Zee Baby Book 1 Page 31

*************************************
*Bayan kwana uku*
Yau take juma’a To fah yau take sallah ga angwaye da amare yau take ranar daurin aure Wanda za’a daurasa bayan sallahr juma’a wlh fadar irin taron da yake cikin wannan gida to bata lokacine bikine fa yau ake na kece reni wlh idan kama zee kallo daya bazakaso ka dauke idanunka akantaba ghaisha da ummi sun yi mata uban gyara da shiri kanwar mijin maijidda yaya Sardauna ce ta cancada mata kunshi da kitson wlh fadin irin kyawun zee bazai faduba gashi ta saki jikinta tabar tunanin Sardauna tun washe garin ranar tayi watsi dashi ta kashe wayarta, ta maida hankali kan abunda yake gabanta kowa yaga kunshin zee da kitsonta sai ya yaba mata mahabeer da yagani saida ya rike hannuta yayi ta lasar kunshin tana masa dariya bangaran nisha ma ta hadu ba karya itako kanwarta Salma ta mata saboda itama gwanace wajan kitos da kunshi yau bakin Nisha baya rufuwa sai washe shi takeyi dan wani ubansu Dinner ne aka shirya karfe biyar za’a tafi gidansu Nisha fah shima cike yake suna sai kidan kwaryar akeyi Nisha daga cikin sai rawa take ita da kawayanta suna ihu sai zuga nisha suke saboda tayi mutikar yin kyau material din ya amsheta gidan Abdulmutallab yau babu masayar haki shagali fah ake sosai harda masu kidan kwaraya sai casu akeyi ciki na kutsa domin samo labari ghaisha na hango cikin wata uwar shadda gizna blue color sai kai komo takeyi bedroom naga ta nufa tundaga kofa nake jiyo ihu zee na hango tsakiyar su hafeeza dan tayi gayar kawayansu na makaranta ga, zainab itama da kawayanta amma sunada aure zee ce cikin wani dankareren material ruwan toka kanta ba dankwali an mata meke-up ta zuba sinare ajikinta kamar bad a kudiba aka saya wuya da hannu da yatsotsinta tilar hancinta da kasan lebanta duk ta sauya musu zinare wlh idan kaganta zaka zaji babu ta biyunta akyau kidane ke tashi sai cashewa suke maryama matar Nuhu ce tsaya tana koya musu irin rawar da za’ayi gun dinner zee sai dariya takeyi haka ghaisha ta shigo ai maryama kamar ta nutse a k’asa zee dariya take harda rike ciki “Aunty wlh kinban dariya ghaisha ta girgiza kai “maryama zo dama ke nake nema idan kin gama koya musu rawar maijidda tayi dariya “ai aunty muna hanaki kikaki sum sum ta fice zee tace”ummina ina ummi dariya ghaisha tayi ” gatacan gun yan kidan kwarya tana dauka awaya dariya zee tayi ghaisha ta fice zainab tace”wow matar yaya wlh ina tsoron daga gun dinner ya wuce dake Brahim estate dariya sukayi ta hararesu ta Mike tana rawa cikin wani shegen Salo da iya taku dan tana mugun son wakar gwanja mata ku taka rawar ganin ido mata kununa farin ciki dariya suke mata itako ko ajikinta dan tanada damuwa dannewa ne takeyi ta wayance dan batasan takamemen damuwarta ba bangaran nisha ma abun ba’a cewa komai itama sunacan suna cashewa ko gajiya rawa batayi da kawayenta abin ya rabu abiyu wasu gidan Umma hauwa wasu gidan ghaisha haka dangi aka rabu ana hidima ko wane gida raguna da saniya aka yanka sai girke girke ake zee Ana hanata saida ta saci jiki ta fito gun yan kidan kwarya ghaisha ce da gudu tazo ta janyeta su hafeeza da intisar ‘ya’yan kawu Saminu da su haulat sai casu suke zainab ma da tsohon cikinta sai takawa take ummi Raiyan na musu barin kudi tana dariya
Da misalin karfe daya na hango Sardauna da tawagar abokaninsa Wata d’anyar Shadda gizna ce yasaka milk color wacce tsayawa fadan kudinta bata lokacine wani irin mugun kyaune yayi saide fuskarsa ba walwala Mahabeer ko sai washe baki yake Shaddarsu iri dayace da Sardauna su Ahmed anci uwar kwalliya kace shine angon bandar ma haka Hadeem ma haka yakub ma haka da Najib kanen anguna kai da sauransu wlh kana ganinsu kasan nera tayi kuka bikin kuma na manyan yarane ba karya Sardauna ya zama tamakar tauraro cikinsu sai surutu sukeyi sigarinsa ya kunna ya sha iya shansa Ahmed na masa tsiya wani shegen kallo Sardauna ya watsa masa ya daga masa gira nuhu ne ya ISO yana dariya “to ku tashi muje masallaci angwaye bayan sallah juma’a acan masallacin za’a d’aura auran murmushi Sardauna yayi ya Mike ya rumgume nuhu “Dr kako ji jikinka zafi rau yawa wuta fa amma dan dauriya kake zaune “wlh Babban yaya kaban dariya saikace mace dagajin zazzabi sai na nemi magani mahabeer ya Mike ya rumgume Sardauna yaji zafin “babban yaya wlh kusan kwana nawa na lura bajin dadin jikinsa ga yawan tari dayake nayi ta tambayarsa amma yacemun lafiyarsa lau jikinsa Sardauna ya fizge yana turo baki dariya mahabeer yayi su Ahmed dariya suka dan suna mamakin shagwabar Sardauna gabaki dayansu suka nufi gun motocin da aka tanada dan zuwa daurin aure abokan aikin Sardauna mota guda sukazo dan ya fada musu bayan sallahr juma’a za’a d’aura aure motocine sama da guda ashirin harda su Daddy da tawagarsa suka nufi masallacin kofar sauro acan suka iske tawagar Bashir mahafin Nisha koda jama’a sukaji sanarwa idan angma sallah akwai daurin aure babu Wanda ya gusa dan yau duk Wanda yaga tawagar Daddy sai ta burgeshi Daddy yaji dadin zuwan mai girma gwamna da sarki dan dakanshi ya kaimusu katin daurin aure bayan anyi sallah an gama Bashir yaba Abdulmutallab Auran Aisha ga Faisal Mamuda yayan Bashir shine alwali Kawu saminu Alwalin Faisal aka d’aura auren Faisal da Aisha kan sadaki nera dubu dari mamudu ya fito da kudin ya nunama jama’a kowa ana gamawa kawu Saminu ya nemi auran Auran Zainab Daddy ya bashi ya ana aka d’aura auran zainab da mahabeer akan sadaki nera dubu dari da hamsin Nuhu ya fito da sadakin ya nuna mai girma gwamna sosai abun yabashi shawa haka sarki ya bukaci angwaye suzo su gaisa Sardauna da mahabeer cikin girmamawa, suka isa gunsa suka zubo suna kwasar gaisuwa albarka ya samusa haka gwamna sai rabon goro ake da halawa harda kudi jama’a sai son barka sukeyi bayan tafiya gwamna da sarki Daddy ya fito da tawagarsa mahabeer baki har kunne suka nufi motocinsu Sardauna ya dafa morfin mota, zai shiga gidan baya ya yanke jiki ya fadi asume jini na fita daga bakinsa da hancinsa agigice gabaki da jama’ar sukayi kansa Daddy har har tuntube yake Nuhu kafin ya isa mahabeer ya rigashi ya fada, saman Sardauna hankalinsa atashe arikice yake girgizashi “Dr Dan Allah katashi me ya sameka ranar farin ciki………..✍????
[ad_2]