Y’AN UWANTAKA NE KO SOYAYYA 3&4

🆓 🅿️3&4
Asalin labarin
” Alh idris da alh Aminu yaya ne da k’ani uwa daya uba d’aya”haifaffun garin adamawa ne”kasuwanci yakawosu garin kano”kowa nasu acan yake”alh idris yanada manyan shaguna akwari yana siyarda atamfofi da laces.”yayinda k’aninsa Alh aminu keda shima nashi shagon”sunada son juna da had’in kai”tun suna tafiya gida sudawo”har Allah yasa suka gina gida babba kowa yaja b’angaren sa….kasancewar ilimin boko iya secondry skul suka tsaya”bayan sun yi aure sai mahaifiyarsu tadawo nan da zama acikin gidansu”wato( hjy)”
Alh idris(abba)yayi aure da habiba(mama)cikin so da k'aunar juna"habiba macece me kirki da son jama'a"suna zamansu naso da k'aunar juna"sau biyu tana haihuwar maza babu rai"ahaka har alh aminu(baba)ya auro jamilah"(umma)"suna zaune kowa na sashensa"amma jamilah nada izzah ,kuma mama tafita wadata"bata sakewa da mama"hakan yasa habiba tayi baya da ita"gefe guda kuma habiba namasifar son tasamu ciki kota haifi ya' mace"kowa yasan yanzun burinta ta haifi ya'mace"wani time d'in hjy tayita mata fad'a akan tanemi zab'in alkhairi....
cikin ikon Allah Jamila watan ta1 tasami ciki”yayinda aminu murna ba’a mgn”cikin jamilah wata 3 itama habiba tasami nata cikin….bayan wasu watanni jamilah ta haifi santaleliyar y’arta (maryam)karka so kaga farin ciki gun alh idris da habiba ba’a cewa komai…sai kace itace ta haifi y’ar”duk wani abu na hidimar haihuwar da ita akeyi”atime d’in tayi nauyi cikinta zaiyi kusan 7 month”jamilah kuwa haushin d’okin da habiba keyi akan y’arta takeyi”shikuwa Aminu farin ciki yakeyi”akan yadda d’an uwansa da matarsa ke nuna farin cikin ganin gudan jininsa…
bayan wata ukku habiba ta haifi d'an ta kyakykyawa namiji (yusuf)tayi murna sosai"tasan k'ila macen ba alkhairi bace agunta"tun bayan ta haihu"kullum maryam da yusuf na gunta tana rainonsu"Jamila kuwa bataso tana d'aukar mata y'a"yawanci idan alh zai tafi kasuwa sai yaje sashensu jamilah ya amso maryam yabawa habiba"itada komawa sai tayi kuka...maryam nada wata goma"yusuf wata 7 jamilah tasami wani cikin"hakan yasa gaba d'aya aminu yamaida maryam gun habiba da aka yayeta"shekaran maryam1 da wata 7 akayi mata k'anwa fatima"hakan yasa aminu yamaida maryam gaba d'aya gidan yayansa halak malak....sosai akayi rikici da jamilah akan bata yardaba"har yaji saida tayi"shikuma aminu yace".tazab'a ko aurenta kotabar maryam gidan yayansa"adole ta dawo d'akinta ta hak'ura..wannan shine dalilin dayasaka umma ke kink'i mama"
atare da yusuf maryam suka taso"komai atare ake musu"ba'a nuna banbanci"sunyi wata iriyar shak'uwa taban mamaki da junansu"time d'in dasukayi 10yrs aka raba musu makwanci"ansha fama da rigima agun yusuf"sannan umma duk idan yusuf yashigo sashenta ta dinga zaginsa da gaya masa maganganu masu zafi"hakan yasa baya son zuwa"saidai suje gun hjy suyita wasa da janta"tun dg yusuf mama bata sake haihuwa ba"yayinda umma ta k'ara 2 duk maza"Ahmed da mubarak"atare aka saka su yusuf da maryam"islamiya da boko suka zama mate"tun tasowarsu yusuf miskiline da maryam kawai zakaga surutunsa da fara'ar'sa"ko yaya yaga tayi fushi shima zai shiga damuwa yayita rarrashinta"itama haka"sannu ahankali har suka tasa suka zama manya"yusuf yakammala karatunsa na ingeeniaring amma be samu aikiba"ita kuma maryam fannin anguwar zoma ta karanta"su duba basu fara aikiba"kasancewar basu jima da gama karatun ba.
yusuf kyakykyawane ajin farko”saurayine miskili me aji da izzah”yanada tsabta dason k’amshi sosai”shine da kansa yasakawa maryam uk’utinah!itakuma tana kiransa broth ko my friend da sauransu”atare suka sauke alk’ur’ani me girma kafin suyi SSCE”yusuf yanada son addini da ibada sosai”sbd yanada ilimi na addini dana zamani”yusuf nada mugun son girma”gaba d’aya mate d’in su na makaranta suna zaton shine yayan maryam”sannan shima yak’i nuna mata shine k’anininta”saidai yanuna mata ai shine yabata wata 3″itadai kawai saidai tayi murmushi”yusuf yana taimakon iyayensa duka biyun”da baba da abba”da wuya yusuf yashiga taron mata wata batace tana sonshiba”abu 2 ke had’ashi fad’a da uk’uti d’insa”shine tace masa yaso wance ko wance ta mutu akansa”sai kuma yaganta da wani namiji”sune ke had’asu fad’a”tun suna yara maryam ke musu wanki, shikuma yamusu guga”har iya yanzun kuma haka sukeyi”ko abinci atare sukeci…yusuf babban telan matane”ya iya d’inki sosai da sosai”shine sana’arsa”dukda yasha alwashin zai dena anan gaba idan yasami aiki”amma fa yanasamun fitinannun kud’ad’e bana wasaba”ya iya d’inki sosai”yawanci matan shuwagabanni da masu kud’i da yaransu yakewa d’inki”baya d’inki na 5k”dg 7k abinda yayi sama yakeyin d’inki”watama yana iya mata na 10k kawai idan yayi tabiya15 kko 20k”sanadin d’inki matan dake nuna suna sonsa basu k’irguwa”hakan yasa ya wakilta yaransa 2″dake saka stones ko masa aikin surfani”duk wacce ta kawo d’in ki su rubuta size d’inta dakomai”dayatashi yad’inka yabasu subata ta bada kud’i”idan kuwa kin matsa shine zaki gani saidai ki hak’ura da d’inkin”sbd bazai kulaki ba”hakan yasa wasu ke masa kallon me girman kai”yamallaki abubuwa ta sanadin d’inki”kuma maryam duk yawanci tare da ita yake zuwa shago”yana fira da ita yana d’inki” amma banda week end”sbd tana zuwa islamiya”komai da budurwa wayayya me aji zata saka ajikinta”muddin yusuf yaganshi zai siyowa maryam shi duk tsadarsa”iyayensu sunso bayan sunyi SSCE maryam ayi mata aure”saita Ida karatunta agidanta kamar yarda kanwarta fatima tayi”amma yusuf yashiga yafita yazugeta akan batada saurayi ita saita gama karatu….
Yusuf beda amini shak’ik’i kamar faruq”faruq mate d’in sane amma yagirmesa sosai”dan zaiyi 30 yrs”ayanzun haka befi wata 2 bikin faruq d’in ba”Duk cikin abokansa shine ya yarda yayi fira da maryam”itama maryam tana girmamashi….yusuf yasha b’atawa da abokansa sbd sunce suna son maryam…..yusuf nada yawan buk’ata”hakan yasakashi yawan yin azumin nafila….
maryam kyakykyawar budurwar ce masha Allah”sbd har kama ta jini sukeyi da yusuf”tanada sauk’in kai”saidai bata iya fushiba”tanada kamun kai”yadda take yiwa yusuf biyayya saiki zata ubanta ne”maryam ba doguwa bace ba kuma gajeraba”tanada dai tsaka tsakkiya”tanada jiki mai kyau”sbd idan kaganta bazakace tayi 26 yrs ba”shiyasa da yawa ke zaton yusuf yayantane”akwaita da sanyi hali ga shagwab’a”sbd kowa yana jida ita agidan”mama na zaune da ita tsakani da Allah tana ruk’onta”bata ban bantasu da yusuf”hakama abba yana kulawa da ita sosai…..gefe guda kuma mama hankalinta yafara tashi akan abubuwan da yusuf ke nunawa game da maryam…..
Acikin layin akwai gidan alh bala mak’ocinsu”yaron gidan Mohd yana masifar son maryam amma shakkar yusuf ,yasaka ya jinkirta dukda yanuna mata…..wannan kenan zakuji komai agaba”
Cigaban labarin….
Anutse yusuf yashirya cikin k’ananun kayan dasukayi mugun karb’an jikinsa”
yana fitowa dg bed room d'in sa yaga maryam bata nan"
wato uk’utinah tafiya tayi tabarni ko?”yafad’a Ahankali yana rufe k’ofar parlourn ya wuce cikin gidan”
abakin k'ofar shiga main parlour yasami hjy(kakarsu)tanata fad'a akan maryam tak'i aure"
hannunsa guda yasaka yajanye hjy ya wuce cikin parlourn”
babu shakka idan ubankane ka janyesa ka wuce ko?
uffan be ceba yazauna agefen maryam yanata kallonta”
matsowa tayi kusa dashi tace”.broth mitar hjy yayi yawa wlh….dakika gayamasa yamun me to?”kin gand’ame acikin gida Duk sa’anninki sunyi aure kekina jibge agida ko?
tab’e baki yusuf yayi ya kalli hjy yace”.da abinda ba huruminkiba da wanda ke huruminki Duk shiga kikeyi…
naje na shiga marar kunyar banza”ai bakwason gsky dg kai har ita d’in”Duk shiru sukayi hjy nata mita ta juya ta fita”
shine kikak’i jirana ko?”yafad’a Ahankali yana kallonta”haba broth meye abin dole saina jiraka?”bekoma mgn ba yamatsa dg kusa da ita”
Shagwab’e fuska tayi tace”.badai fushi kayiba pls”
Hmmm uk’utinah yanzun Duk kincanzamun”amma babu komai”bara naje nayi alwalah ankusa kira”
ni ban yardaba kaje”kefa bakyayin sallah”ko bakyaso nasami jam’ine?”
Ba haka bane kaida ke fushi dani”tafad’a tana kallonsa”d’ago kansa yyi suka had’a ido”yamatso kusa da ita har jikinsu na gugar juna”
meyasa d’azun kikak’i jirana?”to bakai bane ke sani inajin kunya”to nadena”yauwa broth bani zobena”tafad’a tana kama hannunsa zata cire zoben…✍️