Zee Baby Book 1 Page 22

**********************************
*Bayan kwana ukku*
Bayan wannan lokacin abubuwa sun faru kamar su gabar Sardauna da zee baby ta dore Dan ko dawasa baya kallon inda take itama haka saidai ita rashinsa na mugun daga mata hankali har ta Dan rame sha’awarsa tana damunta ta rasa ya zatayi ta gaji da rashin Sardauna tana bukatarsa tanason gumin jikinsa tanason kamshinsa da sauraron zazagar muryasa da sweet d’in lips dinsa amma haka ta daure ta basar yada ya basar da ita suke rayuwa cikin k’unci da takura Nisha ko tun wahegari da sasafe ta gudu gidansu tace bazata iya rayuwa dukaba dama saboda zee ta matsa abarta ta dado tarinka zuwa makaranta daganan Najib ya kaita gida mahabeer dai yananan ras babu abinda ya samesa soyayyarsu da zee sai abunda yaci gaba suna kula da junansu zee said sangarta take maza iri iri zee ko ita da Aunty amarya basa wani shirin duk da ita zee sam batasan abinda ya faruba ranar amma washe gari fur ta hana ta zaman parlo gashi malam yace karta kuma nemansa sai wa’adi ya cika ita da khalisat farin ciki sukeyi Sardauna ya tsallaka magani jiran lokaci kawai sukeyi na wajan Daddy kuwa tun washe gari da zata hada masa babban aminin mairan karfe Alhaji Nuhu ya rasu a daura daga zuwa ganin dangi dama jikin tsofa ba lfy bace dashi gabaki dayansu mazan suka dunguma daura har Dr amma shi da mahabeer basu kwana ba su Nuhune suka kwana Daddy ko na can shine ya saka bata bashi maganin ba sai yaune zata bashi khalisat yaune zata wanke fuskarta da magani,
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
da misalin karfe shida na Yamma Dr Sardauna ya bari asibiti ya nufo gida yana zuwa yayi parking ya fito ya rufe motar cikin takunsa na isa da kasaita ya yake tafiya cike da kuzari waya manne akunnesa sanye yake cikin suit bakake sunyi masifar yi masa kyau gashinsa ya Dan sabko wuyansa said zuba uban kamshi yake ya nufi part d’insu ghaisha a parlo kuwa baby kowa said zee baby zaune tana game awayarta su Aunty amarya ko tana kitchen Ana k’ulla mugun Abu sai nanah da nawwara na kallon Tv da sallama ya shigo parlon yana waya sai murmushi yake aciki na amsa sanin darajar sallama ko kallo bata ishesaba ya wuce ta gabanta ya nufi kujerun can nesa da ita Wanda ko kallon juna basayi ya zauna tunda na kallesa na dauke kaina zuciyata na bugawa da karfi saboda irin kalaman da na tsinto yana fadama mashakurah ga muryasa ta kashe mun jiki ga kamshinsa kasala naji ta kamani daurewa nayi naci gaba da sha’anina cikin dauriya kiran ya katse dama hira irin kayan da take sone sukeyi dan asatinan zai hado akwatina ganin ita dayace a parlon yasa ya Mike yana kiran ghaisha shiru bata amsaba ya nufi d’akinta zee tashi tayi jikinta amce tabar parlon bedroom ta shige Nawwara tace”yayamu mama tana gidan Daddah sai Aunty amarya a kitchen juyowa yayi ya nufi kitchen d’in har ya shiga kuma ya fito ya juya zai fita kenan khalisat ta fito daga d’akin Aunty Amarya fuskarta sharf da ruwa cikin farin ciki ta karasa”Yayamun Dr………….✍????
[ad_2]