare zuciyoyunsu suka buga atare da sauri tana k’ok’arin janyewa shima yana k’o’karin janyeta kansa ya kauda ya tureta ta fadi k’asa ya shige parlo mik’ewa nayi raina ab’ace amma sanin bamu harakar juna yasa nayi hakuri dan shma da dane sai ya mareni ya shigar dani jikinsa na shaki kamshinsa haka na nufi hanyar gidan Daddah kamshinsa ya dagamun hankali jina akirjinsa yasa tsikar jikina mik’ewa ga kasala amma Dole na basar ina shiga na dauko wayar na dawo part d’inmu kusan mahabeer na zauna shiko yana jikinta ghaisha sai kansa take shafawa tamkar wani dan jariri yamun mugun kyau Ya Mahabeer nashiga nunawa pic d’inmu ina dariya ta karfin hali asace nake kallonsa ko kallon inda nake bayayi haka yasa nima na daina masa kallon sata na shiga sha’anina khalisat kuwa ta zuba masa idanu tamkar zata cinyesa sab’anin nisha da Allah ya samata mugun tsoron Sardauna sam bata iya zama inda yake yanzuma jitake ta takura su Daddy suka shigo da sallama shida Aunty amarya zee baby ta dago tana dariya “Oyoyo Daddy ai tanakai kallonta ga Aunty amarya ta Mike zumbur jikinta na karkarwa idanunta suka rikide sukayi jajur da gudu tayi kan Aunty Amarya “Wallahi baki isa ki shigo mana da wannan masifar ba Aunty Amarya tanajin haka tayi kofa da gudu jikinta na rawa zee beby kafin ta cinma Aunty Amarya ta fara ganin duhu luuu tayi zata fadi kafin ta isa gunsu Mahabeer da gudu yayi kanta itako Aunty Amarya tuni tana kofa tana zaro idanu duk abinda ake Sardauna ko kansa bai dagoba ko ghaisha da tace ya dagata kansa ya dauke saman cinyarta ya Mike ya ficiwarsa daga parlon Mahabeer ya tarota jikinsa ta zube tana buge buge “wlh sai nayi maganinta muguwa ghaisha ta karaso gunsu tana mata Addu’a kamar yada Mahabeer yake mata Daddy ya iso”Wai me ke faruwane da momy Mahabeer yace Daddy Aunty Amarya ce…………✍????
[ad_2]