Hausa Novels

Zee Baby Book 1 Page 30

zee na kwance har tasaka kayan bacci taci kwayoyi kwallaba daya ta shanye ta sirot dama ita daya ta rage mata hafeeza ta tambyeta meye Tasha tayi banza da ita Dan yan isakan sunzo kanta akwance ummi Raiyan ta iskosu murmushi tayi isowa bakin gadon tayi ta dauketa cak kuka ta saka mata “ummina wlh ni saukeni nayi fushi ta kalli hafeeza”diyata kiyi hakuri natafi nayi lallashi tare zamu kwana shiru zee tayi tayi lamo jikin ummi dakinta ta nufa da ita ta kwantar da ita cire abayar jikinta ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta saka kayan bacci ta hayo gadon ta rumgume yarta da take kukan sangarta ba hawaye Dan kwayoyin sun fara aiki”zainaba yi shiru yar autata bari namiki waka mai dadi waka ta fara mata akunnanta ta larabci kunsandai balaraba da zakin murya tana shafa gashin kanta tun tana turjewa, har ta tsaya tayi shiru tana sauraro tayi lamo jikin ummi bata jimaba bacci ya dauketa abinka da tayi shaye shayenta ummi bata bariba saida taga baccinta yayi nisa Addu’a ta tofa mata taja blanket ta rufesu Dan itama so take tayi baci ko ta farka cikin dare tayi sallah tana rumgume da yarta har bacci ya dauketa hafeeza tana dakinsu ita daya itama tayi bacci rashin zee baby dama itace ke hanata bacci da wuri sucika dare suna hira can dare ta gudu gun umminta ta kwana,

Sardauna yana zuwa wanka yay yayi shirin kwanciya yayi sallahr nafila raka’a biyu ya jima zaune yana Addu’a ya Mike ya cire jallabiya ya ballo maganinsa yasha ya fada saman bed yaja blanket ya rufa jikinsa yana juyi har bacci ya daukesa koda mahbeer yazo lokacinma Sardauna yayi bacci shima wanka yayi yay shirin bacci ya kwanta amma yay cikin wuya yayi bacci sha’awar zee dinsa ta adabeshi ga tunanin zai barta yayi tafi wacce yasan zasu kusa sati haka yayi ta juyi har yayi bacci bangaran Nisha tunda Sukayi magana da Dr Sardauna muryasa ta dimautata ta gigitata don bata taba wata magana ta arziki dashiba sai yau kwance take saman gado sai juyi takeyi motsi kadan ta kalli wayarta Dan yace zai kirata zuwa dare sai lumshe idanu take Dan bacci takeji gashi ya Mata kashedi baya kira aki daukan kiransa haka dai har bacci ya kwasheta cike da begen Sardauna Asubah ta gari,

**************************************

*agurguje bayan sati uku*

Bayan wannan lokacin abubuwa daya sun faru harda zuwansu ghaisha da ummi Raiyan da mahbeer Dubai Wanda suka dauki tsawon sati guda sun hado kaya na kece reni gadajema iri daya aka sayoma zee baby da Nisha haka akwatuna ma iri daya da kayayakin sawa hata kayan kitchen d’insu iri daya saida suka kwashe kwana bakwai cur suka dawo zee ton washe garin tafiyarsu ta koma gidan Nuhu can Nisha take iskota suna hira Sardauna shima baya gari saida ya dauki kwana biyar a Abuja rashin zee baby ya adabi rayuwarsa kamar yada itama rashinsa ya dameta har zazzabi tayi amma tasama zuciyarta hakuri bangaran Sardauna da Nisha ba laifi yana kiranta suna Dan hira amma ba sosai ahaka dai har suka Dan shaku tun bayan dawowar su mahbeer daga Dubai su ghaisha da ummi suka shiga ma zee gyaran jiki na uban mamaki cikinta da waje gyarata suke dan sun b sayo kayan gyaran amare iri iri magani kala kala nasha sai banka mata suke da murjeta da turaruka iri iri yanzu ko parlo sun hanata zama Dan ko mahbeer ghaisha ta hanashi ganinta Dan so take zee ranar auranta ta fito matakar tauraruwa cikinta da bai dinta Dan jinta take tamkar ita ta haifeta ba surukaba zee amugun takure suke daga ita har Sardauna cikin dubara Sardauna da yaje gun Nisha ya amshi wayarta ya dauki number zee baby ya kirata ta gane shine amma saboda yan iskan suna kanta ta fitsareshi tace idan yasake kiranta sai ta hadashi da mahbeer haushi yasa ya tsinke kiran bai sake kiranta ba tayi kukanta har tagaji sai Akan dining suke haduwa idanunta kade ake gani cikin katon hijab take fitowa harda niqab aikin ghaisha ne wanan canma bangaran Nisha umma ba karamun gyara take mataba ciki da bai bayan zauwasu da satine aka kai kayan Nisha akwatina 12 shake da kaya iri iri masu tsada nagani na fada Wanda ya burge kowa Nisha ji take tafi kowa, sa’a aduniya yan makarantarsu Nisha ma sun zuzuta kanyanta sosai da mijinta na tserema sa’a haka zee baby duk iri dayane aka musu ita da Nisha zee sosai komai na kayanta ya burgeta yada taga mahbeer ya mata taji dadi sosai dangi kowa ya yana yabo ummi Raiyan har kukan farin ciki tayi aboye bangaran Aunty amarya Abu ya lalace mata Dan ajiyane taje gidan boka kafi maduba ta iske babban bala’i kafi madubi ya kumbura ya tsage gida biyu wani irin ruwa baki da manya tsotsotsi na fitowa jikinsa ai wani irin ihune ta Saki ta fita aguje tana so she so she kurajen jikinta sunyi budur budur duk inda ta Sosa sai ruwa wani baki ya bultso mai wari haka tabi titi tana gudu tsautsayi wata mota saman titi ta bugeta take ta samu karaya uku direban ya gudu bai tsayaba saida takusa wuni gefen titi ayashe ta suma daket aka samu wasu maga Allah suka dauketa sukayi hospital da ita rayuwa kenan Asiya ma kawarta aranar mijinta ya mata Saki uku da Dan banza duka saida ya karya mata kafa da hannu ya janyota kofar gida ya rufo kofar haka yara suke taruwa akanta suna mata ihu daket tasamu wani Dan shaye shaye ya kirawo mata adedeta ya cicibeta sukayi gidansu dagacan sukayi hospital,

✨✨✨✨✨✨

yau ya rage saura kwana uku daurin aure An shiraya ma Nisha dakinta tsafa a Narkeken agidan Dr Sardauna Wanda ya hadu tamkar gidan turawa Wanda yake unguwar, barhim estate kitchen dinta kadai abun kallone, ginda ya hadu iya haduwa haka dakin Dr Sardauna da Nisha, ya hadu Dan shima, komai sabo ya zuba abangaran sama da, kasa, Dan kayansa sunfi na Nisha tsada shi komai NASA kirar Italia ne yazuba sama da k’asa duk inda yayi sha’awa zai kwanta sab’anin Nisha kasa take wlh idan kashiga gidan kace bazaka fitaba yada, zee baby taji Family su na yabon irin yada gidan Nisha ya tsaru har kuka tayi abarta taje ghaisha ta hana itama nata gidan akayo video aka kawo mata saboda kusan komai iri dayane sai ban bance ban bance saboda gidajan ajere suke iri daya ne saide kowa da yanayin gininsa amma gaskiya gidan Sardauna yafi haduwa nesa ba kusaba shi harda Swimming pool tafkeke da rumfar shakatawa gashi gidan makeken na akwai fili rumfar ajiye motocima kadai ba karamabace wata ga ko ina shifkokine franni gwanin shawa zee ganin yada gidansu ya tsaru da mahbeer sai taji aranta na su Nisha baikai nasuba ni ko nace zee da kinga gidan Nisha bazaki hadashi da nakiba wlh idan kaga yada zee baby ta dawo sai tabaka sha’awa tayi mugun kyau taji gyara cikin da waje ko inanta sheki yakeyi saide maganin da suke bata ya adabeta koda yaushe zuba takeyi har wani kaikayi gabanta yake da nonota shiyasa kwana biyu take azumi ga tunanin rashin jinta jikin Sardauna ya dameta sama da kwana ashirin basu rumgumi junaba basusha yawu ba duk acikin mugun hali suke Sardauna yafita damuwa danma kwana biyu suna waya Dan ya kasa daurewa bayan ta masa rashin kunya da ya huce ya kirata to wannan Karon bata masaba sosai suke shan hira sai sukai kusan Asubah tayi ta zuba masa shagwaba amatsayin yayanta shikuwa ya biye mata to shima abinda yasa kenan tunaninta ya Dan rage masa suna chatt da juna gamuwace basuyi ko sun hadu a parlo idanuta kadai ake gani Nisha ma ta hadu ba karya Sardauna ma saida ya yaba mata tayi ta jin dadi Dan ba laifi yana kula da ita tunda yasan kaddarasa, ce auranta ba mashakurah ba mahbeer ji yake kamar ya, maido yau auransu Dan ya kasance da, zee Dan yau yakai sati yana azumi shakuwarsu kuwa tana nan ghaisha ta Dan barshi suna hira amma zee ba’a, ganin kominta sai idanunta ummi abin. Namata dadi sosai shirye shirye ya kankama saura kwana uku daurin aure anko masu tsada wajan kala hudu akayi su zee anyi dinkuna na kece raini abin sai Wanda ya gani abokin mijin Salma kanwar Nisha ne ya tsatsara musu dinkuna masu uban tsada haka bangaran mahbeer da Sardauna ma sunyi dinkuna na kece reni tare da su Ahmed da bandar da Hadeem kai wannan aure saide muce Allah kaimu lafiya gaskiya akwai shagali babba, Dan baki har sun fara zowa daga niger

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button