Hausa Novels

Zee Baby Book 1 Page 30

*????????30*

….”kika sake fitowa ahaka sai na bata miki rai gida cike da maza zaki rika fita ahaka “yo my heart ai babu Wanda ya ganni fah sai Yaya Sardauna kuma ni yaya mahbeer kabarmun fada Allah ni banason fada sai Karina min fada jifa hannuna kajimu wayyo Yaya Sardauna kagani my heart yajimun ciwo ko? “yi hakuri my zeena zo mugani janyeta yayi ya kamo hannuta suka zauna kusan Sardauna ya kwantar da kanta kafadarsa ya rike hannuta “Dr ango kaji zainab tana kullamun Sheri wai na jimata ciwo ya fada yana murmushi yana murzawa zee baby hannuta Sardauna dagowa yayi Wanda ransa yayi mugun baci ya danne yama Nisha sallama yace Zai kirata da dare ya kalli mahbeer yace”my bro kaima naga irin fisgar da kamata ai kashinta bai kwarin da zaka fizgeta hakaba sai kajimata ciwo zee najin haka Sardauna ya daure mata gindi ta b’are baki ta fashe da kuka tana bekama Sardauna hannunta ya riketa ransa wani irin mugun baci yayi kwashe wayoyinsa yayi ya Mike yabar gun mahbeer yace”Dr Namu ka tsaya kaji labari mai dadi bai juyoba yace” toilet zan shiga zamuyi maganar anjima ya tafiyarsa dukansa zee ta fara tana kuka”to ni sakeni na tafiyata wlh ba ruwana dakai tunda ka kori Yayana gashinan kajimun ciwo daket ya riketa ya shiga lallashinta yasamu tayi shiru tana zumburo

baki saida ya lallabata har ta sabko ta Saki ranta ya jata suka nufi gun ruwan abayar ta cire taba mahbeer ya rike mata tana dariya “my heart naje nayi wanka ta nufi ruwan da gudu ta tsumduma mahbeer na zaune sai murmushi yakeyi yana lumshe idanu yana jinsa a farin ciki zee nutso kawai take ruwan saboda ta iya ruwa sosai idan tayi nutso ta gaji sai ta leko a kirayi mahbeer tana dariya shima dariya yake mata sai takoma yay yay da ita ta fito sutafi taki saida taji Ana kiran sallah ta fito gashinta har gadon baya na tsagar da ruwa mik’ewa yai ya taro ta ya rikota yana goge mata gashinta da mayafin abyar tana dariya ta shafi fuskarsa”my heart ina sonka murmushi ya Saki ya saka mata rigarta ya yane mata kanta da gyale ya mata kiss agoshi “nima ina Sonki ina kaunarki wlh bazan iya rayuwa babu keba rumgumesa tayi tana dariya” nima wlh Yayana ina Sonka ina alfahari da kai janyeta yayi ya kamo hannuta suka nufo cikin gida daide part d’insu ya Saki hannunta “my zeena alwalla zanyi na tafi masallaci dariya tayi ta wuce part d’insu shima ya shiga part d’insu akofar get sukayi Karo da Sardauna ta dago da Sauri face ya had’e ta tare hanyar ta marerece fuska”Yayana ina wayata hannusa yasa ya matsar da ita bai kalleta ba yace”tana gun ummi zatayi magana ya buga mata wata uwar tsawa jikinta na rawa ta shiga ciki da gudu tsaki yaja ya tafiyarsa tana shiga ta wuce bedroom ta cire kayanta ta daura towel ta shiga bathroom saida tayi wankan tsarki saboda rumgumar da Sardauna ya mata ta zuba sosai tana fitowa

ta saka Riga da siket yan kanti rigar mai dogon hannuce ta fesa turare ta fesar da gaahinta ta shafa mai ta daureshi da ribbon ta saka hijab ta hau darduma ta tayar da sallah hafeeza ce ta shigo itama ta dauro alwalla ta tayar da sallah zee ko da ta gama bata tashiba zaune take tana hailalah da salatin Annabi hafeeza ma zaune take tana karatun Alqura’n mai girma har aka kira sallahr isha suka Mike sukayi atare suna idarwa zee ta tashi ta cire hijabin ta nufi D’akin ummi tana zaune kan darduma tana Addu’a hawaye na zuba saman fuskarta jin motsin zee yasa tayi saurin gogewa ta shafa fatiha ta Mike ta kalli zee tana zaune bakin gado wayarta ta dauko”ga wayarki inji Sardauna amsa zee tayi tana jujuya wayar ahannuta tanajin kamshin Sardauna jikin wayar ummi ta zauna ta rumgumo zee “zainaba kinada damuwane? dariya zee tayi”kai ummina wlh babu abinda yake damuna ummina murmushin farin ciki tayi zee ta budewa umminta kai” wow ummi kizo nayi miki kitso mana ko Dan bazai kitsu ba ta fada tana warware gashin Wanda tsayinsa ya wuce mazauninta dariya ummin tayi tana ma zee dukan wasa “sakarmun gashi hirasu suke cikin so da kauna hafeeza tashigo da sallama “ummi ghaisha na kiranki murmushi tayi “to ganina zee tashi muje kici abunci rumgume ummi tayi”to ki goyani janyeta tayi ta Mike tsaye ta daure kanta ta kama hannu zee suka fito tana mata rigima sai ta goyeta dariya su Daddy suka musu kan dining suka nufa Sardauna na zaune yanacin hadin salak da akwai Daddy yace kaga Dan gatan ghaisha kallonsa zee tayi ganin fuskarsa ahade ta kauda kanta ghaisha tayi serving d’insu mahbeer ne ya Iso yana dariya ya nufi gun Sardauna ya zauna yasa hannunsa cikin plate din “ango baka bani gorona ba fah? ” murmushi Sardauna yayi “bro zan baka karka damu Daddy yace “yauwa idan mun gama

cin abuncin zamuyi magana kunga Abu ya gabato suka amsa da to zee ta kalli mahbeer “my heart ba ko magana ko? ” zo muci salak akwai dadi” Allah Ya mahbeer to bari nazo naci ta Mike tana kallon Sardauna ido suka hada wani irin abu ya sokeso atare wani mugun kallo Sardauna ya watsama zee da nunin karta kuskura tazo dabbas ta koma ta zauna Dan ta gano kashedinsa baki ta murguda ta hararesa taja tsaki ta kauda kanta tanajin wani irin yanayi na baibayeta Mahbeer yace ya kika fasa zauwa? cikin sanyin murya tace “Ya mahbeer banaci ne Sardauna spoon d’in ya ajiye cikin plate ya mike ya dawo parlo sude iyayansu abuncinsu sukeci mahbeer yayi yay da zee tazo taci salak taki dam Sam ya fice mata arai abuncin kadan taci Dan bata fiye cin abunci sosaiba da dare surutu tayi ta zuba musu har suka gama suka dawo parlo Sardauna na zaune yana waya da wani Dr da yake Abuja Akan yazo Abuja gobe zee tana jikin umminta kwance Sardauna na gama wayar Daddy yayi gyaran murya yace”yauwa dama abinda nakeso daku shine maganar lefene

Kai Faisal nasan aiki aiyuka sunma yawa Mahbeer kaine zaka jagoranci tafiyar kaida ummi Raiyan da khadija zaku tafi Dubai ku hado kayan lefe da da kayan daki da gadaje har na Aisha nine zan mata komai ya kasance kun musu iri daya kamar yada gida janku yake iri daya to hata kayan da za’a zuba agidan ma ya kasance iri daya akwatina ma iri daya komai yazama iri daya dama na gama shirya koma jibi idan Allah ya kaimu zaku tafi momy sai muyi zaman mu ni dake da hafeeza har su dawo ko? ” wayyo Daddy atafi dani please sai nazabo komai Dan Allah Daddy na fada ina son yin kuka ummi tace”nafa San halinki idan munje bazaki barni nasake ba nayi abunda ya kaini ba kukan shagwaba na saka mata na Mike na nufi bedroom Sardauna da kallo ya bita yana lumshe idanunsa zuciyarsa na bugawa Daddy yace”ko atafi da ita sai tazabi irin abubuwan da take so ummi tace”abarta wlh bazata barni na sakeba yanzu zan shiga na lallasheta zata hakura murmushi Daddy yayi
Sardauna gun ghaisha ya dawo ya zauna ya kwantar da kansa cinyarta kansa ta shafa masa “Autana ya dai Mamana gobe zan tafi Abuja insha Allah amma kwana biyu zanyi ko uku “Allah ya kaimu ya.kaika lafiya ya bada sa’ar aikin da akaje yi Daddy yace”ni bazaka fada munba tashi yayi ya koma gun Daddy ya rumgumesa “sorry my Daddy dariya sukayi mahbeer yace”Dr Sardauna namu wai bazaka bani gorona ba murmushi yay ya kallesa “Allah bro kafiye takura yo ni goro gareni kuda kukaje kuka kai kudin auren kukasa ranar aure ai Kane zaka bani goro ko Daddyna ya fada yana rumgumesa Nawwara da nanah dariya sukayi suna kallon Sardauna harara ya zabga musu ghaisha tace ka firgitamun yara mahbeer yace”au haka kace ko gira Sardauna ya daga masa yana dariya ya kalli ummi “ummi kije zainab fah na kuka ita daya ki lallasheta dariya mahbeer yayi “eh lallai tama zaben mata ummi mik’ewa tayi tamusu sallama ta nufi bedroom d’insu zee hira suka taba kadan Sardauna ya Mike ya musu sallama Dan da Asubah yakeso ya kama hanyar Abuja mahbeer ko yana nan suna tattauna yada komai zai tafi atsari sai karfe kusan shadaya ya tafi part d’insu ummi da ta shiga

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button