Hausa Novels

Zee Baby Book 1 Page 41

ya bi sahu aka sallahci Dan uwansa hawaye na zuba a idanunsa Ana gamawa akayi masa Addu’ aka daukesa sai gidansa na gaskiya wlh fadin irin jama’ar da mahbeer ya samu bazai faduba saide nace Allah yayi masa gafara kawai haka suka kaishi gidansa na gaskiya suka binneshi jama’a kowa yabon halinsa yakeyi yan gun aikinsu ma dayawa sunyi kuka rufe kamfanin akayi akace sai bayan sadakar ukku direban da bikesu tamkar zaiyi hauka kuka yake yana cewa yakashe mutum wuni jama’a sukayi ana shiga ana fita har bayan la’asar har yanzu Sardauna bai sama cikinsa koda ruwaba Nuhu ne ya fahimci hakan daket ya lallabashi ya kawo masa tea ya kurba ciki gun mata ma hakane babu Wanda ya iya sama cikinsa wani Abu har dare bayan sallah isha’i Daddy yace Sardauna ya daure yaje ya dubo zainaba ko da sauran ranta Dole yasa Najib ya tukasa suka tafi yayi mata, dube dube babu wani alamun motsi jikinta haka suka dawo Sardauna sai zubar da hawaye yake Allah kadai yasan halin da yake ciki, Nisha ma bata sukuni abun ya mata yawa tafe kawai take hauwa tana dan kula da ita tsakiyar dare kowa ya nemi guri ya kwanta Sardauna yana saman darduma yana sallah yana kuka saida yaji kafafunsa basu daukansa ya hakura, ya zauna yana ma dan uwansa da zee Addu’a yana kuka, da yagaji nan ya bingire ya kwanta har barawon bacci ya daukesa saboda jiya babu Wanda ya rumtsa Asubah ta gari

**********************************
*Bayan sati guda*

Yau mahbeer yacika sati guda da mutuwa wlh har yanzu idan ka kalli yan gidansu sai ka tausaya musu saboda sunsa mutuwar aransu saide Dole suka fara hakura tunda sunsan bazai dawoba yan niger motoci biyu sukazo bayan sadakar uku suka koma amma minata da tuwasai sunce bazasu ba sai bayan arba’in Sardauna saida akayi sadakar ukku daket ghaisha ta matsa masa, suka koma gidansu saide kullum idan sunzo sai dare suke komawa, yarame sai fari da ya kara ya tara k’asumba Nisha ma tarame dan mutuwar ta shigeta dadinta daya har yau Sardauna bai kusancetaba bangaran zee baby har yau bata farkaba tsawon sati daya hankalinsu ba karamun tashi yayi ba ummi har tagaji da kuka tanaso tace abata ita sutafi saudiya amma ta kasa ganin yada suke nuna damuwarsu akan zainab gashi suna tatalin ummin da kwantar mata hankali duk da suna cikin tashin hankalin mutuwa akullum Sardauna so uku yake zuwa dubo zee tanada rai lokacin farkowarta ne baiba

da misalin karfe biyar na yamma Sardauna na zaune cikin parlon yana kallon tashar Sunnah TV zauwarsu Kenan daga gidansu”Nisha ki kawo mun mana” gani fah yi hakuri Rabia ce take aiki agurin na nuna mata wani abune zama tayi kusansa ta kafa masa cup glass d’in abaki ya kurba yana yamutsa fuska jikinsa ta kwanto” my Dr yi hakuri kasha please kaifa kace na hadoma coffee mai dadi muyi hakuri babu yada zamuyi da hukuncin Allah amsa ya rikayi tana bashi abaki yanasha idanunta sun ciko da hawaye Sardauna ko tunda ta rumgumeshi yaji yana bukatar kusantarta dan satin da yayi tashin hankaline ya kauda masa sha’awarsa amma yanzuma sam bazai wani iya tabuka komaiba bashida kwanciyar hankali mutikar baiga zee baby ta farka ba bayan ya shanye coffeen ya rumgumeta gam yana sabke ajiyar zuciya”Nisha kibar kukan mu amshi kaddara da hannu biyu kara shigewa jikinsa tayi tana buga bayansa itama

alamar lallashi wayar Sardauna ta dauki ringing idanunsa ya bude ya kalli screen d’in wayar yaga Dr Nabeel da sauri cikin rawar jiki ya dauki wayar gabansa na faduwa yayi picking ya kara, akunnensa” hello Dr meya faru? ” Dr Sardauna kayi kokari kazo yanzu na’urorin jikin zainaba Faisal Hashim Almahadee sun dauki ruri alamar ta farka ai bai tsaya, sauraren karshen zancanba ya janye Nisha ya zaunar da ita”Nisha natafi hospital sai nadawo key din mota ya dauka, aguje ya fice Nisha hankalinta atashe tana Addu’ar Allah yasa dear dinta ce ta tashi Sardauna yana shiga mota ya figeta da karfin gaske kafin ya ISO mai gadi ya bude masa get ya fice aguje wani irin gudu yakeyi Allah ne ya kawoshi hospital lafiya ko parking bai gama yiba ya bude ya fice aguje ya yashige direct d’akin da zee take mai cike da na’urori ya nufa har likitoci sunyi tsaye kanta, yana zuwa suka matsa gefe kowa ya fice dubata ya fara ko minti uku baiba ta fara motsi tana fizge fizge cikin farin ciki Sardauna ya riketa gam yana kuka “Zainab ina mutikar farin ciki da farkawarki kanwata yau tsawon sati gudu banaci bana sha saboda rashin Abu biyu masu mahimmanci arayuwa sosai yake kukan farin ciki ya matseta jikinsa har ta daina fizge fizgen amma idanunta arufe hawaye yana kwaranya saman fuskarsa ya zuba mata manyan idanunsa cike da tausayinta ya zauna ya cire mata na’ururin ya rumgumeta gam ya kirata”zainab tashi bude idanunki kinji ahankali ta bude idanunta ta sabkesu akan Sardauna tayi masa kuri da idanu murmushi ya sakar mata hawaye fuskarsa suna zuba saman fuskarta ” zainab sannu ya jikinki da idanu ta kafesa ko giftawa batayi “my kanwas bazaki mun maganaba ya fada yana langwabe kai yana sakar mata murmushi ga hawaye na kwaranya daga idanunsa duk dan ya saka mata kwarin gwiwa murmushi ta sakar masa ta dora hannuta saman fuskarsa ta shafo hawayen ta langwabar da kai ahankali kamar mai koyon magana tace” my kanwas bazaki mun maganaba ta fada tana sakin murmushi kara rumgumeta yayi hancinta yaja” banson raini ni sa’an kine murmushi ta saki ta beka hannuta saman dogon hancinsa ta ja tace” banson raini ni sa’ankine idanu ya zaro” my kanwas ni ko itama tazaro manyan idanunta ta tsaresa da kallo tace “my kanwas niko gaban Sardauna ne yayi wani irin faduwa da Sauri ya janyeta daga jikinsa ya Mike tsaye ya kwantar da ita ya jona mata wata na’ura akanta ya nufi gun wata na’ura da gudu dan ya kunnata ya binciki zee tashi tayi ta fashe da kuka tana kokarin cire na’urorin jikinta da ya jona mata dan tabishi arikice ya nufo gunta “zainab tsaya ganinan………….. ✍????

 

 

????????Ladingo Yar ilu

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button