Zee Baby Book 1 Page 28

yayi ummi Raiyan ma dariya tai” kai amma naji dadi Allah ya Sanya Alkhairi sukace Amin Daddy wayarsa ya ciro ya kira Abban Nisha bugo daya ya daga da sallama ” wa’alaiki sallam Alhaji Bashir inason ganin ka da yamma zanzo? OK nagode sai anjima ya tsinke kiran yace” Saminu bayan la’asar sai mu tafi yace zai jiramu? ” to shikena ba damuwa Allah ya kaimu yasa haka shi yafi Alkhairi Nuhu yace” Ameen Daddy yace kutashi mutafi gun mai ran karfe yaji komai ghaisha tace”wai yau baza kuci abuncin ranaba ne har karfe uku zatayi Raiyan tashi muje Auta tashi muje kaci abunci fuska ya yamutsa ashagwabe yace.” Mamana ni banson cin komai? ” No tashi muje kamashi tayi suka nufi kan dining su Daddy suna dariya suka Mike ya kama hannun zee baby Dan duk abinan da ake tana jikin Daddy tayi lakwas tarasa meke mata dadi dukansu kan dining suka nufa kowa yaja kujera ya zauna zee gun mahbeer ta koma ghaisha tayi serving d’insu jalof din shinkafa ce taji nikeken naman rago da kayan lambu da soyayar kaza asama sai uban kamshi take zee kore damuwarta tayi sunacin abuncinsu tare ita da mahbeer Wanda hakan ya Kular da Sardauna daket ghaisha ta takura masa yaci mai Dan yawa ya Saki jikinsa saboda ghaisha sai tambarsa take ko bashida lafiyane Daddy yace”abinda abokinsa da matar da zai aura suka masa jinki abun karamine khadija ai Dole zai damu murmushi yay “Daddy wlh basa gabana dama ta ficemun arai Aishar tayimun dari bisa dari Allah ya tabbatar da Alkhairi sukace “Ameen Allah yayima Albarka ya Amsa da “Ameen zee ta kallesa karaf suka hada idanu wani irin mugun yanayi suka shiga atare idanunsu suka lumshe atare zee kanta ta boye jikin mahbeer tana sabke ajiyar zuciya idanunsa ya bude yana kallonta ganin yada ta manna kanta jikin mahbeer yasa ya Mike yanajan tsaki yabar gurin Sam babu Wanda ya lura suna aikin kwasar jalof mahbeer ya kalli zee ya dagota Dan yau tayi mugun taso masa sha’awa daurewa kawai yakeyi yanzu haka sai yayi wanka Kafin yayi la’asar” zee ki zauna kin koshine kallonsa take tana lumshe idanu Wanda suka fara Ja murmushi ya Saki ya Mike ya kama hannuta Dan yagano bacci takeji
dariya suka musu suna binsu da kallo yana rike da hannuta har bedroom can ya dauketa ya kwantar da ita ya lulubeta da blanket ya rankwafo ya mata kiss”my zee babyna maza bacci rikoshi tayi ta fashe da kuka” Ya Allah don Allah ki sakeni my zeena kinaso ki kaini bango ganin ba sakinsa zatayi ba ga kukan da take yasa ya tsaya yaga ita gudunta bata masa komaiba rumgumeshi tayi gam tana kuka bayanta ya fara bubbugawa ya gyara mata gashinta yakai bakinsa kunneta yana mata waka yana shafa gashinta da lalami da kalamai masu dadi shiru tayi ta Kara makaleshi sai sukurtu take tamkardai bataji yada take so ba da ta rumgumeshin cikin wayo da dubara yasamu tayi bacci yaji tana fitar da numfashi tare da sabke ajiyar zuciya murmushi yai ya janye jikinsa ya gyara mata kwanciyata ya sakar mata kiss saman lips d’inta yana shafa kyakywar fuskarta” I love u my zeena wlh ina tsananin sonki da kaunarki na matsu a daura mana aure hakurina ya fara gazawa akanki dauriyata ta kare wlh duk lokacin da zaki rabenni sai nayi wanka gashi ke baki dauki komai ahakaba juyi yaga ta fara tana lalube ta kwabe fuska tana kiran “Sardauna tana nishi sai mimmk’ewa take dariya yayi “kai rashin jituwa batayi ba kijifa fitina me Dr yayi kuma jin ta riko hannusa tana cewa”Yaya Sardauna please kark.. Da Sauri ya janye hannusa yana dariya ya Mike ya rufeta yana cewa ” karya mike Allura ko ya fice yana dariya lokacin da ya fito su Daddy sun tafi part din Daddah sai ghaisha da ummi Raiyan nanah na zaune saman cinyarta suna hira kunya tasa ya nufi hanyar fita yana Sosa kai dariya ummi Raiyan tayi ghaisha tace”wlh mahbeer akan momy bashida kunya dariya kawai yayi ya fice yana zuwa part d’insu bedroom dinsa ya nufa yayi wankan tsarki ya canza kaya ya fito ya nufi part d’insu Daddah Dr Sardauna ko yana zauwa ya kure karfin Ac ya fada saman bed ya shige cikin blanket ya kwanta yana juyi da Jan tsaki har bacci yayi Nasara daukeshi, Daddy ko suna part d’in Daddah mahbeer ya iskosu har sun fada musu abinda ya faru da shawara da suka yanke tunda Sardauna yace Zainab ta zaba mashi Aisha kuma ya amince yana Sonta Daddah da mai ran karfe sunji dadi sosai, Ana sukaci gaba da hira saida aka kira sallah la’asar suka tashi akayi Alwalla suka nufi masallaci daga can zasu gidansu Nisha Kiran sallah la’asar ne ya tashi Dr Sardauna bathroom ya shiga ya dauro alwalla jallabiya ya dora kan kayansa ya tafi masallaci ummi Raiyan ce ta shigo bedroom d’in taga zee sai sharara bacci take tashinta tayi fargigit ta farka ta kalli umminta “tashi maza kiyi sallah “ummina yanzu ne fah na fara baccin? ” eh tashi dai sabkowa tayi ta shiga bathroom tana turo baki ta dauro Alwalla ta fito ta yafa mayafi ta hau saman Darduma ta tayar da sallah ummi ma tashiga ta dauro Alwalla ta fito ta shimfida wata darduma ta tayar da, sallah zee tana gamawa hafeeza ta shigo zee ta kalleta” sister ina kika shiga tun d’azu? ” ina gidan Daddah fah bari nayi sallah yau wanka zani Swimming pool nayi murmushi zee tayi “zan biki amma bazan wanka ba ta fada tana nufar dressing mirror ta gyara gashinta ta daure da wani ribbon mai shegen kyau ta gyara fuskarta wardrobe ta bude ta ciro wata Riga pink color mai santsi iya gwiwa mai masifar kyau ta cire ta jikinta ta saka Dan ko tayi sha’awar wankama sai tayi wow nace tayi wani mugun kyau amma komai nata ya fito rigar ba karamun karbarta tayiba ummi Raiyan ta kalleta ta Mike”zainaba kinci gidanku bazaki fita ahakaba shagwabewa tayi” ummi Swimming pool zamu fah abaya ta dauko ta sakamata saman kayan “bakiga akwai ma’aikataba agidan kuma ta gabansu zakubi idan kunje sai kicire Dole ta hakura ummi ta janyo hannuta “muje parlo idanu hafeeza ta gama shiryawa sai ta fito ku tafi Dan tasan halin ‘yar tata zata iya cirewa shiyasa ta mata wayo suka fito parlor ta jirata
Bayan sallah la’asar su Daddy suka tafi gidansu Nisha Daddy ya kira babban amininsa Alhaji shazali harda mai ran karfe aka tafi Alhji bashir ya tarbesu da hannu bibbiyu bayan sun gama gaisawa ne Daddy yayi gyaran murya yace”Bashir abinda ya kawomu Akan maganar Aisha ne da Faisal yace ita yakeso kaddara ta rabashi da wacce zai aura to da nace yasamo wata yace Aisha ya zaba wai harma yazo sunyi magana shine nace to bari muzo kar muyi k’asa agwiwa Abu na gidane mairan karfe yace “idan babu damuwa Bashir munaso atsayar da magana munzo neman aure Bashir k’asa yayi da Kansa cikin jin kunyar surikin NASA yace” to madallah ai duk Abu na gidane tunda har sun daideta banida ja bari na kira Alhaji yanzu mik’ewa yayi ya fito yana farin cikin abun dama shi yaron da Nisha take so bai bawani kwanta masaba parlon ya shigo da sallama umma Hauwa na zaune Nisha na jikinta akwance ta Mike hayatu na zaune yana waya zama Bashir yayi yana kiran waya Babban Wansa ya kira yake sheda masa komai cikin farin cikin yace gashinan zai zo ya bada auran Aisha cikin jin dadi ya kashe wayar Hauwa ta kallesa” Alhaji bangane ba fah ta kalli Nisha wace tayi tsuru tsuru da idanu sai kif kif take da idanu Bashir yayi dariya ya kalli Nisha”Aisha kinason Dan uwanki zaki aureshi ko? kunya taji ta rumgume Hauwa ta boye kanta tana daga kai Hauwa tace”ikon Allah Bashir ya warware mata duk yanda akayi har zauwar Sardauna gun Nisha zauwar Dan uwansane yasa ya Mike ya koma gunsu Daddy suka nemi auren Aisha Mamuda ya basu har sadaki Saminu ya bayar nera dubu dari nan take mamuda ya amsa aka tsayar da ranar aure daide da na mahbeer kwana ashirin da bakwai yau daide yayi saura kowa agurin farin cikin yake da wanan Abu mahbeer ana gamawa ya Mike ya shigo ya gaishe da hauwa wacce itama tayi farin cikin sosai sai waya take da kawaye da abokan zama suna tayata murna irin wannan Abun Alheri kai tsaye da Allah ya kawo hayatune yasa nisha gaba yana zagi “Dan ubanki kika yarda aka hadaki da wannan mugun Dr Mara imani zakici ubanki shegiya karaf akunne mahbeer hayatu na zagin Dr Sardauna kuma yasan dalilin zagin da sallama ya shigo Nisha na ganinsa ta Mike ta taresa ta rike hannusa “Oyoyo bro dariya yayi “Amaryar mu aban goro sakin hannusa tayi cikin kunya ta ruga daki da gudu ta boye kai ya girgiza ya zauna kusan umma dariya umma tayi ” mahbeer kasa kanwarka jin kunya kaga masifafan da ya takurata tun dazu mik’ewa hayatu yayi yabar parlon ko kallo bai ishi mahbeer ba Dan yaji zafin zagin da yama Sardauna dama yanada haushinsa murmushi mahbeer ya saki” umma ina yini ” lafiya lau ina momy kai ya Sosa na barota tana bacci yau rigima takeji dariya umma tayi zatayi magana wasu mata uku suka shigo da sallama mahabeer ya Mike “umma suna jirana na tafi “to zanzo gidan zuwa dare dariya yayi ya fice a bakin get ya samu su Daddy sun fito suna shiga motar Nuhu da sauri ya karasa mairan karfe zai shiga mota ya rikeshi yana tsokanarsa sandar hannusa ya kwada masa dariya mahabeer yayi ya sakeshi ya gewaya mazaunin direba ya tashi motar ya mata key yabi banyan motar su Nuhu get aka bude musu suka fice………………. ✍????